Showing 108001 words to 111000 words out of 225640 words
yadda ta nuna min na lulluba da bargo mai laushi ya lumshe idona ba dan bachi ba, sai dan tunanin kwanan da Aliyu yai yana gadina wai har yana tsoron kar wani abun ya same ni, abunda wani mutum be taba min ba, babu ruwan kowa da inda zan kwanta ko da ko gurin mai cutarwa ne balle har ayi gadina idan ba mahaifiyarta ba, amman a karon farko wani ya yi gadina kuma yana tsoron wani abun ya same ni, wanin ma Aliyu mutum mai girman kai da ji da kai mai kyamar talaka, idan har na boye na ce ban jidadin abunda yai min hakika na yaudari kaina. Unkurawa nai na sauka daga kan gadon na nufi kofa na fita daga dakin daman Amina ta fita daga dakin tun bayan data fada min sakonsa. Tun da na fara takawa zan sauko downstairs ya dago daga zaune da yake samanb kujera yana kallona har ya sauko.
“Ina son naje gurin Nana”
“Koma ki kwanta sai idan za a kai abinci za a wuce da ke”
Ya fada fuskarsa babu alamar wasa, juyawa nai na dawo dakin na sake haye gadon na kwanta, amman bachi ya ki daukata har rana ta bullo, ba dan komai ba sai dan tunanin abunda Aliyu yai a yau da kuma son ganin Nana da zuciyata ta kwadaitu da shi. Ji nai an turo kofar dakin an shigo hakan yasa na bude kaina daga cikin bargon ina kallon Amina data shigo rike da brush ta mika min.
“Ki shiga bathroom din nan akwai man goge baki ki zuba a kai ki wanke bakinki kuma ki yi wanka”
Har ta fadi hakan sai kuma ta nufi bathroom din tana fadin.
“Bari dai na hada miki ruwan wanka”
Bayan wani lokaci ta fito tana rike da brush din a profile zuba mai akai ta mika min.
“Idan kin yi wanka ki dauro tawul ki fito karki maida kayan za a kawo miki wasu tufafin”
“To na gode”Na fada ina nufar bandakin, wanke bakin na fara yi sannan nai wanka da ruwan data hada min da kuma sabulu mao tsada na dauki tawul din da na gani rataye na daura sai ya tsaya min iya jinyoyina. Haka na fito daga bandakin na samu gafen gado na zauna, bana son na taba wani abu ta zo ta ga na mata ba daidai ba, na fin son sai idan ta zo ta fada min man da zan shafa. Ina zaune ina kallon yatsun kafata masu tsawo kuma sirara na ji an bude kofar dakin na yi zaton Amina ce sai na ga Muhseen yana rike da wayarsa. daga can bakin kofar da yake ya tsaya yana kallona tun daga kaina har zuwa kafafuwana, daman rabin cinyata a waje suke. Ba zan iya fassara mana'anar kallonsa ba, domin a yadda na ke makaskanciya ban yi zaton wani mutum mai daraja dan masu daraja wato nera zai min kallon sha'awa ba, balle har yai tunanin yi min wani abu, sai dai yaba kyauwo na wannan na san wani abu ne da ba ko wane namiji ne zai iya rike bakinsa daga furtawa ba, sai miskilin mutum kamar Aliyu wanda nake ganin kamar ba shi be taba ganin kyau nawa ba domin be taba yaba wa ko nuna zai yaba din ba, kallon ma da yake min ina jin kamar na kurilla ne dan kawai nai magana ko kuma na tsargu. Ya dade yana kallona kamin ya karaso kusa da ni yana ta yawo da idonsa a kan surar jikina. Tsarguwa na soma yi irin tsarguwar nan ta jin haushi idan wani na kallonka tsabanin Aliyu da bana jin haka, ga kuma kallon da yai min lokacin da nake canja tufafi da lokacin da nake wanka, sai na soma jin ba dadi duk kuwa da kasancewar kallon mace ko tana jikinta a gurina ba wani abu bane, domin kuwa da wani babban abu ne da Nana ta zaunar da ni da fada min a matsayinta na mahaifiyata.
