Showing 102001 words to 105000 words out of 225640 words
kalli kudin kamar ya karba sai kuma ya dan tsaya jan aji.
“Ai ba kudi ba... ”
“Idan zaka karba ka karba kawai ba zan tsaya magana da kai ba na fada maka ina da matsala”
Hannun mutumen ya kai ya karbi kudin yana dan nuna kamar be so ba. Aliyu ya juyo ya bude motarsa ya shiga mutane sai kallonsa suke yai mata key ya sake hawa titin yana ta tasbihi saboda samun fin karfin fushinsa. Wani guri ya samu can kusa da ga ďan k'ane hotel ya faka motarsa ya fito yana shakar iskar gurin. Har yanzu ya kasa daina jin kalaman Ataa a kunensa sai dai wannan karon a maimaikon ransa ya bace kamar dazun sai tausayinta ya soma rabar zuciyarsa fiye da da, yarinyar da ke tsoronsa da masu kudi tun da har ta iya bude baki ta fada masa magana irin wannan tabbas tana cikin damuwa da bakinciki, ya sani ko Ataa zata fahimcin ba nan kusa ba kuma ba a yanzu ba. Yanzu ma laifin ba nata bane na Muhseen ne, for what zai fada mata cewar mahaifiyarta zata manta da ita? For what zai mata karyar cewar da hadin kan Aliyu aka cire mata koda? Komawa yai cikin motar a fusace ya dauki hanyar gidansu Momy.
**ZAKI
By Khadeeja Candy
32...
Abinci kusan kala hudu Mama Fulani ta shirya ma bakon da zaizo, ko da tara tai gaba dayansu sun shirya Maryam da Rukaiya sukai wanka Baby ce kawai ta wuce scul. Amman shiru bako be iso har goma da rabi. Sai misalin sha daya Abbah ya kira yace mata bakon ya sauko Nigeria gashi nan ma zai taro shi a airport.
A sannan ne Mama Fulani ta saka su maryam suka kwashi kulolin abincin suka jera part din Abbah, ita kuma ta kunn turaren wuta irin mai kamshin nan sosai na larabawa ta kara kunna dayan ac sannan ya dawo part dinta, a daki ta samu su Maryam da Rukaiya sai kara gyara fuskarsu suke suna fesa turare. Wani dadi ne ya lullube ta ganin duka yayan nata sun fito fes gwanin sha'awa. Suna jin tsayawar mota sukai hanzari yafa gyalensu suka jiyo bayan Mama Fulani dake cikin wata shadda yar mali ta sha paint work gwanin sha'awa.
Mota biyu ce ta Abbah da kuma wata mai tsada da suka shigo, ta kamfaninsu da ke nan Abuja. Suna fitowa daga motar Mama Fulani na fitowa ita da su Maryam suna musu marhabun bakin Mama Fulani har kunne, a maimakon mutum daya sai suka ga samari biyu dayan sanye da kananan kaya dayan kuma sanye da farar shadda ya nada bakin rawani a kansa kamar wani balarabe.
“Lale marhabun Lale lale marhabun da manyan baki”
Mama Fulani ta fada tana kokarin sauka daga balcony din ta nufi inda suke, sai duk suka saki murmushi suna kallonta.
“Sannu da zuwa”
Maryam ta fada kamin Rukaiyah ta dora da nata. Dayan ne ya amsa yayinda yadan kuma yake ta kallonsu yana murmushi kamar baya jin abunda suke fada. Abbah ne yai gaba zuwa part dinsa yana musu iso sai suka bishi a baya, bayan sun shiga ciki sun huta ne Abbah ya shigo part din Mama Fulani ya kira dan taje su gaisa da su, sannan ya shiga bangaren Ammy ya same ta falonta zaune ita da yaranta suna kallon wani film da ake hassaka a mbc Bollywood.Ganin Abbah yasa Batula da Zainab tashi zaune suna murna domin ba su san da shigowarsa ba sai ganinsa a falon.
“Sannu da zuwa”
Ammy ta fada tana dariya, sai ya zauna kusa da ita yana kallonta.
