Showing 162001 words to 165000 words out of 225640 words
matan sai ya tashi ya raka abokansa, ina jin lokacin da motacinsu suka tashi suka bar cikin gidan sai kuma na ji yana jan kofar falon alamar rufewa yake.
Da zai dawo dakin sai da yai sallama sannan ya shigo, ni kuma na kasa amsawa har lokacin kaina na kasa ina ta wasa da yatsun hannuna, a inda ya zauna dazu ya sake zaunawa.
“Amarya.... ”
Sai na ji wata kunyar ta sake rufe. Kara hawowa yai saman gadon ya miko hannunsa ya bude mayafin da ke kaina ya dora shi a bayana yana murmushi sai kuma ya saka hannun na sa ya dago kaina sai na lumshe ido.
“Godiya ga Ubangijin da ya mallaka min wannan halittar ta inda ban yi zato ba, tsarki ya tabbata a gareka ya Allah”
Ya fada sannan ya Hura min iska a saman idona da suke kulle.
“Bude idonki ki kalli Masoyinki, bude idonki ki kalli mijinki na har abada”
A hankali ya bude ido sai na sauke su a cikin na shi, ta cikin kwayar ido muke kallon juna ni da shi wani irin sako yake aika ta cikin idon da ban wayanci na minene ba, ni ko hawaye sai aikinsu suke a idona. Wani lallausan murmushi yai min ya kai hannunsa a fuska ta share min hawayena sannan ya kara matsowa kusa da ji yai min masauki a kirjinsa, rumgume ni yai kamar wata yar baby sai juyani yake a hankali irin yadda ake yi ma yara. Ni kuwa na samu damar yin hawaye iya son raina, sai na ji dumin bakinsa a goshina, ya sumbace ni ba normal sumbata yai min ba yadda yake dora lips dinsa a goshin nawa ya sotsa ya dauke kamar zai janyo jinin goshin nawa ya sha ne, sai kara matseni yake a kirjinsa kamar wani zai kwace masa ni, a take jikina ya fara rawa domin ba a tana rumgume irin yadda ya rumgume ni ba. A hankali ya dago fuskata shi kuma ya duko da fuskarsa ya sumbaci tsinin hancina, ya sumbanci kumatuna sai kuma ya sake komawa ya sumbaci goashina kamin ya hade bakina da na sake rumtse ido ina jin wani irin kyankyami da kuma faduwar gaba a lokaci daya. A hankali yake shan lebena na kasa sai kuma ya yai sama da bakinsa ya sha na saman.
ALIYU POV.
Tana da soft and sweet lips Aliyu mutum ne mai son kiss sosai, ji yake kamar yana shan wata madara a bakinta, har Lumashe ido yake yana budewa, sai ya fi jindadi da kwanciyar da zakin lips sumbatarar a yanzu fiye da yadda ya sumbace ta a last time a kitchen wata kila saboda ya fi bukatatar a yanzu ne ko kuma saboda ya fi kwanciyar hankali da sakewa ne. Ya dauki tsawon lokaci a haka kamar ita da shi za su dauwama a haka ne sannan ya sake ta ya dago yana bude idonsa da su sauya kala ya jingina goshinsa saman nata yana ta kallon idonta da ke rufe sai shima ya rufe idon yana sauke numfashin a hankali.
“Taso mu yi alwala mu yi sallah”
Ya fada yana bude idonsa, kokarin dagawa tai daga jikinsa sai yai saurin bude idon ya rigata sauka daga kan gadon ya cire babbar rigarsa ya aje gefe ya bude mata bandakin. Takawa ta fara yi a hankali yana ta kallon fuakarta kamar zai hadeta har ta karaso kusa da shi ta shiga bandakin. Shiga yai ya kunna tap din ya tara hannunta ya wanke mata ya tara hannunsa ruwan suka taru ya kai mata a baki ta kuskure sannan ya shaka mata hancin da kansa, ya wanke mata fuska, hannu har ta kai ga shafar kai, ya kwakula mata kunnenta sai kuma ya dagota ya tara kafarta ya ya wanke mata dayar ma yai mata haka sannan ya sauketa ya sumbaci samman gashinta. Shi kan sai da ya tabbatace wani bangare na jikinsa sannan yai alwalar ya fito ya sameta bakin gado zaune.
