Showing 219001 words to 222000 words out of 225640 words
yin wani abu na hukunta shi zai siye masu kamar yadda yai min, amman idan daga manyansa ne matukarvsuna son adalci dole su bi gaskiya kuma su kwato mana hakkinmu su kuma wanke kansu daga bata musu da aiki da yake kokarin yi.
Ba mu bar gurin ba sai da suka suka fada mana cewar za su tisa keyar Doc Asim kotu tare da na su hujojin idan sun kara bincike, hakan kuma ba ni kadai yai ma dadi ba har da sauran mutanen. Balle kuma Nana da ba a magana, sai dai sun bukaci dukan mutanen da ni kaina mun kawo takardun da suka nuna hakan kuma suka ba ce za su kai Mama asibiti su sake bincikawa.
Gobe zan yi long post In-Sha-Allah 🙏uzuri ne ya rike ni yanzu nai typing wannan.
AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.
Na fara zuwa makarantar koyon girki da ke badon 3bedroom, a ranar da aka fara da sabin dabibai. Ban wani sake sosai a ranar ba saboda ina jin kunya da nauyi saboda yawan daliban da ke gurin, malamar ta rubuta mana abubuwan da za mu siyo da kuma abubuwan da za mu fara koya.
 Kamar wasa na fara maida hankali ina koyon dukan abubuwan da suke koya mana, wani lokacin idan na dawo gida kuma sai na gwada, da na fara sabon da yan mata da kuma wasu sabin aure da suke makarantar sai ya zama idan ma naje bana son dawowa saboda samun kawaye da nai kuma kawaye masu mutuncin da sanin ya kamata. Mun yi musanyar number wya da wasu daga cikin yan matan da kuma matan auren, yawan matan auren da suka girmi sai dai na kira su da Anty ko Maman wane saboda ina jin nauyin fadin sunansu hakan nan kawai wasu su kira na da yata kasancewar ina da sunan yarsu wasu kuma su ce min kanwata.
Daga lokacin na fara fa'idantuwa da wayar da Hamma ya siyo min, domin ta nan nake chat dasu idan sun ga wani abun mai amfani sai min sharing su tambayi tafiya da ta miji, masu grps suka saka ni wata babban a cikin mu kuma ta bude mana wani grp na koyon girkin d muke, wai ko da akwai abunda Malama tai jawabi wanda mutum be gane ba sai yai tambaya a fada masa ko a kara wayar masa da kai. Na kara ilmi ba kadan ba, domin a cikin groups din da nake ana yawan turo abubuwna da suka shafi matana aure na inganta zamansu yadda za a iya kula da miji yan'uwan miji da sauransu, a cikinsu akwai wani wai shi Women Diaries na wata marubuciya, ina karuwa da grp din sosai abunda ban fahimta ba kuma sai nai tambaya a take za a fayyace min komai.
  Daga ranar da akai wacab case din ba ba su sae kira ba, har na sawon wata daya, sai da suka kara bincikensu suka tattara dukan hujojinsu suka tabbatar da abunda ake zargin Doc Asim da shi bayan sun tsananta bincike sannan suka mika shi kotu. Wani abun mamaki Doc Asim har da daukar lauya mai kare shi, ni da Mama ma lauya ne yake tsaya mana duk wani abincike ko gabatar da shaida shi yake yi. Hakan ya saka wani lokacin ba da ni ake zuwa kotun ba domin cikin nawa wani lokacin sai ya taso min da zazzabi wani lokacin kuma kamar ba ni ba. A cikin wannan halin Hamma ya dauke ni muka koma Abuja daman wani lokacin yana tafiya yana dawowa saboda aikinsa, ni kuma baya son tafiya da ni saboda koyon girkin da nake. Yanzu kuma na kamalla daman ajin akwai na wata daya akwai na wata biyu uku hudu biyar har shakera uku ma ya danganta da wanda ka zaba. Ni kuma ya biya min na wata biyu ne kawai kuma babu laifi na iya abubuwa da dama na zamani da kuma irin na da da ake saffarawa a girka tun daga kan na sha wato home drink's har abincin. Wani abun kuma ina ra'ayi zan leka YouTube na duba na fada masa ya siya min kaza da kaza idan babu ina son na hada.
