Showing 144001 words to 147000 words out of 225640 words
ta miko min wai Muhseen yana son magana da ni, hakuri ya fara bani sannan ya fada min cewar ya hakura duk abunda zai raba kan Mahaifiyarsa da Mahaifiyar Aliyu zai iya hakura da shi, duk kuma abunda zai iya shiga tsakanin mahaifinsa da mahaifin Aliyu zai iya hakura da shi, ya fada min idan kika aureshi ba ki auri Aliyu ba, Aliyu da iyayensa za su ga cewar ba ki kyauta musu ba kuma ba mu musu karamci ba, idan kuma kika auri Aliyu kika barshi zai hakura amman ba zai taba iya cire son ki a ransa ba, kuma yasa iyayensa ba za au daina ganin cewar iyayen Aliyu sun yi son kai ba, ya ba ni hakuri ya fada min akwai zumuncin mai karfi a tsakaninsu, kar na bari zumincinsu ya lalace”
Na dan yi shiru ina tunanin wata kila tsoron lalacewar zumincin ne ya saka Momy ta tafi Abuja, ko da yake daman na san tana da ra'ayin zuwa tun a wacan karon da tai min albishirin zuwa da ni.
“Amman Nana wannan abun ya isa ya saka ki ce mu bar gidan nan? Idan muka tafi ina zamu zauna? Babu mai karbar mu sai yawon rabe rabe a titi, haka rayuwar mu zata kare? Ba kowa a tare da mu kuma sai mun yi ba ra mu ci? Kullum wani kalar kabulen muke fuskanta? Indan har za mu bar nan kamata yai ace cikin danginmu za mu koma, Nana ban san kowa na ki ba, ban san kowa na mahaifina ba, miyasa kika gudu kika dawo nan kin kasa fada min kullum sai boyewa kike bayan nima ina da hakkin sani domin ni yarki ce”
“Ba dadi ne ya rabo ni da iyayema ba, shiyasa ba zan iya koma musu ba, na musu tuluci sai kuma yanzu na ce zan koma? Ai abun ma da kunya”
“Mi kika aikata Nana? Butulcin me kika musu?”
Shiru tai na wani lokaci tana hawaye.
“Na yi ma iyayena budulci, kuma na gudu na barsu ina jin kunyar komawa a yanzu ina jin kunyar arba da mahaifina da mahaifiyata waya sani ko su yi min mummanar kalami bayan tafiyata”
“Mi kika yi har ya koreki?”
“Ba korata yai ba guduwa nai a karan kaina”
“Saboda mi nana?”
“Saboda Soyayar mahaifinki, na so mahaifinki kamar na mutu ina ta ganin kamar idan zan yi rayuwa ba da shi ba zan iya mutuwa ko na fada halaka, a Masarautar mu mace ba ta zabawa kanta mijin aure sa dai iyaye su zaba mata, ni kuma nai kuskuren zaba da kaina kuma a ganina ba laifina ba ne idan na zabawa kaina mijin da ya fi kwantar min a rai”
“Masautarku kike ce Nana? Kin saka kaina a cikin duhu ban gane ba”
“Ba zaki gane ba Ataa ba lallai ne kowa ya yarda ba balle har a iya tsayawa a gane, kowa yana ganina a wulakance a kaskance amman ni jinin sarauta ce ni kadai ce ya mace a gurin Sarki Bashiru Muhammadu, ni kadai ce Gimbiya Nana Asma'u a duk fadin masarautar Agadez”
Ba zan na kasa yarda da abunda Nana take fada min ba, amman tabbas labarin nan abun rikitarwa ne.
“Amman Nana muka kare a bara?”