Carpet biyu ya shimfida musu tashi tana gaban tata sannan ya fita daga dakin zuwa dakinta wardrobe ya bude inda aka zuba mata duka kayanta yai ta ya mutsa har ya samu hijab ya dauko mata ya dawo dakinsa, fa kansa ya saka mata Hijab din sannan ya matso da ita ya kawo ta gurin carpet din ya tsayar da ita kamar wacce aka ce masa bata gani, har sallah ma ji yakd kamar yai mata domin yau son ta a zuciyarsa na musamman ne. Sai da ya fara ikama sannan ya kabbata. Raka biyu sukai suka sallame sannan ya daga hannunsa yai ma Allah godiya yai musu addu'a ya shafa ita ma ya shafa sai ya juyo ya kama goshinta ya karanta addu'a sai ya sumbaci goshin, kamin ya saka hannunsa ya cire mata hijab. Tashi yai yaje ya dauko wata leda da ke gefen gado ya bude mata gassashiyar kaza ce da madara irin fresh milk din nan mai kyau. Da kanshi yaje ya dauko cup daya ya zuba mata milk din sannan ya dauki kazar ya kai mata a baki sai ta kawarda fuska.
“Na koshi”
Be ce mata komai ba ya mika hannunsa janyota ta dawo kusa da shi ya kwantar da ita a jikinsa sai ta lafe kamar wata kanwa, dibar naman kazar yake a baki yana taunawa kadan sai ya dago kanta ya hade bakinsu ya tura mata naman a baki, a dole take taunawa ta hade kamin ta hade ya tauna wani ya sake hade bakinsu ya tura mata a ciki. Madararce kawai ya daga kofin ya kai mata a baki ba tare daya gunda ta ba, sai ta bude baki kadan kamar wacce bata saba cin abinci ba tana sha a hankali. Wacce ta zubo mata a gefen baki sai ya saka halshensa ya lashe da kuma wacce ta tsaya a saman lebenta.
“Kin koshi?”
Ta gyada kai a hankali sai wani nutse kai take kasa, gaba daya ta zama wata solobuyu duk yadda ya juyata yi take.
Tashi hai ya shiga bandaki ya wanke hannunsa sannan ya fito falo ya nufa ya kashe wuta da tv da aka bar musu sake ya dawo dakin.
“Ta so”
Ya mika mata hannunsa, dagowa tai tana kallon hannun sannan ta mika masa nata mai zanen lalle sai da mike tsaye sai ya sumbaci hannun ya juyo da shi ciki ya sumbaci tsakiyar sai halshensa yake sakawa yana wasa da tsakiyar hannunta. Kamin ya kai hannunsa ya fara shafa gashin kanta yana shinshinawa. Jin ta hade yawu da karfi ta matsa baya yasa ya kalleta sai ya dagata ya kwantar da ita bakin gado ya risina daga gurin kafafunwa ya fara shafa lalleta fa farar kafarta mai taushi wacce ta sha dilka. Saman kafar ya fara kissing sai kuma kasan kafar sannan ya saka babban yatsansa a bakinsa ya fara tsusa kamar yaro ya samu sweet. Saurin fisge kafar tai ta tashi zaune sai shi ma ya tashi tsaye yana tande baki.
“Hau gado ki kwanta”
“Aa kasa zan kwanta”
Matsawo yai kusa da ita ya kai hannunsa ya ja lips dinta.
“Kin taba ganin Amarya ta kwanta kasa ranar aurenta?”
