Showing 24001 words to 27000 words out of 225640 words

Chapter 9 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

ya kaini ofishin yan sanda, yana tafe gabana na faduwa abunda da wacce ba ta saba ba, musamman a lokacin dana sauka daga Napep din na doshi cikin ofishin, sai bugun gabana ya karu ina jin kamar ba zan iya ba, ganin irin manyan bingogin da suke rike da su. A haka dai na daure na shiga gurin ina sallama muryata na rawa kamar mai jin sanyi.

“As..sa.. La.mu...Alai..kum.”

Mutum biyu suka amsa min, sauran kuma suna ta kula da wasu mutane da ke kusa da su suna musu wani complain din dabam.

“Wa kike nema?”

Wani mai babban muryar ya tambaya yana kallon yanayina.

“Karar wani likita na kawo”

“Likita kuma? Me yai miki?”

“Kodar mahaifiyata ya cire, ba tare da saninmu ba, kuma ni ban ce ya cire mata ba”

Na fada ina kuka. Sai daya daga cikinsu ya zaro ido.

“What...?”

Sai dayan ya ce.

“Koda? Babbar magana, Robot bude nata file ka dauki statement dinta”

A take na zayyana musu komai yadda ya faru cikin har da maganin da ya bani da kuma abinci, sannan na fadi yadda wacan likitan na uduth ya fada min.

“Amman ke ai ba ki da shaida”

“Amman ai hoton ya nuna bata da koda kamar yadda likitan ya fada, kuma ashe ba ayi ma dafin maciji tiyati ni ban sani ba”

Cikin kuka nake wannan maganar ina share majina da Hijab dina.

“Dan Allah ku taimaka min ku kawto min hakkin mahaifiyata, yanzu haka tana asibiti babu kudin jinya sakamakon kodar nan da ya cire mata”

“Kin san inda likitan ya ke?”

“Ban sani ba, amman na san asibitinsa kuma can yake aiki kusan ma can yake zama kullum”

“To yanzu kin san yadda za ayi kina da na mai?”

Na mika masa dubu da dari biyar din da ke hannuna.

“Wannan kudin ne kawai ban sani ba ko za su isa”

Daya daga cikinsu ya karba sannan ya zagayo tare da wasu polisawan uku suka fito daga ofishin, sai da suka janyo motar yan sanda suka ce da ni na zo na shiga na nuna inda yake, cikin kuzari na shiga motar ina ta jindadi da ganin kamar za su kwato min hakkina ne, ashe ban sani ba gwanwo ne zai juye da mujiya.





_______________
Ayi hakuri na yau be kai yawan na kullum ba, gobe zan cika In-Sha-Allah.
https://my.w.tt/PWohUhlPv9.

*Z A K I*

By Khadeeja Candy


1️⃣1️⃣

“Momy muna neman mai aiki wacce zata rika gyara mana gida”

Ya fada yana aunar jalof din taliya da Momy ta zuba masa.

“Yar talakawa za'a nemo maka kenan, kaga ko dan za a ci amfaninta”

“Za tai ci amfaninmu ai biyanta za a yi”

Momy ta yi murmushi.

“Dan wajen Fulani har yanzu ka ki yarda da cewar za ka ci ribar talaka ko?”

“Momy kece ai kin ji ki gane, idan ba wani abu zaka saka talaka ba ka biya shi me zai hada ka da shi, Mama Fulani tana yawan yi min bitar kar na yarda ko rigata talaka ya rika balle kuma har ta kai ga alaka, kin san talaka dan hassada ne”

“Lallai kuwa, ina jiye maka tsoron ranar da zaka fara kaunar talaka, wata kila abun ba zai zo maka da sauki ba”

“Kamar ya?”

“Ba a son fariya, Allah zai iya jarrabarka ya koma talakan cikin talakawa, ko kuma Allah ya jarrabe ka da son yar talakawa wacce zaka duka har kasa kana rokon ta so ka?”

