Showing 63001 words to 66000 words out of 225640 words

Chapter 22 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

ne Aliyu?”

“Ban sani ba, iyakar abunda na sani zan iya ajiyarsa har karshen rayuwata, kawai kasa a nemo min Doc Perry ina son magana da shi”

“Haka zaka daukarwa kanka a duk lokacin da zata je ganin wani likita sai ka samu kudi ka bashi a rufe maganar? Anya hakan zai haifar maka da da mai ido Aliyu? Idan ma kai baka son ganin iyalinka ai familynka suna so, muma kuma muna so”

“Matata tana da muhimmanci a gareni Nasir, idan ta san gaskiya ni ne zan fi shiga damuwa domin zata saka kanta a damuwa ne, kuma duk abunda nai mata zata ga na mata ba daidai ba, and kasan Mama Fulani ma zata fara damunta just like Momy daman can ba jutuwa suke da Momy ba”

“Amman wannan kawai ya isa ka kasa kanka a wannan matsalar? Kana ganin idan kai ne Rahma zata zauna da kai? No ina da Tabbacin duk yadda take son ka ba zata zauna da kai ba, shekarar ku takwas da aure Aliyu idan baka fara tunanin samun haihuwa a yanzu ba, zuwa yaushe zaka fara? Lokaci yana tafiya, a yanzu nan gaba kadan karfin ragowa zai yi ba karuwa ba, ya kamata kai tunani”

Aliyu ya tsaya cikawa bakinsa iska a lokacin daya riga Nasir shiga office din.

“Kamin na ga wasu yayan Rahma na fara gani, be kamata ace wani abun ya shiga tsakaninmu ba”

“Haihuwa ita ce shiga tsakani? Kai ba haihuwar ka akai ba?”

“Yes i mean kasan yanzu idan kowa ya gane gaskiyar Rahma zata shiga matsala ta shiga damuwa, kuma muna son junanmu ni da ita, be kamata abunda be riga ya zo ba ya saka mu damuwa”

“Ina da tabbacin da akanka ne Wallahu Rahma ba zata zauna da kai ba, zata fi son ganin gudan jininta fiye da kai, ballantana tana ganin cewar tana yar nai nera zata iya samun wani mai nera ta aura”

“Baka san yadda Rahma take so ba ne Nasir baka san so ba ne”

“Fine, idan kana son ka gane gaskiya ka daina cewa kai da ita ba ku da matsala, ka fada mata cewar kai ne mai matsalar wannan karon idan kunje tare ka biya Doc Perry ko nawa yake so ya fada mata haka, na tabbatar zaka ba ni wani labarin dabam”

Aliyu yai shiru yana nazarin kalaman Nasir. Ta wani bangaren yana ganin kamar be dace ya gwada Rahma kamar haka ba, wani bangaren na zuciyarsa kuma yana ta zugashi akan ya gwada din. Har ya bar office din be samu matsaya daya akan gwadarwa ko kin gwadarwa ba, ya sa dole zata kira shi tace mishi tana asibiti ya sameta a can a gwada lafiyarsu ta bangaren haihuwa kamar yadda ake musu a ko da yaushe, sai dai ba shi tabbaci ko Doc Perry zai yarda da hakan ba har ya aikata domin shi babban likita da kowa ya san da zamansa cikin garin Abuja, matukar kana amsa sunan mai nera to ka san Doc Perry, likita daya kware akan aikinsa kuma yake fadin gaakiya a ko da yaushe, ba iya nan kawai yake duba mutane ba har kasar waje an san da zamansa, sai dai Rahma bata taba damuwa da su je gurinsa ba, sai a yanzu da haihuwar ta fara damunta. A hanya yai sallah la'asar sannan ya isa family house gurin wato gidan Alhaji Hamza. A harabar gidan yai parking amman be fito cikin motarba ya tsaya dannen dannensa har ya hango Ataa ta fito daga Garden daga ita sai daura gaba, kirjinta a cike ga farin daya bayyana kansa a jikinta, gashin kanta a jike da alama wanka tai ko kuma ruwa ta fada, amman idan ruwa ta fada ai dole har tufafin jikinta zai jike, be taba kula da surar mace karamar yarinya kamar yadda ya kula da ta Ataa yau ba, karamar yarinya ce amman tana da abunda yake kauna a jikin mace wato breast ga yawan gashin kai, wanda ko Rahma da take babbar mace bata kaita breast ba, ga gashin kai kamar wacce akai wa dashe ya kwanta har gaban goshinta gwanin sha'awa, and every takunta jikinta motsawa yake fatarta na sheki kamar mai shafa wani kasaitaccen mai. Kasa dauke idonsa yai daga kanta har ta shige garejen ba tare da ta kula da shi ba.