Ya fada mata a kunne kamar mai rada sai ya saka mata halshensa a kunneta ya fara wasa da kunnen nata yana tsosa a take ta soma jin ba dadi, sai ta fisge kunnenta daga bakinsa ta hau saman gadon ta kwanta dan dole ta. Wani kasaitaccen murmushi yai ya nufi wutar dakin ya kashe sai ya rage sauran bed side lamp kawai, ya hau samna gadon ya kwanta ta bayanta sannan ya kashe bed side lamp din, gudu ya mamaye dakin gaba daya, baka hango haske sai ta gurin curtains din windows din dakin shi ma ba sosai ba domin curtains din masu kauri ne sosai. Bayanta ya fara kissing yana ta yamutsa gashin kanta na baya har gurin kiyar kanta yake kissing, saurin juyowa tai dan ya daina ashe bakinta ne abunda ya fi bukata a yanzu, a cikin hudun ya hade bakinsu yana sani irin jan numfashinsa yana fitarwa ita numfashin take ja ta fitar sai dai yana da banbanci da na shi nata na wahala ne da tsoro shi kuma na jindadi ne da samun abunda ka dade kana muradi.
Jin wasansa zai fi karfinta yasa ta fashe masa da kuka, tun yana kissing din bakinta har ya sauko gurin wuyanta ya nemi masauki a kirjinta, duk inda ya rika a jikintan riko yake mata bana wasa ba, tun yana mata a hankali tana yin shiru tana amsa sakonsa dan dole har ya fara fin karfin kwakwalwarta, daman can haka yake idan yai marmari baya wasa da wannan babin.
“Aliyu dan Allah kai hakuri ka bari kaji Yaya Aliyu, dan Allah”
Juyar da ita yai ya kifar da ita yai karasa cire abunda ya rage a jikinta, tana ta ta yawo da hannunsa yadda yake so bayanta kamin ya juyo da ita. Jin yana kokarin kaiwa inda take jin ba zata taba iya barin kowa ya kai a nan ba yasa ta fara kuka kamar daman can ta tanadi kukanta ne kawai dan domin irin wannan ranar ta yau.
Addu'a ya karanta sannan ya fara yi da kamar hankali kamin ya birkice mata, babu kalar kukan da batai ba tun tana kiran dan Allah dan Annabi har ta koma hada shi da Momy da Daddy, ta kira Nana can kuma ta koma tana hada shi da Mama Fulani amman sam baya ma jin ihunta balle har tausayinta ya shiga ransa, shi be tana tausayin mace a wannan bangaren ba.
Sai da yai kwanka sannan ya kwanta bayanta ya saka ta a kirjinsa ta bayanta ya rumgume yana jin sani irin son ta da kaunarta na masa yawu a zuciya da jiki da duka wani guri da jini da numfashi yake shiga.
Kiran sallah asuba ya tashe shi sauka yai daga kan gadon ya kunna wutar dakin wanda hakan yasa Ataa ga bude idonta ta kalleshi, zuwa yai ya yaye blanket din jikinta sai ga babu komai a jikinta, daukarta yai ya shiga da ita bathroom ya hada mata ruwa mai zafi ya saka a ciki, kana ganinta kasan bata da wani karfi ko kuzari a jikinta, ba zancen kunya ko wani abun take a yanzu ba, ta wani zama kamar ba ita ba. A cikin ruwan ya barta sai da yaje masallaci yai sallah ya dawo sannan ya sake lekowa bathroom din sai ya sameta a cikin tana lumshe ido alamar bachin take ji har yanzu.
Wani lausayinta ne ya kama shi ya san abunda yai ko Rahma tana kuka da shi wani lokacin balle kuma Ataa. Gashin kanta ya fara rikawa ya tufke mata shi guri daya sannan ya tambayeta.
“Kin iya wankan tsarki?”
Ta gyada masa kai.
“Waya koya miki?”
Ta daga hannu sama domin magana ma a yanzu wahala take mata.
