Showing 75001 words to 78000 words out of 225640 words

Chapter 26 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

ta isa ta saka wani abu ya faru, domin ita wacan da aka cirewa ba mu san halin da take ciki ba....”

“What if na bata hakuri?”

Nasir yai saurin tarar numfashinsa.

“Karka tinkareta kai tsaye yanzu tun tuni ya kamata kai wannan kuma ba kai ba”

“No baka san yadda nake ji ba ne a yanzu Nasir, bana son na rasa Rahma”

“Ai ba cewa akai zaka rasa ta ba, amma
...”

“No hakuri zan bata Nasir”

Ya fada yana jan murfin motarsa ya rufe. Cikin saurin Nasir ya nufi tashi motar ya shiga ya bi bayan Aliyu.




ATAA POV.

Na tashi da safe da zazzabi da kuma rashin kuzari, dukan abunda ya faru jiya sai ya zame min kamar mafarki ciki kuwa har da maganar da Muhseen yai min. Bayan na gabatar da sallah asuba na dauki jakata na nufi garden na shanya duka kayana da suka jike sannan na shiga part din Mama Fulani na fara gyara falon, na nufi dakin Ammy na gyara mata nata falon, ina cikin saka air freshener na ji tana fadin

“Jiya ba ki dawo karbar abincin dare ba, ko da mun fita asibiti amman ni da wuri na dawo saboda Alhaji”

Abubuwa ne suka zo min a rai, zancen Alhaji na san tana da mijin da suke taraiya ita da Mama Fulani domin wani lokacin ina ganin yadda suke kokarin shirya abincin ko wani abunda ya ke nuna mijinsu suke yi ma amman ban taba jin zancensa a bakinsu ba, haka ma a gurin yayansa, ban taba cin karo da shi ba, fitar da shigowarshi duka ban taba gani ba, da wace motar yake fita ko yake shigo cikin gidan ban taba sani ba. Sai kuma zancen zuwa asibiti waye ba lafiya? Kamar ta san abunda na ke sakawa a raina sai na ji ta ce.

“Matar Aliyu ciwon ya tashi Wallahi”

Da sauri na kalleta.

“Miya ke damunta?”

“Wai ciwon koda ne daman tun tana karama haka take har ta girma, to sai daga bayan kododin duka biyu suka lalace, daker aka samu wata aka siya aka saka mata a waje, yanzu kuma wai kodar ta kone, Wallahi ni yarinyar har tausayi take ba ni wannan jarabawar rayuwa”

Wani yanayin na ji, shi ba dadi ba shi kuma na bakinciki ba, a take na girmama Allah a zuciyata lallai sakamakon zalinci ba mai kyau ba ne, koda ta kone abunda ban taba ji ba, sai dai na ji ance ta lalace amman wani iko na Allah yau na ji ance ta kone, lallai Allah ba azzalumin kowa ba ne.

“Lafiya?”

Ta tambaya ashe kallonta nake ta yi tun dazu ni ban ma sani ba. Har na bude baki nai magana sai muka ga an turo kofar falon an shigo, Kamal ne fuskarsa dauke da murmushi yana sanye da uniform din sojoji sun matukar karbarsa abun ka da dogon mutum sai yai kyau da kakin kamar yadda na ganshi a wacan karon. Ledar jiya ce a hannunsa kai tsaye ya nufo inda nake yana gaisawa da Ammy da alama ya saba shigowa gidan, domin ita ma naji tana masa korafin ya daina zuwa kwana biyu kamar yadda Mama Fulani ma na ji tana masa.

“Wallahi aiki ne yai min yawa, yanzu ma kaduna zan je da safen nan sakon kawai zan bawa ba Mamar nan taki”

Kallonsa kawai Ammy take har ya karaso kusa da ni ya mika min ledar.

“Ga kayanki nan”

Tsayawa nai kallon ledar kamar mai shawarar karba, sai ya aje min ita kasa yana kallon agogon hannunsa.