“Yauwa Hajiyar gida, ban fada miki za'ayi ba ki ba?”
“Na sani na fada min, amman naga ai Hajiya Fulani ce zata shirya komai ko?”
“Ko dai zata shirya ai ya kamata ku gyara ku fito ku tarbesu, na fa sha fada miki cewar bana son yawan kebe kanki da kike yi”
“Bana son yawa shiga Safgar Hajiya Fulani ne, bana son nai mata abunda zai zo ya zame mana matsala ko ka zo kana mim fada”
Be sake ce mata komai ba ya kalli yaransa.
“Batula ku tashi kuje ku gaisa da baki”
Gaba dayansu suka tashi suka Batula ta tashi ta shiga dakinta ta dauko mayafi Zainab kan haka ta fita ita Humaira daman abaya ce a jikinta da dankwali, Abbah ya biyo bayansu yana jerowa da Ammy Inteesar kuma na rike da hannunsa suka nufi part din. Ko da suka shiga Mama Fulani na zaune saman kujera tana watsar hakora Rukaiya da Maryam kuma na zaune a kujera daya ko wacce na duba wayar hannunta ala ala kowa waccensu take daya daga cikinsu ya ce yana sonta. Ganin Abbah tare da Ammy ya mugun batawa Mama Fulani rai, domin ita kwata kwata bata son yana kula Ammy da yayanta, sai dai kawai ya ji da ita da yayanta. Abbah ya zauna yana nunawa bakin nasa iyalansa sannan ya juyo yana fadawa Mama Fulani.
“Wannan Sunansa Amir saboda yana da sunan Mai Martaba da shi shiyasa ake ce masa Amir baya jin hausa sai faransanci da buzanci sai kuma English wanda shi gama duniya ne a yanzu, wannan kuma Sunansa Usman shi yana jin hausar”
Da turansanci Maryam ta shiga gaishe da Amir din da idonsa ke kan Zainab, ya amsa mata ita da Batula sai ya sake kallon Zainab wannan karon sai da suka hada ido. Da yaren faransanci Zainab ta gaishe shi sai ya amsa mata yana dariya tare da tambayarta wai ashe tana jin faransanci, sai tai dariya ta soma fada masa cewar ta yi karatu ne faransa ita da Batula, bakinciki kamar ya kashe Mama Fulani domin shi ma dayan ta lura Humaira yake kallo yana ta murmushi gashi ba ma wata kwaliya sukai kamar na yayanta ba.Bayan sun gama gaisawa ne sun fice Abbah ya kira wani daga kamfanin ya zo suka soma nuna masu yadda abubuwan suke, ba dan ba su sani ba sa dan kara tabbatar musu da komai a agabansu. Daga bisani suka fito domin zuwa ganin cikin Kamfanin, a lokacin ne Ammy da yaranta ita da Mama Fulani suka fito gaba dayansu suna musu sallama domin daga can ba za su koma ba zasu dawo nan ba.
Usman ne ya ciro kudi mai yawa ua bawa Inteesar ya ce su raba, sannan ya ciro wasu ya bawa Ammy da Mama Fulani, Amir kan sai da ya shiga mota a side din da yasan Abbah ya ba zai hango su ya sauke gilashin motar yacs ta Zainab ta zagoyo cikin yaren faransanci sannan ya rufee glass din. Zagayowa tai kamar yadda ya bukata sai ya mata sallama sannan ya mika mata katinsa da kudi mai yawa wai su raba. Godiya tai masa sannan ta matsa baya dayan ya shiga mota Abbah yaje ya shiga tashi suka bar gidan.
“Kawo kudin nan?”
Mama Fulani ta fada rai a bace sam bata jidadin yadda ya kira Zainab ba.
“Batula karbi ki bata”
Ta fada tana mikawa Batula kudin kamin Batul ta karba suka fadi kasa bata tsaya komai ba ta juya zata tafi sai da Ammy ta daka mata tsawa.
