Showing 153001 words to 156000 words out of 225640 words

Chapter 52 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

ba, sai makusantan Aliyu ciki kuwa har da abokansa duk kuwa da wasu ba su samu zuwa ba bikin ba kawai sun samu sakon ne daga Aliyu wasu kuma daga Nasir gashi lokaci ya kure ba su samu zuwa ba. Sun samu addu'a sosai albarka jama'a kasancewar massallacin juma'a kuma babban masallaci wanda mutake ke taruwa sosai bayan daura auren nasa aka daura na wasu mutanen biyu.
  A cikin mutanen da suka samu halartar daurin auren har da Kamal wanda Nasir ya sanar da shi amadadin Aliyu, baya farinciki da auren Aliyu da Ataa sai dai kuma baya bakinciki, domin ya san daman Aliyu yana son ta kuma tunda aka ce tana gidansu daman yasan tsakanin Muhseen da Aliyu dole sai ta auri daya. He know what he did to Mama Fulani be kyauta ba, Mahaifiyarsa ma ta masa fada akan hakan kasancewar Mama Fulani kawarta ce kuma makociyarsu bugu da kari kuma mahaifiyar Aliyu domin kamar uwa take a gurinsa. Daman yana neman hanyar da zai shirya da abokinsa kuma ya bashi hakuri kan abunda ya faru, sai dai ba zai iya iya kiran Aliyu kai tsaye ba sanin halinsa na wulakanci zai iya neman ya wulakanta shi ganin ya kawo kansa da kansa kamar yadda yake ganin Mama Fulani ma zata iya masa.
  But sanar da shi da Nasir yai cewar Aliyu yana gayyatarsa dauren aurensa ya sa bari duk wani aiki da yake da shi a ranar friday din ya halarci daurin auren, yana ga jin kamar ace shi ne ya auri Ataa. After daurin auren aka wuce shukura hotel aka ci abinci mai kyau drinks ma sai wanda ran mutum ke so.
Ango ya sha kyau shaddar jikinaa ai wani haske take yana wani maiko kana gani ka san shaddar masu naira ce, ko masu nairan ba kananan ba, farar shadda ce wacce ta sha aiki, ga wasu expensive shoes da be taba zuba zuba kudi mai yawa ya siye takalmin da suka kai wadanda Nasir ya zo nasa da su daga Abuja tsada ba, hular kansa kadai tana siyen tufafin wani mai kudin kala goma. Zuciyar Aliyu kal ransa fes kamar babu abunda ya taba bata masa rai a duniya, wasu family friends dinsa har mamakin yadda ya sake da mutane yake ta dariya suke domin sun san ba halin Aliyu ba ne. Amman sai dariya yake baki har kunnuwa yadda yai muran da zuwan Kamal sai ka dauka ma wani abu be shiga tsakaninsu ba, farinciki aure ya saka ya manta da komai.
  After lunch a hotel wasu suka kama hanyar Abuja wandan suka zo daga can ciki kuwa har da Abbah da wasu aminansa, yan wasu garuruwan ma suka kama hanya, har da yan Yola wato yan uwan Mama Fulani domin sun san Aliyu dan Mama Fulani ne sai dai Abbah ne ya sanar da su ba Mama Fulani ba, har da kanen Ammy biyu da goma suke Kaduna sai da suka zo.
   Momy tana gida tana fama da nata Familyn da kuma Familyn Daddy ana ta wasa da dariya sai tsarguwar juna suke ita da tabasanta da kuma tabansan Daddy, abun gwanin burgewa, Husna da Siyama da wasu cousins dinsu mata su suke rabawa baki abincin, a gidan an yi jalof din shimkafa da kuskus, fried rice, waina da kuma tuwan shimkafa. And su snacks cake da donuts. Drinks ko tun daga na zobo kunun aya, kunun waken suya, ginger da na waje babu kalar da babu, daga Candy Restaurant Momy tai order komai, sai ka dauka ma wunin biki ake ba wai daurin aure ne kawai ba. Yadda aka taru abun har Mamaki ya bawa Momy domin wasu dai bata san ta fada musu ba, musamman ma matan da suka zo na zaton ko har da wunin bikin ne. Komai na Nana Momy ware mata tai ta aika mata a bangarenta.
   Sai kusan magariba Momy ta samu kanta, daman wasu daga familynsa da suka so yan matan sun ce a nan za su kwana, Husna da Siyama sai labari ake yana jindadi an hadu da yan'uwa, Amina ce kawai bata nan kowa sai tambayarta yake sai a fada musu tana can tare da Amarya, sai dai ba a fada musu inda Amarya take saboda Momy ta fadawa su Husna da Siyama cewar bata son a damu Ataa domin bata san da daurin auren yau ba kuma bata saba ba, ba karamin aikinta ne ba ta sakawa mutane kuka.

