Showing 78001 words to 81000 words out of 225640 words
Husna ku tashi ku yi sallah muje mu duba ta, Rukaiya da Maryam da Baby ma ku shirya muje”
Sai a lokacin Husna da Siyama suka motsa domin tun da aka fara fadan suka make guri daya kamar basa nan, ba halinsu bane kuma ba halin Momy ba ne masifa ta kan yi amman sai idan rai ya bace sosai. Gaba dayansu suka tashi suka nufi upstairs Rukaiya na fadin abunda Kamal yai be kyauta ba, Husna na taba mata duk kuwa da bata san shi sosai ba, sai dai ta taba ganinsa sau biyu tare da Aliyu.
Muhseen ma tashi yai ya fice daga falon cikin bacin ran abunda Kamal yai wanda be sake shi ba har yanzu. Momy ta kalli Mama Fulani.
“Fulani Wallahi ku canja wannan zama na ku, tun yaushe ake abu daya? Kishi fa ba hauka ba ne, Fisabilillahi haka za ku taso kuna abu a gaban yayanku kuma manyan yaya ba ko kanana ba? Wannan ai bara kan yayanku kuke yi Wallahi”
“Alhaji be auro Ramatu ba sai da amincewata kuma sai da ta yarda zata min biyayya, dan haka bata isa ta yi jayya da ni ba idan kuma har ta ce za tai nasan tsaf Alhaji zai sake ta komai yayanta”
Momy dai ban da kallon Mama Fulani babu abunda take, ta sani Alhaji Hamza yana son Ammy sosai amman yadda Fulani take mata yana kyaleta abun har mamaki yake ba, duk kuwa da irin masifarsa domin shi mafadacin mutum ne sosai.
Guraren la'asar Momy ta shirya ita da su Maryam, Rukaiya, Baby, Husna da kuma Siyaka suka fito harabar gidan sai Momy ta aika aka kira Inteesar da Batulu, Zee da Humaira suka shiga mota uku suka dauki hanyar asibitin.
ALIYU POV.
A lokacin da ya bar asibitin gidansa ya koma ya, yana shiga ya samu guri ya kwanta ba dan yana jin bachi ba sai dan ya samu sauki abunda ke zuciyarsa, matsalar iyeyen Rahma da kuma ciwonta a dayan bangaren kuma ga Ataa ta ta tsaya masa arai a yanzu yake tunanin ta ina zai fara taimakonta, what is best now is ya taimaki mahaifiyarta ta samu lafiya, sai dai be san ta inda zai samu mahaifiyar ba domin be san inda take ba, and Ataa bata bashi wata dama da zai iya sanin Familynta ba, sai dai yai ma kansa alkawarin zai taimake ta tai shiga rayuwarta ya nuna mata halinsa mai kyau da be taba nuna kowa ba, wata kila hakan zai sa ta aminta dashi har ta bashi damar sanin inda mahaifiyarta take, and ya ma kansa alkawarin ba zai sake bari a takura mata a cikin gidan nan ba, shine mataki na farko da zai dauka. Haka dai yai ta tunaninsa ta bangaren Rahma kuma idan ya fara sai ya rasa ta ina zai tuke, zancen neman wata kodar a yanzu be ma taso ba, ba dan kudi ba sai dan gudun kar a samu irin wacan matsalar idan kuma ba a samo mata wata ba, hakan na nufi nan da wani lokaci zata mutu kenan? Ko kuwa akwai wani magani da za a bata wanda zai saka kodar ta samu lafiya, ya kamata ya san wannan, idan ma zaa samu kodar a yanzu to dole ne sai ya ga mai ita kuma ya yi magana da mai ita ya aminta, da kuma amintaccen likita ba kamar Doc Asim ba. Idan kuma ba za a samu ba ya zame masa dole ya cire tashi daya ya bata domin yana son ganin matarsa a raye, and zai iya sadaukar mata da komai na sa ciki kuwa har da ransa idan da dama.