Ya tofar da ragowar abincin da ke bakinsa.

“Allah ya tsare ni Momy, ni ai bana da ra'ayin mace fiye da daya, Rahma ce kawai bayan ita babu wata”

“Wallahi yayan talakawan nan akwai tarbiya, da ace Rahma yar talakawa ce da zata fi ganin girma da girmanka fiye da yanzun”

“Ko a yanzu tana ganin girman ki Momy, kawai dai ita ta tashi a rayuwar turai ne, kuma kin san irin Rahma bata tashi gidan wahala ba shiyasa....”

“Hmmm To Allah ya kyauta”

Shine abunda Momy ta fada daga karshe sannan ta tashi daga dinning din ta nufi kitchen. Sai bayan sallah magariba ya biya gidan family house dinsu Rahma ya dauko matarsa suka dawo gida. Kamar wata marar lafiya haka ta shigo cikin falon tana takawa kamar mai jin wahalar tafiyar.

“Wani abun ne Dear?”

“Aa Daddy be dawo ba, kuma ance yai hasara kudi da yawa a shopping mall dinsa daya kone”

“Shine kuma za ki dauki damuwar ki saka a ranki? Bayan kin san lalurarki?”

Tai murmushi tana kai hannayenta ta zagaye wuyansa.

“Ina kokarin kawarda damuwar fa ko dan saboda na rayu da kai”

Kissing din lips dinta yai sai kuma ya rumgume ta a kirjinsa.

“Ka yi Momy maganar mai aikin? Ni wallahi har kyamar shigowa dakin nan na ke, duk datti”

Yai shiru be ce da ita komai ba.

“Bathrooms din mu duka suna son gyara fa, ga tarin wanke-wanke, ga kitchen din mu and bedrooms duka datti, ko mopping an dade ba ayi ba, kuma kasan ba zan iya ba”

“Shiiiiiiiii”

Ya fada yana shafa bayanta, yasanta da  yawan magana wani lokacin kamar radio, ga shi kuma baya son yawan magana sai idan da Mama Fulani ne ko Momy.

“Doc Asim zai rika zuwa yana duba ki kullum”

Ya fada bayan ya saketa, sannan na nufi upstairs.

ATAA POV.

Mun taki sa'a domin kuwa mun isa cikin asibitin a lokacin da yake tsaka da aiki, ina gaba polisawan ba bayana kowa sai kallon mu yake har muka isa ofishinsa, da muka shiga sai muka tarar baya ciki wai yana dakin tiyata, a ofishin mukai tsaye cirkocirko muna jiransa har ya fito daga dakin tiyatar ya shigo ofishin, da fari tsayawa yai yana kallon polisawan kamin ya maida dubansa a zuwa gareni, da alama an labarta masa zuwan mu tun kan ya shigo ofishin.

“Kai ne Doc Asim?”

Daya daga cikin yan sanda ya fada sai ya gyada masa kai.

“Yes wani abun ne?”

“You're Under arrest”

“Akan me?”

Ya tambaya kamar da gadara, ni kuma nai karfin halin bude bakina na ce.

“Kai ka cirewa Mahaifiyata koda dan haka dole a kama ka kuma a kwato mata hakkinta”

“Kodar da kika siyar? Blackmailing dina za ki yi? Are you out of your sense?”

Mamakin furucinsa ya hanani ko da motsin kirki balle har na sake cewa wani abu, waina siyar da koda, yaushe na siyar? Wa na siyarwa ya ma za ayi na siyar da kodar mahaifiyata.

“Oficer kar yarinyar tai wasa da hankalinku ta raina muku aiki, kar kuma ku isko ni har cikin ofishin ku ce za ku ci min mutumci akan aikin, muje station din ku hada da dan sanda ku daya zan saka shi motata sai mu tafi station din amman ni ba zan shiga motar ku ba”

Yadda ya bukata haka akai, ni da sauran polisawan muka koma a motar da muka zo, shi kuma ya shiga motarsa da dayan dan sanda bayan ya dauki wasu takardu.
A motar yan sanda sukai ta tambaya wai da gaskiya na siyar da kodar nai ta musu rantsuwar ban siyar ba, ban ma ya cire ba, idan har na siyar mi zai sa na kawo kararsa gurinsu, a nan suka min tausayawa kuma suka ce za su kwatar min hakkina, dan sanda yana ya matse ni sosai jikinsa na ta gogar nawa.

