Showing 48001 words to 51000 words out of 225640 words

Chapter 17 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

take watsa masa harara da alama bata jindadin yadda yake min magana ne. Fitowa nai daga part din na nufi garden din, ina shiga na samu kaina a cikin wani irin katon guri mai shuke shuke kala kala ga wani bangare an ware anyi pool mai zubar da ruwa gwanin sha'awa. Inda na hango fanfo na nufa na kunna daya nai alwala na shimfida dan kwalina kamar dazun nai sallah, da nai sallah sai na yi zamana a gurin ina ta kalle-kalle kamar an ce na juyo sai na hango mutum ta windows mai gilass yana kallona, kasa nai da kaina ina jin tsarguwa da kallon wata kila ma ya dauki tsawon lokaci yana kallo ban sani ba. Tasbihi na shiga yi da hannuna ina tasbihi da na gaji na tashi na koma part din dan na fara jin yunwa sosai, ina ko shiga na samu su sukansu a dinning suna cin abincin, a inda na zauna dazun na sake zama na labe bayan kujera.

“Yar kyakkyawa zo ki karba”

Muryar Ya Muhseen ce hakan yasa ni lekowa sai yai kirana da hannu, ba musu na tashi na karasa inda suke sai ya miko min plate din abinci cike da nama.

“Muhseen you know me well bana son haka, bana son wani ya ci abinci da kwannon da muke ci”

Mama Fulani ta fada tana kashe ido.

“Yunwa take ji”

“Dan tana jin yunwa sai ta ci abincin a plate din ka? What nonsense is this? Ke tara dankwalinki ki zube, kamin a duba miki wani gurin”

Mai nema sai hakuri, a haka na cire dankwalin kaina na aje akasa sannan na karbi abinci na zube a dankwalina yana ta kallona cikin yanayin da ke nuna be jidadin hakan ba, na dauka na fito daga falon gaba daya na koma garden na zauna na ci abuna sai da na koshi sannan na bude fanfan ko na sha ruwa na wanke dankwali na shanya. Ina gurin wani matashin saurayi dan kazo na zo ya same ni a gurin yana fadin.

“Ke zo a nuna miki gurin kwananki”

Tasowa nai na biyoshi yana gaba ina biye har muka isa gurin motocin gidan, wani tsohon gareji ya bude ya nuna min shi.

“Nan za ki rika kwana”

“To na gode”

Sannan ya juya ya tafi ni kuma na zauna a gurin, ina ta kallon yadda yai datti, ba a dauki lokaci ba sai gashi ya dawo da tsintsiya ya bani wai na gyara gurin, haka kuwa akai na share gurin tas sannan ya sake dawowa ya miko min tabarma yai tafiyarsa. A gurin na shinfidata na koma part din Mama Fulani na dauko yar ghana most go dina na dawo dakin na aje, sannan na dauko dankwalina. A gurin an kwana har safe asubar fari na farka daman ban yi bachi kirki ba, sakamanon rashin abun rufe gashi garin da sanyi, garden din na nufa nai alwala na sake dawowa nai sallah. Ina gamawa na nufi part din Mama Fulani ina taba kofar na ji ta a bude na yi mamakin hakan ganin jiya da muka zo da Maman Salma sai da aka bude mana, kitchen na nufa neman tsintsiya ba dan na san tana nan ba, sai dan neman tunda babu wanda zan tambaya, ta can kofar fita daga kitchen din ta dayan bangaren na samu tsintsiyar da mopper na dauko na zo na share falon tas kamar yadda aka fada min sannan na fara mopping.
Ina gaf da gamawa Ya Muhseen ya shigo falon yana sanye da Jallabiya.

“Eyyy ashe jaruma aka kawo mana, tun da safen nan kike mopping”

Na risina har kasa ya gaishe shi.

“Ina kwana”

“Lafiya kalau”

Sai ya amsa min da kamar mamaki.

