Showing 225001 words to 225640 words out of 225640 words
karatu ba ko da yake ina da burin aikin sai dai na san Hubby ba zai bar ni ba. Na canja daga burina na karatun likita zuwa na gadon gidan mu wanda Mai Martaba yake son kowa yai saboda yin aiki a karkashinsa da kuma sanin ilmi akan kasuwanci da yadda zaka iya tafiyar da shi yadda ya dace. Al-hamdulillah ko a haka rayuwata ta kare ba tare da na yi aikin da Hubby baya son nai na samu abunda na ke kuma na gode Allah na, wata kila a gaba ya canja ra'ayinsa ya bar ni na cigaba da karatun wata kila kuma ba zai yarda ba, daman kuma ba duka buri ne yake cika ba, ba komai ake nema a samu ba, ba kuma duk a abunda kake so ne alheri a gurinka ba, sai dai ba zan kasa gode masa ba akan dukan kulawa da goyon bayan da ya bani har na samu cikar burina da ba ni damar amsa sunana AISHA UMAR MRS ALIYU MUHAMMAD.
*AL-HAMDULILLAH*
Dukan yabo da godiya su tabbata ga Allah mai kowa mai komai wanda ya ba ni ikon rubuta littafin mai suna Z A K I da kuma kareshi cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Na sadaukar da wannan littafin a gareki Mama Aisha Kabir A A Ladan.
Godiya ga dukan masoyana waenda suke cikin paid groups, na gode sosai da irin kaunarku a gareni Allah bar kauna. Waenda suka karanta ba su biya ba kuma na bi ku bashi indai hakkina ne.
Sai mun hade da ku a littafi na gaba idan mai rai da lafiya ya yarda. Ba littafi ne irin na yau da kullum ba littafi ne da zai tabo wani bangare na rayuwar wasu mutane da kuma wata macen da kaddara ta fada mata.
Ba kaddarar talauci ba ce kamar ta Ataa (Zaki)
Ba kaddarar Aure ba ce kamar ta Nawwara (Rai Biyu)
Ba kaddarar soyayya ba ce kamar ta Zinneera (Zabin Rai)
Ba kaddarar gudun iyaye ba ne kamar na Namra (Zagon Kasa)
Ba kaddarar asiri ba ne kamar na Hafsatu Manga (Hafsatu Manga yarinyar kauye)
Ba kaddarar rashin uba na gari ba ne kamar na Jodo (Khadijatu)
Ba kaddarar Ciwo ba ne kamar an Minal (Babban Goro)
Ba kaddarar kauyanci ba ne kamar na Maryam (MAIRO)
Kaddara ce dai wata ta dabam, wata kalar kaddara ce bata rashin gata ko ilmi ba ba kuma ta shashanci ko wauta ba. Labari ne tafe da rayuwar wasu mayu, da suke cikin wata alkarya.
Labari ne mai maida mace namiji ba, namiji a siffa da kamani, namiji a zuciya da jini.
Labarina na wata duniya biyu mai cike da abun mamaki da al'aji, labari mai hada Kasar Katsina da Bauchi a wata hadaka ta ba zata. FULANI labari na daman na Fulanin asali❤
*Daga yar Mutanen turankawa Fulanin kwarai, jinin Shehu Khadeeja Candy ce👌Yar mutane sakkwatawa*
AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.