Showing 57001 words to 60000 words out of 225640 words

Chapter 20 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

tsaki.

“Aliyu kana da matsala Wallahi, taya akai kai kaga tana kallon ka? Haka kawai za ka ce kar ta kalleka kai kuma ka kalleta?”

“How dare you zaka fada min wannan maganar sa'an ka ne ni?”

Aliyun ya fada yana mikewa tsaye cikin zafin rai kamar zai da ki Ya Muhseen. Ya Muhseen ya mike tsaye yana kara jan tsakin.

“Rayuwarku batai ba Wallahi, arziki ai ba hauka ba ne, shikenan dan tana talaka bata da gata kallon ma sai an shar'anta mata kalar da za tai?”

“Muhseen enough! Wai Aliyu ba yayanka ba ne kake fada masa wannan maganar?”

Mama Fulani ta fada tana mikewa tsaye tare da shiga tsakaninsu.

“Shikenan dan ya girmeni yayi ba daidai ba ba za ayi magana ba? Waye shi?”

“Amman ka san Aliyu ba ita ya hana kallonsa ba, ko su Maryam da Batulu da suke kannensa basa tsare shi da ido ko? Ina ruwanka da shi ne? Wai ku kullum kuka hadu a waje daya sai fada ya shiga tsakaninku? Kamar kare da Mage! Haba sai ka ce wasu abokan adawa”

Mama Fulani ta fada cikin yanayin da ke nuna damuwarta karara. Ya Muhseen be sake cewa komai ba ya watsawa Aliyu harara ya fice daga falon, sai da ya fice sannan Aliyu ya koma ya zauna sai ya maida idonsa a kaina, ni dai nai kasa da idona gudun kar Mama Fulani ta ce na yi laifi, amman idan ta shi ne bana tsoron duk abunda zai fada, lokaci zuwa lokaci idan na dago na sai na ga ni yake kallo, ka ji wani tsantsar zalinci amman ni ya ce ba zan kalleshi ba. A dago ta hudu da nai muka hada na watsa masa harara kadan sannan na maida idona kasa.

“Ke tashi ki fita bakar munafuka”

Mama Fulani ta fada min a tsawace tana watsa min harara, ba musu na tashi na fice daga falon, na koma garejen na zauna abuna ina ta jin zafin kalmar munafuka da Mama Fulani ta kira ni da ita. Zaune nai a gurin na rumgume hannayena ina turo baki kamar an min wani abun bayan wannan, ina jin motsin shigowar Ya Muhseen a garejin nai saurin gyara zamana.

“Pretty ta so muje part din Ammy”

Ya fada yana zuba duka hannayensa aljihu, ni kuma na mike tsaye na karasa inda yake ba tare da na san bakina yana nan a yadda na turo shi ba.

“Fushin ne har yanzu? Ki daina damuwa da lamarin Mama haka rayuwarta take, amman Aliyu idan yai miki ki rama”

“Idan na rama ai Mama Fulani fada za ta min, ko kuma shi ya dake ni”

“Ba zai dake ki ba, wai baya dukan mata sai maza, Aliyu ba shi da kirki ko kadan”

Ban sake cewa komai ba muka jero ni da shi muna tafiya har muka isa part din Ammy, Anty Humaira ce zaune ita da Inteesar suna playing wani gate da ke cikin plate da wani abu mulmulalle, kusa da Anty Humaira Ya Muhseen ya zauna ni kuma na zauna daga can gurin kofar shigowa falon ina kallonsu, Anty Humaira aka fara ci kamin aci Ya Muhseen abun gwanin sha'awa sai dariya na ke.

“Zo mu yi”

Ya Muhseen ya fada min yana kirana da hannu, sai dan bata lokaci ina jiran naji ko wata daga cikinsu zata ce ba za tai da ni ba, da ban ji komai ba na taso na karaso kusa da Inteesar na zauna aka so ma yi da ni, duk da ban iya komai ba amman Ya Muhseen ne ke fada min inda zan dora abun sai dai hakan be hana a ci ni ba, Inteesar ce kawai wance ba a ci ba sai dai ta ci wani.