“Na rantse da Allah kina da matsifar kyau Ataa, look at you karamar yarinya da ke amman Allah ya miki sutura komai ya ji”
Ya fada yana kokarin zama kusa da ni sosai yana kallon kirjina da fuskata.Na sani kyau na daga cikin abunda yake burge Muhseen ba tun yau ba tun a lokacin da ya taba ganina a gidansu da sunan aiki ya umarce mahaifiyarsa cewar a zabe ni saboda kyau, sai da yadda yake koda kyau nawa har mamaki yake ba ni domin shi ma yana da na shi kyau daidai gwargwado.
“Ataa....”
Sunana kawai ya fira be fadi abunda yake da niya ba, sanadin shigowar da Aliyu yai dakin hannunsa rike da mug fuskarsa babu annuri yake kallona da kuma Muhseen.
“Wai kai baka jin kunyar kanka? Ka shigo cikin daki ka kebe da yarinya kamar wannan kuma da tawul kawai a jikinta? Ji yadda ka zauna jikinka na kusan taba nata”
Muhseen yayi murmushi yana mikewa tsaye.
“Ina ce yanzu nan Amina ta fada min cewar kai ka kawo ta, waya san inda ka fito da ita? Kai da ba a zarge ka ba? Kao kullum na zaka kyautatawa mutane za to ba? Ka dinga min abu kamar baka san inda na fito ba? Ko kuma mai mim fatar sheri? To yanzu muka fara tsakanina da kai Aliyu dan kana son ta be isa ya hana ni sonta ba, kai ma din ban san kalar son da kake mata ba”
Yana fadar hakan ya fice cikin bacin rai. Aliyu kuma ya nufo inda nake zaune ciki ba fada.
“Wai ke baki san haramun ne mutumen da ba muharramin ka ba ya kebe da kai?”
“Be min komai ba”
“Oh sai ya miki komai ne zai zama matsala? Kallon jikinki ko taba jikinki shi duk ba matsala ba ce? Ba ki tana sani ba?”Na gyada kai alamar ban sani ba din.
“Wace makarantar islamiya kika yi?”
“Bama zuwa makaranta saboda bara”
Na amsa masa ina dan turo baki kamar an min wani abu. Kallona ya rika yi irin kallon nan na mamaki jin furucina.
“To haramun kallon jikin mace da ba muharramar ka ba, kin san abunda ake nufi da muharrami ma?”
Na sake girgiza kai alamar ban sani ba.
“Kina cikin matsala”
Na fada yana juyawa sai kuma ya juyo ya ya nuna ni da tsaya.
“Kar na sake ganin kin zauna kusa da wani namiji, kar ki sake sakin jikinki har wani namijin ya gani ko da ni ne ko wani can dabam kuma ki kama kanki bana son yadda kike sakewa da kowa”
“To”
Na fada ina gyara daurin tawul din a kirjina sai ya matsa kusa da ni ya miko min mug din hannunsa.
“Ki shanye yanzu za ku tafi asibiti”
Hannu biyu na saka na karba garin karbar hannuna ya taba na shi.
“Kar hannunki ya sake taba nawa idan za ki karbi abu, kar kuma ya sake taba na kowa”
Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin. Ni dai ban da binsa da kallon babu abunda nai yi.
ALIYU POV.