ALIYU POV.

Da kansa ya raka wasu friends dinsa airport yana ta musu godiya cikinsu kuwa har da Kamal, sai dai ya kasa sakewa yana ta jin kunyar Aliyu har sai da ya ga Aliyun ha wayance kamar ba shi ba, ko kuma ya manta da abunda ya faru sannan shi ma ya saki jikinsa har yai ma Aliyun sallama su kai shaking hands.
  A  hanyar su ta dawo gida tare da Nasir yake driving yana sokonar Aliyu.

“An daura auren nan dai hankali ya kwanta”

“Wallahi kuwa yanzu hankalina a kwance yake fes ba ni da wata matsala malam”

“Ango ango angon da ba Amarya”

“Inji uban wa?”

Nasir ya kyalkyale da wata mahaukaciyar dariya wacce ta saka Aliyu da kansa shi ma ya dara.

“Ai kasan dai Momy ba zata baka amarya nan yanzu ba ko? Sai ta girma”

“Girma? Ta girma a gidana na yarda dai ba zata tare a yau ba”

“Kuma daidai ne ace yadda ka sha shaddar nan ajima a kai maka amaryar ka”

“Na rantse da Allah kau, Nasir kai mugu ne Wallahi”

Nasir din ya sake saka masa dariya har da buga sitarin motar. Aliyu yai murmushi yana cire hularsa ya shafa kansa, sai a yanzu yake jin cewar lallai yayi dacen auren Ataa daman yana son yan latsu wato karamar yarinya kamarta wance bata iya komai bata san komai ba bata waye ba a komai ba, kuma bata taba soyayya ba, he know littafinsa ne zai bude a kwakwaltar da kuma zuciyata domin ya san duk abunda ya koya mata shi zata haddace ya zauna a kanta.
   A harabar gidansu Momy Nasir ya faka motarsa ya riga Aliyu fita ya shiga ciki domin gaisawa da Momy daman tun da ya diro garin be leko nan ba, kai tsaye na nufi gurin abokinsa, daga can suka nufi gurin daurin aure kamin su soma hidimar abokansu.
  Aliyu na kokarin fita motar wayarsa tai vibration alamar kira, ciro wayar yai daga aljihunsa sai ya ga bakuwar number yar waje saman screen din wayar na nuna masa ana masa kiran ne daga Dubai. Kai tsaye ya fahimci cewar mai kiran tasa ba kowa ba ce face Rahma. Murmushi yai ya danna picking ya kafa wayar a kunne.

“Hello Dear ya Dubai? Hope hutun yayi miki dadi?”

“Aliyu ka yi aure?”

Ta tambaya a sanyaye gabanta sai faduwa yake tana son ya amsa mata da capital NO.

“Yes Yau din nan aka kara dora min wani nauyi da kuma hakki, daraja ta ta dagu daga mai mata daya zuwa biyu”

“Aliyu?”

“Ana wasa da aure ne Rahma? Ai kin san ko zan miki wasa da komai ban da aure ko?”