“Yanzu kan a dora kudi idan an ci zan bada dan kunne na”

Inteesar ta fada tana aje dankunnen zinarin da ke kunnenta. Sai Ya Muhseen ya cire agogon hannunsa ya aje.

“Ni ma ga agogo na”

Anty Humaira kuma ta aje karamar wayarta.

“Ni ma na waya”

“Ke mi za ki saka?”

Sai nai shiru ina kallon Inteesar da tai min tambayar kuma ta tsare ni da ido tana kallona.

“Ita bulala biyar biyar za a mata idan an cita”

Ya Muhseen ya fada yana dariya nima dariyar nai na ce.

“Ban yarda ba, gaskiya ba ban yarda ba, idan an ci ni a saka ni aiki kawai”

“Wanki za ki min”

Inteesar ta fada Sai Humaira ta sa dariya tana fadin.

“Inteesar ke muguwa ce Wallahi”

Har Inteesar ta bude ba ki za tai magana sai na ga ta mike tsaye da sauri da kamar razana a fuskarta.

“Ya Aliyu”

Humaira ta kalli kofar da sauri sannan ta gyara zamanta, ni kan kallo daya nai masa na dauke kaina har ya karaso cikin falon ya zauna.

“Ya Aliyu sannu da zuwa”

Inteesar ta fada tana nufar inda yake ta zauna, sai ya mika hannu ya kama hannunta.

“Yauwa Intee, ina Ammy?”

“Tana dakinta”

A nan Humaira ta mika masa gaisuwarta sai yai banza da ita be ko kalli inda take ba, ya mike tsaye ya nufi bedroom dinsa Ammy yana rike da hannun Inteesar.

“To mi nai kuma? Na gaishe shi ya ki amsa min”

Anty Humaira ta fada tana kallon Ya Muhseen.

“Wacan dan iska kike damuwa da shi kamar ba ki san halinsa ba”

Ya Muhseen ya fada yana tashi daga kasan da yake zaune ya koma kusa da ni saman cushion ya zauna, a nan Anty Humaira ta mike tsaye ta nufi daya daga cikin dakunnan da suke gefen na Ammy. Ni kuma na taso na baro part din na nufi garden kusa da fanfo na zauna na kunna fanfon na tara kafafuna ina ta wankewa ina wasa da ruwan. Kamshin turaren da na ji ne yasa ni saurin juyowa sai ganinshi nai tsaye nesa da ni yana ta kallona da alama wata maganar yake son min ya kasa ko kuma so yake ya ce na kalleshi oho. Juyowa nai na cigaba da abunda na ke, sai jin kamshin turaren nai ya karu hakan ya tabbatar min kara matsowa yai kusa da ni.

“Ina Mahaifiyarki? Tana raye?”

Kamar saukar aradu haka na ji tambayarsa ta sauka a kaina ta shiga kunnena. Juyowa nai na mike tsaye na daga kaina ina kallonsa domin ya Ya Muhseen tsayi da dan fadi, balle kuma ni da ba wani tsawo ne da ni sosai ba.

“Idan tana raye kasheta za kai? Saboda asirinku ya rufu ko? Karka da mu ba sai ya sake zalintar mu ba, babu wanda zai sake jin wannan sirrin, ba zan fadawa kowa ba, sai dai akwai ranar da komai baya boyuwa ko da na yi kokarin yin hakan”

Na fada masa sannan na ratsa gefensa ban wuce sai ya juyo fuska a hade ya ce.

“Ba ni na saka aka cire mata koda ba, biyansa nai”

Juyowa nai na kalleshi.