Yana kwance Siyama ta kira ya ga kiran amman ya ki ya daga domin ba shi da time din wani magana ko wani abun dabam a yanzu, sam ya manta da zancen zuwan Momy ma tsabar tunanin daya saka a gaba. Bathroom ya shiga yai wanka ya fito ya shirya cikin wasu kayan ya fito yana ta kamshin turare ya sauko kasa ya nufi wata motar dabam ba wacce ya shigo da ita ba ya shiga ya dauki hanyar asibitin.
Ko da ya shiga dakin da Rahma take ya same ta zaune saman gadon mahaifiyarta kuma akan kujera suna ta kuka, ba a fada masa ba, ya san cewa mahaifiyar Rahma ta fada mata gaskiyar ciwonta. Ganinsa yasa mahaifiyar ta tashi tana share hawayenta ta fice daga dakin shi kuma ya karaso ya zauna a kujerar da ta tashi tana ta kallon yadda Rahma take kuka. Hannunsa ya kai ya kama hannunta yana fadin
“An fada miki gaskiyar ciwonki kenan?”
Sai ta kalleshi cikin hawaye ta ce.
“Ina son rayuwa Aliyu, amman rayuwa bata so na, tun ina karama na ke ta fama da matsalar kodar nan, ima gidan aurena aka cire min daya saboda ta lalace, dayar ma aka ce sai an samo wata a dasa min, duka yaushe aka min kashen koda da har za a ce wannan ta lalace?”
Tashi yai ya koma saman gadon kusa da ita ya zauna ya ja zuwa jikinsa ya rumgume cike da tausayinta....Gyara kanta tai a kirjinsa tana hawaye.
“Babu abunda Allah ya rage ni da shi sai lafiya da haihuwa, ina da Uwa Uba yan'uwa miji duka a raye kuma duka suna so na, amman ba ni da lafiya kuma ban haihuwa, yanzu idan na mutu na zama mai yankaken baya kenan?”
“Za ki samu lafiya Rahma sai mu cigaba da neman haihuwar ki daina zancen nemam haihuwar nan a yanzu”
“Wata kila zan iya samun ciki na haihuwa ban mutu, amman zancen samun lafiya na warke kamar kowa na san ba zan taba samu ba, a da na yi zaton na warke idan aka dasa min wannan kodar amman sai gashi yanzu kuma ance ta kone”
“Dan ta kone ba shi yake nufin ba zaki rayu ba, kika sani ko ki samu sauki mu cigaba da rayuwarmu”
“Samun sauki ba abu ne mai sauki ba Aliyu, samun saukina yana nufin samun wata kodar, kai ma kuma na san ka fara gajiya da ni, Mommy ta fada ka ce ba za a sake samo wata kodar ba...”
Dago kanta yai ya rika fuskarta.