“Miyasa tai wanka a Garden?”

Ya tambaya kansa cike da mamaki kamin ya tuna da cewar ai babu bandaki a garejin. Then miyasa ba a aje ta BQ ba? Ya sake tambayar kansa sai dai wannan karon a zuci yai tambayar kamin ya hade yawun bakinsa ya bude motar ya fito ya nufi part din Ammy sai da ya fara gaisawa da ita kamin ya shiga part din Mama Fulani. A falo ya samu kowa ban da Muhseen, Maryam da Rukaiya na ganinshi suka natsu sosai ko motsi kirki basa yi, cikin mutumci suka gaishe shi ya amsa musu kamar yadda ya ba fuska a daure sannan ya gaishe da Mama Fulani ita kan fuska a sake. Be yi zaman mintuna biyar ba Ataa ta shigo falon sanye da wani milk lace wanda ya kara fito da kyau sosai sam ba zaka ganta a hanya ka za ci yar talaka ce ba, lace din ya kara fito da kyauta da jan fatarta sosai ta yi mugun kyau duk da kasancewar bata shafa mai ba balle ma hoda haka ta fito naturally beautiful. Kasa dauke ido daga kanta Aliyu yai yana ta kallonta kamar yau ya fara ganin mace mai kyau, yanayin tausayin da ke fuskarsa yasa shi jin tausayinta ba tare da wani dalili ba, q nan ya lura da tabon bulalar da ke fuskarta da kuma kumburar da fuskar tai da idonta, tafiya take kamar zata fadi saboda rashin karfi na yunwar da take ji. Tana karasowa gaban Mama Fulani ta zube tana mika mata ragowar sabulun da ke hannunta.

“Gashi na gama wankin na wanke dika”

Ta fada cikin wata sautin murya daya saka tsigar Aliyu tashi.

“Je kitchen ki aje”

A nan Ataa ya hade hannayenta ta kama kafafun Mama Fulani ta rike ta fashe da kuka.

“Ki taimaka min dan girman Allah ki ba ni abinci yunwa na ke ji kamar na mutu....”

“Bata ci abinci ba?”

Aliyu ya tambaya yana kallon yadda hawaye suke sauko a idonta kamar ba gobe.

“Ai tun jiya da tai maka rashin kunyar nan ban bata abinci ba, kuma na fadawa Ammy karka bata, na sa Maryam ta zane mata jiki, kuma yau na hada ta wankinsu tun safe sai yanzu ta gama, haka zan rika mata tun da ta zabi yi ma mutane rashin kunya”

Wani irin abu yaji na rashin jindadi yana ratsa zuciyarsa a take tausayinta ya rufe shi, how old she's da za a ace tai wanki tun safe har la'asar and an a hana mata abinci kuma a saka Maryam ta dake ta duka saboda shi, a tunanin Mama Fulani rashin kunya tai masa shiyasa ta yanke mata wannan hukuncin.

“Ke zubo mata abinci”

Ya fada yana kallon Rukaiya, da sauri ta tashi ta nufi kitchen din ta zubo mata abincin a plate ta kawo sai ta tsaya gabanta.

“Tara dankwalinki a zuba miki ko kuma ki je ki dauko plate dinki”

“Bata da darajar da zata ci abinci a plate din ne? Give it to her....!”