“Amman tarbiyarki ta burgeni, ya sunanki ma?”

“Aisha”

“Ashe ki Mamansu Ammy ce, amman ke Fulani ce ko?”

“Buzuwa”

Na bashi amsa a takaice. Sai ya zauna saman sofa yana fadin

“Kina makaranta?”

Na girgiza masa kai.

“Miyasa ba ki san karatu yana da amfani ba”

“Na sani”

Na bashi amsa a takaice zuciyata na sosuwa da tambayarsa, na san da ace ina da halin karatun da babu abunda zai kawo ni nan, kuma babu abunda zai saka Doc Asim ya cuce ni.

“Ni nan da kika gan ni babu ruwana da karatu bana makaranta”

Kallon mamaki nai masa kamin na ce.

“Ka kare dai”

“Aa ban kare ba ni ban taba yin karatun ba”

“Likita ne kai fa”

“Inji wa?”

“Ranar da na ganka uduth da kayan likitoci na ganka kuma wani ya ce Doc”

Ya dan wara ido.

“Kai ashe kin iya gulma”

Kunya ce ta baibaiye ni har na kasa sake daga kai na kalleshi shi kuma ya saka min dariya. Ni dai ban ji ta kansa ba har nai na gama na koma kitchen din na gyara na wanke komai na aje, ina kokarin ficewa sai gashi ya shigo ya nufi gas yana fadin

“Kin iya amfani da gas ki dafa min Lipton?”

“Ban taba ba”

“Okay bari na nuna miki saboda wata rana, and wadacan plates din ba haka ake aje su ba, idan Mama ta gani zata miki fada gogewa ake sannan a jera”

Shi ya nuna min yadda ake kunna gas din sannan ya nuna min inda kyalle yake na dauko na goge komai naje a yadda ya nuna min. A yadda na lura Ya Muhseen ne ya fita dabam da mahaifiyarsa da kuma yan'uwansa domin mutum ne mai son fira ga far'a ba shi matsala da mutane domin a jiya kawai da na zo gidan zuwa yau da safe na ji na sake da shi kamar na sanshi.
Bayan na gama da falon na nufi falon Ammy ita na gyara mata, ko da na dawo part din Mama Fulani na samu duk sun fito daga dakunansu sai na sauki tsintsiya na nufi upstairs da zimmar gyara musu bedrooms dinsu sai Mama Fulani ta ce da ni.

“Idan kin gama kije ki gyara part din Muhseen”

“To”

Na amsa a ladafce sannan na haye sama na tura dakin farko.




1️⃣6️⃣


*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
18.

A hanyarsa ta gida ya kunna datarsa ya aikawa Nasir sako ta whatsapp.

“Yarinyar an ce tana Kaduna unguwar Malali, ka sa a bincika min ita daga gobe, ka saka kudi a nemota”

Yana rubutawa Nasir hakan ya aje wayar da a cinyarsa ganin Nasir din baya online ya cigaba da driving dinsa, a hankali yake tukin har ya isa gidansa, horn daya ya danna aka bude masa gate din, be shigo ciki ba sai ya tsaya a jikin gate din yana kallon katon gidansa, wani dogon numfashi yaja ya sauke yana kara duba tsarin gidan kamar wanda ya fara ganinsa a yau, maganar nan ta dazun ce ta tsaya masa a rai, how on earth za a ce wani be da gidan kansa kuma be da kudin da zai iya biya ya kama haya? Mai gadin ne ya zo gurin motar ya dan risina yana daga masa hannu.

“Ranka ya dade lafiya dai?”

Ya tambaya dan a tunaninsa ko shi yai masa wani abun da ba daidai ba. Kallonsa kawai Aliyu yai ya dauke kansa yaja motar zuwa harabar gidan yai parking.

“Shiyasa take yin bara take wankin mota a titi aikin maza?”

