Showing 186001 words to 189000 words out of 225640 words
yana rike da ledodin a hannunsa. Fork ta dauko ta saka ya debo taliyar sai ya busa masa a bakinta sai da huce sannan ta kai masa a baki, luma daya ya rumtse ido saboda wani azababen yaji da ya ji, da sauri ya aje ledodin hannunsa ya dauke plate din.
“Wallahi ba za ki ci wannan abincin ba”
“Mi yai?”
“Wannan uban ya jin?”
“Ji nai ina son ya ji shine an cika kadan”
“Wannan cikin be wani kwari ba za ki ce za ki ci wannan yajin, noooooo ga wani abincin na siyo miki ai zo mu ci tare”
Ta mairairaice fuska.
“Haba Aliyu ina so Wallahi”
“Haba Baby ki tausaya min mana”
Aje plate din yai gefe ya bude dayar ledar mai waya ya dauko ya mika mata.
“Ga waya ke ma ki fara bugawa kina daukar hoto”
Ba shiri da zaro ido ta karbi wayar da sauri da daka wani irin tsalle kamin da dire yai saurin cabeta.
“Ke yanzu fa ba ke kadai kike ba, ki daina irin wannan abun”
Ina bata ma jin me yake fada sai ihu take ya rumgume shi sabar farinciki har da yi masa kiss a fuska.
“Na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na”
Haka tai ta maimaitawa sai da ya rufe mata baki, sai kuma ta fashe da kuka kuka irin sosai din nan kamar wacce akai wani abu rasa tai me zata yi, ita a rayuwarta bata taba rika waya ba ko karama balle babba irin wannan mai screen kato.
Rikota yai suka baro kitchen din suka dawo falo suka zauna, sai ya karbi wayar ya bude mata ya hada mata.
“Idan na fita ko kuma zan saka Nasir ya siyo miki layi mai kyau na ki na kanki, kuma yanzu sai an saka wayar carji idan ta yi full sai a fara tabawa”
Ta yi saurin tashi daga kan kujerar tare da carjar wayar ta nufi socket ta saka ta zauna s gurin ta tsare wayar. Shi kuka ya tashi ya koma kitchen din ya dauko musu abincin daya siyo musu ya zo kusa da ita ya zauna ya bude abincin.
“Aliyu ka dauko Nana na nuna mata wayata”
“Ba yau ba dai, gobe ai zamu je mu gaisheta sai ki nuna mata”
“Har sai gobe”
Ya gyda mata kai yana deban abincin ya bata a baki, jin tai bata gamsu ba har sai da ta dawo saman jikinsa ta zauna ta rumgume.
“Na gode sosai Allah ya kara arziki ya tsareka daga dukan sheri Allah ya biya maka bukatunka na alheri”
“Nima na gode da ki kai ciki”
Rankwashinta ya ji a kanta ya ji kamin ya ji sautin dariyarta yai murmushi ya kara rumgume ta. Ba wani abun kirki ta ci ba abincin tsabar zumudin waya ya saka ta manta da wani zancen cin abinci duk kuwa da tana jin yunwar. Ranar a gaban wayar ta kwana duk yadda ya so ta dawo ciki daki su kwanta kin tai tana ta jiran har sai wayar ta yi full sannan ta fara tabawa, a dole ya dauko matashin kai ya aje a gurin yai mata matashin kai da hannunsa ya lulluba musu mayafi suka kwana a gurin har safe.
MAMA FULANI POV.
Tun da Abbah ya dawo ya fada mata abunda ya faru kuma ya ce mata Mahaifiyarta Ataa zata zo kuma a nan zata sauka sai ta fasa inda zata saka kanta sabar kunya, dole ne tai mata tarba ta musamman kasancewar yar sarkin Agadaz sai dai taya? Baya ta wulakanta yarta? Ta sani har abada ita da Ataa ba za su taba ganin kimarta ba, yadda za tai ido biyu da ita ma take tunani. Gabanta be kara faduwa ba sai da ta ji tsayawar motar Aliyu da sauri ta tashi ta shige dakinta har da hadawa da gudu.
Saman gado ta haye ya lulluba da blanket tana jin sallamar Aliyu ta fara rawar sanye abunda bata taba ba a rayuwarta.
“Mama ba ki da lafiya ne?”
Ganin shi kadai ya shigo yasa ta tashi zaune cikin yanayin damuwa tana kallonsa ta ce.
“Aliyu ina jin kunyar hada ido da Ataa da mahaifiyarta, ba ni da wannan idon na kallonsu ko na ce zan musu wata magana, waya taba tsammanin haka Aliyu? Ko daman can ka sani?”
