Showing 18001 words to 21000 words out of 225640 words

Chapter 7 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

kawai na karbo ma juyo na dawo inda nurse din suke na mika musu sai suka nuna min dakin likita.

“Can za ki shiga ki kai”

Na doshi dakin da sauri na tura na shiga ina sallama can ciki saboda kuka.

“Ga hoton”

Na mika masa sai ya karba yana ta turanci da wani mutumen dake zaune a daya daga cikin visitors chairs, likita yai rubutu cikin wata farar takarda ya miko min.

“Idan ki siyo ka bawa nurse su saka mata”

Na karba da sauri sannan na fice duk abunda nake Lukman na biye da ni a baya a duk inda na saka kafata dana dauke sai ya saka tasa. A nan ma sai da na tambaya aka nuna min pharmacy sannan na kai takadar su ma suka ce sai na je wani guri kusa da inda ake bata kati na biya kudin maganin da suka rubuta min a jikin takardar, haka na juyo cike da jin haushi irin tsarin na nu na wahalar da mai rai na je na mika takardar sai ya fada min cewar zan ba shi dubu biyar da dari uku da naira arba'in, a nan ma sai da nai ta roko sannan ya karbi jikakkun kudin ya bani yan canjina sai na koma can na kaiwa mai pharmacy ya bani amfanin da ledar sakawa. Kamar yadda likita ya fada min haka na mikawa nurses din sai suka hau dora mata ruwan suna saka maganin a ciki sukai nata allurai sannan suka dora ragowar maganin akan wani dan karamin abu mai kamar bedside drawer, sai ta sauke wani irin ajiyar zuciya bachi yai gaba da ita. Ni kuma na koma dakin likitan Lukman na biye da ni a baya na tura na shiga, har yanzu magana yake ta yi da mutuman dazun.

“Na ba su sun saka mata”

Sai ya dago ya kalleni yana dago hoton ya ce.

“Ba dafin maciji ke damun matar nan ba, gurin da aka cire mata koda ne ke mata zafi maybe ayi aikin yadda ya kamata ba”

Ji nai kamar ban ji abunda ya fada daidai ba, har sai da na sake tambaya cike da tantamar.

“Ban gane ba koda kuma?”

“Yes an yi mata tiyatar koda ko?”

“Aa ba ayi ba”

“Gashi nan hoto na nuna matar nan bata da koda ďaya, kuma gurin da aka cire kodar ne ke mata ciwo”

“Ba a mata tiyatar ko da ba likita, maciji ne kawai ya tsareta aka cire dafin”

“Ba ama cizon maciji tiyata allura kawai ake, wannan tiyatar koda ce aka cire mata”

Ji nai kamar ba a duniyar nan na ke ba, sama na ke kasa na ke sai na kasa tantancewa yawu suka cika min baki daman can ido suna ta aikinsu na hawaye. Kar dai ace likitan nn ya da taimake mu kodarta ya cire? Kar dai duk taimakon da yai mana na siyen kodarta ne?

“Amman dan kara tabbatarwa ki je ki yi wannan babban hoton”

Ya miko min wata takardar. Da na cira kafar na je na karbo sai na ji kamar an rike ni kafafuwan suka lauye gurin daya suka min majiyar kamar wacce ta shekara a tsaye.

“Wane likita ne yai mata tiyatar yace za a cire dafin maciji?”

“Wa... Ni... ”

Na amsawa likitan maganar na fito min a rarrabe.