Muna saura kwana biyu muje Abuja Hamma yake fada min zancen baikon da za ayi ma Amina, na yi murna sosai ina jin na taka wani da za a kira matar yaya kuma a fada min wani abun na kanen mijina idan za ayi. Sosai na so mu fasa zuwan har sai an yi baiko amman Momy ta hana saboda tana son na walkilce a gidan Mama Fulani na kai lefen Muhseen da za'ayi wanda ba zata samu zuwa ba saboda baikon Amina ita ma Mama Fulani ba zata samu zuwa ba saboda kai lefen.
 A ranar da muka sauka Abuja a gidan Mama Fulani muka sauka kamar yadda Hamma ya saba idan yayi tafiya zai sauka a gidan Mama Fulani idan a sokoto ne kuma zai sauka a gurin Momy. na yi mamakin yadda muka samu Mama Fulani ta murje ido kamar ba ita ba, sai marhabun take mana da far'a da komai irin yadda take tarbar Hamma, tana ta nuna kulawarta akaina ni dai ban sake jikina sosai ba sai dai na lura hakan ba karamin dadi yai ma Hamma ba, ba ita kadai ba har su Maryam da Rukaiya sun murje ido suna sakewa da ni kamar komai be faru ba, ni kuma na kasa mantawa a duk lokacin da na kalle su ko kuma suka min wani abun na karramawa ko kulawa sai na tuna da baya. Suna ta shirye shiryen kai lefen Muhseen da za'ayi kamar yadda Momy ta fada.
Sai da muka huta a gidan sannan muka doshi gidanmu da ke can Abujar, an gyara ko'ina na gidan kamar muna ciki muna rayuwa.
“Na yi mamakin ganin gidan nan a haka, haka wacan zuwan na tararda gidan wanke fes”
“Gyarawa ake”
“Wa ke gyarawa?”
“Aljanu”
Ya fada yana kanne min ido kamin ya fada min cewar mai masa gyaran fulawoyi da gida ne yake gyarawa. Washe garin ranar da muka so ya kama Saturday a ranar a aka kai lefen a wata unguwar masu hannu da shuni da ke garin abuja, lefe na mai amsa sunan lefe da babban gida na masu naira irin dai wanda Mama Fulani take kwadayi kuma take so. Sun yi mana goma ta arziki bayan kayan ciye ciye har da kudi masu yawa suka hadu mana. Ni dai ina so ganin yarinyar domin Hamma ya fada min wai ya ganta a wayar Mama Fulani tana da kyau sosai.
 Bayan mun dawo mun huta ina bangaren Ammy na shiga whatsapp dina sai ga hotonta da aka hada da na Muhseen da kuma lefen ana tayata murna a status din Husna na gani, gaskiya kyakkyawa ce sosai fara mai jiki sai dai ba sosai ba, ban yi mamakin kyauta ba daman can irinta yake ai, wato mace mai kyau na san da hakan tun daga lokacin da aka kawo ni aiki a gidansu, kyau na cikin abunda yake burge Muhseen, kuma ba laifi ba ne dan ya so mace mai kyau musulunci ma ya yarda a auri mace dan kyauta.
 Â
Daga gidan su Mama Fulani aka aiko mana da na mu kayan baikon Amina, ta bangaren Abbah da yake akai komai da shi, a lokacin da aka kawo mana na mu na sha dariyar Hamma saboda korafin da ya rika yi wai nawa ya fi na shi yawa, kuma haka din ne nawa dabam mai yawa na sa kuma ba mai yawa sosai ba, a waya Momy take fada min wai mai yawan shi ne nawa wata kila ina da kawaye da zan rabawa na jidadin da Momy ta kwarrama ni ta tabbas da ace ina da kawaye a nan Abuja babu abunda zai hana ni raba musu baikon kanwar mijina. Sai dai kasancewar kawayen da nai sabo da su yan makarantar koyon girki ne kuma duk a sokoto suke babu daya a nan.
