Showing 123001 words to 126000 words out of 225640 words
dawowar maraice yai domin ana daf da kiran sallah magariba ya shigo gidan, direbansa ne ya bude masa mota sannan ya fito ya dauki jakarsa ya shigar masa da ita part dinsa, Daddy kuma ya nufo part din Momy yana gyara zaman babbar rigarsa, tun kan ya kai hannu ya bude kofar ta bude masa fuskarsa da murmushi.
“Sannu da zuwa”
“Yauwa”
Ya amsa yana naso kafarsa cikin falon, kujerar da ke kusa da kofa ya zauna yana sauke agajiya, Momy ta nufi gurin freezer dake gefen dinning ta dauko masa gorar ruwa da kofi ta kawo masa.
“Yau dawowar wuri akai SSG?”
“To mun gama abunda za ayi, zama na me kuma?”
“Ai ko ka dawo a daidai, da na so ma na kira kuma ban samu dama ba”
Sai da ya sha ruwan da ta mika masa sannan ya kalleta ya ce.
“Wani abun ne?”
“Dazun ne Dan wajen Fulani yake fada min cewar wai Rahma bata gidansa tun sati biyu da suka wuce”
Daddy yayi fuska manya irin ta mamaki da son tantace magana.
“Tana ina?”
“Wai ta yi fushi”
“Fushi? Fada suka yi?”
“Ba fada suka yi ba, kawai dai akasan yarinyar nan da ke jinya asibiti, ita Rahma ta saka aka je aka daketa da zo na fada masa shi ne tai fushi”
Daddy ya kyalkyale dariya kamar ba wanin abun ba.
“To ko kishi take? Yaushe akai abun?”
“Tun sati biyu da suka wuce dazun ma aka sallamo Nana daga asibitin, ni ban ma sani ba sai dazun yake fada min wai a masa bikon matarsa”
“Kuma fa muna yawan haduwa da Alhaji Nasiru Gobir be taba min maganar ba”
“Wata kila yana maka kallon ka sani ne”
“To Allah kyauta mutanen ne basa da dattako sam, ace yarka ta dawo gida har na tsawon sati biyu ai ya kamata ya bincika ya ji miye dalili”
“Dalili ya wuce bin bayan yarsa, kasan duk abunda ta fada shine daidai, sam ba su mata tarbiya mai kyau ba, ace abun kadan ka debi kafafuwa zuwa gidanku, yarinya lafiya ma bata isheta ba duk dawainiyar da yake da ita basa gani, wani lokacin Wallahi har tausayi yake bani, kwata kwata dan wajen Fulani ba san dadin aure ba”
“To shi kuma a haka son abarsa yake, da dai ya samu wata ya kara ai ita ma zata bawa kanta lafiya, mace idan tana ita kadai kuma tana ganin gata ya mata yawa zata ta yi abubuwa da dama ai, ko da yake Aliyu dan boko ne ba son mata biyu yake ba”
“Ba wani gata rashin tarbiya dai ne tun a gida ba a koya musu tarbiya mai kyau ba, ni da gatan be saka na yi wani abun ba”
Daddy ya mike tsaye yana zolayar Momy
“To ke duk kika gwada yi ai sai a kawo miki kanwa, ga mata nan duk inda na shiga kallo na kawai suke”
Momy ta dan harare shi.
“Ai ba kai suke kallo ba mukamin ka da kudinka suke kallo, idan ba dan kudi ba waye zai so tsoho? Ko ma watan ka kawo ai na gama cin moriyarka kuma na zama uwargida mai yayan gida sai dai ta bi”
Dariya suka yi har ita da tai maganar domin ta kareshi maganar ne tana wani murmuda ido irin na su na manyan mata.
“Ina yarana? Ban ji motsinsu ba”
“Husna da Amina sun fita Siyama kuma tana can bangarensu Ataa”
“To Alhajin Fulani ya samu cigaba kamfanin nan da yake ikirarin za a siyar wani dan kasuwar kasar nijar ya siye shi, Kuma ya bar ragamar tafiyar da kamfanin a hannunsa, ya kamata ko ban samu zuwa ba ki shirya da yara ko kwana daya ne suke ku masa murna, samun cigaban dan'uwana kamar nawa ne, ba ni da wani wanda ya fi shi a yanzu”
“Gaskiya na masa murna sosai, Allah ya dafa ya taimaka, daman haka muke so ai, to wannan tafiyar fa?”