Ya dakawa Rukaiya tsawa, da sauri ta mikawa Ataa plate din, cikin wani irin rawar jiki Ataa ta karbi plate din ta aje a gabanta ta saka hannu biyu tana cin abincin da su bata iya hakurin har ta cinye da dama ta sake debowa saboda azabar yunwar da take ji, sai dai idan ta ci da dama ta ci da hagu bata ma tsayawa tauna abincin sai dai kawai ta hade, jikinta na ta rawa sosai. Wani irin tausayinta ne ya rufe shi, ko ba komai saboda abunda akaiwa mahaifiyarta take aiki a gidan saboda ta sama mata magani kamar yadda ta fada masa, kuma sune silar ciwon mahaifiyar kusan shine silar komai ma, domin ko dukan da Mama Fulani ta saka Maryam tai mata ai saboda shi ne, iya kar abunda yake jin zai iya yi a yanzu na taimakonta ne ta samu saukin rayuwa a gidan kamin ya karkato da hankalinta har ta yarda ya taimaki mahaifiyarta ya nema mata magani.

“Mama pls karki sake horata da yunwa”

Ya fada cikin taushin murya kamin ya kalli Maryam yana mai jin haushi na rashin dalili cikin kakkausar muryar ya ce.

“Karki sake dukanta, tun da ba yar ki ba ce”

“To Ya Aliyu”

Ta amsa da sauri sannan ita da Mama Fulani sukai kallon kallo, mamaki ya gama cika su gaba dayansu. Wani bakin haushi da bacin ran abunda akai ma Ataa ya rufe shi, ga kuma tausayinta a bangare daya, yana ta kallon yadda take auna abincin a bakinta kamar wacce bata taba cinsa ba sai yau. Tsarkiwa tai ta fara tari tana ta wani abu kamar za tai amai saboda cikinta daya kulle.

“Kawo mata ruwa”

Ya fada yana kallon Maryam da mamaki ya kusa kashe a inda take zaune. Tashi tai taje ta debo mata ruwan na fonfo ta kawo mata Ataa ta saka hannu biyu ta karba.

“Na gode”

Ataa ta fada sai ta kafa bakinta ta shaye ruwan gaba daya. Tana dire kofin Sulaiman Mai ban ruwan fulawoyin gidan ya shigo da sallamarsa, aka rasa mai amsa sai Aliyu saboda kasaita kowa ganin yake ba zai iya amsa sallamar wanda yake kasa da su ba.

“Wai Kamal ya ce yana sallama da Aisha”

Aliyu ya kalleshi Mama Fulani da sai yanzu ta samu damar magana ta ce

“Aisha ko Maryam dai?”

“Aisha dai ya ce”

“Ba mu da Aisha a nan gidan”

“To”

Ya tashi da sauri ya fice, sai kuma ga shi ya dawo ya sake zubewa kasa kamar dazun.

“Ya ce wai Aisha mai aikin a nan gidan Ataa”

Mama Fulani ta kalli Ataa da bata san wainar da ake toyawa ba sai aikin aika abincin take a bakinta sannan ta kalli Sulaiman ta ce.

“Wane Kamal din wai?”

“Kamal dai soja wannan makocin mu”

“Ya ce yana kiran wannan yarinyar”

Mama Fulani ta fada tana nuna Ataa da tsananin mamaki.

“Haka dai ya ce”

“Tashi ka yi tafiyarka”

Aliyu ya fada masa sannan ya mike tsaye ya bi bayansa yana wani irin taku na kasaita da isa. Mama Fulani ta kalli Maryam.

“Wai ko dai manta sunanki yai?”

“Hmmm Wallahi ba wani mantawa kyau ne yake rudarsu, ba ki ganin wannan yarinyar kamar aljana”

Rukaiya ta fada tana kallonta, sai Mama Fulani ta kirata dan kara tantancewa.

“Ke”

Ataa ta dago ta kalleta.

“Na'am”

Mama Fulani ta kura mata ido tana ta kallonta kamin ta gyada kai.

“Eh lallai ko ba shakka”

Maryam taja tsaki.