Na tambaya cike da zakuwar son jin labarinta. Numfasawa gai sannan ta ce
“
Yankin Agadez shi ne ya fi kowanne yanki girma a Nijar, yankin Agadez ya hada da hamadar Tenere da Bilma da kuma yankin Air mai cike da tsaunuka. Mafi yawancin jama'ar yankin Abzinawa ne, akwai kuma Tubawa da Fulani da kuma Hausawa, mahaifina shine sarkin Agadaz, babban sarki ne mai tari dukiya da kaddarori da mu kan mu yayansa ba za mu iya fayyace ta a lokaci daya ba, mu goma shar tara mahaifinmu ya haifa a dakinmu mu bakwai ne, mahaifiyarmu ita ce uwargida, bayan ita yana da mata biyu, amman ni kadai Allah ya ba shi mace duka sauran maza ne, na taso a cikin wani irin gata marar misaltuwa, kasancewa ta mace sai ya zama ta ko wane bangare ina samun kulawa, bangaren Mai martaba ba, yayyuna maza har ma da kanena maza idan wani abun burgewa na mata suka gani sai su siyo min, domin ni ban san taso a gidanmu na san wani wai kiyaya ki yan ubanci ba, dukanmu idan ka ganmu zaka dauka uwa ta haife mu, boyona ake bana fita ko'ina sai idan makaranta ne ko wani muhimmin abu, karatun addinin ma malami aka samo a gida yake koya mana komai, a lokacin da na gama karatu matakin na biyu, sai mahaifina ya kai ni faransa domin ci gaba da karatuna, a lokacin ban iya komai ba sai faransanci da buzanci a wacan lokacin, ina dawowa a duk lokacin da hutu ya samu sai dai na kan yi watanni kamin na dawo gida, a wata dawowa da nai sai na samu masarautar mu ta yi sabin gyare gyare cikin har da daukar sababin ma'aikata mahaifinki na daga cikin ma'aikatan da aka dauka, ranar da na sauka masarautar mu mahaifinki ne ya bude min mota”
Ta yi shiru na wani lokaci sanna ta cigaba.
“Yana kyau sosai kamar ki, tun a farkon ganin da nai masa na ni ya kwanta min a rai, duk kuwa da kasancewar ban san soyayya ba, saboda mahaifina baya bari wani namjin ya rabe, saboda mazan gidan ma ma zabin mata ake musu balle kuma mata, amman a lokacin da na ga mahaifinki sai ya shiga raina sosai na kamu da son shi, ba kasafai na ke fitowa a harabar masarautar mu ba, amman zuwan mahaifinki sai na fito na zauna nai ta kallonsa ko kuma na kuma na rika lekensa, ina yin duk wani abu da zai kusantar da ni a gareshi, idan lokacin zuwansa yai be zo na duk sai na bi na damu, har wata na shirya fita ta musamman zuwa gidan gonar Mai Martaba da sunan shakatawa, ni da kaina na zabi wadanda za su raka ni, a ciki na za bi mahaifinki, mutumen ne mai far'a da son mutane, sai dai yana tsoron ko da kallona yai kasacewata yar saurata, sai dai na yi da jansa a jikina ina nuna masa kauna, ya labarta min yan'uwana da kowa na sa da ke garin Agadez, wasa wasa kauna ta shiga tsakaminmu amman a boye bana bari a sani, ina daf da komawa makaranta Mai martaba ya gabatar min da wani dan aminsa atsayin mijin da zan aura idan na kammala karatuna, a lokacin ne na juyawa Mai martaba baya na fada masa kai tsaye cewar mahaifinki ne so, a lokacin ne mai martaba ya cilasta ni kula dan aminsa, mahaifinki kuma aka koreshi daga masarautar, babu yadda mahaifiyata ba tai ba dan ta fahimtar ta shi amman ya ki fahimta, aka cilasta min komawa makaranta a cikin wannan yanayin, na shiga damuwa matuka ina jin cewar da zarar na sakw dawowa a garin mai martaba zai aura min wani ne dabam na ummaruje ba, daga makarantar na dawo nijar ba tare da sanin mai martaba ba, na sauka a wani hotel na chanja shigata nai shigar da ba za a taba iya gane ni ba, na je da kaina har cikin gidan su Ummaruje, tsoro sai ya kama mahaifiyarsa da mahaifinsa da dukan yan gidan kasacewar gidan yawa ne, suna ganin cewar idan mai martaba ya san na zo