“Zainab dawo ki dauki kudin nan ki bata”
Juyo tai ya dawo ta duka har kasa ta dauko su ta karaso gurin Mama Fulani ta mika mata. Wani bakin haushi Mama Fulani ta ji ganin kati a hannunn Zainab tasan bata shi yai.
“Wato rashin kunya za ki min ko? To bari ubanki ya dawo sai wani kadadi take jikinta na rawa wai ita ta ga maza”
Uffan Zainab bata ce mata ba, saboda Ammy na tsaye a gurin kuma ko ba komai tasan Mama Fulani matar mahaifinta ce be dace tai mata rashin kunya ba. Fisgar kudin Mama Fulani tai har kumbarta na yagar hannunn Zainab.
“Fitsararriyar yarinya marar tarbiya”
“Zainab tana da tarbiya Hajiya Fulani domin uba daya ya tarbiyantar da su”
Cewar Ammy cike da jin zafin yadda Mama Fulani take ma yarta tana jan hannun Inteesar su nufi part dinta, daman tuni Mama Fulani ta karbe kudin hannun Inteesar.
“To ai daman na san ke kike koya musu yadda za su min rashin kunya da rashin kamun kai an ga maza sai karkadi ake ba ko kunya”
Mama Fulani ta fada cikin daga sauti tana bin bayan Ammy da yayanta da harara. Kamin su juya su koma ciki Maryam uwar masifa bakinciki ya hana ta cewa komai domin ita kan ta kyasa da ganin Amir din.Sai da suka zauna a falo sannan Mama Fulani ta kallesu.
“Ku kuma kun wani cika hoda kamar aljanu ai dole ba za su ga yadda ainahin kyauku yake ba”
“Ba wani rashin ganin kyau wannan kwaliyar da ke maida mummuna mai kyau ma, kawai dai bakij asirin Ammy ne ba banza take ba rinsu ba, tun da dai ba kyau suka fi mu ba”
Cewar Maryam tana wani bata fuska tana cin magani. Rukaiya ta tsire baki.
“Haka fa ranar muka fita da Inteesar wani ya zo yana ta daukar mata kaya sai rawar kai yake, ga ni ni babban amman Wallahi ta Inteesar kawai yake har da wani cewa Antynmu za ki ba ni wannan? Sai da na ce masa Abbah mu fada yake idan yaga ma muna magana da maza sannan ya kama kansa”
“Waya sani ko asiri tai muku ma? Ni fa abun nan har mamaki yake ba ni da tsoro ga kunan Masha-Allah da ku amman ace babu wanda zai zo ya taya, idan an zo ba za a koma ba, sai wani jikon ke Maryam Kamal din nan ke kawai yake zuwa gurinki shima sai can ba a rasa ba yanzu kuma yana ganin wannan shegiyar yarinyar Ataa ya koma kanta har ta kai mu ga tsabani”
Maryam ta kalli Mama Fulani da ke zancen ta ce.
“Nima fa abun yana bani mamaki Wallahi, kin ga zata iya mana mu aki mu ita a so yayanta, ba ki ganin yadda Abbah yake rawar jiki da ita?”
“Ai ku ba ku san komai ba, ni nan na san komai lokacin da aka kawota tana amarya a gidan nan sai kun ga yadda Abbah ku yake rawar kai da ita, ina tunanin tun can gidansu aka shirya mata ko minene sai da na tashi tsaye sannan na samu yancina a gidan nan, amman barta ko yanzu ai ba zan zura muku ido ba, shekara nawa da kare makaranta kunan babu mai shinshini, amman ita ko jiya na ga Batula tana tadi da wani”
Mama Fulani na fadin haka Maryam ta tashi ta nufi upstairs cikin wani irin haushi abunda ya faru.ATAA POV.
Zaunawa nai kamar yadda Doc Bukar ya bukata shi kuma ya fice daga dakin. Fita Doc Bukar yai a dakin be dade ba ya dawo dauke da gorar ruwa da tissue ya miko min, karba nai na share magina da hawayena sannan ya bude gorar ya dauki kofi ya zuba ruwan mai sanyi ya ba ni, da na sha sai na ji wani sanyi a raina har an samu sauke ajiyar zuciya.