“Ban ce ba ba a sake samun wata ba, amman dai ba ta bangaren Asim ba, saboda gudun abunda ya faru ya sake faruwa”
“Amman da ada ne kome zai faru ai zaka aminta ya faru ni na rayu, amman a yanzu ka canja wata kila ka fara gajiya da ni ne”
“Taya zan gaji da ke Rahma miyasa bakinki zai rika furta irin wadannan kalaman? Ai nasan da ciwon ki kuma na aureki a haka neman kodar nan da akai har aka dasa miki ita ba wayayi ba ni ba? Idan na gaji da ke ai ba zan dauki duk wannan dawainiyar ba, amman maganar gaskiya ba zan sake yarda a cutar da wata saboda ke ba, zam iya komai dan ki rayu amman ba zan kashe wani ko na gulgunta rayuwar wani saboda ki rayu ba, ba kuma zan yarda a cire ko da kowa dan zalinci a dasa miki ke ki rayu ba, ko da kuwa hakan na nufin idan ba a saka miki ba ba zaki rayu ba, ba zan zalinci wani na raya ki ba Rahma duk kuwa da irin son da nake miki I'm telling you this form the bottom of my heart, sai dai zan yi dawainiya da ke har ki samu lafiya”
“Ko kuma na mutu ba, saboda kai ka san zaka iya auren wata mata idan bana raye amman ni na tafi kenan. What if maybe kana daukar dawainiyata ne saboda kai baka haihuwa ni kuma ba ni da lafiya, sai mu taru a haka mu mutu? Ban san yadda zaka dauki abun nan ba Aliyu, amman lokacin da ba Mommy ta fada min cewar koda ta ta kone, mutuwa ce farkon abunda ya fara zuwa min a rai, da kuma haihuwa idan na mutum ban bar baya ba, na tafi kenan, amman idan na haihuwa zan iya barin abunda za a rika tunawa da ni idan ana kalleshi”
Murmushi Aliyu yai irin murmushin nan da yafi kuka ciwo, yau wai Rahma ce take fada masa wadannan kalaman yasan tana son haihuwa kamar yadda shi ma yake sonta, tabbas mai irin matsalar ta zai son ganin zuri'arsa ko ba dan mutuwa, shi kansa yana son haihuwa amman gudun shiga damuwarta yasa shi kawarda tashi. Iyakar abunda zai iya yi a yanzu nuna mata kalamanta basu bata masa rai ba, domin idan har ya bari bacin ransa yai tasiri akansa zai iya fada mata magana marar dadi ko kuma yai fushi da ita wanda yake ganin hakan be dece ba a yayinda da take cikin rashin lafiya. Ba karamin kokari yai ba na kai bakinsa yai kissing goshinta kamar yadda ya saba yana sauke ajiyar zuciya a hankali.
“Ki kwantar da hankalinki idan kin samu lafiya za mu nemi haihuwa”
“Wata kila matsalar da daga ni ne, da yanzu Mama Fulani da Momy sun saka ka kara aure saboda ka haihu, domin ko wannensu yai min gorin haihuwa, amman da yake ka boye musu gaskiya kace dukanmu ba mu da matsala sai suka daga min kafa suna ganin kamar wata rana zan iya haihuwa, ni ma haka na ke ta saka rai ni da iyayena shiyasa na dage gurin neman magani ashe matsalar ba daga ni ba ne”
Sakinta Aliyu yai ya mike tsaye ya saka hannayensa aljihu ya tsaya gaban windows dakin yana kallon waje zuciyarsa na masa mugun kuna. Rahma kuma ta bishi da kallo tana hawaye, har ga Allah tana son Aliyu kuma tana kaunarsa amman matukar ta tabba matsalar daga shi ne dole zata hakura da shi ta auri wani saboda ta samu haihuwa domin ba zata yarda ta bar duniya ba tare da ta bar baya ba, and tana da tabbacin wata kila da ita ce da matsalar da ba zai zauna da ita ita kadai ba, da yanzu ya yi aure ko ma ya rabu da ita gaba daya kamar yadda mahaifiyarta ta fada mata a lokacin data labarta mata gaskiyar cewar matsalar daga Aliyu ne a wacan lokacin kamin rashin lafiyar ta kamata. Sai dai me wata kila idan babu Aliyu a rayuwarta ba zata iya rayuwa ba, wata kila ba zata iya komai idan babu shi ba, domin ta shaku da shi kuma tana kaunarsa irin kaunar da ba zata iya misaltawa ba.
Aliyu be juyo ba har sai da yaji an taba kofar dakin an turo an shigo. Momy ce ita da siblings dinsa. Yayi kokarin boye damuwarsa amman ya kasa har sai da Momy ta karanci yana cikin damuwar a fuskarsa. Ita kuma tai saurin share hawayenta tana kokari kirkiro murmushi, tsaye sisters dinsa sukai suna mata sannu Momy kuma ta zauna a kujera tana ta duban yanayinta da na Rahma. Aliyu ya yi farincikin ganin Momy domin be tsammaci za tai saurin zuwa a yau ta duba Rahma ba saboda yawan complain din da take cewar Rahma bata son zuwa inda take, sai dai be yi mamaki ba dan yasan halin Momy da dattako da kuma maida komai ba komai ba.