“Ki samu wata kuje daman biko ai na mata ne”
Yana fadar hakan ya fice daga falon ta biyo bayanshi tana ta taya shi murnar samun siyen kamfanin da akai har tana fadar ranar da ya dace suje.Bayan sallah magariba Momy ta kira kawarta Hajiya Ramatu ta fada mata cewar za su je bikon Rahma. After sallah isha'i idan tana da time, ana saukowa daga sallah isha'i sai ga Hajiya Ramatu ta zo gidan ita da danta wanda shi ya janyo motar ya kawo da ita a gidan, tana shiga falon Momy ta fito sanye da mayafi suka gaisa a tsaitsaye suka koma cikin motar Hajiya Ramatu, kamin su isa gidan Alhaji Nasiru Gobir wato mahaifin Rahma Momy take labartawa aminiyarta Hajiya Ramatu abunda ya faru tsakanin Rahma Aliyu. Tsaki Hajiya Ramatu taja cike da jin haushi ta ce
“Wai Hajiya Hadiza miyasa ba za ki saka Aliyu ya kara auren ba? Wannan iskacin da jin kan da yarinyar nan take masa ya yi yawa, wallahi idan yanzu ya kara aure duk wannan iskancin dainawa za ta yi kuma dole ta kama kanta idan ta ji ba zata iya zama ba ta fita”
“Kamar a gaban ki akai, Wallahi dazun mahaifinsa ma haka yace kin san ko maza ma basu cika kula da sha'anin aure kamar mu mata ba”
“Wallahi akwai haushi Hajiya Hadiza abunda ake masa ne ai yayi yawa, duk irin hidimar da yake musu basa gani? Bawa ne shi?”
“Ido ne nawa idan ya ji wuya shi zai nemi karin auren da kansa ai, amman na san da Fulani ta san da wannan Wallahi da sai tana zuwa bikon nan daman can ba son aurenta da Rahma take ba”
“Ke ma dai ai da ba ki je ba Wallahi da ya zuba musu ido ya barta tai ta zaman gidan har sai zaman gidan ya isheta”
“Kin san iyayen miji idan ba su yi ba, basa fita idan ma suka kai ba fitar suke ba, yanzu ma sai an dora laifin a kanmu”
Hajiya Ramatu ta tabe baki cike da jin haushi. Ba laifi yan'uwan Rahma yayanta da kannen sun tarbesu cikin girmamawa da mutunci, sai dai mahaifiyar Rahma na fitowa sai ta canja musu fuska kamar wacce bata son zuwansu. Ciki ciki ta gaisa da su Momy na ganin hakan ta dauke kai ta ki cewa komai sai Hajiya Ramatu ce tai bayanin abunda ke tafe da su.
“To ya gaji kenan? Yarinya ta zo gidansu sati biyu dan tsabar wulakanci be zo ba be aiko ba, sai yanzu idan ya gaji da ita ai ba sai ya wulakanta akan yar talakawa ba, wai har ya mari Muneera akan wata banza can sha sha sha, yarinyar da be san inda ta fito ba, idan ma gajiya yai da ita mu ai muna son ta ba mu gaji da ita ba”
Wani wawan kallo Momy tai mata har tana kashe ido tsabar bacin rai.