“Shi haka ya fada lokacin da na kai shi gurin yan sanda, sai ya juyar da abun a kaina aka kulleni a cell har na tsawon kwana hudu, ya bar ni da wahala babu wani abun da za ku fada min da zai saka na yarda da ku, cuta kun riga kun cuce ni kuma babu abunda zan yi iya yi a kai, kun cire kodar mahaifiyata kun raya wata, sanadin cire kodar da kukai na rasa kanena, aikin da na ke a nan saboda ita nake yi saboda na samu lafiya, na rufa min asiri ka taimake ni karka saka nai abunda zai saka Mama Fulani ta koreni a gidan nan, zalinci ne kun riga kun min, kuma na maka alkawarin ba zan fadawa ko na gidan nan ba, ba zan tona maka asiri ba, domin tona maka asiri daidai yake da bakin aikina a gidan nan, idan kuma na bar nan ban san ya rayuwata zata kasance ba”

Na karasa hawaye na bin fuskata. Sannan na juya na fice daga garden din hawaye na bin fuskata, garejen na nufa na zauna ina ta kukan bakinciki a da mutanen nan suka saka min, hakika sun zalince ni iyakar zalince abunda ba zan iya yafewa har duniya ta nade. Da zaman ya isheni ne na tashi na fito harabar gidan na nufi gurin gate na fice na farkon na wuce na biyu na isa na uku na bude na fita sai na ji wani iska mai dadi yana ratsani, daman garin hadari ya hadu sosai kamar za a sako da ruwa, iska sai kadawa yake a ko'ina, rumgume hannayena nai ina ta kallon titin da ba kasafai mota take wucewa ba ga manyan gine gine gwanin sha'awa komai a tsare, gaskiya garin Abuja yana da kyau sosai. Ina tafiya ina jin takun mutum a bayana sai dai hakan be sa na waiga ba har sai da na ji an gashin kaina, saurin juyowa nai sai mukai ido hudu da Kamal yana sanye da shadda sky blue fuskarsa dauke da murmushi. Ban san hawaye ne a fuskata ba har sai da ya nuna fuskar tawa yana tambaya.

“Mi yasa kike kuka?”

Hannu na kai na taba sai na ji hawaye a fuskata sharewa nai sai wasu suka zubo min.

“Miyasa kike kuka? Ko kin marmarin gida ne?”

Ban ce masa komai ba na daga kaina a sama ina ta kallon hadari, kokari na ke naga na tsayar da hawayen amman suka ki tsaya min.

“Yi magana mana ko cikin gidan ne akai miki wani abu?”

“I zuwa yanzu nima ban san dalilin kukana ba, gida na ke so ko wani abun yake damuna ban sani ba”

Na fada ina fashewa da kuka, kuka nake yi sosai irin kukan nan da ke fitowa mutum da ko ina, wanda ban san dalilinsa a yanzu ba. Sai ya ciro handkerchief dinsa ya miko min.

“Share hawayenki fada min abunda akai miki”

“Kai ba ka kyamar talaka?”

“Wani ya nuna miki kyama ne?”

Na yi shiru ban ce komai ba sai kallon kyalen na ke. Sai ya dago fuskata ya saka kyalen ya share min hawayena.

“Ni ma lokacin da ina kamar na yi irin wannan kukan, ina ta tunanin makomata da ta mahaifiyarta da ta kanena, zan mu jidadi ko aa”

Na kauce fuskata daga rikon da yai min, sai ya cigaba da maganar ba tare da ya damu ba.

“Na san darajar talaka, su ne mutanen da na kaiwa kuka aka taimake ne a lokacin da nake bukatar taimako,ba dan talakawan ba, da yanzu ban samu wannan aikin ba, ban kai wannan matsayin ba”

“Amman mutane da yawa basa son talaka, suna nuna mana kyama kamar mu din wata al'umma ce ta dabam”

“Kar hakan ya dame ki, yatsun hannunki ma ba ayi su daidai ba, taya kike tunanin mutane ma za su yi daidai a tunani da hankali? Arziki da taluci duka na Allah ne, a lokacin da na ke kamar ki talaka ne mai neman na kansa, amman yanzu gashi ina cikin masu kudin suna yi da ni”

“Ba arzikin ne damuwata ba, kyamar da ake nuna mana ne ke damuna kuma....”