Zaunawa yai kusa da ita cike da damuwa da damuwarta domin ita din ma uwarsa ce kuma mai damuwa da abunda ya dame shi.
“Ban sani ba Mama ban ma taba kawo wa a rana cewar wata wana haka zai faru ba, iyakar abunda na rike wata rana dole yan'uwanta za su bayyana, amman ban taba kawowa kaina cewar masu kudi ba”
“Ka huta, Momy ma bata mata komai ba sai ni oh ni Fulani yau na jin kunya na shiga uku, Wallahi ko a mafarki aka fada min cewar wata rana yarinyar zata zama haka ba zan yarda ba, amman ji abunda ya faru? Ina ta zagin yarinyar nan ina ta ci mata mutunci ashe ma har ta fi mu komai”
“Mahaifiyarta tana can falo, Ayusher kuma tace zata tsaya bangaren Ammy”
“Eh ta tsaya can ai tana gaskiya, ni ai muguwa ce na san haka take kallona, ka ji fa rashin rabo jiya na hana yarinyar ruwan sha a gidan nan ashe ashe.... ”
Wannan karon har da kwalla gaba daya duniyar ta rikice mata, domin yadda take son zuri'ar masu hannu da shuni da ace ba tai wa Ataa haka ba da yanzu sai ta kulla abota da Nana, kuma ta sake jikinta da ita amman ina ta bata komai. Tashi Aliyu yai ya fice daga dakin, ya barta ita kadai tana da tufka da warwara, har da dan lekowa ta leki fuskar Nana ta koma cikin dakin, gaba daya kunya take ji kamar wacce tai sata ko. Maryam ce ta shigo cikin dakin sai Mama Fulani ta juyo da sauri ta kalleta.
“Ke kin gaishe ta?”
“Eh na gaishe ta ni da Rukaiyah”
“Ta karba miki?”
“Ta karba mana amman tana ta kallonmu”
“Kunyar sauka na ke ji”
Ta fada gumi na karyo mata.
“Wallahi Mama da kunya wa ya saka ran haka zai faru? Kara ma Ammy bata taba mata komai ba, ita da Ya Muhseen da balle Ya Aliyu da yake mijinta gaba daya”
Mama Fulani ta dora hannu saman kai.
“Kai ni dai kan na shiga uku naga ta kaina, ni yanzu ya zan yi na fita na ganta?”
“Ai ita bata san ki ba, kuma kin san Ataa kila ma bata taba fadar abunda kika mata ba, kuma ai dole ki fita tunda Abbah yasa an kawo ta nan”
Babu yadda Mama Fulani ta iya da abunda ya fi karfin wuta, dole ta kulle kunyarta a baren zane ta fito tana saukowa a hankali.
“Lale lale mara da Hajiya ashe har kin iso da yake ina wanka ban san shigowarki ba”
Ta fada tana dariya da far'a kamar ba ita ba, Nana kan kallonta kawai take har ta zauna saman kujera tana gaisheta kamar zata risina.
“Hajiya Ina wuni? Ya gida ya hanya?”
“Lafiya kalau Alhamdulillah”
Nana ta amsa a hankali ba tare da ta saki fuskarta ba.
“Aa ya ba a kawo mata komai ba? Ke Rukaiyah me kike yi baki kawo mata komai ba”
“An kawo mata ruwa da lemu ta ce a dauke wai ta koshi”
“To ko kin fi son na gida irin wanda ake hadawa wannan?”
“Bana jin kishin ruwa ko yunwa a yanzu, ki ce Fulani?”
Mama Fulani ta ji kamar ta nitse cikin kasa.
“Eh ni ce, ai ni ce na rika Aliyu a hannuna na girma tun yana dan yaye, ai shi mai gidan nan mijina shi da mahaifin Aliyu uwa daya uba daya suke, mijina shine yaya sai mahaifin Aliyu ne kane, da yake a wacan lokacin ni da Momy a makaranta kawayen juna ne sosai tare mukai karatu a ABU zariya, mahaifin Aliyu dan'uwanta ne sun hada kakanni daya kuma......”
Ganin Nana ta zuba mata ido sai ya saka ta ji kunya har da yin kasa da kai.
“Ataa na yawan ba ni labarinki ai”
“Ehhh Wallahi ni ce fa Mama Fulanin dai, Allah sarki Ataa baiwar Allah, Wallahi Ashe abun haka ne, Wallahi ehh huh”
Mama Fulani sai kame kame take cike da kunya. Sai ta mike tsaye ta nufi kitchen.