“Zaki bata min lokaci ko? Na shiga can a aka ce kina nan”

Juyawa yai ya nufi kofa yana yi ma Ammy sallama da kallo na bishi har ya fice sannan Ammy ta kalleni tana dariya ta ce

“Ina kika san Kamal?”

“Ranar na fit gate shine ya kira na ce masa nan nake, sai kuma da muka fita da Anty Rukaiya shine ya ce na raka shi mu yi siyayya”

“Ok shine ya kawo miki na ki tsara? Tooo lallai yarinyar nan ashe ko ko zai janyo miki rigimar Maryam, saurayinta ne fa”

Na wara ido.

“Da gaske?”

“Eh yana dan zuwa gurinta can ba a rasa ba, yau kuma ya dawo gurinki? Oh Maza akwai iya son mata”

Ta fada tana dariya ni kuma na nufi inda na dauko turaren na aje sannan na dawo na duka na dauki ledar na fito daga part din na nufo gareji ban tsaya duba komai ba aje kawai nai na dawo part din Mama Fulani dan karasa gyaran kamar yadda na saba, ko da na shiga ita da yayanta suna dinning suna karyawa, fuskar Anty Maryam ta kumbura sosai har gurin idonta daya ya rufe bata iya gani da kyau da shi, wata kila marinta Aliyu yai ta yi ko kuma wani abun ya buga mata a fuska oho, ni dai kallo daya nai mata na dauke kaina na shiga dakunansu na gyara ko'ina na wanke bandakunan sannan saka turare Awwaba na fito na sauko kasa.

“Zo ga abincinki ki dauka”

Ya Muhseen ya fada yana aje min plate din a gefen taburin. Sai da na karasa kusa da shi sannan ya kalleni

“Ya jikinki? Na manta jiya ban saka miki kada ba amman ai baya jini ko?”

“Eh ba ya yi”

Na amsa shi jikina nata rawa domin na lura da yadda Mama Fulani take watsawa Muhseen harara shi kuma be ma gani ba, gaba daya hankalinsa yana gurina, da sauri na karbi abinci naje na zube a plate dina na kawo masa sannan na dawo garejin na zauna ina cin abincin ina duba kayan da ke ledar, kayan da ya siya min ne jaya turare da auduwar mata da man goge baki sai kuma chocolate da biscuit mai madara. Ina jin lokacin da motoci har biyu suka tsaya a harabar gidan, ni dai ban leko ba domin ban damu na san ko suwaye suka zo ba, a cikin jaka ta na saka man goge bakin da sauran kayan biscuit din kuma na aje shi a saman katifa ta da zimmar idan na dawo na ci, sai na dauki plate din da cup na nufi garden dan wankewa, ina cikin wakewa na ji kamshin turaren Aliyu da sauri na waigo sai na ganshi tsaye yana ta kallona cikin yanayin da ke nuna yana cikin tsananin damuwa. Ni ma tsayen nai ina ta jiran na ji idan wani abun zai ce min amman be ce komai ba, ganin hakan yasa na juya na cigaba da wanke plate din sai na ji motsinsa a bayana daf da ni. Mikewa nai tsaye ina kallonsa, sai ya bude ba ki kamar zai yi magana sai kuma ya kasa cewa komai. Daukar plate din nai zan wuce sai ya kira sunana.

“Ataa... ”

Sai na tsaya a tunanina wani abun zai ce na masa, sai kuma yai shiru be ce komai ba ya kawarda fuskarsa yana hade yawu, da alama wasu kalmomin yake hadawa ko kuma yana saka abunda zai ce min ne.

“Matata Rahma bata da lafiya.... ”

Sai kuma yai shiru ya dawo da dubansa a kaina.

“Ataa na san ba a kyauta miki ba am.... ”

“Sai yanzu ka sani? Saboda kodar matarka ta kone ko? So kake a sake cire ta mahaifiya a saka mata?”

Ya girgiza min kai alamar aa.