“Yanzu kuka zo?”
Aliyu ya fada yana kai hannu ya riko hannun Inteesar, sai ta dawo kusa da shi ta tsaya tana dariya.
“Tun dazun muka zo, ai na saka Siyama ta kiraka baka daga ba”
“Na ga kiranta amman ban dauka tare ma muka zo ba, na dauka rokonta ne ya tashi”
Sai dai duk sukai dariya ban da shi da yai maganar, sam ba zaka kalleshi ma ka ce shi yai maganar ba, daman haka yake ko abun dariya ya fadi na kasafai yake dariyar ba.Bayan sun gama ganinta Momy ta kallesu ta ce.
“To ai sai ku wuce ku koma, kar likitocin su zo suce mun yi yawa, kuma mun baro Fulani ita kadai gashi beta gama fucewa ba”
Aliyu ya kalleta kamar ya tambayi abunda akai mata har Momy take fadar hakan sai kuma wata zuciyar ta hana shi. Rukaiya ce tai kwafa
“Wallahi kwata kwata Kamal ba shi da mutunci kuma ba shi da tarbiya”
A take zuciyar Aliyu ta kwadaitu da son jin abunda ya faru amman ya kasa tambaya har sai da Zee da ke son ta ji labarin ta tambayi Rukaiya.
“Mi Kamal yai hala?”
Rukaiya da Maryam ne suka labarta abunda ya faru a nan Aliyu ya ji komai, wayarsa ya ciro kamar be damu ba ya nufi kofa rike da hannun Inteesar ya fice. Sai da ya fito daga ward din sannan ya turo Inteesar ta kira masa Zee, ita da Inteesar har a rigengen zuwa suke domin sun san Aliyu baya son jira, kuma abu kadan ya saka ransa ya bace.
“Zainab So na ke ki kira min Kamal ki tambaye shi wace asibiti ya kai Ataa”
“Ya Aliyu bana da number Kamal”
Ya mika mata wayarsa ba tare da ya ce mata komai ba, tana karba sai taga number Kamal a sama sakawa tai a wayarta ta kira bugu biyu ya daga.
“Hello Kamal ina wuni”
“Lafiya kalau wake magana”
“Zainab ce, wai Ammy tace a tambaya wace asibitin ka kai Ataa”
“Ammy? Ko Mama Fulani dai”
“Ammy dai”
“Perry Hospital female ward room 104”
“Thank you”
Tana fadar hakan ta sauke wayar ta yi karya da Ammy ne domin ta lura da Aliyu baya son asan shi ya saka ta kira, da acce yana so da shi da kansa zai kirashi tun da abokinsa ba sai ya saka ta ba.
“Ya ce Perry Hospital female ward room 104”
Ta fada tana mika masa wayarsa, karba yai ya saki hannun Inteesar ya fice daga gurin. Ita da Inteesar suka dawo dakin da Rahma take.
“Ku wuce kawai gida, ni zan tsaya a nan sai an jima Dan wajen Fulani zai maida ni gida”
Sai da suka mata Allah ya sauwake sannan suka fita. Bayan sun fice ne Momy ta kalli Rahma da ke cikin damuwa ta ce.
“Ciwo fa ba mutuwa ba ne, dan ba ki da lafiya ba shi yake nufi zaki mutu ba, ko babu kodar a jikinki idan Allah ya so sai ki ga ya raya ki”
“Ba neman lafiyar ne abunda ya dame ni yanzu ba Momy, haihuwa ce abunda ta dame ni a yanzu, ina son na haihu kamin na mutu”
“Duka dai na Allah ne, kuma idan yace yanzu abu ya kasance za ki ga ya kasance”
“Wata kila da matsalar daga ni ne da zan iya samun sauki ko kuma wata mafitar, amman matsalar daga Aliyu ne na san ba zan taba samun waraka ba”
Momy ta kalleta irin kallon nan na ban fahimci zancen ki ba.