“Ban ma dora girkin rana ba da yake bana dan jindadi, Rukaiya ki kaita gurin Ammynku su gaisa kamin na gama abincin, sai dai ban sani ba ko kina da ra'ayin wani abun da za a dafa miki?”
“Aa”
Nana ta amsa tana mikewa tsaye ta bi bayan Rukaiyah wacce tuni ta nufi kofa, sai da ta fice Mama Fulani ta fadi zaune a kofar kitchen ta dafe kanta.
“Wai ni Allah wannan abun be min dadi ba, ai dai kam ba zata ci komai nawa ba, tun da yarta zata fada mata cewar na hanata ita, ai idan da kunya ni ma ba zan ce zan bata ko?”
Magana take kamar mai yi da wani gaba daya abun ya dameta a yanzu, wacce suke wulakantawa suna gani ba komai ba, yau ta koma sama da su, a cikin arzikin kakanta suke tsoma ludayinsu su ci.
Kamar kallon yadda Ammy take da far'a haka ta amsa mata sallamarta tai mata lallen marhabun, sai a lokacin Nana ta dan saki jiki har tai murmushi Rukaiya sai kallonta take ganin ta sakewa Ammy, kamin ta juya da fita.
“Aiko yanzu yanzu nan Aliyu ya fita tare da Ataa”
“Allah sarki ke ce Ammy ko?”
“Eh ni ce Allah dai ya sa lafiya?”
Ammy ta fada tana dariya sai Nana ita ma tai dariyar.
“Lafiya kalau labarinki na ji a gurin Ataa, har da kowa da wa yaranki”
“Allah sarki ina ruwan Ataa, yaran duka basa nan sai Humaira ita ma yanzu ta fita ko bangaren Hajiya Fulani tai ban sani ba, ya gida ya hanya?”
“Alhamdulillah”
Ammy ta shiga ciki ta kawo mata ruwa da da dan abun tawa, a nan kam Nana ta sha ruwa har da cin abinci ma domin ita ta gama nata abincin rana tuni, Mama Fulani ma abunda ya faru ne yasa jikinta yai sanyi har taji kamar bata da kuzarin girkin.
Mama Fulani na zaune bakin kofar kitchen din tana jimami sai ga Rukaiya ta dawo tana labarta mata cewar Nana ta sake a gurin Ammy har da dariya. Mama Fulani dai abun duniya ya isheta ta bata ce komai ba sai domin ta san duk abunda akai mata bata da bakin magana a yanzu kuma ta cancanci fiye da hakan ma. Maryam ce ta fito rike da wayarta ta sauko kasa ta kawo mata. Ganin number Nasir yasa tai saurin picking.
“Mama ina wuni?”
“Lafiya Nasir ya gida”
Ta amsa da muryarta kamar ba ita ba.
“Lafiya Kalau Mama kira nai na miki albishir kamin kowa ya riga ni”
Gabanta ya fadi domin a halin da take yanzu tsoron jin komai take.
“Albishir kuma?”
“Eh Ataa ce bata jindadi Aliyu ya kaita Asibiti shine suka ce ciki ne”
Dif Mama Fulani tai daukewar wuta, ta zaro ido ta mike tsaye da sauri sai kuma ta cire wayar daga kunnenta ta duba mai kiran ta ga Nasir din dai ne ta sake mayarwa a kunnenta sai idonta ya cika da kwalla.
“Allahu Akbar, Allah mai iko Allah sarki”
Ta kashe wayar sai ta koma saman sofa ta zauna sai hawaye suka fara mata sallama.
“Lafiya Mama? Miya faru?”
“Wai Ataa tana da ciki, kiji wani al'amari daga Allah, duka abubuwan nan sun zo mana ta hanyar da ba za mu iya nuna farincikinmu ko kulawarmu ba, a da idan wani abun farinciki ya samu Aliyu ni yake fara yi ma albishir kamin kowa, amman yau ya fadawa Nasir wannan albishir din bayan ya san na fi kowa bukatar ya samu haihuwa, be fada min ba saboda yana tunanin bana son Ataa ba zan yi farinciki da samun cikin ba, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”
Tashi tai jiki ba gwari ta nufi dakinta, zazzabi ne ya rufe ta gaba daya yamma cin batai shi da dadi ba, da ada ne da yanzu ta fara kiran Momy da duk wani makusancin da labarta masa abun dadi da murna ya samu amman yanzu babu wannan damar, da dare ma kasa runtsawa tai tana son ta kira Aliyu ta yi magana da shi amman tana jin nauyi saboda ta san yana tare da Ataa, kuma tai ta jiran ya kirata be kirata ba har garin Allah ya waye.