“So na ke na baki hakuri”

“Kana tunanin Hakuri zai canja zalincin da aka min ne? Kana tunanin hakuri zai saka Rahma ta tashi a take ne? Ko kuma kana tsoro kar matarka ta tafi ta barka ne ka dandana zafin rashi kamar yadda na dandana na rashin dan'uwana saboda kai? Ko tsoron jinya kake kamar yadda nai ta mahaifiyata? Har ka fara tsorata da abunda ya samu matarka tun yanzu? Likitoci sun fada maka zata rayu ko ba zata rayu ba? Ai kana da kudi sai mu gani idan kudinka za su tare mata mutuwa, ko kuma za su sama mata lafiya a take, ko da yake za ku iya neman wani talakan marar gata irina ku cire masa kodar ku saka mata ita ta rayu”

Duk abunda na ke fada masa be ce min komai ba, wani abun mamaki sai ma cika da idonsa sukai da kwalla. Wani mutum ne ya shigo garden din wanda ba zai wuce sa'ar Aliyu ba ya karaso kusa da inda muke tsaye yana ta kallo.

“Ke ce Ataa?”

Na kalleshi

“Wani ya baka labarina ne?”

Sai ya kalli Aliyu ya sake kallona.

“Sunana Nasir ni abokin Aliyu ne kuma Aliyu ya fada min komai akanki, Ataa mun san an zalince amman....”

“Amman me? Amman ba ku gane ba sai yanzu? Ya kasa jure abunda ya same shi ko? Ni na jure jinyar mahaifyarta da kallon halin da take ciki har na tsawon wata daya da wani abu a asibiti, kullum ina ta zullumi zata mutu ko ta rayu? Ban sani ba, yanzu haka mahaifiyata tana can gida na baro ta na zo nan aiki saboda na sama mata kudin magani, wata kila ko da zan koma ta mutu, ko kuma rashin lafiyar ta kara tsanani, tun da na baro garin ban sake jin muryarta sai dai idan na kwanta nai mafarkinta? Saboda abunda mutanen nan suka min, har yau bata san cewa an cire mata koda ba, da wane ido zan kalleta na fada mata? Su wa zan ce suka cire mata? Har yau mahaifiyata bata san gaskiyar ciwonta ba bata san komai a kai ba, kun jefa rayuwata cikin damuwa da bakinciki, amman duk ba ku gane ba sai yanzu da Allah ya jarraba Rahma na dan lokaci, sai ka kasa jurewa? Miye amfanin zuwa da kukai a nan? Na yafe muku? Ko kuma na fada muku Rahma ba Zata mutu ba? Kun cutar da ni Wallahi babu wani dadi bakin da za ku min na yarda da ku, za ku iya cilata ni yin komai saboda ina talaka amman ban da yafiya, ba zan taba yafewa ba.... ”

Na karasa cikin kukan dana fara tun dazu sannan na nufi hanyar fita dGa garden din har bana iya gani da kyau saboda hawayen da suke min zuba.
ZAKI

By Khadeeja Candy

26...


Duk kokarin Kamal na rike ta kar ta kai kasa be saka ya iya taro ta ba har sai da ta kai kasan, be san abunda ya faru ba amman tabbas ya ji karan mari a lokacin da ya kawo bakin kofar falon da zimmar shigowa kawo ma Ataa tsarabarta. Gaba daya falon yai tsif Husnat da Siyama suna ta mamakin zafin rai irin na Fulani, Maryam da Rukaiya kam abun dadi yai musu daman ko su ne za su iya yi mata haka, sai dai suna tsiron kar Aliyu yai musu ba dadi amman idan Mama Fulani ce babu abunda zai yi. Momy ta girgiza kai tana kallon Ataa cike da tausayawa domin ta san ba lallai sai ta yi ma Mama Fulani wani babban abu zata yi mata irin wannan dukan ba, tasan halinta sarai tana da zafin hannu a wajen yayan wasu ban da yayanta, ita kam nata yayan baka isa ko yatsa ka nuna musu ba balle ka ce za ka dake su.