“A karo?”
Na girgiza masa kai alamar a a sai ya karbi kofin ya aje ya zauna a kujerar da Aliyu ya tashi yana kallona.
“Za mu iya magana?”
Na kalleshi tare da gyada masa kai ima ta shisshikar kuka.
“Siyarda kodar mahaifiyarki kika yi wa Aliyu ko?”
“A a cirewa yai da karfi shi da wani likita, cin amanata yai ya zalince ni”
“Kamar ya ba da saninki ba?”
A nan na labarta masa abunda ya faru tun daga kan saran macijin har kawowa yanzu. Tausayina ne ya bayyana a fuskarsa karara wayarsa na ringing ya ki ya daga sai kallon yadda na ke hawaye yake.
“Na san Doc Asim kwararen likita ne mai zaman kansa, kuma likita da zai iya komai saboda kudi, wata kila ya yaudare ki ne ya cire kodar ya siyar musu”
“Taya mutum zai siye koda be san mai ita ba? Taya?”
Na tambaya cikin kuka, sai dan risino kusa da ni yana kallona.
“Ba lallai ne sai Aliyu ya san da hakan ba, kuma ina tunanin idan Aliyu ya sani ba zai karyata ya ce miki be sani ba, domin na san Aliyu tun ba mu san kanmu ba, he's my childhood friend mun dade a tare, da ya sani zai amsa miki ya sani ko da kashe shi za'ayi, Aliyu mutum ne kai fi daya, idan yace maka yes go yes din ne ko dai ka yarda ko karka yarda”
“Wata kila ya yi hakan ne dan ya kare kansa”
“Idan kokarin kare kansa yake, kotu zai kai ki yace zaki bata masa suna, ko ka ya saka a koreku daga garin nan, domin Mahaifin Aliyu babban mutun ne mai mutunci a garin nan ko a gurin gobna yake so abu a take ake masa, ko dan saboda gudun bacin suna zai iya sakawa a koreku ko kuma ya kyaleki mahaifiyarki ta mutu ke kuma ki shiga wata rayuwar kin ga shikenan ko? Amman har jininsa ya bawa mahaifiyarki jiya gora uku aka saka mata, zan iya yarda Aliyu yayi kuskure na rashin bincikar inda kodar ta fito, kuma zan iya runtse miki cewar ba da hadin bakinsa akai miki haka ba, kudin aikin da akai ma mahaifiyarki ma a yanzu shi ya biya kuma ya biya na magani da komai and ya fada min cewar yana son mahaifiyarki a raye”Sai yai kamar be ji me nace ba ya nufi gurin jinin yana gyarawa sannan ya ce.
“Ba zata farka da wuri ba wata kila sai nan da awa 48, ba lallai ne idan ta manta komai ya zama ta tuna ba, ba lallai ne kwakwalwarta ta dawo ba”
Kasa ce masa komai nai domin na fahimce na kuma fahimci abunda yake fada.
“Gaskiya kin yi kuskuren barin mahaifiyarki tana cikin wannan ciwon na tsawo lokaci haka, da an dauki mataki da yanzu duk hakan ba zai faru ba”
Har yanzu hawaye kawai nake har bana iya ganin fuskar Nana da nake kallo. Ko da na yarda cewar Aliyu ba da saninsa aka min haka ba, ba zan taba iya ganin kimarsa ba har abada, domin saboda matarsa akai wa Nana haka. Ji nai an dago fuskata sai hawayen suka kwanto min na ga fuskarkar Muhseen da ke kallo na ido cikin ido.
“Mahaifiyarki zata tashi ta ji sauki na tabbatar miki wannan, amman ba zata iya gane wacece ke ba ba kuma zata iya tuna komai ba, sai dai karki nuna mata cewar akwai wata rayuwa ta baya da tai a yanzu, sai nan da wani lokaci idan ta fara shan magani”
Sai a lokacin na iya bude bakina na amsa masa da to ina kawar da fuskata daga rikon da yai min.