“Aliyu ina nufin aure na sunna a daura maka irin wanda aka mana”

“Irin shi akai mana da kanwarki Aisha a yau”

“Aure fa Aliyu? Wallahi ka ci amanata ka cuce ni Aliyu ba zan taba  yafe maka ba, tun ina da rai zaka fara nuna min hakinka ba ma sai na mutu ba?”

“Wacce zata iya zaman aure ta kula da mijinki kawai na aura”

Ta tsinke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba shi kuma ya maida wayar aljihu ya nufi cikin gida. Yana shiga wasa da dariya zoyata tsakaninsa da tabansansa ya tashi sai dai duk yadda suka tsarge shi sai dai yai dan murmushi baya cewa komai, daman can haka yake indai ya hadu da abokan wasa sai dai yai murmushi ko yar dariya kadan idan akai wani abun.
  After sallah magariba Nasir ya shiga gari domin ganawa da wasu friends dinsa. Aliyu kuma yana gida gurin Momy sai tunanin inda aka kai Ataa yake, domin ita kadai ce abunda idonsa ke son gani a yanzu, muradin zuciyarsa. Amman baya jin zai iya tambayar kowa ina Ataa ai da kunya. Sai dai ya duba yaga duka sisters dinsa suna nan ban da Amina dan haka ya tambaya.

“Ina Amina?”

“Wai tana can tare da Amarya yau duk abunda akai ba da ita akai ba”

Wata cousin sister dinsa ta fada, a take ya mike tsaye ya fito harabar gidan ya kira Amina.

“Hello Ya Aliyu”

“Kina ina?”

“Ina ina ina kebbi”

“Wasa na ke da ke?”

“Ya ina sama road”

“Ni da Ataa”

“Aisha... Anty Aisha”

Ta kara da Anty gaba daya. Ya san mutane biyu ne a sama road Mama Zuwaira wato kanwar Momy sai kuma Aminiyarta Hajiya Ramatu.

“Gidan wa?”

“Idan Mama Ramatu, amman Momy ta ce karna fadawa kowa inda muke har da kai”

Ya katse wayar ya ya koma cikin falon dan karbo keys din motar Momy domin ya baro tashi motar da duka keys dinsa a main house. A falo ya tsaya ya aika Siyama ta karbo masa key motar Momy, sai Samira ta mika masa nata.

“Ga tawa idan fita za kai”

“No”

Sai da Siyama ta karbo masa na Momy sannan ya fice daga falon ya nufi motarta ya shiga sai da ya cire babbar rigarsa ya jefa seat din baya sannan yai ma motar key ana bude masa gate ya dauki hanyar sama road yana ta tsara yadda zai ce idan ma yaje, daga karshe yai yanke shawarar tsayawa a waje ya kira Amina ya ce ta masa dabarar fitowa da Ataa.

ATAA POV.

Na kasa yarda cewar an daura min aure a yau ai ba yau bane gobe ne Saturday.

“Ko dai ba ni ba Amina ba sai gobe ba”

“Yau akai Daddy ya canja sharawa ne kawai dai ba a fada miki ba ne, amman an fadawa Mama cewa da Nana jiya da dare”

Rungume hannayena nai ina jin komai kamar ba gaske ba, murna zan yi ko kuka sai na rasa na farawa, Amina kan sai murna take har da nuna min hotunan daurin aure da akai yana tare da friends dinsa. Ni dai har bana iya gani da kyau na zama kamar wata dabam ba ni ba, duk wani abu da akai a can gidan sai da Momy ta dibo ta aiko mana, ni dai ko wanar ban iya ci ba yunwar rana ma sai ma nemeta na rasa, sai yanzu na gano dalilin sa a kawo ni nan da Momy tai. Lokaci zuwa lokaci Amina take mita wai ita kadai ce a nan sauran duk suna can suna da hidima. Da yamma Hajiya Ramatu ya hada min ruwan wanka mai kamshin gaske ta sa aka kirana na shiga bandakinta nai wanka ina fitowa ta ba ni wani bakin lace na saka ta fesa min turare sannan ta zaunar da ni a dakinta ta zubo min tuwo ta kawo min wai na ci.

