Showing 126001 words to 129000 words out of 225640 words
gode”
Wani irin dadi ne ya lullube ni, babu wanda na kawo a rai na sai Kamal, zan jure wulakanci Mama Fulani tun da da Momy za mu je kuma saboda Kamal zan je, haka na share gidan tsaf cikin nishadi, a dayan bangaren kuma ina tsoron kar Aliyu ya zo ya hana ko kuma ya iya zama tafiyar mai dadewa cewa ba zai yi naje na bar Nana ba, sai idan tafiyar kwana biyu ce.
**ZAKI
By Khadeeja Candy
38...
Juyi yake ta yi akan gadon idonsa biyu ba dan yana jin bachi ba sai dan kishin da ke tare da shi, lips din bakinsa ya ke cizo kamin ya unkura ya tashi zaune yana shafa kansa. Short and white ves ne a jikinsa ya samu minti goma a haka sannan ya mike tsaye ya ware red curtains din dakin, ya bude class windows din haske ya shigo sai ya juya yana kallon bed dinsa. Sai kuma ya nufi kofar fita daga bedroom din, kasa ya sauko kai tsaye ya nufi kitchen ya kunna electric kettle ya dauko wani kofin ya matsa lemun tsaki da kanwa a ciki, ruwan zafin na tafasa ya zuba a cikin kofi ya bar shi a haka ya dauki wani kofin ya hada Lipton da suga kadan, sai da ya jira lemun tsamin da kamwar sun dan huce sannan ya dauka ya sha ya dora da ruwan Lipton din. Freezer ya bude ya dauko kankara a gorar ruwan faro ya dawo bedroom dinsa ya shiga bathroom ya fashe kankanrar ya zuba a cikin bokiti ya sirka da wasu ruwan ma su dan dumi yai wankan da ruwa mai sanyi sosai sannan ya fito daure da tawul yana jin ya samu relief. Be dauki minti talatin ba tsakanin shafa mai da saka tufafinsa wani irin kuzari yake ji sosai, kamar ba shi ne ya kwana a gado jiya kamar marar lafiya ba. Maroon shirt ya saka da white jean colar shirt din ta karbi jikinsa sosai ta kara fito da farinsa da kuma kyan fuskarsa, haka ya firo harabar gidan fuskarsa har ya wani annuri take. Tun kan ya karasa gurin motar ya danna keys din hannunaa yai kara hakan ya hankaltar da mai gadinsa yai saurin isa gate ya bude masa tun kan ya tashi motar. Yana shiga yai mata key ya dauki hanyar arkilla wato gidan Momy, daman ba shi da gidan zuwa sai can ko lokacin da Rahma take nan balle yanzu da bata nan. Sau daya ya danna horn mai gadin ya bude masa gate, kusa da inda Ataa take zaune tana gyaran doya ya faka motarsa, zaunawarsa yai a motar yana ta kallonta ta cikin gilashin motar, ita ma kallon bakin gilashin motar take ba dan ta san wanda ke ciki ba, sai dan yau murna take Momy tace zata je da ita Abuja, murmushi kawai take abinta kana ganinta kasan tana cikin farinciki sosai. Ya dade yana ta kallonta kallonta na burge musamman idan shi kadai yake kallon nata ba tare da ita din tana kallonsa ba, domin yana tsarguwa idan tana kallonsa. Samun kansa yai da murmushi ganin murmushi a fuskarta duk kuwa da be san silar farincikin nata ba, but seriously ta burge shi and he like her smile more than everything yanzu, bude motar yai ya fito har ya rufe ita yake kallo ita kuma sai murmushi take mishi har da wani.
“Laaa kai ne? Ina kwana?”
Be amsa ta ba ya nufi bq yana ta mamakin dalilin farincikin nata ko mi akai mata take wannan far'a oho. Ko davya shiga Bq Nana na zaune balcony tana kallon itacen guava dake kusa da bq din, har kasa Aliyu ya risina ya gaishe da ita yana wani kasa da kai kamar mai jin kunya.
“Ina kwana?”