A fisace ya fito daga dakin ya rasa dalilin son shiga jikin Ataa da Muhseen ke yi, ya sani Muhseen ba dan iska ba ne amman ba shi da tabbacin zai iya rike kansa be fadawa Ataa ba, shi kansa a yadda ya ganta a yanzu haka ya ji wani abu dabam balle kuma Muhseen da kyau mace kadan kan iya jansa balle kuma Ataa ba zai iya misaltata da kowa ba.A falon ya samu Muhseen zaune yana lasa wayarsa Momy kuma tana kitchen ita da Amina da Siyama hada breakfast. Be cewa Momy ya tafi ba ya fice daga falon zuwa cikin motarsa. Sai da ya dauki hanyar gidansa sannan tunanin abunda zai fadawa Rahma ya fara fado masa a rai, be so yayi bachi a can ba, shi be san ma lokacin da bachin yai gaba da shi ba, and ko da ya farka tsakiyar dare ne gashi ta jera masa miss calls din da be san adadinsu ba, idan har ya daga be san amsar da zai bata ba, idan kuma yace ya dawo cikin dare a wannan lokacin be san irin kallon da zata masa ba, kuma be ji zai iya tafiya ya bar Ataa a nan ta kwana ita kadai, da ya barta a nan ba shi tabbaci shi din zai kwana a cikin natsuwa da kwanciyar hankali kamar yadda ya kasa samun sukuni har sai da ya jingina da kwanon dakin da take kwana, domin yana jin idan ma babu mutun wata kila wani abu mai cutar kamar kwari ko dabba za su iya zuwa su cutar da ita duk kuwa da ya san ba a daji take ba. Driving din yake yana juya kansa dan kwanan da yai cikin motar kamin ya fito juyansa ya yi ciwo ga sanyin dake sauka sai ya saka kansa yai masa nauyi.
A harabar gidan yai parking ya fito yana saka wayarsa aljihu ya nufi kofar falon kai taaye ba tare da tsoro ko tunanin komai ba. Kamar yadda ya tsammata a tsaye ya samu Rahma cikin falon fuskarta futik futik alamar ta sha kuka har ya gode Allah.
“Ina ka kwana Aliyu?”
Ta tambaya tana doso inda yake idonta cike da hawaye. Tsaye yai yana kallonta har ta karaso kusa da shi.
“Ni ya kamata na tambaye ki ina kika je saboda ni na aje ki ba ke kika aje ni ba, na zo gidan nan da rana ban same ki ba”
“Ka sani kuma kai ka bani dama idan ma na fita ba ya wuce na je gida ko kuma gurin kawaye na, amman kai baka kwana a gida ba Aliyu, kuma na ta kiran wayarka baka daga ba, na kira Siyama ta fada min baka gida ina kaje?”“Fushi nai na bar gidan na kwana a gidan gona na dauka ko ba zaki dawo ba”
“Amman baka saba haka ba, kuma baka taba yi ba Aliyu”
Ya rika fuskarta da hannayensa biyu yana shafa kumatunta da babban yatsansa.
“Karya zan miki?”
“Amman.... ”
Be bari ta fadi abunda zata fada ba ya hade bakinsa da nata ya shiga aika mata da wani irin sako mai muhimmaci da girma, sakon daya sauko masa tun a lokacin da yai arba da surar Ataa wace rabin jikinta kw waje, cinyoyinta gashin kanta ta ya jike da ruwa ya kwanta a jikinta da goshinta ga fari da kuma gurin wuyanta da ke ta sheki.
Tsayuwar ce ta gagaresu har ta kai ga yayi baya ya jingina da kofar falon, sai kuma juyar da ita ta zama ita ce jikin kofar shi kuma ya mata rumfa. Duk yadda Rahma ta zo ya hakura har su isa daki kasa hakura yai daman haka yake idan abun ya bijiro masa baya jira kuma baya iya yiwa mace uzuri matukar uzurin ba na musmmman ba ne, domin Aliyu ba shi da hakuri a wannan babin.A falo sukai komai daga bisani ya rumgume matarsa suka shiga bedroom dinsa a tare sukai wanka kamar yadda ya saba mata bayan sun fito ya saka wasu tufafi ita kuma ta daura tawul domin babu tufafinta a dakinsa, a kan gadonsa suka kwanta yana rumgume da ita har bachi yai gaba da shi.