“Na koshi”

“Daure dai ki ci ji idonki duk ya fada tun karin safe fa”

A dole na saka hannuna na soma ci ba dan ina jindadin tuwon ba domin ni ko sinadin miyar ba na ji, aure kawai na ke ta tunani wai an daura min aure, ji na ke kamar na saka kuka kuma babu damar shi gaba daya na ji na damu kuma ba damuwa ba, na saka sakewa a gidan kuma bana jin zan sake a ko'ina ma.
  Bayan sallah magariba ina zaune dakin ni kadai sai ga Amina ta shigo ta matso kusa da ni tana min magana kadan kadan.

“Ta so ki rakani wani guri kamin Mama Ramatu ta dawo”

Da sauri na tashi daman zaman dakin ya isheni ina nema inda zan sha iska na ga wasu abubuwan ko zan sake. Hijab ta dauko ta bani na saka daman ita akwai veil a jikinta sai kawai ta rika hannuna muka fita sai leke leke take kar Hajiya Ramatu ko yayanta ko wasu yan gidan su gamu, muna kawowa babban falon Wata yarinyar Hajiyar ta ta ganmu.

“Ke ina za ki je da ita?”

Amina tai mata alama da tai shiru kai Hajiya Ramatu ta ji. Ta ja hannuna muka fice daga falon muka bar yarinyar tana dariyar da ban san dalilinta ba. Gaba daya muka fice daga gate din sai da muka yi dan nisa muka kawo gurin wata mota sannan ta tsaya jikin motar ta bude min front seat.

“Shiga”

Kin shiga nai hango Aliyu a ciki rike da wayar da ke haska fuskarsa yana kallona. Amina bata tsaya bin ta kaina ba ta juya da sauri ta nufi hanyar gida, bude motar Aliyu yai ya fito ya zagayo inda na ke, na yi zaton ko motar zai saka ni sai nai saurin rufe gambun motar na juyo na fara takawa sai ya sha gabana yana murmushi. Takowa yake ta yi ina jin baya yana matsowa har na isa jikin motar gabana sai faduwa yake ban taba jin kunyarsa da tsoron a raina kamar na yau ba, domin duk wani tsoro da nake masa na gudun duka ne ko ba cin rai a yanzu kuma ban san na minene ba. Matseni yai sosai har ina iya jiyo numfashinsa kamar yadda yake jin nawa sai nai saurin rufe idona gam, hannayensa ya saka ya kama hannuna ya saka yatsunsa cikin nawa, dayan hannun ma haka yai masa sannan ya jinginar da fuskasa jikin tawa fuskar, hancina da na shi suma goga juna, goshinsa da nawa a hade ya lips dinsa kuma a saman nawa, numfashin da nake fitarwa yake shaka idan ni kuma zan shaka sai ya fido da nasa na shaka a haka muka dauki tsawon lokaci muna musanyar numfashi, jikina sai rawa yake sosai domin ba a taba min haka ba, sanyi na ji a kumatuna, idanuwana na bude sai gashin idona ya taba nasa, na yi zaton shi ne yake hawayen ashe ni ce, a hankali na ji lips dinsa a kasan idona yana sumbatar inda hawayen nawa suke taruwa.

“Ali...Al.... ”

Na kasa kiran sunansa balle na ce ya daina, sulale nai kamar zan duka kasa sai sai yai min masauki a kirjinsa ya rumgume ni tsantsan ko motsin bana iya yi, kaina ma saitin zuciyarsa ina jin yadda take bugawa da sauri. Sai da aka  fara kiran sallah isha'i sannan ya sake ni ya leki fuskata sai kuma ya kama hannuna ya dora a kirjinsa. Ya saka dayan yana murza yatsuna a hankali sai kallon fuskata yake. Ni kuwa numfashina sai gargada yake kamar zai fita daga jikina shigarsa ma daker ne, saurin lumashe ido nai na yi sai na ji sanyin yawunsa a lips dina, halshensa ya saka a cikin bakina, ba tsosar lips dina yake ba ba kuma tsutsa zai yi ba, a tsakanin lip din kasa da na sama ya zira halshen yana goga min dogon hancinsa a hancina. A take na fashe fa kuka saurin dagawa yai da kansa ya matsa baya sai ta juyar da ni ya jinginar jikin motar ya kwanto bayana ya rumgume ni.