nan zai iya fusace yai musu wani abun, ni na fada masa durina na guduwa, kuma ya yarda saboda so na sosai daga Agadez muka yi doso gurin wasu yan'uwansa, suma suna ya jin tsoro daker muka samu suka yarda aka daura mana aure a sirrance, sai labarin neman Ummaruje ya fara karade nijar, muka sake guduwa da dan abunda yake hannuna muka dawo kamba, da kudin hannuna muka kama haya, mahaifinki kuma hai shago kofar gida, kuma sai Allah yasa albarka abun ya karbu, sai da na shekara biyar a kamba sannan na haife ki, daga nan sai mutane suka fara tambayar dangina, ganin kowa be zo sunanki ba daga dangin mijina har nawa, daga haka muka fara jin mutane umguwa na zancen wai ni yar sarki ce, sai zaman ya gagare mu a nan saboda tsoro da fargaban abunda zai biyo baya, muna ta ganin kamar Mai martaba zai iya aikowa nemana ko kuma ya saka a kama Ummaruje, ya siyarda komai nasa kudin hayar mu kuma muka barsu nan muka koma argungu, zaman a can be karbe mu ba saboda sanar'a shagon da mahaifinki ya fara yi sai ta soma komawa shiririta, sai muka bar yankin gaba daya muka shiga bodinga, a lokacin ne mahaifinki ya fara sana'ar tura ruwa yana siyarwa, sai dai zaman kaune babu dadi saboda ban saba ba, tun ina jin kunyar na je na yi itace shi kuma ya fita siyar da ruwa har ya zame min jiki, sai na kwana biyu uku ban yi wanka ba, wasa wasa har nai sati kuma babu wanda ya kula ko ya damu da hakan, a hakan ma har na ke ganin na fi wasu tsafta, daga bodinga mahaifina ya rika shigowa cikin sokoto yana haduwa da wasu fulani da kuma buzaye, idan ya dawo sai ya rika ba ni labarin sokoto ita dai kamar kamba tana da tarin yan nijar da yawa a ciki, ya fada min cewar akwai da yawa a cikin fulani da buzaye da suke rabawa a irin gidajen da ba a gama gina ba su zauna, sai nai sha'awar mu yi haka saboda ina son na dawo sokoto da zama daga haka muka tattara muka dawo sokoto, a talatar mafara muka fara sauka, a nan muka fara fakewa a wani tsohon gidan da ba a kare ba, ya cigaba sana'ar siyarda ruwansa, ni kuma ina kulla gida ina siyarwa, kwata kwata na koma kamar ba yar saurata ba, kalar fatata ta canja wahala ta rufe ni ga kuma cikin Lukman da na samu a wannan lokacin, ya sani laulayi har na haife shi, mijina yana nuna min kauna sosai yana kula da ni iya gwargwado, bama cikin matsalar komai domin yana kokarin kawo wa mu ci, har kuka girma ya sakaki a makaranta sai dai yana rasuwa komai ya canja mana Ataa kin sani.... ”
Kuka take kamar yadda nima na ke kukan, hakika na sani na san lokacin lokacin da mahaifina yai bankwana da duniya ba tare da ciwon komai ba a cikin gida muna fira da shi sai kawai muka ji yayi shiru ya risina daga zaunen da yake muka jijjiga shi shiru Nana ta kira sunanshi ta zuba masa ruwa amman shikenan mai kasacewa ta kasance, bayan mutuwarsa muka muka siyar da baronsa da duk wani abu na sa muka bar unguwarsa zuwa gidadawa a nan muka kafa bukkarmu kamar yadda muka ga Baba yayi, muka zauna a gurin har zuwa lokacin da masu gidan suka bukaci abunsu, muka sake tashi, da haka mukai ta yawo zama guri guri Nana kuma na fita tai mana bara ta kawo kudin mu siya abinci, har muka fara zuwa tare da ita da muka tara mai yawa sai ta saka ni a makarantar Yakubu mu'azu ni na fara zuwa lukman kuma ya hakura sai gaba, kudin tsintsiya da kudin pta suka hana ni komawa makarantar sai na cigaba da ya islamiyar ita ma ina haruffa na daina zuwa saboda baran ya shiga kaina na, kuma wani lokacin da yunwa na ke zuwa na dawo, karatun ma sai ya daina zama a kana ya zama bana gane komai, Nana kuma bata damu ba saboda bara kawai ta saka a gaba.