“Yar talakawa da ba a san inda ta fito aka dauki kodarta aka sakawa yarki, sai yanzu na gane ashe Rahma bata rage komai daga halinki ba, ke kika koya mata kyamar talaka talakar ma wacce ta taimake ke ku, ba mu damar zuwa bikon Rahma ba sai yanzu, shi kan shi mijin na ta ma be so mun zo ba, domin ba shi ya koreta daga gidan ba, yarinya kamar wata mai shan nono da an yi abu ta dauki kafa zuwa gida ko kunya babu, mi Rahma zata nuna mana? Gata ko kudi ko family? Ba ta nuna mata dukiya ke kanki kin sani zuri'a kuma duk sokoto an sani babu wanda ya fi torankawa asali da tarin yan'uwa, duk abunda take muke shanyewa muna shanyewa ne saboda muna son ta zauna lafiya da mijinta, domim Rahma bata san wani abu wai aure ba, dan abu kadan ta kwaso kafa zuwa gida haka ake yi?”
“Au daman ba shi ya aiko ku ba kuka zo? To ki koma Rahma ba zata koma yanzu ba sai ta huta, sai Aliyu tako da kansa ya dauki matarsa, dacan idan ba nan ba so kike ta koma gefen titi tana bara kamar yar da danki ke so? Abun kunya wai kamar SSG ace dansa yana son yar bara a titi, mutum mai daraja wanda ya rika mukamai masu girma ace an rasa wacce dansa mai kamfanin Sky global resources yar talakawa makaskanciya, ku kanku ai abun kunya ne a wajenku”Momy ta girgiza kai tana kiran sunan Aliyu baro baro.
“Sam ni nikam abun alfahari ne yau Aliyu ya auri Ataa ko babu komai zai inganta rayuwarta kuma sai san yayi aure, ya kuma gane banbancin tarbiya da rashinta”
“Daman ai saboda kin cusa nasa son wata ne kike wannan bobotan, indai yana son Rahma ta koma dakinta to ya janye neman aurensa da wannan kazamar yarinya, ya hada Rahma kishi da yar wani mai kudi ba amman ba wannan ba”
Momy ta yi yar dariyar takaici tana mikewa tsaye tare da Hajiya Ramatu wacce ta kasa cewa komai tun da aka fara fada.
“Hajiya Talatu kin yi tutu gonar mai munta, zaman gida dai ko? Rahma tai ta zama har Mahdi ya bayyana, idan kuma zaman ya isheta sai ki dauke ta ki kaita dakinta, amman wani daga ni ko Aliyu ba zai zo bikon wannan yar ta ki ba, kuma ki zuba ido indai ina raye Rahma sai ta kishi da yar talaka...!”
Momy na kawai nan ta nufi kofar fita a fusace, daf da zata fice Hajiya Talatu Mommyn Rahma ta ce.
“Ai dole ku nema masa yar talaka, domin kin san babu yar gata gabas da yamma da zata zauna da juya, dimmar da yai mata ai ya mata ne saboda ya san baya haihuwa su taru su mutu tare”
Momy ta juyo ta kalleta.
“Ke Hajiya Talatu idan ba ki gode ni'imar Allah ba za ki gode ma azabarsa, ruwan cikin lokali ya ishe mai hankali wanka kuma ki rubuta ki aje da ikon Allah sai Aliyu ya yi aure ya haihu....”
A fice Momy ta fice daga falon tana nadamar zuwan bikon da tai. Momy na fita Rahma ta fito idonta shakaf da hawaye ta fadi a kusa da Mommynta kamar zata narke.
“Na shiga uku Mommy mi yasa kikai fada da su? Na rantse da Allah Aliyu ba zai zo bikona ba, tun da kika taba masa uwa, Wallahi ba zai sake ganin kimata ba, Aliyu baya son a taba masa family”
“To sai mi? Aliyu shi kadai ya rage a duniya ne? Ko sakin ki yai sai kije ki auri mai haihuwa ki haihu, kar wannan abun ya daga miki hankali matukar yana son ki dole ya dawo, ai yasan gidan da ya dauke ki gidane mai daraja da kima”
Cikin kuka Rahma ta tashi ta koma dakinta, Muneera ta taso daga dayan bangaren na falon daman falon ya kasu biyu ne, ta nufo inda Mommynsu take tana dariya.Husna ta tashi ta nufi karamin firjin din dake dakin ta dauko mata ruwa da kofi ta kawo mata ta zuba mata, sai da Momy ta sha sannan ta labartawa Husna abunda ya faru.