“Yarinya kyakkyawa da ita za a ci amanarta, ki sha kuruminki sai mun kwato miki hakki”

Shine abunda ya fada yana kallona da jajayen kamar dan shaye-shaye. A lokacin da muka isa Station din sai muka shiga ciki, a nan ya fiddo da wasu takardu ciki har da takardar da na sakawa hannu lokacin da za ayi ma Nana tiyata.

“Kin san kin saka hannu a wannan takardar ko ba ki sani ba?”

“Na saka”

Na amsa masa ina kallon takardar.

“Magani kawai na dubu nawa kika siya mata? Abincin da kike ci safe da rana da dare daga Hotel ake kawo miki duk ina kika samu kudin?”

Kasa magana nai sai hawaye na ke gaba daya ya gama dauren kafafu kai har ma da jikin gaba daya. Sai kuma ya juya gurin polisawan ya ce.

“Yi ma Babban likita irina sheri abu ne mai sauki domin ta samu kudi, yarinyar nan ina zaman ta dauko mahaifiyarta ta kawo wai maciji ya tsareta, kuma babu yadda zata yi ita bata da gabas bata da yamma, na ce ni ba zan taba ba, sai an kawo kudi, sai kawai ta ji ina magana da wani mai neman koda a nan tace zata siyar kuma babu yadda ban yi da ita ba akan ta nemo manyanta sai tace daga ita sai mahaifiyarta suke wai basu da kowa a nan, kuma idan ban taimaka na siye kodar mahaifiyarta ba, babu inda zata samo kudin da za ayi mata allurar dafin macijin, a haka tai convince dina na yarda na bata takarda ta saka hannu, na bata kudinta ta ce aa na aje gurina na siya mata magani ragowar canjin na bata wannan ne kawai abunda na sani”

Cikin kuka na nuna shi da yatsa na ce .

“Allah ya isa, karshenka ba zai yi kyau ba, kuma za ka ga abunda zai same ka?”

“Kaji ko? Oficer nima bude min file sai na ji akan me take kokarin bata min suna”

Ya fada yana nuna ni. A maimakon polisawan suyi wani abu sai na ga kamar suna tsoronsa, ashe ya siye dayan sandan daya shiga motarsa, sai kawai na ga sun fita waje har da shi Doc Asim din sun kebe suna ta magana da juna, suna kawowa sai suka fara tuhumata wai waya biyani na bata masa suna.

“Babu wanda ya saka ni, amman wallahi karya ya fada”

“Kina da wata shaida ne? ”

“Ba ni da ita, amman Allah shine shaidata”

“Aikin banza, haka kawai za ki nemi batawa mutum aiki da suna?”

“Wallahi ba bata masa nai ba, gaskiya na fada”

“Wannan duk shairin makiya ne, so kawai take ta bata min suna, dan haka su saka ta a cell sai ta fada muku wanda ya saka ta yin wannan sherin”