“Ya cuce ku ne kawai ko kuma an gada kai da shi an cuce ku, amman dafin maciji ai ba a masa tiyata”

Daker na karasa na karbi takadar ya juyo kamar kazar da kwai ya fashewa na fito daga dakin likitan ina hawayen da ban ta ina ake turo min su ba. Ban san nawa hoton zai ci ba amman tun da ya ce babban hoto nasan sai ya ci fiye da dubu da wani abu da wacan karamin hoton ya ci, gashi sauran kudin da ke hannuna ba su kai ma dubu uku ba. Da wowa nai kusa da ita na zauna a kujerar roba da ke gabanta, ta bude baki tana sheda da nan da alama numfashin da ke fita daga hancinta baya isarta. Wani irin tausayinta ne ya lullube ni ina ta kallon fuskarta kamar yau na fara ganinta, taya zan iya fadawa Nana ya cire mata koda? Taya ma zata rayu ba koda? A tunani idan mutum ya rasa wani abu daga sassan jikinsa mutuwa zai yi.

“Shikenan Nana shikenan”

Na fada ina jan Lukman na rumgume, sai na saka kaina cikin jikakkar rigarsa na fashe da kuka marar sauti, ganin haka ba yasa shi ma ya fashe da kuka yana ta kallonta.





ALIYU POV.

Babbar asibiti ce kuma kwararriyar a duk fadin duniya, tun da aka ce za a mata dashen a can a cire dayar wacce ta fara lalacewa sai ya hankalinsa ya kwanta domin manyan likitocin ne za su mata aiki kuma sun san kan aikinsu. Within week din da suka je London aka yi mata aikin cikin iyawar Allah da ikonsa aka yi nasarar cire wacan kodar aka dasa mata wata. A can aka cigaba da kula da ita har na tsawon wata daya a ciki wata na biyu ne suka sallamota ta dawo gida Nigeria tare da mijinta da kuma mahaifiyarta wacce sukai tafiyar tare.
A nan gidan ma kusan kullum sai Doc Asim da wani likitan Doc Jonah sun zo dubata, sosai ta so su tare a Abuja tun dawowarsu daman a can suke zama, amman Aliyu ya ki saboda yana son ya koma Abuja da zama a halin da matarsa take bukatar lokacinsa, ya san duk yadda ya ke son bata kulawa idan har suka je Abuja dole ne sai ya leka office amma a nan yana tare da ita tun safe har dare.
At early morning ya farka yau kamar yadda ya sabawa kansa tun da suka dawo gida. Da kansa ya shiga kitchen ya saffara mata abunda zata ci idan ta farka sannan ya dawo falo ya zauna yana duba wasu abubuwan a laptop dinsa.

“Aliyu...”

Ta kwala masa kira daga dakin da take kwance duk da tasan ba zai amsa ba amman ta san zai ji ta, daman can baya amsa kira idan aka kira sunansa, sai dai idan yana kusa da kai ya kalleka ko kuma ya taso ya zo idan shine a kasa da kai, idan kuma kai ne a kasa da shi sai dai ka je ka same shi. Laptop din ya aje ya mike tsaye ya nufi upstairs fuskarsa ba yabo ba fallasa.
Zaune ya sameta saman gadon ta dukunkune da bargo ta wani bata fuska kamar karamar yarinya.

“Sanyi na ke ji waya ce ka kunna ac”

Sai ya kai hannu ya kashe ac ya hauro saman gadon ya yaye blanket din da ta lulluba da shi yai kissing fuskarta.

“Ta so muje ki karya kin san sun ce ki rika karyawa ba sai kin ji yunwa ba”

“Me ka dafa min”

“Doya da madara ka san kina so ai”

“Ba ka iya ba fa”

“I try ”

Ya fada, yadda yake amsa maganar sai na rantse da Allah ba a bakinsa take fitowa ba, domin babu wata alama da ke nuna cewar magana yake. Saukowa yai da ita saman gadon ya nufi bandaki da ita da kansa ya wanke mata baki as usual sannan ya fito tare da ita.

“Gidan nan duk yai datti kuma bathroom din ma yai wata ba a wanke ba ni kyamar Shiga ma na ke”

Ta fada masa a daidai saitin kunnensa ba ce da ita komai ba ya ja suka nufi hanyar fita daga bedroom din.

“Ka ji?”