“Mama (Nana)”
Ta gyada kai sai yai murmushi. Da taimakonsa tai wankan ta ya fito da ita da kansa domin shi kanshi yana jin ba zata iya tafiya da kafafuwanta a lokacin, babu tufafin a jikinta ya fito da ita ta zauna bakin gado tana ta natse kafafuwanta saboda azabar da take ji a guri har jin take kamar wani kwaro na mata motsi a gurin, duk inda wata halitta nata na jiki na musamman yake zafi yake mata kama daga kirjinta har zuwa kunkurunta da take jin kamar karewa zai yi idan ta mike tsaye, kasanta ma zafi yake mata na fitar hankali sai hade yawu take tana bin Aliyu da kallo duk inda yai har ya fita yaje ya dauko mata abaya ya saka mata da hijab gaba daya ta koma kamar wata yar baby.
Shi ya shimfida mata carpet ya zauna ya zuba mata ido yana ta kallonta har tai sallah ta gama sannan yaje ya dauko kur'ane ya zauna kusa da ita ya kwantar da kanta a cinyarsa ya bude kur'anin ya soma karantawa da kira'a mai dadin sauraro. Tun tana jin kirara tasa har bachi yai gaba da ita, ya dade yana karatun sai da Rana ta fito sannan ya daga kanta a hankali ya aje kasa sai ta bude ido ta tashi zaune, maida qur'anen yai a muhallinsa sannan ya dawo ya miko mata hannunsa.
“Ta so”
Bata fuska tai ya tana kokarin gashewa da kuka, domin a tunaninta abunda yai mata jiya zai kara mata a yanzun ma. Dayan hannunsa ya sake miko mata.
“Ta so mana baby na”
Ta mika hannayen duka biyu ya mikar da ita tsaye sai ya tura jikinta zuwa gurin gadon bachinsa. Cire mata Hijab yai ya aje gefe ya rikata ya kwnatar saman gadon sannan shi ma ya kwanta yana kissing gaban goshinta.
“Hug me”
Ya fada jin ta yi shiru yasa ya sake cewa.
“Rumgume ni sai ki yi bachinki babu abunda zan miki”
Ba musu ta rumgumeshi ta shigar da kanta jikinsa ya runtse ido. Kwakwalwarta na tariyo mata abunda ya faru jiya, shi kanshi abunda ya faru yake tunani wani irin farincikin ne da nishadi a zuciyarsa da ruhinsa, ya sameta fiye da yadda ya za ci zai sameta ya jita fiye da yadda yake tunani a duk ma'aunin da zai aunata a zuciyarsa yanzu zai ga kamar ya rage mata matsayi ne. Saman kanta ya dinga kissing kamar wani mahaukaci ya kuma rumgumeta tsantsan a kirjinsa kamar yadda ta rumgume shi saboda kunyarsa da ta taso mata yanzu.
Na su yi bachin minti talatin zuwa arba'in ba door bell din falon ya fara kara alamar akwai mutum a waje. Bude ido yai a hankali ya sauka daga kan gadon ya sumbace kumatunta sannan ya gyara mata zanen ya lulllube abarsa da kyau sannan ya fito falo bude kofar ma a hankali yai kar kararta ta tashe ta. Siyama ya gani da wasu cousins sisters dinsa su hudu suna dauke da abinci.
“Ina kwana yaya? Momy ta ce akawo muku abun karya”
Amsa nata da dan murmushi a fuskarsa kamar yadda yai ma sauran sannan ha basu guri suka isa cikin fakon suka aje abincin a muhallinsa suka juyo suka fito da sauri kamar wadanda ake kora. Kulle kofar yai ya dawo dakin da ya bar Ataa sai ya same ta zaune tana hawaye.
Saman gadon ya hau ya raba kafafuwansa biyu ya saka nata a tsakiya ya matse fuskarta tana jin saukar numfashinsa yana jin nata.
“Minene?”