Ya furta yana fitowa daga motar, be san dalilin daya hana shi jindadi ba jin cewar su Ataa basa da gida har sun raba a wani gurin an koresu, he know be cika damuwa da sha'anin kowa ba but wannan ya tsaya masa a rai for no reason.

“Zata iya jefa kanta a matsala saboda kyauta”

Ya fada yana ta tuna fuskarta, dagon hancinta manyan idanuwanta masu kamar madara ga gashin daya gani a bayanta duk kuwa da kasancewar ba a gyare yake ba amman dai ya fahimci tana da long hair.

‘Ina ruwana da halin da zata jefa kanta, ni dai abunda na sani an cuceceta and ya kamata na fahimtar da ita abunda akai ba laifin mu bane that's all, babu ruwana da wani rayuwarta can be ma kamata nai wannan tunanin ba’

Sai ya ji kamar darajarsa ta rage taya ma zai yi wannan tunanin tun a farkon fari, rufe motar yai ya nufi kofar shiga falon wayarsa a hannunsa daf da zai shiga wayar tai vibration sai ya shiga ya samu kujerar da ta baya stairs baya ya zauna yana mayarwa Nasir da amsar sakon da ya turo masa.

“Zan saka a bincika, amman Momy ta san da maganar kuwa?”

“Kai dai ka saka a bincika kawai, idan an ganta ka fada min zan fada maka next abunda za ayi”

“Za a bincika In-Sha-Allah”

Thanks.

Yana rubuta masa haka ya kashe datar ya mike tsaye sai ganin Rahma yai a bayansa idonta taf da hawaye har wasu sun fara sauko mata, saurin aje wayar yai a kujera ya zagoyo inda take ya dafa ta.

“Minene?”

“I was such a fool da na yi tunanin ba zaka iya son yarinyar nan ba, ashe ita kaje nema? Yanzu kuma ita za aka saka Nasir ya nemo maka? Why Aliyu? Kazamar yarinya kamar wannan”

“No no no, haba Rahma yaushe kik fara munanamin zato? Ko zan yi soyayya da wata ai ba wannan kazamar ba, yar talakawa taya ma? Wallahi ba son ta na ke ba, kawai yarinyar tana bala'in ba ni tausayi ne, kuma kin ga sanadin mu an zalince ta be kamata mu kyaleta ba”

“Ba mu muka zalince ba Aliyu miyasa ka kasa ganewa? Shi kansa Doc Asim ba zai zalince ba, ai ya fada maka ya bata kudi ita ce take son masa sheri wata kila ma hadin kai ne da ita dan ta bata mishi suna”

Ya san duk yadda zai yi kokarin fahimtar da ita a yanzu ba zata fahimta ba, domin ranta ya bace sosai and ya san wani abu makamancin wannan be taba shiga tsakaninsu ba, ba lallai ne ta karbi abun a zuciyarta ba, musamman a yadda tai masa fahimta baibai,rumgume ta yai ya saka yatsunsa cikin nata. Ita kanta bata taba jin abu ya daki kirjinta ya ratsa zuciyarta yana neman numfashinta ba irin yau, ashe haka kishi yake, ashe haka ko wacce mace take ji idan mijinta na son wata? Bata taba samun kanta a cikin wannan yanayin ba sai yanzu, fashewa tai da wani irin kuka kamar an mata mutuwa shi kuma ya kara matseta a kirjinsa yana shafa bayanta, one of abunda ya tsana is kuka, kukan kuma ya zama shine silar musamman Rahma da baya son abunda ya taba ta. Sakinsa tai tana saka hannunta ta share hawayenta, sai ya mika dukan karfinsa ya rika ta a tare suka rika taka stairs din har ya shiga da ita dakinta bakin gadon suka zauna ita da shi, ta saka duka hannayenta ta rike masa riga hawayen na bin idonta.

“Wallahi Aliyu idan ka so wata zan iya mutuwa, ba zan iya sharing dinka da kowa ba, ba zan so wata ma ta so ka ba balle har ka so ta i just can't”

Tausayinta ne ya kama shi sai ya kara natsowa kusa da ita ya kai hannunsa ya rika fuskarta.