“Mi tai miki kika mata wannan irin marin? Ta suma fa”

Jin hakan yasa Kamal ya dago daga kokarin rika Ataa da yake ya kalli Mama Fulani cikin bacin rai.

“Ba lallai sai ta yi mata wani abu ba, ai zalinci ne zata iya dukanta tun da ba Maryam ba ce ko Rukaiya, waya isa ya taba Baby ma da take karama a cikin yayanki amman kin iya duka wata saboda ba ke kika haife ta ba”

Da mugun mamaki Mama Fulani da Rukaiya kai har Momy suke kallon Kamal jin abunda ya fito daga bakinsa, Mama Fulani ta nuna kanta tana kallon Kamal

“Kamal ni kake fadawa wannan maganar? Ni Fulani?”

“An fada miki ko nima dukana za ki yi?”

“Kai Kamal karka kuskura ka ce...”

Maryam bata karasa ba ya daga mata hannu yana daka matsa tsawa.

“Yi min shiru shashashar yarinya, ba ku iya komai ba sai bakin girman kai da zalinci haka kawai ku saka karamar yarinya a gaba kuna azzabtar da ita saboda kawai tana karkashinku, babu wanda zai baro iyayensa ya zo karkashin wani ya tare yana musu aiki sai da babban dalili ba ku san abunda ya rabota da iyayenta ba amman kun saka ta gaba kuna mata wulakanci kala kala son ranku, ku ku yi mata mahaifiyarku tai mata arziki hauka ne? Shikenan ku mutum idan ba shi da kudi ba shi da daraja a gurinku? Wannan wace irin rayuwa ce?”

Momy ta ce.

“Kamal be dace ka shigo har cikin gidansu abokin ka ba ka fadawa mahafiyarsa irin wadannan kalaman sam be da ce ba”

Kamal ya kalleta

“Ko ke kikai ba daidai ba dole na fada miki gaskiya balle kuma ita da ba haihuwarsa tai ba, sai mummunar akida da ta saka masa na rashin ganin kan kowa da gashi”

“Yar aikin mu ce dan haka duk yadda muka ga dama haka za mu yi da ita, babu uban da ya isa ya hana idan kuma a akwai sai yai na gani, ai ban san ka isa da ita ba har sai ka dauke ta daga gidan nan ko kuma ka rama mata marin da aka mata, sai na san na isa da ita ko kuma na san zumuncin uwa kuka hada ko na uba”

Cewar Rukaiya tana wani irin marmadi kamar zata matsa kusa da shi ta dake shi.

“Zumunci musulunci muka hada wanda ya fi na jini, kuma zan nuna miki na isa da ita, kuma zan nuna miki ita ma tana da gata kamar ke”

“Ba dai kamar ni ba Wallahi, karyar makaskanciya irinta Wallahi abun kunya kana son yar aikin gidan abokinka kuma budurwarka tirr Wallahi”

“Ke ce makaskanciya ke da baki san darajar dan adam ba, kuma ni ban taba cewa ina son Maryam ba, duk zuwan da nake gidan nan ina kiranta mu gaisa ban taba cewa ina son ta ba, gata a nan tsaye idan na taba fada mata cewar ina son ta sai ta fada, kuma na gode Allah da ban taba furtawa ba, domin yanzu na gane irin tarbiyarku ba kuma za a je a tarbiyantar min da yaya haka ba, a gurinki yake abun kunya son yar aiki, a gurina abun alfahari ne ko ba komai zan zama mutum na farko da zan fara jiyar da ita dadin rayuwa, kuma zan auri mace mai tarbiya ba irinku ba”

Kamal na aje numfashi Muhseen dake sauko daga upstairs ya dauka yana yatsina masa fuska.