Be farka ba sai da aka kara kiran sallah azahar, shi ya riga sauka saman gadon ya shiga bathroom ya dauko alwala fito sannan ya tashe ta, sai da ya tabbatar ta tashi zaune sannan ya sumbanci goshinta.
“Tashi ki yi sallah”
“Aliyu motar na ga ya fashe a gaba”
“Yeah accident muka samu amman da sauki Allah ya tsare babu abunda ya faru”
“Garin ya? Allah ya kare tsarewa”
“Amin”
Ya fada tare da daukar agogonsa ya daura a hannun sannan ya fice daga dakin yana fadin
“Na tafi masallaci”
Da kallo ta bishi har ya fice, sannan ta kawarda idonta ta dafe kanta ita dai har yanzu bata gamsu Aliyu ya kwanta gidan gona saboda ta fita ba, be taba haka ba be kuma tana haka ba.
MUHSEEN POV.
Ransa be taba baci kamar yau ba, ya rasa dalilin daya saka Aliyu yake shigar masa hanci, iyakar abunda ya sani yana son Ataa saboda tana kyau kuma ya san ba haramun bane son mace mai kyau and yes Ataa ta kai mace da za a kalleta a so ta, daman ya dade yana som aure mace mai kyau, bayan son na aure ba shi da wata manufa zuwa ga Ataa amman yadda Aliyu yake masa ya sashi jin haushi sosai,a yanzu ne ya shirya taba ta ko kebewa da ita da kuma neman aurenta domin ya lura kamar Aliyu yana kishi ne, ba taba ta ko kebewa da ita kawai ba ya dauki alwashin har kiss sai ya mata a gaban Aliyu sai dai idan mutuwa zan yi ya mutu idan kuma ya fusata shi sai ya yi mai gaba daya daman dai aurenta zai yi dan haka yana jin ko kaiwa yai a jikinta ba wani abun ba ne face samun damar da zai saka Mama Fulani da duk wani da zai masa karan tsaye ya amince ya aureta.
“Muhseen”
Momy ta kira shi da karfi jin tana ta kiransa kadan be amsa ba tana can wata duniyar yana tunani. Kallonta yai sai yai murmushi.
“Momy magana kike?”
“Ina ta magana baka ji ni ba, lafiya dai?”
“Wallahi Momy ba lafiya ba, abunda Aliyu yake min ne bana jindadins akan yarinyar nan”
Momy ta zauna a kujerar dake kusa da tashi.
“Mi yake maka? Daman Husna ta fada min jiya kun yi fada miya faru?”
“Momy bana da halin nai magana da yarinyar ko na kebe da ita sai ya saka zargi, kuma wallahi Allah ya sani bana da wani manufa akanta bace na aurenta”
Da mamaki Momy ta kalleshi.
“Aure kuma?”
“Eh na taba fada mata tun a lokacin da take Abuja cewar ina sonta, Mama ma ta san da maganar sai dai bata yarda da ni ba, kin san yadda take tsanar talaka tana ganin kamar kaskancine na auri mace kamat Ataa, amman ni har ga Allah ina son ya Momy dan Allah ki shige min gaba”
Ya fada yana wani marairaicewa kamar zai saka kuka.Maganar sam ba tai ma Momy dadi ba sai dai ba zata muna nuna masa ba.
“Amman Muhseen yarinyar nan yanzu ba soyayya ko aure ne a gabanta ba, ta mahaifiyarta take”
“Na sani Momy, ni ma ban yanzu nake nufi ba, sai hankali ya kwanta, amman Momy ke kadai zan iya rikewa domin ke nake da tabbacin za ki fahimtar da Mama kuma ki share min hawaye na”
“In-Sha-Allah ni mai maka komai ne Muhseen, bari na tashi na kira ta fito muje asibitin na gama abincin”
Momy ta fada tana mikewa tsaye cikin yanayin na rashin jindadi.