“Babu kowa a zuciyata sai ke ke kedai, ba zan taba son wata dabam ba, ko da ba ki da rai ballantana kina raye, kina jin kin kyauta min idan kika kawo ma kanki cewar zan iya son wata yarinya kamar wacan yarinyar? Karamar yarinya kuma yar talakawa yarinyar da ta zo aiki a gidana? Haba Rahma ki rika tunani kamin ki yi abu mana you should trust your husband”

“Tana da kyau amman”

Ta fada tana yawo da idonta a fuskarsa.

“Yes she's pretty amman ba hakan zai saka na so ta ba, taya wai zan so wannan yarinyar ai abunda ba zai taba yiyuwa ba ne, ki ma daina wannan tunanin kar mu samu matsala da ke”

Ya fada yana tuna masa bacin ransa karara, dan har ga Allah da ba matarsa ce Rahma tai masa wannan zargin ba da ba zai dauka ba, shi be ga dalilin daya da zai saka shi son Ataa ba, daga kawai ya nuna tausayinsa sai Rahma ta kasa fahimtarsa, tausayinma da ba a zalince dalilinsu ba da be ga abunda zai saka shi jin tausayin nata ba. Cewar da yai yes tana she's pretty yasa Rahma jin kamar ya ce yes sai na aureta, at least ya yara kyauta ai abunda be taba ba, ko a tv suke kallo be taba kallon wata a gaban idonta ya ce tana da kyau ba, idan ya kama dole ya fada sai dai ita Rahma ya ce tana da kyau, domin kullum cikin yaba kyauta yake, amman a yau yace yes wata bayan ita tana da kyau and ita kanta da take mace ta san Ataa na da masifar kyau balle kuma Aliyu da yake namiji, bata jin nadamar sanin wani a rayuwarta kamar yadda ta ji na sanin Ataa ba, daman tana yawan jin cewar ba a son daukar an aiki kwace miji suke amman bata taba yarda ba sai yau, da tun farko Ataa bata zo aiki gidan ba, da Aliyu be ganta ba, har ta ga Doc Asim ta masa wannan kazafin da zai saka Aliyu ya tausaya mata.
Yana rungume da matarsa har aka kira sallah magariba, sannan ya sake ta yana kallon fuskarta ya ce.

“Zan je masallaci daga can zan mana takeaway okay”

Ta gyada masa kai tana jin zuciyarta na yi mata yawo da wani abu marar dadi. Goshinta ya sumbata da alama sumbantar goshi yana cikin abunda ya fi kaunar yi a jikin mace, sannan ya tashi tsaye ya nufi kofar fita yana takunsa cikin kasaita kamar yadda ya saba, ita kuma ta bishi da kallo har ya fice, sannan ta tashi ta koma gurin windows ta cigaba da hangensa har ya kunna motar aka bude masa gate ya fice. Sallah ce kawai ta zame mata dole, ita a gaggauce tai yi ta kamar wacce ake jira ta dauki guntun veil dinta ta saka ta dauki makullin motarta ta sauka downstairs tana ta sauri kamar zata tashi sama, tun kan ta shiga motar ta fadawa mai gadi cewar ya bude mata gate, tana shiga ta fisgi motar kamar ba daga cikin gida zata fita ba. Arkilla ta nufa so take taje ta labartawa Momy abunda yake shirin faruwa dan ta san Momy bata san Aliyu yana ganin ya zalinci wata yarinya ba.
  Ta isa cikin sa'a domin ta isa a lokacin da duka sisters din Aliyu suke falo Momy kuma tana dakinta zaune bayan gama sallah magariba, su kansu sun yi mamakin ganinta a gidan domin ba karamin abu ke kawo ta gidanba, sai idan za su koma Abuja ta zo bankwana ko kuma idan anyi wani biki ko gaisuwa rasuwa ko wani abun dabam. Cikin mutunci suka gaisa da ita dan haka suke daukarta kamar ba matar yayansu ba ko irin wasan nan na matar yaya da kannen miji bata yi da su, wai kar su rainata daman ta san family miji ba son matar dan'uwansu suke ba.