“Matsalar daga Aliyu ne? Kamar ya?”
Rahma ta yi shiru bata ce komai ba, domin ta fahimci be fadawa Momy ba. A take hankalin Momy ya tashi fiye da da, domin a da tana daukar daga shi har Rahma ba su da matsala kamar yadda yake fada mata likitoci sunce yanzu kuma Rahma ta ce matsalar daga shi ne, amman miyasa be taba fada mata ba? Daman Rahma ta san da wannan ta rufa masa asiri take zaune da shi a haka ko kuwa daga baya ne abun ya bullo? Anya Mama Fulani ta sani ma kuwa? Har Momy ta bude baki zata sake tambayar Rahma sai ga wani Doc ya shigo tare da nurses kusan biyar suka hau duba Rahma suka bata magani sannan suka bawa Momy takardar sallamarta domin su a gurinsu ta ji sauki tun da ta farfado kuka bata jin ciwon komai sannan kuma an riga an san matsalar koda ne, sun kuma dorata akan magani. Daman haka suke yi sai dai idan mutum yana son ya cigaba da karbar magani a asibitin sai ya bukaci su barshi yai ta biyan kudi yana karbar magani har ya kare. Momy ta yi kokarin nuna farincikinta duk da irin tashin hankalin daya same ta na jin gaskiyar maganar cewa matsalar haihuwar daga Aliyu ne, har ga Allah ta jidadin samun lafiyarta domin ko bata san inda Rahma ta fito ba za tai farincikin samun lafiyarta a matsayinta na musulma balle kuma matar danta ce dan ta take aure. After like thirty minutes da fitar likitan Mommyn Rahma ta shigo da kanenta ai ko suka hau murna kamar su cinye Rahma sun jidadin ganin an sallame a take hakan na nuna jikin nata da sauki keman kuwa da kasancewar kodar na ta a kone yake.
“Mahaifinki ya ce ya saka cigiya a gurin likitocin daya sani a nemo duk inda koda take kuma ko nawa take za a siya miki, kin kwantar da hankali lafiya zata samu In-Sha-Allah”
Mommyn Rahma ta fada tana dariya sai dai ita Rahma bata wani farinciki sosai, domin tana cikin damuwa a yanzu. Momy ce ta kira Aliyu ta fada masa an sallami Rahma kuma ya zo ya maida ita gida, da murna ya amsa mata sannan tai hanging call din ita da farinciki tana kallon Rahma, sannan gaisuwa ta biyo bayan tsakaninta da Mommyn Rahma har suka dora da labari.ATAA POV.
Ban san adadin wannin dana dauka a sume ba, shin sumar ma nai ko kuwa dai wata duniyar na tafi na dawo domin Nana nai ta gani da kuma wata rayuwa da muka kai da ita a can baya, da kuma ganin da cikin wani daki mai kamar na kasa ba kuma kasar ba, shin haka suman yake ko kuwa fitar hankali ne kawai daga jikin duk ba zan iya tantancewa ba. Da wani irin karfi marar misaltuwa na ji na dawo duniyar motane da dabbobi har ma da sauran hallitu, duniyar da ke cike da kazanta da gurbatacciyar rayuwa da ba kowa ke tsira cikinta, wasu abu nake gani su ba mutane ba kuma su ba aljannuna ba, ganina nai kasa bana iya tantance ko mienene sai dai ina ganin kan abun yana yawa kuma suna sanye da fararen kaya. Daga bakina har hanci da ido numfashi suke fiddawa da karfi wani kuma na shiga da karfi, wani abu ne a kirjina kamar dutsin guga da zarar numfashin nawa yai kasa sai su goga shi da dan'uwansa su manna min shi a jiki sai na ji makamancin abunda na ji dazun, haka sukai ta min har