Nan ma be ce komai ba har suka sauko downstairs, daman can haka yake kamar wanda maganar take masa wahala, kujera yaja mata ta zauna akan dinning.

“Ba ka ce komai ba”

“Za mu samu wanda zai rika mana shara da gyara gida”

Ya fada sannan ya zauna ya shiga serving dinta, da kansa yake feeding dinta har ta koshi sannan ya zuba ma kansa ya ci.

“Yaushe za ka samo?”

Haka ta dinga tambayarsa amman be ce mata komai ba, har ya gama cin abincin ya tashi.

“Ni wannan miskilancin na ka damuna ya ke”

A dai-dai lokacin da zai stairs ta fadi haka, sai kawai ya juyo ya sakar mata murmushi gefen fuska ya juya ya haye sama.



________
An ciye kidney din wata an raya wata 😪
https://my.w.tt/PWohUhlPv9.

*Z A K I*

By Khadeeja Candy


9️⃣

A saman kujera na kwana a zaune ina ta kallon Nana tun ina kuka da hawaye har na koma ina ta rare kukan kawai babu hawaye. A kasan gurin Lukman ya kwana. Tun da asubar fari masu sharar asibiti suka tashe Lukman ni kuma suka ce na fita za su gyara gurin. Ba dan babu yadda xan yi ba da ba zan fita ba, domin ina jin kamar idan nai nisa da Nana mutuwa za tai ta barni.
A haka na fito ward din ina jin zuciyata babu dadi, Lukman kuma na ta murja ido alamar bachin be isheshi, kai tsaye gida na nufa kai tsaye domin samawa Nana abunda zata ci da ita da Lukman, wannan karon da kafa na iso kasancewar daga unguwar Clapperto zuwa uduth babu wani tazara sosai ga talaka irina wanda ya saba da tafiyar kasa. Ina janye da hannun Lukman har muka iso kangon gidan. Tsaye nai ina ta tunani ta inda zan fara, rashin lafiyar Nana ta tsaya min a rai har na so min kamar bana da wani sauran kuzari.

“Ataa ya me za mu yi?”

Maganar Lukman ce tasa na dawo daga dogon tunanin da nake rakiyar zuciyata da shi.

“Koko zan siya maka kai da Nana”

“Ni ba zan sha ba”

Ya fada yana mitsintsika ido.

“Saboda me? Ko waina kake so?”

“Aa bana son komai Nana na ke son ta samu lafiya, Ataa ai zata tashi ko? Zata ji sauki ko? Na yi mafarki ta samu sauki tana min magana”

Wani irin tausayinsa da na kaina nd ya lullube ni a lokaci daya, duk yadda na ke shakuwa da Nana nasan Lukman ya fini shakuwa da ita domin shi karamin yaro ne, kuma kusan kullum tare suke zuwa bara tsabanin ni da wani lokacin na ke zuwa wani gurin dabam.

“Zata ji sauki idan kana cin abinci,Nana tana son ta ganka kana cin abinci”

“Haka ta fada miki? Da na yi kwana ta farka?”