“Wallahi ina cikin farinciki Babyna, ban san yadda zan misalta miki ba, ban san yadda zan fada miki ba”

“Hajiya Ramatu tace kar na dade”

Da sauri ya daga daga jikina ya juyo da ni ya rike kunkuruna.

“Ta san kin zo?”

Na gyada masa kai sai ya shafa kansa da dayan hannunsa.

“Kai Amman Amina wawuya ce”

Kumatuna ya sumbata da saman hancina sannan ya ce min.

“Wuce ki je”

Yana ba ni hanya na fara sauri kamar an biyoni har tashi faduwa nai. Da hawaye na shiga gidan ban san da hawayen ba sai da Amina ta tambayi abunda na ke yi wa kuka sannan na tuna da zaman hawayen a fuskata, saurin sharewa nai na dan turo baki kamar an min wani abu.
   Har muka kwanta a dakin da Hajiya Ramatu ta bamu ni da Amina ban daina jin jikina na rawa ba, ina ta mamakin abunda Aliyu yai min sai kyamar bakina na ke saboda halshen daya saka min a ciki daman da na je alwalar isha'i sai da nai ta wanke bakin da amma ban daina jin kyama ba.
   Washe gari muna gama sallah asuba Aliyu ya kira Amina a waya ta ba ni, ni kuma da na karba sai na saka cewa komai.

“Good morning Babyna batar kin tashi lafiya”

“Lafiya kalau”

“Mashallah, Amaryata mai tsada”

Na ji kunya ta lullube ni kamar ina gansa.

“Ki ci abinci ki koshi kin ji?”

Na gyada kai ba tare da na amsa ba, sai ya ji yayi murmushi mai sauti.

“I love you....”

Ya fada kamar mai rada. Sannan ya kashe wayar, ni dai mamaki ya kasa barina gaba daya ka kasa yarda cewar Aliyu ne.
Misalin takwas na safe a kawo mana abincin karyawa kala kusan uku ni dai dankalin kawai na ci na sha ruwan sanyi domin ko tea din ban ji ina shawa'awar sha ba. Ina kokarin cire tufafina na shiga wanka Amina ta miko min wayarta wai Momy ce.

“Hello Momy ina kwana”

“Lafiya kalau Aisha kin tashi lafiya”

“Lafiya kalau”

“Mashallah kina bukatar wani abun ne?”

“Ana mana komai a nan”

“Masha-Allah haka na ke so, sai anjima da dare za ku dawo gida kinji? Amman yanzu ba ri a akaiwa Nana waya ku gaisa”

Na amsa da to, haka na rike wayar har aka kaiwa Nana ina jin muryarta sai na ji wani farinciki ya cika ni cikin far'a muka gaisa da ita sannan na mikawa Amina wayar.
Kamar yadda Momy ta fada ban mu koma gida ba sai da dare na yi zaton direba zata aiko ya dauke mu ashe Hajiyar ce da kanta zata kai mu, bayan ko wace awa biyu sai Aliyu ya kira wayar Amina ya ce ta ba ni tun tana dauka tai magana har ta kai idan ya kira sai dai kawai ta dauka ta miko min, tambaya yake wai ko ina bukatar wani abun sai na ce aa sai ya tambaya na ci abinci na ce masa ce daga haka kuma sai yai shiru yana sauraren numfashi har an wani lokaci sannan ya kashe. Ko da muka shiga gidan babu kowa sai wata budurwa da kuma su Siyama da Husna da gudu suka zo suka tarbe ni

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login