“Lafiya Kalau, ke tashi lafiya?”
“Lafiya kalau ya jikin na ki”
“Al-hamdulillah, Allah ya saka da alheri mun gode mun gode sosai”
“Ba komai, idan dai kina bukatar wani abun ko kuma kinji wani abun sai ki yi magana”
“Yayi kyau ba matsala In-Sha-Allah, Allah ya biya”
Ta fada da murmushi a fuskarta har ga Allah Aliyu yana burgeta yadda yake hidima da ita da kuma irin kulawar da yake nuna mata tana jindadi sosai, wani karin abun farinciki ma da Ataa ta fada mata har jininsa ya bada aka saka mata sai ta ji kamar ta dauki zane ta goya shi a bayanta.Ya fito bq din yana wasa da bq din hannunsa yana murmushi, at least now na durkusa har kasa ya gaishe da Nana bayan gaisuwar da ya taba mata a asibiti da risinawa, abun ya burgeshi shi kanshi ya ji kanshi a wani mutum daban. Murmushi da Ataa ta gani a fuskarsa lokacin da ya fito bq ne yasa ta kyalkyale da dariya for no reason tana kallonsa, kallonta yai har sai zai wuce ya shiga falon Momy sai kuma ya ji ba zai iya ba sai ya ji dalilin wannan farincikin da Ataa take yi. Karasowa yai kusa da ita ya tsaya a akanta ita kuma ya daga kanta sama tana kallon still murmushi a fuskarta.
“Mi akai miki kike dariya?”
“Ba komai”
“Ba koma kike jindadi?”
“Momy ce ta ce zata je da ni Abuja, kwana biyu zata yi ta dawo”
Yasan Mama Fulani bata son Ataa kuma ta yi ta gana mata zaba ita da yayanta, dan haka ataa ba dadin zaman dake ji a can ba, to miye abun murna dan ance za a kai ka inda ba dadi kake ji ba.
“Miye abun murna a cikin?”
“Idan na je ai zan ga Kamal ko?”
Ta fada da sigar tambaya kamin ta cigaba.
“Shine na ke jindadi ai”
Ta fada tana murmushi ba tare da ta bude hakoranta ba, wani irin abu ya ji ya daki kansa ya soki zuciyarsa yayi cikin ɓargonsa, a take ya nemi nishadin zuciyarsa da na fuskarsa ya rasa, ya wani hade rai har idonsa na canja kala.
“Ita kuma Nana ki bar ta a hannun wa?”
Ta yi shiru tana bata fuska sai ta soma yanka doyar da karfi tana jin haushin maganar da Aliyu yai a yanzu. Be sake ce mata komai ba ya nufi kofar falon ya tura ya shiga, Amina ce har yanzu zaune a falon remote a hannunta kamar dazun Husna kuma na kitchen ita da Momy.
“Ina kwana Yaya?”
“Lafiya Kalau”
Ya amsa mata kamar baya son karbawa. Tashi tai ta nufi dakinta shi kuma ya nufi kitchen.
“Ina kwana Ya Aliyu”
A takaice ya amsawa Husna yana mikawa Momy nata gaisuwar.
“Lafiya, Momy ina kwana?”
“Lafiya kalau, Husna ki hada da doya idan Ataa ta kawo”
“Okay”
Husna ta fada tana cigaba da soyan dankalin da take Momy kuma ta juyo ta fito daga kitchen din zuwa falo tare da Aliyu, yana ganin yanayin fuskarta ya sam bata cikin nishadi, sai da ta fara zaka sannan shi ma ya zauna.
“Momy ke kika ce zaki tafi da Ataa Abuja?”
“Waya fada maka?”
“Ita ta fada min yanzu”
Momy ta yi murmushi.
“Eh Daddynku ya ce Abbah ya samu mai siyen kamfanin nan an har siye kuma an biya kudi za a cigaba da komai karkashinsa, ni ban ma sani ba sai jiya shine yake cewa ya kamata muje mu masa murna ko da shi be samu zuwa ba, to ta shigo ta tarar ina waya da Fulani ta ji zancen zuwa Abuja shine ta ce tana son za ta bi ni”
“Karki je da ita Momy”
“Saboda me?”