“Aisha”

Kiran da Inteesar tai min yasa ban karasa fadar abunda zan fada ba, na juyo da sauri na nufo cikin gida a lokacin har an fara ruwa sai dai ba sosai ba.

“Mama Fulani na kiranki”

Jin hakan yasa na hada da gudu na dan na isa part dinta cikin sauri. Ina shiga ciki ta rufe ni da fada.

“Dan ubanki ba aiki kika zo ba da zaki kama hanya ki fita”

“Ba wani gurin na je ba, ina bakin gate ne...”

Ban gama rufe baki ba ta wanka min kyakkyawan mari ban san lokacin da na fashe da kuka ba nai baya da sauri dafe da kuncin ina jin yadda yake min wani mugun zuji.

“Mama dan Allah ki yi hakuri ba zan sake”

“Ki ma sake ki ga yadda zan yi da ke a gidan nan, yar iskar yarinya kawai, uban wa kika sani a abuja da zaki kama haya ki fita, ko bakin yawon gantalin na ku ne ya yayan takawa za ki fara? Salon ki bace a dora mana lalurar neman ki ko? Jahilar banza, wuce ki ba ni guri”

Da sauri na fito daga falon jikina na rawa ina ta kuka na nufi garejen da na ke kwana, wani abun mamaki sai na samu Aliyu a ciki tsaye kan tabarmata kamar mai jiran shigowata.


ALIYU POV.

Ji yai kamar ta saka gatari ta sare duk wani kuzari da karfi da yake jikinsa da zuciyarsa, hawayen da na ga suna zuba idonta a lokacin da take fada masa maganar da tafi ko wace zafi a duniyar nan yasa shi jin babu dadi. Azzalumi take kallonsa, then why ma zai mata magana daga ganinta? Taya zai fahimtar da ita? It's necessary for him? Zalincin da ya ke gudun da kira shi da shi ashe haka take kallonsa, sai ya ji ya damu da kukanta da kalmominta da kuma kallon da take masa na azzalumi. Kamar marar muzari haka ya fito daga garden din ya dawo part din Mama Fulani ya zauna. A lokacin tana kitchen tana hada masa fried rice saboda ta san yana sonta sosai. Zaman kawai yai amman be zuciyarsa tana waji gurin dabam tana yayo masa wani tunanin akan Ataa. Tashi yai ya shiga kitchen din yana fadin

“Mama favorite dina kike dafawa i know”

Sai ta juyo ta kalleshi tana dariya

“Eh mana ai dole nai maka abunda kake so Aliyu, wai ina yarinyar nan ne ma ta yanka min albasa?”

Yasan Ataa take nufi dan ko ba a fada masa ba yasan aiki ta zo yi a gidan, kuma ya san Mama Fulani ba zata saka yayanta aiki ba sai dai mai aiki.

“Ina take zama hala? Waya kawo muku ita?”

“Wannan matar ce mai kawo mana yan aiki, ita dai wannan ina ganin kamar ba za mu dade da ita ba, dan kazama ce kuma bata cika son aiki ba ga shegen shishigin tsiya, and i hate yadda Muhseen yake rawar kai a kanta”

“Ina take?”

“Gareji take kwana, ban san inda take ba balle ta gyara min albasar nan”

Kofar baya ta kitchen din ya bude ya fita ta nan ya zagaya gurin motocin ya isa gareji, bude ya same shi garejin an shimfida tabarma a ciki sai yan jakarta a gefe rabe da plate da cup a gafe daya ta rufesu da dankwalinta mai raga. Yana kallom gurin zuciyarsa na sosu a tunaninsa kamar be dace ta zauna a nan, if he is one da yai causing duka wannan matsalar a rayuwarta. Jin kukanta ne yasa shi juyowa yana kallon kofar gajerin sai gata ta shigo tana dafe da fuskarta tana kuka. Yawun bakinsa ya hade saboda sautin kukanta da ke shigar masa har cikin gashi yana ta masa ruri a kunne kamar shine silar kukan. Tsaya yai kallonsa.