“Mutanen nan suna ba ni mamaki, wai talauci hauka ne? Shikenan dan suna da arziki sai su taka mutane yadda suka ga dama”
“Su taka wanda yake neman abu gurinsu dai, arzikin da ba na shi ba, mai tinkaho da abun wani duk uwar dukiyar da yake kuri da ita idan aka kasa uku ko kashi daya ba zai dauka ba, dukiyar wani ce wanda idan yau ya kaushe abarsa sai dai tu koma rabe raben wani, shi har abun tinkaho ne? Wai wanda ya gaji arziki baya haka”
“Gaskiya abunda suke yayi yawa, haba jama'a wai Wallahi sun ja mata domin Ya Aliyu ba zai je bikon ta ba”
“Tai ta zama a can har sai zaman gidan ya isheta ta yi hankali aure dai sai Aliyu yayi kuma Ataa zai aura sai dai su mutu?”
“Momy da Ataa?”
Husna ta tambaya tana zare ido.
“Eh ba ni za su nuna isa ba? Sai ya aureta?”
“Ya Muhseen fa?”
“Amina zan bashi, daman ai Fulani ba zata yarda ya aureta ba, kuma ko aurenta yai ba dadin zaman zata ji ba, amman yanzu Aliyu nake son ya aureta ya maida mutum kamar yarsu in ya so sa su mutu”
“Amman Ya Aliyu zai yarda ya aureta ne? Kin san fa ba sonta yake ba?”
“Ba son ta yake ba yake kishinta? A banza ake kishin mace? Idan ma baya son ta sai ya fara daga yanzu”
Cewar Momy tana wani cika har yanzu zuciyarta ta ki ta sauka daga bacin ran dake tare da ita.
“Amman Momy Ya Muhseen zai ga kin masa rashin adalci”
“Na ce miki Amina zan ba shi ai yasan idan bana sonsa ba zan ba shi yar cikina ba, amman Ataa sai ta auri Aliyu In-Sha-Allahu”
“Idan kuma ita Ataa din bata son shi fa?”
Momy ta yi shiru alamar tunani kamin ta daki kan gadonta tana ta rawa da kafa.
“Ina bukatar sanin waye Ataa ina suka fito, shine kawai abunda na ke son sani a yanzu, amman bayan shi talauci ko wani abun ba zai hana wannan auren ba”
Husna dai ta kalli Momy ta janye fuskarta tana tunanin yadda za ayi wannan chakwakiya domin Muhseen ma ba kyalle ba ne, kuma yadda yake nuna yana son Ataa yana da wahala ya iya yarda ta auri Aliyu yana kallo.
Haka Momy ta kwana da bacin ran abunda ya faru ta tashi da shi, Daddy kan dariya kawai yake mata daman haka yake mata idan ta saka kanta a wani abun at the end kuma be yi kyau ba, sai dai bata fadawa Daddy kudirin na na aurawa Ataa Aliyu ba, domin ta san ba zai zabi Aliyu ya bar Muhseen ba, duk kuwa da kasancewar be san Muhseen na son Ataa ba, bayan maganar tafiya Abuja da suka aje jibi babu wata maganada ta sake masa.Lokacin data dawo part dinta bakwai da kwata ne na safe, sai da ta fara shiga kitchen ta kunna gas ta dora ruwan zafi sannan ya fito falon tana dauke da dankalin turawa ta shiga dakin Siyama, sai ta same ta zaune tana home work din da bata samu yi jiya da dare ba.
“Momy ina kwana?”
“Lafiya kalau rubutu kike?”
“Eh homework ne da ban yi ba jiya”
“Okay ba ri na kaiwa Husna ta gyara min dankalin”
Ta fada tana juyawa ta fice daga dakin Siyama zuwa na Husna, ita ma zaune ta sameta sai dai waya take tabawa, tana ganin Momy tai saurin saukowa daga saman gadon da kayan bachinta ta karbi robar hannun Momy.
“Momy ina kwana?”
“Lafiya kalau kin tashi lafiya”
“Lafiya kalau? Ya bacin rai?”