Na gyada masa ina hawaye, sannan na saki hannunsa na shiga neman tsohuwar butarmu kuma basasshiya cikin duhun asuba, na yi alwala na mikawa Lukman ragowar ruwan shi ma yai alwala, wani masallaci na bi na gabatar da sallah magariba bata, na yi ma Nana addu'ar neman lafiya, sai kuma na rasa wacce za yi ma Doc Asim, bana son nayi masa mummunar addu'a ya zama ba gaskiya ba ne, domin har yanzu zuciyata tana min kwankwanton cewar ba gaskiya ba ne idan ma ya cire wane amfani zai yi da ita wane amfani zata masa? Mi ma zai yi da ita? Wata kila kuma siyarwa zai gi idan ana siya, waya sani ko wani ya ce ya cire? Amman kuma wa Nana ta sani da har zai sa ayimata haka? Ko shiyasa aka Anty Shukura ta ce mu bar asibitin idan ina son mahaifiyata araye? Shiyasa ta rika girgiza min kai a lokacin da zan saka hannu a takardar nan? Gaskiya ne idan har ba cire mata koda yai ba, mi zai sa yai ta taimakonku haka da yawa magani ma kadai ya kashe mata kudi mai yawa, abinci ma shi yake siya mana, anya idan ba wani abun zai mana taimako haka mai yawa? Haka dai zuciyata tai ta min wasiwasin gaskiya da kuma akasinta a lokaci daya.
Fitowa nai na tsinci kwanon mu a inda mugayen mutanen suka harba mana kayan cin abinci da kafa na wanke na bawa Lukman yaje ya karbo mana koko, bayan ya dawo na sake aikensa ya siyo ma Nana waina mai yaji dan nasan ita ce favorite dinta.
Kadan na kur6a kokon shi ma dan ina jin kamar bana da kuzari ne wai ko zan dan samu karin karfi, na mikawa Lukman sauran kokon ya shanye ba ko suga. Sauran ragowar kudin na fito da su ina kargawa da na hada sai na ga ba su kai ma dubu uku ba gaba daya dubu biyu ne da dari hudu da naira talatin, haka na hada kudin guri daya, na kurawa Lukman ido ina ta kallonsa yana shan koko duk da kasancewar hankalina a gurinsa ya ke ba. Bayan ya gama na dauki wainar da ragowar canjin mu doshi asibitin ni da shi ina tafiya ina jin kamar ana turani gabana sai faduwa yake. Lokacin da muka isa asibitin sai masu gadin ward din suka hana mu shiga, wai ba a zuwa ganin marar lafiya sai da yamma haka dokar asibitin ta ke.

“Ba ganinta na zo ba, abinci na kawo mata kuma ni nake jinyar ta”

Na fada cikin muryarta ta gajiyayyu mutane marasa galihu.

“To bari likitoci su fito sai ki shiga”

Na koma gefe na tsaya kamar yadda na tararda wasu mutanen a tsaye, ina nan zaman jiran likitonci su fito wata Nurse ta fito daga dakin tana tambayar mai jinyar Asma'u Ummaru.

“Ga ni nan”

Na fada da dan kuzarina.

“Shigo ciki ana nemanki”

Na bi bayanta kamar yadda ta umarta Lukman kuma ya biyo sai securiting ya rike shi a nan ya fasa masa ihu kamar zai tashi kunnuwansa a dole ya sake shi ya biyo bayana.
Kusan likito ci hudu ne tsaye akanta ta farka har sun tashe ta ya dan jingina da gadon tana kallonsu bakinta ya bushe sosai har fatar bakinta ta fara kankara kamar wace ta shekara ba ta sha ruwa ba.

“Ke kike jinyarta?”

Daya daga cikin likitocin ya tmabaya yana kallona, wata kila gani yake kamar na yi karama ko kuma kyauwo na yake kallo oho.

“Eh ni ce wani abun ne?”

“Babu wani babba sai ke?”

“Bata da kowa sai ni, ni ma kuma ba ni da kowa sai ita”

“Ina hoton da na rubuta miki jiya kin yi?”

Sai da yai maganar na iya gane daya daga cikin likitocin wanda ya karbe mu ne jiya da muka zo.

“Ban yi ba, sai yau zan je na yi”

“To kije ki yi, yana da kyau a kara tabbatarwa, abu na biyu kuma karki kuskura bata komai ta ci drip din da aka saka mata ba zai bari ta ji yunwa ba, ba za ta ci komai ba sai an yi mata hoton an kara tabbatarwa”

“To na gode”

Na fada cike da sanyin murya, sannan dayan ya miko min wata farar takarda.