“Bakin azzalumi mi kake nema a nan kuma?”

Ta fada masa kai tsaye tana kallonsa da jajayen idonsa. Yana jinjina kokarinta yadda ta ke fada masa duk abunda ya zo bakinta, ba karamin burge shi take ba at least ya hadu da mai iya fada masa magana kai tsaye bayan iyayenshi.

“Bayan abun da kai wani abun kake nema kuma? Tun na bar aikin a gidanka nake ta godiyar Allah daya sa na gane ku ne kuka zalince da wuri har na bar aikin a gidan, amman yau saboda rashin sa'a na sake haduwa da kai, tun da na zo gidan nan ba a taba duka na ba sai yau, a duk lokacin da na hadu da kai wani abun ne yake samu na marar kyau, bayan ka zalince a can nan kuma kana kokarin nuna min fin karfi, mi kake takama da shi? Duniya? Wani yana can ya fika arzikin be ma san da zaman ka a duniya ba, Wallahi duk arzikin da kake takama da shi wani yana can ko kan akaifarsa baka kamo ba, indan ka tara dukiya kamar karuna mutuwa za kai ka barta, ba za asaka ka kabarinki da naira biyar ba, na nice kai taimako zan yi da duniyar da zan amsawa Allah amsar inda da samo ta daga naira da kuma inda na kashe ta ba wai zalince ba,tir da mai dukiya irinka da zuri'arku tirr da dukiyar da zata rufewa mutun ido ya kasa ganin darajar dan 'adam din da Allah da kansa ya karrama....!”

Tun da ta fara magana yake ta kallon cikin idanuwan, hawayenta na sauka da bugun zuciyarsa, ba a taba hasali kamar haka ba, wani beisa ya tsaya gabansa ya fada masa marar dadi kamar haka ya kyale shi ba, ransa be tana baci kamar haka ba, wata magana bata taba shiga cikin zuciyarsa ta saka shi raina kansa kamar yau ba, ba a taba kaskanta tashi kamar yau ba. Wani irin abu ya ji kamar ya dake ta kuma ba zai iya dukan nata ba, da ace yau wani tsaye agabansa ba Ataa ba ya fada masa bakar magana kamar haka babu abunda zai hana shi taka shi yadda yake so.
Jin be ce komai ba sai kallonta da yake da jajayen idonwansa naman fuskarsa na rawa yasa ta juya da zimmar fice, sai ya kai hannunsaya fisgota ta juyo da ita ya nuna ta yatsa bakinsa na ta rawa kamar zai ce wani abu kuma ya kasa furta komai. Kamar wanda ya tuna wani abu sai yai saurin sakinta yana kallon hannunsa kamar mai kyama, ita hannun nasa ta kalla kamin ta kalli kafadar daya rika.

“Gaskiya ne, be kamata ka rika ni ba, kar na saka maka talauci, talauciabun gudu ne na sani, ni kaina ba dan talauci ba da baka isa ka saka a cire kodar mahaifiyarta da matar da bakin likitan nan kuma na barku kuna yawo ba, ba dan talauci ba da baku isaku gan ni a wannan asibitin ba balle har ku zalince mu, da ba dan talauci ba da ba mu raba a kangon gidan babansu Rahma ba da har wulakanta mu, ba dan talaucin ba da baka isa ka shigo inda na ke kwana ka taka shi da kafafunka da suke da takalmi ba, ba dan talauci ba da ban zo aiki cikin gidan har a wulakanta ni ba, ba dan talauci ba da yau Mama Fulani bata daga hannu ta mareni ba balle yar ta kirani yar iska, komai saboda talauci ne komai komai ina nufin komai”

Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login