Cewar Doc Asim cike da gadara. Ni ko ina jin haka sai tsoro ya kamani take na saka kuka, ni ce da gaskiyata amman na risina har kasa ina rokon Doc Asim yafiya, sai ya fisge kafarsa ya daka min hannu har sai da dan yatsana ya fashe saboda zafin takalmin kafarsa. Haka suka rika ni saboda tsabar zalince suka saka ni a cell din mata ina ta kuka kamar raina zai fita.
  Daga cikin matan da ke cell din ta daka min tsawa wai na yi musu shiru na cika musu kunne da hayaniya, a haka nai shiru na samu guri na rabe a cikin dakin mai cike da sauro da duhu sai wari yake.
   Ba a bari ka fito ko da sallah za kai, fitsari ma sai dai kai a cikin cell din gaban kowa da kowa. Dukan tunani sai ya karkarta gurin Nana ban san halin da take ciki ba, ban san iya tsawon lokacin da zan dauka a nan ba.
Da dare yai sai naga ana fita da mata masu kyau, can da asuba kuma aka kawo su, ni dai ina zaune jigum har safe ban saka komai a bakina ba, sai can da azahar wani dan sanda ya bude min yace na fito a nan na samu damar yin alwala na raba gafen masallacin mazan nai rama sallah da akd bina sannan na gabatar da azahar, a lokacin ne dan sanda ya kawo min abincin shimkafa da miya har da kabeji da nama, kadan na ci saboda cikina ya daure sosai bayan na gama ya bani ruwa mai sanyi na sha.

“Idan an jima da dare zan zo na dauke ki, sai mu fita mu sha iska, idan mun dawo zan yi belinki da safe kin ji”

Na gyada masa kai cike da fahimtar inda manufarsa ta dosa, ba sai ya fada min na fahimci dan iska ne, ashe abunda suke da matan da suke fita dasu da dare kenan.
Yadda ya fada haka ya nufoto ni da dare guraren karfe goma sha biyu ya bude cell din wai na fito, ni ko na ki yarda na fito din, da ya shigo ya jani da karfi sai na fasa masa kuka ina ta masa ihu kamar zai sace ni a dole ta saka ya kyaleni yai tafiyarsa.
A haka na kwana hudu a cikin cell babu wanda ya zo belina, abinci kuwa sai idan polisawan sun ci sun rage su ba ni raguwar ko kuma mutane za da ke cell din idan an kawo musu sun ci sun koshi sai su ba ni ragowar. A cikin kwana biyu Allah ya hada jinina da daya daga cikin yan matan cell din, na dauke ta kamar yaya ita kuma ta rike ni tamkar kanwarta kasancewar ta girme ni nesa ba kusa ba. Bata fada min dalilinta na zuwa cell din ba amman na fahimci kamar shaye-shaye take har aka kawo ta nan, da fira tai mana dadi take tambayata dalilin zuwana gurin na fada mata sai ta tausaya min sosai. Ita ce ta taimaka min ta fitar da ni daga cell a lokacin da aka zo belinta sai akai belinmu mu biyu ni da ita.

Ranar da na fito daga cell din har iskar sai na ji ta badan ina ra jina kamar mai hanci, abu ga marasa shi, daga station din zuwa uduth akwai dan karen nisa amman haka na taka da kafa idan na gaji sai na tsaya na hutu har na isa cikin asibitin, ban san time din da na isa ba, sai dai da naje sai suka hanani shiga, a gurin na zauna har hudu tai sannan na shiga ciki, gurin da na san na bar Nana na nufa sai na samu babu ita a gurin gadon ma har an dora wata, ban tambayi kowa ina take ba na juyo na kamo hanyar Clapperto ina kuka. A iya tunani Nana ta rasu, idan ma ta rasu ina suka kai gawarta? Kangon gidan na nufo sai na tarar an saka kwano an zagaye shi an rufe ruf ba ta inda mutum zai iya shiga, a gurin na zauna nai ta rare kukana sai da nai mai isata, ban dauki wannan abun komai ba, face kaddara da kuma jarabawar rayuwa wacce ko waji dan adam yake fuskanta sai dai kowa da irin tasa, amman a iya ganina da jina ban tana ganin wanda ya shiga matsanaiciyar rayuwar da na shiga ba, kullum abun gaba yake ba baya ba, idan na natsu ina tunani sai na ga ban kashe kowa ba, ban hada Allah da wani ba, amman abubuwan da suke faruwa da ni kamar na kauce hanya ne, wata kila akwai wani abun da na ke ba daidai shiyasa Allah yake jarrabani, kuka nai mai isa ta sannan na tashi na doshi gidansu kawata Farida. Ina shiga ta yo kaina da gudu ta dafani.