“Momy na nan?”

“Eh tana dakinta”

Rahila ta amsa mata, sai ta nufi dakin da tana gyara veil dinta wai za a hadu da suruka, iyakar kokarin da tai na tara hawaye a idonta ne yadda Momy zata fahimci akwai damuwa a tare da ita, duk da yake a fuskarta kadai ya nuna tana cikin tashin hankali. Da sallama ta shiga tana maida kofar dakin ta rufe, Momy ta amsa mata tana aje wayar da ke hannunta tare da kallonta. Kusa da Momy ta zube zaune ta fashe da kuka, wanda hakan yasa hankalin Momy ta shi sosai.

“Momy kin san Aliyu yana son wata yarinya yar talakawa wacce ta zo aiki gidanmu?”

Jin hakan yasa hankalin Momy kwantawa daman can farko ta dauko wani abun ne na dabam ba wannan ba.

“Yana son wata? Shi ya ce miki yana son ta?”

“Ya ce ba sonta yake ba, wai tausayinta ya ke, wai sanadin mu aka zalince ta, ina tunanin karya take saboda ta san Aliyu baya son ya zalince kowa ne shiyasa ta ce haka, domin Doc Asim ya ce ya bata kudinta, amman Aliyu duk ya bi ya damu da ita har saka a nemo masa ita, Momy ace ya rasa wacce zai damu da ita sai yar talakawa? Ni shi ya komai bata min rai”

Ta fada cikin kuka, Momy tsayawa kallonta tai, tun da take da ita bata taba tunanin cewar barin yau ta shirya taje ta gaishe da surukarta ba amman ta dauko kafafu ta zo ta kawo mata karar danta.

“To shi dan wajen Fulani ce miki yai ba zai taba kara aure ba?”

“Ba shine damuwar ba Momy yar talakawa fa, kaskantaccin mutane”

“Yar talakawa ai ta miki amfani Rahma ba kodar mahaifiyarta ce a jikinki ba? Ko da siyarwa tai ballantana zalintarta akai aka cireta, talaka shi b mutum ba ne da kike kiranta kaskantacciya? Wannan wace irin magana ce?”

Bude baki Rahma tai tana kallon Momy jin kamar maganar bata dame ta ba, a tuninta Momy irin Mommynta ce da bata son talaka wanda jin hakan zai saka ta hana Aliyu kula Ataa amman ga mamakinta sai ta ji wani abun da ba tai zato ba daga gurin Momy.

“Wallahi Momy idan Aliyu ya ce zai so ta zan iya mutuwa”

“To ki shirya mutuwa tun yanzu, domin Aliyu ba zai zauna da ke ke kadai ba, ko dan shi ma ya samu ganin nasa yayan, ko ba ita dole Aliyu zai kara aure ko dan Allah ya ba shi haihuwa, shekara takwas da aure amman har yanzu be haihu ba, ko ba dan haihuwa ba ai namiji ba zai maka alkawarin cewar ba zai kara aure ba ka yarda”

Rahma ta kalli Momy hawaye na sauko mata zuciyarta cike da jin zafin maganarta.

“Haihuwa na Allah ne Momy idan lokaci yai zan haihu, dan ban samu ciki a yanzu ba ba shi yake nufin ba zan haihu ba, komai na Allah ne”

“Shi kuma talaucin ba na Allah ba ne ko? Yarinyar da kike raina wata rana za ki ga tayi arziki kamar ki ko ma ta fiki, kuma bari kiji na fada miki idan ma dan wajen Fulani na yawan fada miki cewar ba zai kara aure ba daga ke ki daina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login