“Mahaifiyarta wa za ta barwa ita? Kuma ko tafiya kika yi da ita Muhseen daukarta kawai zai yi yayi ta yawo da ita”
“Wannan ai ba hujja ba ce, daga ni sai Husna zan je sai kuma ita, Amina da Siyama ai za su iya kula da Nana, tun da zata iya kai kanka bandaki ta fito da kanka”
“Momy karki je da ita dan Allah, Wallahi saboda ta ga Kamal zata je, yarinyar nan tana son sakawa kanta soyayya da kurciyarta, Wallahi idan ba a takawa yarinyar nan burki ba zata iya lalacewa”
Momy ta yi dariya.
“Ita tace maka saboda Kamal zata je? Son Kamal din take ne?”
Yayi shiru be ce komai ba ganin Ataa ta shigo dauke da robar doyar da wuka.
“Gashi Momy”
“Kai kitchen”
Kai tsaye ta nufi kitchen din, Aliyu ya kalli Momy ya ce.
“Momy ki fada mata tun yanzu Wallahi ba zan bari taje ba”
Ban da Murmushi babu abunda Momy take har Ataa ta kai doyar ta aje ta fito rike da farce, da alama ta yanke ne.“Ataa babu zancen zuwa Abuja da ke in ji Dan wajen Fulani”
Ataa ta bata fuska sosai tana murza yatsan.
“To mi nai? Kin fasa zuwa da ni kenan?”
“To sai mum gani dai yanzu”
Momy ta tambaya tana kallon yadda take mursa hannun nata. Ban da kallon ta babu abunda Aliyu yake ban da kallonta ya lura da yadda take murza hannun.
“Mu ga hannun”
Kamar jira take yana cewa haka ta maida hannayen nata duka baya ta turo bako idonsa na cika ta kwalla ta nufi kofar fita, sai da ta lura da idon Momy basa kanta sannan ta murguda masa baki hawaye na sauko mata, a maimakon ya ji haushi sai ta yi mugun burgeshi har yayi murmushi ya maida fuskarsa gurin Momy wacce ta dauko masa wani zance.
“Jiya an fada min ba dadi a gidansu Rahma, ta yi min gorin haihuwar wai baka haihuwa shiyasa kake dawainiya da Rahma, kuma wai Rahma ba zata koma ba sai nan da wani lokaci”
“Miya kawo haka?”
A nan Momy ta labarta masa komai car ciki har da zancen Ataa da mahaifiyar Rahma tai, sosai ran Aliyu ya bace duk wani abun da mace take masa yana shayewa ya kyale amman ban da taba masa family ko da kuwa kannensa ba sam baya daukar wannan balle kuma har ace Momy da kanta.
“Kin fada musu gaskiya Momy, Wallahi ko Rahma kadai ta rage a gidan nan ba zan je bikonta ba, ganin damar ta ce tasa ta tafi ba dan an mata wani abun ba, and zan nunawa Rahma ko waye ni”
“Bana son ka mata komai, bana son ka ce mata komai ko ka nuna mata damuwarka, abunda na ke so kawai ka bata mamaki, ka tabbar min da alkawarin da mai musu kuma ka cika min burina na abunda nai niyar hadawa”
Kallon rashin fahimta ya yi mata.
“Kamar ya?”
“So na ke ka kara aure...!”
Shiru yai for a while maganar Momya ta masa nauyi duk kuwa da shi kansa ya san yana bukatar auren, amman wa zai aura? Shi kwata kwata be taba kawo zancen zama da mace biyu a rayuwarsa ba, but if wannan hanyar ce zata saka Momy ta huce haushin abunda Mahaifiyar Rahma tai mata dole ya yi, ko dan ya nunawa Rahma he can live without her and to avoid zina da alfasha.“Idan karin auren ne abunda kike so consider it done, zan kara auren daman burinku kenan ke da Mama Fulani”
“Na jidadin hakan, wannan kadai zaka yi ka saka Rahma ta shiga hankalinta, kai ma kuma ka samu rayuwar da kake muradi domin sai ka auri wata ne zaka gane wacece mace wacece muna mace”
Murmushi yai ya mike tsaye ya nufi dinning.