“Ba zai gushe ba ai sai na cika burina, kar wannan maganar ta fita ki barta tsakanina da ke ko Amina bana son ta ji”
“In-Sha-Allah Momy”
“Idan kin gyara dankalin ki kawo kin kitchen, kuma kin san bana son kazanta ki fito waje ki gyara ba a daki ba”
Momy ta juya ta fice daga dakin Husna, da kanta ta shiga dakin Amina ta taso daga guntun bachin data fara na safe.
“Amina ta so muje kitchen ki min wanke wanke”
“Tau”
Ta fada tana sauko daga kan gadon sanye da doruwar rigarta, Momy na gaba Amina na baya har suka shiga kitchen din, sai da ta soma hada kayan wanke wanke ta tana wankewa Momy kuma na shirya abun karin kumallo ta ce mata.
“Amina Muhseen fa ta fadawa Daddy ku wai a tambaya masa ke idan kina son sa?”Amina ta ji abun wani banbaragwai. ta tambaya har tana nuna kanta
“Ni...?”
“Ke fa”
“Ya Muhseen ba Ataa yake so ba?”
“Nima haka nai zato, yace idan zan je yi ma Abbahsu murna na wuce masa da sako”
“Yaushe za ki je?”
“Jibi shiyasa na ke son jin ta bakinki tun yanzu, idan ma tunani da shawara za ki yi sai ki yi kamin na tashi”
Dariya Amina tai domin sam bata dauka da gaske Momy take ba.
“So dai suke ku hada mu Momy, amman Ya Muhseen ai Ataa yake so”
“Karya zan miki kenan?”
Amina bata sake cewa komai ba bayan dariyar da tai.
ATAA POV.
Da wani kallon haushi na bi Aliyu bans an dalilin son nuna isa da yake min ba, abunda yake min ko kanensa baya yana ma haka, domin su ai suna wayar be taba hana su ba sai ni. Haka na tashu ta tunzure bakina na tafi bq din mu na zauna bakin kofar dakin da Nana take ciki kwance, ina ta jin haushin karbe wayar da Aliyu yai domin ban gama waya da Muhseen ba, kuma ina son idan mun kai karshe na tambaye ko yana da labarin Kamal amman wannan bakin Aliyu ya zo ya karbe wayar.
Bayan sallah isha'i Siyama ta kawo mana abinci a wata kula da plates mai kyau, tuwon shimkafa ne da niyar ganye ban wani ci sosai ba amman Nana ta ci shi sosai har sai da ta rasa masokar tsintsiya a cikinta. A katifa daya muka kwanta, kasancewar yarwantacciyar katifa ce ba kamar gadon asibiti ba da iya mutum daya yake dauka, katifar mai fadi ce sosai amman na matse bayan Nana na kwanta jikinta kamar zan tsaga bayanta na shige ciki, nai bachina cikin kwanciyar hankali har safe.
Bayan mun gama sallah Nana ta ce shiga bangaren Momy na taya ta aiki, ni kuma ban shiga ba sai da rana ta fito domin a tunani ba su farka ba a wannan lokacin duk kuwa da na san suna tashi sallah asuba amman ai suna komawa. Har na fita haka sai kuma na dawo na dauki Hijab na saka gudun kar na hadu da Aliyu ya sake min masifar ban saka Hijab ba, ko da na shiga part din a samu Momy a kitchen Amina kuma tana zaune falo rike da remote tana kallon tv sai dai kana ganinta kasan hankalinta ba a gurin tv yake ba. Sai da na gaishe ta sai na sannan na nufi kitchen din dan gaishe da Momy sai na same ta tana waya, da alama da Mama Fulani take wayar domin na lura tana cikin far'a har ma tana fadin jibi za mu zo, sai da ta gaka wayar ta sauke sannan na gaishe ta amsa, na nufi inda kofar bayan kitchen din take dan dauko tsintsiya na ce.
“Momy Abuja za ki je?”
“Eh jibi In-Sha-Allah ko za ki je?”
“Eh Momy”
“To ki shirya da wuri yata”
“To na