Sati daya da kai lafen Muhseen aka kawo baikon Rukaiya na ni kadai ba, har Hamma sai da yai mamakin jin zancen ta samu miji domin shi kansa be san wani na nemanta ba, daga ni har shi har su Momy mun ji abun ne daga sama, a ranar da Abbah ya fada masa za a kawo baikon sai da ya kira Mama Fulani a waya yana tambayar anya dai an yi bincike akan mutumen kuma an san waye shi? Ina jin lokacin da Mama Fulani take fadar wai ai yanzu an daina zufafa wannan binciken da ake kuma yaron dan kano ne iyayensa sun zo har da wamban kano (Fake Name) ya fada musu shine babansa kuma sunansa yake bearing, dan haka ba sai an fadada bincike fa, aiki kuma shine manager a gidan man da ke nan Abuja. Tana ta fada masa irin kudin da ya kashewa Rukaiya daga haduwarsu zuwa yau ya kashe mata kudi masu yawa, gashi kuma Abbah yana zancen hade yayan Ammy su uku da Muhseen ai kara a hada da Rukaiya tun da ita din ta samu kuma yace a shirye yake.
Ni kaina na yarda da zancen Mama Fulani cewar mai kudi ne tun daga kan kayan baikon da ya aiko kayana masu yawan da gaske irin waenda ake kaiwa a manyan gidajen, a ranar Momy ta zo har da Daddyn ma da wasu yan'uwan Mama Fulani da ke Yola.
Kamar yadda Hamma yai min alkawarin saka ni a wata makarantar be saba alkawarinsa ba, duk kuwa da kasancewar cikin nawa wata biyar ne ya lokacin har da yan kwanaki a kai, amman a haka ya aminta ya saka ni a Royal Academy, wata makarantar kudi ce da ke nan Abuja ta masu koyon karatu da rubutu da kuma waenda ba su samu damar kare karatunsu ba kamar ssce.
 Karfe tara ake zuwa a taso sha biyu ga irin mu ga yan sss2 da 3 kuma suna zuwa da safe misalin takwas su tashi biyu saura. Gaba daya makarantar da turancin ake magana tambaya da kuma bada amsa ko da kuwa tsakanin dalibi da dalibi ne, ma ji tsoro sosai ganin irin ka'idar makarantar sai dai hakan ya saka na kara dagewa da maida hankalin wajen ganin nima na iya turancin kamar sauran, ba musulmai kadai ba ne a makarantar akwai kistoci ma har da waenda ba hausawa ba, akwai matan aure da yan mata a ciki akwai maza akwai mata sai dai bangaren mazan dabam matan ma bangarensu dabam, ko a cikin matan daga ni sai wata haulatu ne muke saka niqab domin ita ma ina jin mijinta irin Hamma ne mai tsananin kishi, ba niqab kadai ba har safar kafa da hannu Hamma cilasta min sakawa yai yi. A dole kuma mai hakan saboda ina son karatun. Shi yake kai ni ya dauko ni idan mun tashi, idan ma ba shi da time sai dai ya ce na jira shi idan ya gama ya zo ya dauke ni, wani lokacin da yar kula ta abinci kamar wata karamar yarinyar yar makaranta ko da yake ba ni kadai na ke zuwa da abincin ba, kuma duk wanda ya gan ni da abincin idan ya lura da yadda cikina ya fara dan tasowa zai san ai lalura ce, domin kuwa cikin nawa na kara girma cin abincin na karuwa abun har mamaki yake ba ni. Sosai na ke son zuwa Nijar gurin Yan'uwan Mama da na Babana na ga waenda ban gani da Waenda kuma na gani na kara ganinsu, duk kuwa da kasancewar sun zo a baikon da akai ma Zainab da Batula na cousins, sai kuma na Humaira da akai kwana biyu da yin na su, aka saka lokacin auren daya da na Muhseen kamar yadda Abbah ya fada cewar yana son ya hade su yai musu auren a tare a bar Maryam kawai ita da bata samu mijin ba.
Karatun da na ke a yanzu ya fara zame min kamar da wahala saboda na hada biyu ne, da yamma ina zuwa wata makarantar islamiya ta matan aure wacce ake zuwa karfe uku a taso budu da rabi, a can ma na yi kawaye amman iyakana da su a makarantar wai kuma a waya da muke chatting. Ga kuma cikina da shiga wata bakwai da shi a yanzu, ba wata wahalar na ke ba bayan nauyin da cikin ke min sai kuma yawan zazzabin da tsandar abinci, sai dai bana nunawa a gaban Gogan nawa saboda na san halinsa yana ganin wani abun zai iya hana ni karatun ko yanzu da be ga wani abun ba yana fadar wahalar tana ma cikin yawa balle kuma ya gono ai a take zai hanani zuwa makarantar.