Da haka har karatun ya gagareni na daina zuwa gaba daya, sai Lukman da ke zuwa shi ma jefe jefi.
Mahaifina yana son mu daga ni har Lukman da kuma Nana, na sani a dan zaman da nai da shi na rayuwar da na samu tare da shi ya nuna mana kauna, a kullum burinsa ya zai inganta rayuwarmu da ta Nana, yana yawan fada min cewar dadi na nan zuwa ko ba shi da rai za mu jidadi ni da Nana da Lukman, shi ya tafi Lukman ma ya tafi ni da Nana kawai muka rage.
Gaba daya jin nai kaina yayi nauyi kuma yana ciwo, saboda tunawa da baya da kuma jin labarin Nana, sai dai bana ganin hakan a matsayin laifin da mahaifinta zai iya cewa ba zai yafe ba, wata kila yana raye ko kuma ya mutu Allah nasani, sosai zuciyata ta cika da kaunar Aliyu domin shine mutumen da ya fara maida ni mutum ya sa na maye gurbin duk wani abu da na rasa kuma yarda ya so ni yadda na ke, ba dan kyau na ko wani abu nawa ba, tsabanin duk wanda zai kalle ni ya so dan kyauna, Momy kuma ta biyo a sahu na biyu a kaunar da ta nuna min na son danta ya aureni saboda ya inganta rayuwarta kuma Rahma ta daina min kallon banza, yana da wahala a zamanin nan ace wani wanda baka sani ba kamar Momy da Aliyu su soka tsakani da Allah. Sai a yanzu na ke gane wasu abubuwan da Nana take hango min.
Hakika zabuwa da iyaye akwai ciwo da damuwa, ni kaina da Nana ta kamu da ciwon nan ina ta tsoro da zullumin rabuwa da ita, ni kenan da ke tare da albarkata ina ga ita da guduwa tai ta bar iyayen? Sai yanzu na gano dalilin cewar da take tana son ta san hannun da zan fada kamin ta bar duniya, tana kuma tsoron gaba saboda tana tunanin ba iyakar kaddararta kenan ba, lallai ko kadan ta ga na kuma abu ya zo da sauki da ya zama kodarta kawai aka cire kuma har ta samu tattafin Aliyu ya nema mata magani ta warke. A yanzu kam na yarda da zancenta cewar kaddarar Aliyu ce ta zo a hannunta kamar yadda tata kaddarar ta zo a hannun Babana.
Labarin Nana be kara min komai ba sai tausayi da jinka da kuma ganin darajar zabin iyaye ko da kuwa mai cutarwa ne, matukar ka bata musu rai dole ne sai wani abun ya same ka ko da ko kadan ne, kaunarta na ji ta karu a raina da kuma son zama kusa da ita, domin a yanzu ni kadai ce wacce take da, kuma ita kadai ce wacce na ke gani na ji sanyi a raina wato uwata.