Kasa amsawa tai sai baya baya take har ya kwanta jikin gadon yai mata rumfa da kirjinsa, ya sumbaci hancinta kumatunta da kuma goshinta sannan ya sauka ya daga kan gadon, tufafin jikinsa ya cire a gurin which is normal for him indai a gaban matarsa ne zai iya kuma yana bukatar yin hakan a gabanta domin ta soma sabawa da halayensa sun yanzu, wanda hakan yasa ta saurin kawarda fuskarta. Yana gamawa da kansa ya janyota ya shiga rabata da gown din jikinta ita ko sai rokonsa take a zatonta yar jiya za a sake yi.
“Wanka za mu yi sannan mu ci abincin karyarwa”
Ya fada yana daukar tawul daya ya daura sannan ya miko mata dayan, kasa daura tawul din tai saboda ta nade a cikin blanket shi kan be bi ta kanta ba sai gai kamar ma be lura da abunda tai ba. Sai da ya fara shiga ya hada musu ruwan wankan sannan ya fito yana daure da tawul din ya bude blanket din ya fito da ita ta daga ta sama cak ya nufi toilet. A tare sukai wankan ba dan ranta ya so ba sai dan dolenta brush din ma sabo daya ya fasa musu sai da ya fara yi sannan ya wanke mata nata bakin, ya saba yi ma mace komai, dafa mata abinci, wanka, brush, kawo mata abincin da ba mai nauyi ba, bata ruwa and so on kuma be tana gazawa ko gajiyawa ba domin a gurinsa matarsa yar lelensa ce kuma yar gata ba yar wahala ba, Rahma ma yai mata balle Ataa da yake ganin yarinya ce ba komai ta sani ba ko ta iya. Tawul daya ya rage a bandakin dan haka ya daura mata shi ya fito a haka ha nufi wardrobe dinta ya bude ya fara saka boxer da vest sannan ya nufi madubi ya shafa abubuwan daya saba shafawa tare da tutaren jiki sai kuma ya dawo ya saka shadda da sauran abubuwa.
Ko da ya juyo tana zaune bakin gadon ka ta a kasa, dan karamin tawul din a jikinta, fita yai zuwa dakinta ha dauko mata wasu riga da wando na yadi marar nauyi ya saka mata da kansa. Sannan ya juya ya tara mata bayansa.
“Hau muje falo mu karya”
ATAA POV.
“Zan iya tafiya da kaina”
Na fada ina dan turo baki sai ya ce.
“Bana son kina min gardama idan na ce ki yi abu ki yi kawai, ko ba a fada miki duk abunda na saka ki yi ba?”
“An ce”
Na fada daker.
“Then hau”
Ya fada yana hadawa da turanci, a dole na hau bayansa ya mike tsaye da ni kamar wata yar baby, sai da ya fara tafiya sai ya saki hannunsa a dole na kankanme shi da kafafuwa da hannuna gudun faduwa kaina kuma a bayansa ma lafe kamar maciji, dan Murmushi na ji yayi mai sauti sannan ya nufo falon da ni. Har gurin Dinning ya kai ni sai ya sauke ni tsaye yaja kujera ya zauna ya nuna min cinyarsa.
“Zauna a nan”
“A nan?”
Na kara tambaya dan tabbatarwa. Be ce min komai sai kallona yake wanda kallon ke ba ni ma'anar zaman a dole na zauna ina jin kamar na fashe da kuka domin na lura sam Aliyu ba shi da kunya gaba daya ni ga ni nake kamar ba shi ne ba. A saman ciyarsa ya gyara min ya sumbance ni sannan ya mika hannu ya shiga zuba abincin ina saman jikinsa, a plate daya ya zuba mana abincin ya rika ba ni da hannunsa, sai da na koshi sannan ya umarce ni da shi ma na bashi, spoon na dauko zan saka na bashi sai ya girgiza min kai.
“No na san da spoon na baki da hannu, da hannu na ke son ki