*Khadeeja Candy*
ZAKI
By Khadeeja Candy
34...
Bayan fitar Aliyu Amina ta sake shigowa dakin ta dauko min man shafi na shafa sannan ta ba ni tufafi na saka ta fesa min turare da kanta.
“Gaskiya kina da kyau Aisha mashallah ga gashi, na ga har kin fi Mamanki kyau ma”
Na yi murmushi ina kallon kaina a madubi.
“Baba na biyo Babana yana da kyau sosai”
“Gaskiya ba laifi kina da kyau sosai Wallahi”
Kasa nai fa kaina ni kaina a yanzu sai na ga kamar na fi da kyau, domin jan yadi ne a jikina irin mai fitar da kyau farar mace.
“Bari na gyara miki gashinki”
Ta warware min gashin kaina ta ta dauko wani katon mataji ta shace min kaina ta saka min jan ribbon daga kasa kuma ta barbarza shi a bayana, sannan ta daura min dankwali ta shafa min kwalli a ido har zata shafa min jan baki sai Momy ta shigo. Murmushi na gani a fuskarka ita kanta da kalleni sai da ta yaba kyau na.
“Ai tayi kyau a haka Amina karki shafa mata jan baki sai kace wanda zai je gurin biki, ta so muje asibitin sai ki karya a can”
“Tau”
Na amsa ina mikewa tsaye sai amina ta dauko wani karamim mayafi ta dora min a kafada.
“Dan Allah Momy dan tsaya nai mata hoto”
Wayarta ta dauko tai min hoto ta sai kuma ta dauke mu tare sannan na bi bayan Momy daman ta dade da fita daga dakin.Ko da na fito babu kowa a dakin sai Muhseen yana zaune saman kujera yana cin dankali a plate ganina yasa shi mikewa tsaye yana kallona fuskarsa da murmushi. Kofa na nufa sai ya kira ni.
“Ataa...”
Tsayawa nai na kalleshi ba tare da na amsa ba har ya karaso kusa da ni ya kai hannunsa zai taba fuskata sai na kwace, fadada murmushinsa yai ya saka dayan hannunsa aljihu.
“Aliyu ya ce miki wani abu kaina ne? Ya ce miki ni dan iska ne ko?”
Na yi kasa da kaina ba tare da na ce masa komai ba.
“Ba dan iska ba ne ni, tun na ke a rayuwata ban taba aikata zina ba, dan kuma na ce ina son ki saboda kina da kyau ba laifi ba ne, shi kanshi da ba ki da kyau da ba zai kula ki ba”
Ya dan yi shiru kamin ya sake kallona ya ce.
“Ina miki fatar alheri ina fatar yanzu ma kije ki samu mahaifiyarki ta farka, kuma ina miki bankwana zan wuce Abuja yau, zan dawo satin sama amman lallai ne idan na dawo yin aikin na biyo ta nan ba, maybe ki ganni nan kusa maybe kuma sai nesa ina mik fatar alheri”
Dagowa nai na kalleshi sai ya sakar min murmushi ya nufi kofar fita daga falon ya bar ni tsaye ina juyo na kalleshi.
“Aisha”
Kiran Momy na yasa na fito daga falon na same ta gurin mota, a front seat na shiga ita kuma ta zauna a mazaunin direba tai ma motar key aka bude mana gate muka kama hanyar asibitin.Ban san dalilin rashin jindadin kalaman Muhseen ba, yanayinsa da yadda yake min maganar ba cikin farinciki ba ne, and i feel like kamar ba zai sake dawowa ba, wata kila wani abun Momy da Aliyu suka ce masa shiyasa ya yanke wannan hukuncin, wata kila kuma ra'ayin kansa ne ban sani ba amman sam kalamansa ba su min dadi ba. Bayan Momy ta yi parking motar ya na bude na fita ita ta bude ta fito sannan ta fito da kayan na rika wasu ta rika wasu muka