“Kar abunda Aliyu yai ya dame ki, ke dai ki maida hankalinki gurin neman lafiyar mahaifiyarki kawai kina mata addu'a”
“To”
Na fada murya can ciki, sai na zauna a kujerar da ke nan na rumtse idona ina hawaye. Ina jin lokacin da ya fice daga dakin ya bar nan a nan na samu damar yin kukana na tausayawa kaina kuma na tausayawa Nana na halin rayuwar da muke cikin, ban taba tunanin za mu jidadi ba amman a kullum ina fatar zata samu sauki mu cigaba da rayuwar mu kamar yadda muka saba. Misalin biyar da rabi Momy ta zo ita da wata bakuwar fuska ta riko mana lemu da ayaba da kankana. Na gaishe ta da muryata mai sautin kuka sai ta amsa min tana kallon yanayi na.
“Ataa ki kwantar da hankalinki Mahaifiyarki zata samu lafiya ta tashi In-Sha-Allah”
“Muhseen ya ce idan ta farka zata manta da komai, ba zata iya tuna komai ba kuma ba lallai ne tunaninta ya iya dawowa ba”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kuma dai? Kai Subhanallahi wannan abun babu dadi ji”
Ta fada cike da tausayawa sannan dakin yai tsif kamar babu kowa a ciki. Ni ina hawaye ita kuma tana ta kallona ta kasa yin komai.Shiru nai ina nazari maganarsa, wata kila da gaske be sani wata kila kuma shi ma wannan likita hadin baki yai da shi kamar wacan dan ya wake kansa.
“Idan na akan kuskure yai ko kuma da ganganci na bar shi da Allah shi da duk wanda ya cuce ni Allah zai saka min”
“Allah zai kwatar miki hakki ki a nan duniya ko kuma gobe kiyama, na jidadin da kika san da hakan kuma kika yarda, Aliyu kuma be biya ni ko ya roki na fahimtar da ke haka ba, hasalima bansan cewa da zalinci aka cire miki kodar ba sai yanzu, sai dai na san da zalintar yai da ba ki isa ki tsaya a gabansa ki fada masa magana mai daci haka ba, idan har shi azzalumi ne a take zai batar da ke ua shafe labarinki a doron kasa, dan haka ki kwantar da hankali ki daina damun kanki da wata damuwar a shekarunki”
Hannu nasa na share hawayena na kawar da fuskata.
“Na sani uwa tana da muhimmanci dole ne za ki ga abunda akai miki da fadi, amman ki rika tsayawa kina tunani a ko wane lokaci kamin ki aikata abu”
Mikewa yai tsaye ya fice ba tare da ya sake ce min komai ba. Ni kuma na kwanta a saman gadon ina jin zuciyata tana min wani mugun zafi, idan har Nana ta manta da komai ciki har da ni ban san yadda zan yi rayuwa ba, addu'a kawai nake ina rokon Allah kada ya kaddara hakan ta faru.
Sai kusan la'asar aka fito da Nana daga dakin tiyata, ko da aka dawo da ita dakin tana bachi suka saka mata jini tare da lullube ta da zanen da Momy ta aiko mana. Ni kuma na tsaya a kanta ina ta kallonta hawaye na ta min zuba kamar ba gobe, tsoro nake kar abunda Muhseen ya fada ya zama gaskiya.
“Ke wai ba ki gajiya da kuka ne?”
Muhseen ya fada bayan ya shigo dakin yana nufo inda nake tsaye ina kallon Nana.
“Anyi tiyata cikin nasara sai dai fatar samun sauki, dan haka ki daina kuka”
Dagowa nai na kalleshi.
“Yanzu da ta farka mantawa za tai da ni ko?”Daga tsayen da take ta zo kusa da ni ta tsaya ta kai hannu ta dafa kafadata.
“Wata jarrabawar da sauri take zuwa wata da dadewa wata kuma sai daga karshe, wadanda take zuwama daga