“Shegiya mai kama da mayu, duk sai na yanke gashin kan nan”

Ataa dai bata ce musu komai ba, da ta gaji da yadda suke ta hantararta sai ta tashi ta fice daga falo dauke da plate din da cofin ruwan domin ta san Mama Fulani ba zata taba son kayan ba tun da ta yi amfani da su.



*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
ZAKI

By Khadeeja Candy

22...


Ya Muhseen ya gyara tsayuwarsa yana kallon da mugun mamaki.

“Me kake nufi? Dan iska ne ni?”

“Ko ma dan ruwa ne kai ta shafa”

Aliyu ya fada mishi sannan yai min alama da na zo na wuce da ido, komawa nai cikin na dauko mopper da tsintsinyar na fito, duk irin rashin tsoron sa da nake yanzu kan na ji tsoron yadda na ganshi na san zai iya min wani abun ko kuma wani fadan ya shiga tsakaninsa da Ya Muhseen wanda a karshe ni ce aciki domin ni za a daka. Sai da na fice sannan ya biyo ni a baya ina ta sauri kar ya cin min har na shige part din Mama Fulani, sai gashi ya shigo cikin tsannanin bacin rai.

“Mama”

Ya kwala mata kira sai gata ta fito daga kitchen din da sauri.

“Mama kar yarinyar nan ta sake shiga part din Muhseen da sunan gyara masa daki, idan a cikin kanennsa ba zai saka wata tai masa ba ya hakura da gyaran kawai”

“Cewa kikai ya miki wani annmimiya?”

Mama Fulani ta fada, nikan tuna har na fara kuka domin na san ni za a dorawa laifi.

“Bata ce ba, ni dai na ke ganin rashin dacewar hakan tun da ba muharramarsa ba ce”

Da mamaki Mama Fulani ta kalleni ta kalli Aliyu sai kuma ta kalli Muhseen da ya shigo yanzu cikin bacin rai.

“Kai wani abun ka mata?”

“Ban mata komai ba, yadda yake dan iska haka yake tunanin kowa ya ke”

“Ni ba dan iska ba ne ka fi kowa sani”

“Then why ni zan zama dan iska? Ba uwa daya ta raine mu ba? Kai baka iya kyautatawa kowa zato? A yadda kaga dama haka kake son taka mutane? Ba zai yiyu ba Wallahi idan zaka taka kowa yadda kake so a gidan nan ni kan ba zaka iya da ni ba, sai dai bakincikina na kashe ka”

Aliyu be sake cewa Muhseen komai ya zauna a sofar da ke kusa da kofar yana ta huci kamar wani zaki.

“Zan baka mamaki Aliyu kuma fadan yanzu muka fara ni da kai”

Mama Fulani ta karasa fito daga kitchen din tana girgiza kai.

“Haba Muhseen? Haba Aliyu wannan wace irin rayuwa ce”

Aliyu ya dago ya kalleta.

“Mama miye laifina dan na ce kar a barshi ya kebe da wacce ba muharramarsa ba? Yarinya mai jini a jika kamar wannan za ki turara dakinsa ace ta share?”

“Kai muharramarka ce da ka kebe da ita jiya a Gareji? Waya san abunda kai mata take kuka?”

“Muhseen....!”

Mama Fulani ta daka matsa tsawa.

“Mama ba za mu taba shiryawa da wannan mutumen ba matukar ne dauke wannan girman kan da son milkin kowa ba, ba zai yiyi yace zai juya kowa yadda yake so ba, ba a karkashinsa na ke ba, dan haka ba zai yiyu ya ce zai juyani yadda ya ke so ba”

Mikewa Aliyu ya ya fice daga falon cikin wano irin zafin rai marar misaltuwa. Mama Fulani ta nufo inda na ke tsaye zata dake ni.

“Zo nan bakar munafuka ai duk ke kika hada komai”

Sai Ya Muhseen yai saurin tsakaninmu ya tare ni.