Daga har ita cikin damuwa da tunani muka kwana, washe gari bayan mun yi sallah na zauna nai yi ma Babana addu'a sosai daman na saba masa a sujida sai dai wannan ta musammance, domin na san a yanzu babu abunda ya ke bukata a tare da ni kamar Addu'a ta. Misalin takwas da rabi na shiga part din Momy na share komai kamar yadda na sabawa kaina Amina da Husna kuma suka shirya abun karyawa suka ba ni nawa ni da Nana.
Na koma na kai mata, ruwan shayin kawai ta sha ta kasa cin komai fuskarta gaba daya ta kumbura, kana gani ka san a daren jiya ta kwana tunani kuma ta sha kuka.
“Nana Babanki zai yafe miki matukar yana raye, shekaru da yawa ya isa ya saka zuciyarsa laushi ya fahimce ki”
“Ba zai yafe min ba, na aikata kuskure na gudu saboda biyan bukatar raina be kamata wuya ta saka na koma ba”
“Ba saboda wuya za ki koma ba, saboda kin yi nadama kin gane kuskurenki za ki koma”
“Wata kila ma baya raye, abun kunya ne ace na haihu har dayan ya koma ga Allah mahaifina be san yayana ba, yayana kuma ba su san yan'uwana ba, ba zan iya komawa garin nan ba har abada, na barwa iyayena da masarautar Agadez abun kunya”
Ajiyar zuciya na sauke ina sauraren motar da naji an faka harabar gidan, hayaniyar Amina da Husna ne yasa na tashi na leka window sai na hango Momy ta fito daga motar ita kadai ba tare da Aliyu ba, wata kila ya tafi gidansa gurin matarsa ko kuma ba yau zai dawo ba.
Fitowa nai na tareta tare da rika jar jakar hannunta na bi bayanta, ita kuma tana ta min murmushi har muka shiga cikin falon, a nan ta zauna Amina ta debo mata ruwa suna ta daukinta kamar wacce ta shekara bata gidan, ita tana marmarin gwanin sha'awa uwa mai dadi.
“Momy ya Aliyu fa?”
Husna ta tambaya.
“Ba yau ba yace zai kwana biyu kamin ya dawo”
Momy na bada amsar zuciyata ta raya min wata kila da matarsa ya tafi shiyasa ba zai dawo yanzu ba. Ballantana na san idan Mama Fulani ta ji cewar saboda ni komai ya faru ba zata barshi ya dawo ba, a take na ji raina ya bace. Da abincin mu na rana na dawo part din mu ina jin cewar yanzu ne ma lokacin da ya kamata na auri Aliyun ko dan Rahma da Mama Fulani sai na ga idan mutuwa za su yi, ace irin tsanar da suke nunawa talaka Aliyu ya aure ni sai ya kenan? Kuma ina tunanin ta wannan hanyar ce kawai zan yi ma Momy tukuicin abunda tai mana, ita kadai ce hanyar da zan saka mahaifiyata cikin farinciki a yanzu na taimake ta ita ma ta sake jindadin rayuwa.
Da yamma ina cikin shirin zuwa makarantar islamiya, Momy ta aiko tana kirana Siyama ce ta shigo ta fada min gana sanye da nata uniform din na islamiya sai dai na ta dabam kamar yadda nawa yaks dabam kasacewar ba makarantarmu daya ba. Kamin na shiga part din Momy na hango mutumen jiya wato ustazu nan yau ma yana cikin shigarsa ta mutunci da kamala. Ina shiga Momy ta ce min.
“Wani na waje yana sallama da ke, wai yana neman izinin mu kamin yai magana da ke, ki fadawa Nana sannan ki je”
“Momy ban iya fira ba, ko naje ban san mi zan ce masa ba”
Na bata amsa a takaice wanda har cikin zuciyarta haka ne, idan na je ban san abunda zan fada masa ba, fira da wani a yanzu ina jin kamar ba zata min dadi ba, idan kuma na ce zan yi da gara duk mutanen