“Ataa ina kika shiga? Mi ya same ki wannan irin ramar fa? Duk kin yi baki kamar ba ke ba”

Kasa amsa mata nai sai kawai na fashe da kuka.

“Ataa ina kika shiga? Hankali Nana duk ya tashi kullum zancen ki take”

“Nana tana nan?”

“Gata a can”

Ta nuna min wani tsohon kitchen dinsu, da gudu na nufi kitchen din ina shiga na samu Nana kwance sai kawai na fada jikinta na fashe da sabon kuka na rumgumeta kankan ina jin kamar wani zai rabani da ita. Ita kukan take ni da ita sai aka rasa mai rarrashi wani, Farida ma da ke tsaye jikin kofa tana kallon mu kuka take.

“Haba Ataa ke kuka ita kuka sai ki saka zuciyarta rauni ai”

Maganar Farida ce tasa na tsagaita kukana na share hawayena ita na saka hannuna na share mata hawayenta. Ta rame sosai wata kila ko abinci bata samu sosai ya akai ma ta bar asibitin ta dawo nan?
Ganin na daina kukan yasa Farida ta fita ta bar ni daga ni sai Nana.

“Nana ina Lukman?”

“Yana gidansa na gaskiya, sai idan Allah ya hada mu”

Wani sabon kuka na ji na cika min ido, sai tausayinta da shakuwarta da Lukman ta rufe ni, daman daga ni sai ita sai Lukman muka rage, yanzu kuma ya tafi ya bar mu mu biyu kawai.

“Ina kika je Ataa”

“Karar wannan likitan na kai gurin yan sanda akan rashin kula da ke da yai da kyau, sai ya juyar da abun a kaina suka rufe a cell sai da wata mata ta fitar da ni”

“Ranar da kika bar ni ban iya kwana cikin asibitin nan ba, sai na saci kafa da suna zuwa bandaki na gudo na dawo gida, a nan na tararda gawar dana, na nemi taimakon mutane akai masa wanka aka siya masa likkafai akai masa sallah aka je makabarta aka binnesa, a ranar mai gidan nan ya turo aka kore mu, da safe ana kewaye masa gurinsa dan kar mu sake zama, Farida ce tasa muka dawo nan ta ba ni kitchen dinsu na zauna a nan nake ta rayuwa da tunaninki, na dauka ma ke ma kin mutu kin bar ni ni kadai”

Na kama hannunta hawaye na min zuba kamar yadda ita suke mata zuba.

“Ban mutu ba Nana, kuma ba zan tafi na barki ba, kuma In-Sha-Allah za ki samu lafiya sosai, zan nema miki magani In-Sha-Allahu”

“Aa ba sai kin nema min magani ba, dawainiyar da kikai da ni ma Allah ya miki albarka, da kuciyarki kin fada cikin wata rayuwa mai tsananin wahala da sarkakiya, kina fuskantar kalubale kala kala na rayuwa”

“Idan ban nema miki lafiya Nana wa zan nemawa? Ba ni da wani wanda ya fiki a gurina, ganinki kawai yana sani kwanciyar hankali”

Dan murmushi tai sai ta koma ta kishingida da alama har yanzu lafiyar bata wadace ba, taya ma zata wadace bayan ba a nema mata magani ba, ba a mata maganin daya dace ta sha ba. Babu abunda ke zuciyata sai Allah ya isa da na ke yi ma azzalumi likitan marar imani da tausayi.
A gurin muka kwana ni da ita cikin matsuwa domin ba kitchen mai fadi ba, gashi duk ya kone saboda girkin da akai cikinsa can baya kamin su daina girki ciki, da dare Farida ta kawo mana abinci da alama ma tuwonta ne wanda zata ci ta kawo mana, dan nasan mahaifiyarta ba zata taba dauka tuwo ta ba mu ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login