“A siyo mata wadannan magungunnan”

“To”

Na fada bayan na karba, sannan na zauna a kujera ina hawaye, su kuma suka nufi wata marar lafiyar dake kusa da mu suna dubata.

“Sannu Nana”

Na fada ina jin kuka kamar zai kubuce min, sai tai murmushin karfin hali ta ce.

“Yauwa, Lukman”

Ta mika masa hannu sai yaje da sauri kusa da gadon ya tsaya yana share hawayen kukan da be gama ba har yanzu na rokewar da wacan securiting yai masa abun ka da mai tsoron mai uniform.

“Mi akai maki? Kin ci abinci”

“Na sha koko, wacan dan sandan ne ya rike ni wa ba zan shigo ba”

Ya fada yana hawan gadon ya zauna, sai ta kalleni.

“Ke kin ci abincin”

Kai kawai na iya gyada mata alamar na ci din, sannan na mike tsaye.

“Ina zaki je Ataa?”

Ta tambaya da yaren buzanci, ni kuma na bata amsa da hausa.

“Zuwa zan yi na tambaya kudin hoton da maganin na ji ko nawa ne”

“Kar ma kije tun da kin san ba kudi da mu ba”

“Ba ki sani ba ko kudin ba shi da yawa, kara dai na tambaya na ji, idan da yawa sosai sai mu hakura”

“To Allah yasa ba bu yawa, akwai ragowar kudi da yawa a hannu hannunki?”

“Eh akwai”

Duk wannan maganar da yaren buzanci mu kai sannan na mike tsaye na fita jiki babu kwari, sai da na tsaya bakin kofar na fadawa security cewar zan dawo kuma ni ce ta dazun mai jinyar marar lafiya gudun kar ya sake hana ni shiga idan na dawo. Wannan karon ban tambayi kowa ba na nufin gurin hoton sai suka rubuta min kudin hoton a jikin takardar dubu takwas da dari biyu wai babban hoto ba ne wanda za a ga duka sassan jikinta a jikin hoton. Sannan na doshi pharmacy na mika musu takardar suka duba suka rubuta min kudin maganin shi ma dubu biyar da yan kai, dukan ya tashi kusan dubu goma sha dubu ba dari uku, ji nai kamar na dora hannuna saman kai na kurma ihu, sai dai idan nai ihun wa zai taimake ni wa zai tausaya min har ya kawo min a gaji, a halin da na ke a yanzu ni kaina tsoron taimakon na ke duk wanda zai yi kare ni da zimmar taimako matukar ba ni na nema ba, na yana da wahala na iya amincewa da shi. Tafiya na ke kaina a kasa idona na zubar da ruwan hawaye, jin na ke kamar fuskata za ta taba kasa saboda maso min da tile din da nake takawa ake ina ganinsa kusa da ni.
Kallon da na ga mutane na min ne yasa na share hawayen na daga kaina sama har na iso ward din na shiga, yadda na bar Nana haka na sameta Lukman na kusa da ita tana ta mata firar mafarkin da yai.

“Kudin na da yawa ko?”

Ta fada tun kan ji ta ji domin yanayin fuskata ya nuna hakan.

“Su na da yawa amman za mu iya samu idan muka yi bara, sai na hada da wandanda suke hannuna”

“Ataa kudin da za muke samu a bara ba su da wani yawan da za mu iya siyen magani”

“Zan yi kokarin na samo su cikin sati biyu, ni da Lukman za mu yi In-Sha-Allah za mu samu kuma za ki samu lafiya Nana”

“Ko dai mu koma asibitin wacan likitan?”

“Aa ba sai mun koma ba, ba kuma za mu koma ba har a bada”

Na fada cike da zafin rai.

“Amman ya taimaka mana ai”

“Eh ya taimaka mana ya ceto ranki daga saran da maciji yai miki, sai dai yanzu tiyatar da yai miki duk ita ce ta ja mana wannan matsalar”

“Cewa sukai wani abu ya samu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login