“Zan baka sati daya ko biyu ko sama da haka ka nemo wacce kake so, ka ga sai a hade aurenku da Muhseen ma”
Momy ta fada tana binsa da kallo shi kuma ta juyo yana kallonta.
“Muhseen ya fitar da mata ne?”
“No ba Ataa yake so ba?”
“Zan dauki lokaci kamin nai auren ne?”
“Ni da na ke son ka y again and a xuiin watan nan ma”
“Amman kike cewa Muhseen ya auri Ataa yanzu? Waya ba shi ita? Yarinyar da zan saka ta a makaranta ta fara karatu yanzu ita kike cewa Muhseen ya aura?”
“Ai zata iya karatu a gidansa zai kula da ita”
“Wallahi Momy Muhseen ba zai auri Ataa ba, indai ba son jefa rayuwar yarinyar nan kike son yi ciki matsala ba, karki aura mata Muhseen ko an yi auren nan ba karko zai yi ba”
“Idan tana son sa fa?”
“Bata san sa bata san wanda take so ba, ita kanta bata san waye ita ba balle kuma ta san wa take so a haka da take, kuma Muhseen ba dan Allah yake son ta ba, kyauta ne kawai yake rudarsa kuma kin sani Mama Fulani ba zata bari ya aureta ba, lalata mata rayuwa kawai zai yi”
“Samun wanda zai auri Ataa a yanzu saboda Allah yana da Wahala ai, yarinyar da ba a san waye nata ba? Yar talakawa kamar yadda Rahma da iyayenta suka fada, kara ma Muhseen din dan kyauta kawai yake sonta wani ma neman fasikanci zai yi da ita ai kara a aurarda ita tun kamin wani ya lalata mata rayuwa domin ba wani wayo da ita ba”
“Momy wai mahaifiyarta tace miki tana son aurarda ita? Ki bar yarinyar nan ta fahimci miye duniya tukuna, dan Allah mu bar maganar nan, kuma karki da ita Abujar nan dan girman Allah Momy”
Ya karasa rai a bace gaba daya ransa ya gama baci, maganar Ataa na zuwa ganin Kamal da kuma zancen Momy ga kuma wannan maganar da wani Muhseen. Kasa cin komai ya yi a dinning din sai kallon kanensa da ke cin abincin yake domin Momy tuni ta tafi bangaren Daddy dan kai masa na shi breakfast din. Tashi yai ya fice daga falon ya dawo cikin motarsa ya zauna sannan ya kira Nasir ya labarta masa abunda ya faru. Dariya Nasir ya saka masa kamar wani mahaukaci.
“To kai yanzu miye matsalar da soyayyarta ta Muhseen?”
“Nasir ba san yadda na ke ji ba na, yarinyar nan bata sam ciwon kanta ba ba ta ma san waye ita ba, karatu ne abunda na ke son yarinyar ta samu a yanzu, that's why na kira ka samo wani mai koyarwa ya rika zuwa gida yana koya mata boko idan ta fara fahimtar komai yadda ya dace sai na kaita makaranta, islamiya kuma zan saka ta ta su Siyama”
Har yanzu Nasir dariyar Aliyu yake, ya san son Ataa yake shiyasa yake kishinta amman jin kai da kasaita ta hana shi fahimtar hakan, wata kila kuma ya fahimta kawai dai baya son nuna ne dan kar a masa dariya, irin yadda ya tsari talaka ace ta kai har ya fara son wata yar talaka.“Za a nemo wani malamin, amman ka san shekaranjiya ma Kamal din yake tambayata ta whatsapp wai ina yarinyar abokina”
“Ka rantse”
“Wallahi, har yake cewa ya san abunda yai be kyauta ba, amman wai ransa ne ya bace kuma abunda Mama Fulani tai bata kyauta ba”
“Sakaren banza har yana da baki yanzu stupid”
Nasir yayi dariya.