 Wani iko na Allah sai na fi gane makaratun arabiya fiye da na bokon da na riga farawa kuma na dan gane wasu aabubuwan a baya domin na iya karanta hausa tun kam na shiga makarantar, bokon ma ba zan ce bana ganewa ba amman na fi gane na arbiyan fiye da na bokon.
 Â
 Wata biyu da kai lefen Muhseen akai soma shirye shiryen biki, tun kan 25 Sept aka soma baki a gidan Mama Fulani ciki kuwa har da su Momy da wasu daga familynta da suka zo bikin, da mutanen yola. Abbah ya gyara ko'ina na gidan an yi sabon fenta an sayo abubuwan tarbon baki da na hidimarsu.
A Abuja aka fara komai na bangaren Mama Fulani ta bangaren Amaryar Muhseen kuma daga Bachi aka fara sannan aka dawo Abuja aka cigaba da shagali. A cikin shagalin biki wani wani labari marar dadin ji ya zo mana, Waenda aka tura su je yin jere Rukaiya sun tararda da karamin gida mai ciki da falo daya da bandaki sai kitchen a tsakar gidan, ma'ana dai irin gidan nan na talakawa masu rufin asiri, yadda Mama Fulani ta sha kuka a ranar abun har tausayi ya bani ba ita ba ba Rukaiya ba ba yan'uwanta ba, Momy ma bata jidadin hakan ba sai dai babu yadda aka iya. Ai ko a lokacin ne Hamma ya hau fada cewar daman can sai da ya ce ayi bincike Mama Fulani tace bincike ba dole ba ne kuma an san iyayensa da sauransu. A lokacin ne Abbah ya kiran Mahaifin yaron yana fada masa awai an je jeren dakin an tararda abunda ba a zata ba, sai Wamban kano yake fada masa cewar ai ba shi ya haife shi ba almajirin gidansa ne tun yana matashi har ya tasa ya koma Abuja yana neman kudi, a gidan man ma shi ba manager ba ne yana cikin amsu siyar da man ne dai a tanki. A ranar Rukaiya suma ne kawai ba tai ba akan bakinciki ita da Mama Fulani. Hamma ne ya saka aka nema masa wani gidan haya mai kyau aka je can akai jeren.
Washe garin ranar da akai Walima akai Dinner, sai da kowa ya halarta sannan daga baya ni naje tare da Hamma, na sha kyau abuna ni kaina na san na yi kyau domin lace din angon blue ne mai fitar da farin mutum, ga kuma tsoraye na aka min suka sauko har bayana, kuma nai sa'a Hamma ya bar ni na fidda abuna sai dai be barni na yafa karamin gyale kamar yadda kowa ke yafawa ba nawa babba ne amman hakan be hana ni yin kyau ba, da man kyau mace ba a fitar da surar jiki ba ne daga kyau tufafi ne da ainahin halittar da Allah yai ma bawansa. An zubar da kudi sosai a gurin karin har nake ganin kamar hakan be dace ba, angwaye da Amare sun sha kyau sosai, duk inda Hamma yai yana rike da hannuna karin ma bayan yayi musu sai ya dawo gurina yana ta min karin ni ko har kunya na ke ji saboda cikin jikina, ban taba daukar cewar Hamma zai iya rawa kamar haka a gaban mutane ba, ba wani rawa yai can sosai ba amman yana takawa a hankali yana wasa da hannuna. Ina tsaye da shi wata cousin sis dinsa ta zo tai masa kari ta dauki hoto da shi, na ji zafi sosai shi kansa sai da ya lura da hakan har yai murmushi. An yi dinner lafiya washe ya kama Assabar sai aka rabu wasu suka tafi Bachi dauren auren wasu kuma suka tsaya a nan Abuja a inda akai na su Rukaiya da Humaira da Zainab da Batula.
A daren ranar da aka daura auren aka tafi da su Zainab da Batula zuwa Agadez tafiyar da akai ta da ni duk kuwa da kasancewar Hamma be so haka ba, ni kuma na lake sai na tafi kuma Momy ta saka baki a dole ya kyale ni a bisa sharadin kwana biyu zan dawo saboda shiga kotun da za ayi. A cikin garin Kaduna aka kai Humaira Rukaiya kuma a kano gidan da Hamma ya kama musu Muhseen kan a Abuja ya tare da matarsa. A gida mai kyau aka aje su su kansu sun san an musu gata, daman mai hakuri mawadaci