“Karki da ke ta Mama, za ki dauki alhakinta ne kawai, ba ki iya ganin laifin Aliyu sai dai wasu, bayan kuma shi ne mai laifin, kuma Wallahi sai na bashi mamaki”

Ya fada sannan ya juyo ya kalleni.

“Wuce daga nan”

Da saurina na fice daga falon har ina tuntube kamar zan fadi, abun ka da mai shegen tsoro haka nai ta kwara ido a garejin ina ta jiran wani daga cikin yayanta ko kuma ita kanta ta zo ta dake ni amman shiru babu wanda ya zo har dare yai, ban fita karbar abinci a part din Mama Fulani ba, sai na je part din Ammy a can na ci abincin dare na sannan na dawo garejin na kwanta abuna na kwana har safe. Kamar yadda na saba da wuri na farka ina gama sallah na shiga na gyara falon Mama Fulani sannan na je part din Ammy na gyara kamar yadda na saba, bayan na gama Mama Fulani ta ce na dauko gurina aka zuba min abincina, har zan fito sai ya Muhseen ya kirani ya kara min da na shi na fito ina ta murna, a garden na zauna na cinye abuna sannan na dauki plate din naje na wanke na kawo gareji na aje. After like one hour Rukaiyah ta shigo garejin tana rike da makullin mota.

“Ke ta so muje ki riko min kaya”

Da sauri na taso na biyo bayanta a zato daga mota zan riko mata su ko kuma a cikin gida zan dauko na saka mata a mota sai na ji ta ce.

“Ki shiga gidan baya”

Juyawa nai da zimmar komawa gareji na dauko Hijab dina sai ta daka min tsawa.

“Ke ina za ki je?”

“Hijab dina zan dauko”

“Ba Hijab ba ubanki shiga mota muje”

Da sauri na nufi motar na bude na shiga daga ni sai lace dina na jiya da sai dankwali, sai da na rufe motar sannan ta shiga mazaunin direba ta tashi motar muka fice, ni dai ina zaune a baya ina ta kalle-kalle har muka isa wani katafaren shago irin wanda na ke gani a tv nan, wanda komai da komai ana saida a ciki kuma komai bangaren dabam, ni kallo ya hanani rufe motar har sai da naji an dangware ni da karfi.

“Bakauyar banza rufe min mota”

Sai na saka hannu biyu na rufe. Na bi bayanta muna ta taka dan karamin matakalin har muka isa gaban babbar kofar wacce wasu masu uniform suke budewa mutum idan zai shiga, wani dan kwando taja ta mika min shi.

“Ja wannan mu tafi duk abunda na nuna miki ki dauka”

Na saka hannu na karba ina turawa, wai ita ala dole sai ta nuna ni din yar aikin gidansu ce ta sha wani bakin gilashi a fuska tana sanye da yadi babu mayafi a jikinta, ni kuwa duk sai naji na takura da rashin mayafin duk kuwa da na lura kusan rabin matan da suke shigowa shopping din basa da mayafi kuma kowa be kula ba, duk inda muka bi kallona ake nasan wannan baya rasa nasaba da gashin kaina da nai masa tsoro daya na ya sauko har gurin mazaunaina, da kuma haskena ga kyau kamar wata balaraba. Turin kwandon be dame ni ba dan ji nake kamar ina tuka mota duk inda na ga dama juyashi na ke ina jindadi. Dauko wannan dauko wancan haka take bani umarni ina bi kamar bawa da uban gidansa, muna isa sashen kayan dadi ta umarce ni na dauko madara ina kai hannuna sai na ji an rike hannun, da sauri na kalli gafena.

“Na kama ki”

Kamal ne sanye da kananan kaya fuskarsa da murmushi kamar kullum ni ma Murmushin nai sai kuma nai saurin kallon Rukaiya wacce ita ma murmushin take sakar masa.

“Rukaiya shopping kuka zo”

“Eh Wallahi har ma mun kare daman ba da yawa zan yi ba ya aikin?”

“Lafiya kalau, sai ki ba ni aron Mamanar tawa ta raka ni shopping tun da kun kare, kadan na gama sai mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login