“Shi ma ai yana son ta ne kamar”
Tsaki Aliyu ya ja ya katse kiran yana rika sitarin motar, sannan ya lalubo number wani abokinsa wanda ya san yana fannin makaranta ya kira shi ya fada masa cewar yana son a sama masa wanda zai rika koyar da wata karatu a gida, domin ganin yake Nasir be dauki abun serious ba, and idan ba karatun ya sakawa gaba ba yana ganin kamar Momy zata iya daukarta ta bawa Muhseen amman idan ta fara karatu dole zata kyaleta.
ATAA POV.
lokacin da na bar falon da kuka na fito zuciyarta cike da jin haushi Aliyu da nasan cewar hana tafiyar zai yi da tun farko ban fada masa ba. Gurin Nana na dawo lokacin tana balcony zaune ni kuma na wuce dakin na hau kan katifa na kwanta ina ta kukana a hankali dan bana son Nana ta ji. Ina jin lokacin da Momy da kanta ta kawo mana abun karya har ta zauna kusa da Nana tana tambayar ina na ne.
“Ya sega ciki dazun ya shiga ta kwanta”
“Ko ta yi fushi ne saboda na ce ba a a Abuja da ita ba?”
“Abuja?”
“Murna za muje yi to tace zata bi mu amman yanzu Yayansu ya zo ya ce ba za a je da ita ba, wai ba zata je ta barki haka ba”
“Ataa haka yake ai wani lokacin da haurin hutsi amman nan da nan ka sauka”
Ban san abunda ya bawa Momy dariya ba har sai da tai magana bayan gama dariya.
“Ke har yanzu hausarki bata gama fitowa ba”Sai na ji Nana ma ta yi dariya ta ce.
“Da san kai baka iya hausa ba, baka ji hausa ba sai faranse sai buzanci, kadan kadan ka fara jin hausa har ka ji ka sosei sosei”
“Amman kin ga Ataa ita ta iya hausa sosai sam ba zaka ce ma tana jin buzancin ba in ba dan kammani ba.”
“Ataa ya tashi cikin hausawa, tun kuna kamba kai da babanka har ka zauna argungun har ka dawo sekoto, Ataa da Lukman mai mutuws duk ka ji hausa sosei”
“Ku yan wani gari ne Nana? Na ji kin ce kun zauna kamba?”
“Daga Agadez ka gudu doso daga doso ka zo kamba sai ka yi argugun ka yi bodinga ka yi sokoto, kana ta yawa yawa yawa kai da mai gida na mu”
Momy ta dade tana fira da Nana a nan na ji cewar a ni a kamba aka haife ni Lukman kuma a sokoto, wanda da duk ban san da hakan ba, domin ni na yi wayo ya bude ido na ganni a sokoto ne kawai kuma ban taba tambayar dalilin zuwanmu ba balle inda aka haife ni.
“To amman miya kawo ku garin nan na? Miyasa kuka baro garinku Agadaz?”
Daga wannan tambayar da Momy ta yi ma Nana ban sake jin Nana ta ce koma ba har na tsawon lokaci, can kuma na ji Nana ta ce.
“Labarinka ba se da dadi ka ji ma kunnenka, baka son kana tuna baya ba se da dadi ka ji, amman kai babban mutum ne mai kima da gima amman yanzu ba shi da amfani, ka koma kai kadai mijinka ya tafi ya barka dan ka ya tafi ya barka yanzu ka koma kai kadan sai Ataa”
“Muna tare da ke Nana, sanin wacece ke ba shi da amfani ma yanzu kuma na jidadin da aka samu Ataa ta hanyar aure, shine babban farin cikina”
Shine abunda na ji Momy ta fada kamin Nana ta dora da nata tana ɗaɗa hannunta.
“Ahhh Ataa yana da ubanta mai kyau kyau kyau kyau sosei, kai ne Ataa ta biyo ai, uban Ataa kana da kyau kana da fari kama da gasi