“Kai ne marar tarbiya marar hankali wawa wanda be san darajar na gaba da shi ba, ban da rainin wayo da rashin kunya ka isa ka shigo har cikin gidan nan ka ce zaka fadawa Mama maganar banza, waye kai a duk fadin Abuja? Kai kana da tarbiyar ne zaka nemi fada mata magana son ranka? Ko kuma saboda baka san darajar iyayenka ba shiyasa baka ganin kimar uwar kowa a duniya, kai ne baka da tarbiya kuma ba san inda ta fito ba, domin mu ba za mu iya ciwa uwar wani mutunci ba, amman kai zaka iya dan tsabar rainin wayo, ina ruwanka da yar aikin gidanmu? Ubanta ne kai? Ko yayanta? Sakare kawai mahaukaci daman sojoji ba ku iya komai ba sai hauka da fitsara”

Kamal ya tabe baki.

“Ka fadi duk abunda yai maka dadi a baki, ban yi mamaki ba ai kai ma dan wajen Fulani ne ko? No wonder”

Yana fadar hakan ya duka ya dauki Ataa da take sume tare da ledar da zo da ita ya juya zai fita sai Muhseen ya nufo shi da sauri.

“Karka kuskura ka ce zaka fita da ita, ko yankata Mama tai ba zaka fita da ita ba”

“Mutuwa ce kawai zata dauke ni a yanzu na fasa kai Ataa asibiti amman ba kai ba balle wani naka”

Ya fice da ita, Muhseen zai bi bayansa Momy tai saurin rike masa riga.

“Karka je Muhseen kyale shi duk inda zai kaita ai dawowa za tai saboda nan aka kawo ta, kar kuje kuna abu kamar yara ka ka taushe fushinka dan Allah”

Muhseen baya iya musawa Momy dan haka ya hakura ya zauna a kujerar jikinsa nata rawa kamar yadda zuciyarsa take yi. Mama Fulani kuma tana tsaye a gurin ta kasa cewa komai gaba daya mamaki ne ya kasheta domin a rayuwarta bata taba samun mutumen da ya iya tsawa gabanta ya ci mata mutunci kamar Kamal ba, cin mutunci ma a gaban yayanta, ita zai fadawa Maryam bata da tarbiya and be taba son ta ba.

“Ni za a ciwa mutumcin a cikin gidana? Ni Kamal zai fadawa magana son ransa? Mi yake takama da shi dukiya ko aiki? To ya jira abunda zai same shi, ita kuma bar ta dawo”

Mama Fulani na rufe baki Zee ta shigo dakin tare da Inteesar dauke da manyan kuloli, suna kallon yanayin mutanen falon sun san akwai abunda ya faru sai dai ba zasu iya gane ko minene ba. A gaban Momy suka dire kulolin sai Mama Fulani ta daka musu tsawa.

“Ke Zainab ku dauke abincin ku maida wai ba na ce Ammy ta daina min shisshige akan bakina ba? An fada mata ban musu abinci ba ne ko?”

Zee ta dago ta kalleta tana kokarin danna fushinta.

“Na ga ai kamar ba bakinki ba ne bakin Abbah ne”

Muhseen ya zaburo mata.

“To rashin kunya za ki mata ko? Ban ballaki Wallahi”

“Ba rashin kunya ba ne Ya Muhseen magana ce kawai”

Ta bashi amsa tana kallonsa.

“Dauki abincin ki fice da shi aka ce”

Muhseen ya fada sai Momy ta dakatar da shi.

“Aa ku aka kawo wa abinci? Ai ni aka kawowa ina ruwanki, Ke tashi ki tafi Zainab ki ce na gode”

A tare suka mike tsaye Inteesar da Zainab suka fice...            Momy ta kalli Mama Fulani cikin yanayin damuwa ta ce.

“Wallahi ni dai bana son halin nan na ki Fulani, miye a ciki dan ta dauko abinci ta kawo min Fisabilillahi?”

“Shishhigi ne da ita kuma na fada mata bana son haka, ni da gidana wani zai min ba daidai ba?”

“Amman ke ma ai ba gurinki na zo ba, ganin matar danki kawai na zo kuma gobe zamu koma, ni rigimar nan taku ban san ranar da zata kare ba, Siyama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login