Misalin bakwai na safe tana zaune saman carpet din da tai sallah kasancewar jiya da yau ba ita ce da girki ba Ammy ce, Nana kuma ta kwana a bangaren Ammy, ban da Maryam da Rukaiya babu wanda ya san bata jindadi domin Muhseen be shigo gidan ba gaba daya tun da ya ga Ataa ta zo ya sake fita be dawo ba. Wayar Aliyu ringing biyu ya daga da far'asa yai mata sallama.
“Assalamu Alaikum”
Ta amsa mishi da muryar mai karantar da shi damuwarta.
“Aliyu kana tunanin ba zan yi farinciki da samun cikin ba shiyasa baka kira da kanka ka fada min ba?”
“Wallahi ba haka ba ne Mama Nasir ne ya ce kar nai rashin kunya na bari zai kira ku ya fada muku amman ba dan wani abu ba”
“Aliyu yadda na ke son ka haihu ko da karuwa ce ta samu ciki da kai zan yi farinciki, saboda na ce bana son Ataa ba shi yake nufin bana son abunda zata haifa maka ba, ita ma kuma da na san da zuwan wannan abun da ban aikata mata komai ba, ina jin kunyarta da na mahaifiyarta na abunda na aikata musu, amman Wallahi ba zan taba kin jininka ba ba zan taba tsana ki nuna kyama a gurin abunda Ataa zata haifa maka ba, ko da ko ace gaskiyar wacece ita be bayyana ba”
Tana gama fadar hakan ya kashe wayar tana hawaye.
ALIYU POV.
Damuwa ce shimfide a fuskar Aliyu, yadda ya ji muryar Mama Fulani abun be masa dadi ba, yadda baya son wani abu ya dami Momy haka baya son abunda ya taba Mama Fulani.
“Minene?”
“Mama ce, bata jidadin yadda na sanar da Nasir zancen samun cikinki ban sanar mata ba”
Ataa ta aje mug din dake hannunta na tea da ya hada mata tun da azuba tana kallonsa.
“Bata jidadin na samu cikin ba? Ko kuma saboda ni ce na samu cikin yasa ba ta jidadi ba?”
Matsowa yai da ita kusa da shi.
“Mama tana son cikin nan, ko da ko ke ko wata ce wadda ta fiki talauci, ko kuma wacce ta fiki arziki, saboda tana son farincikina, kuma tun kamin Momy ta fara damuwa da rashin haihuwa ta, ita ta fara min zancen karin aure kamin Momy, Mama Fulani bata son wani abun da zai taba ni ko kadan, shiyasa ko a wacan lokacin da na ake fada mata cewar ni ne da matsalar ba Rahma sai ta nuna damuwarta kuma ta nuna min na kara aure idan ban haihuwa sai a barwa Allah ko kuma a cigaba da neman magani”
“Kana da wata matsala ne?”
“Ba ni da wata matsala, Rahma ce mai matsala domin kwa haihuwa baya iya zama a cikin mahaifarta, amman sai na boye mata, da farko wace na ke ni d ita duka ba mu da matsala sai na biya likita kuma na roke shi ya fada mata haka, saboda kar damuwar tai mata yawa, ga ciwonta kuma idan ta ji bata iya haihuwa abun zai nata yawa, daga baya na maida abun kaina na ce mata da kowa cewar ni ne mai matsala ba ita ba, saboda Nasir ya ba ni shawarar yin hakan”
“Amman Aliyu miye alakar da Mama Fulani? Na san Momy ce ta haife ka”
“Momy ce ta haife ni tabbas, amman a hannun Mama na girma, Mama Fulani da Momy aminan juna ne tun a makaranta a lokacin Mama Fulani tana Yola kasancewar ta yar can, Momy kuma yar sokoto amman sai suka hadu a ABU zaria gurin karatu a daki daya suke komai tare suke kamar yadda na samu labari, Daddyn dan'uwan Momy ne Cousin brother dinta ne ta gurin uwa, tun tana makaranta ta fada min wani lokacin a sokoto suke hutu ita da Mama Fulani, wani lokacin kuma a yola suke hutu gidansu Mama Fulani, after sun gama makaranta aka saka ranar aurenta da Daddy, a gurin bikinsu ne Abbah wanda yake kanen ga Daddy ya ga Mama Fulani har ya fara sonta har Allah yai abun ita ya aureta, a sokoto suka zauna dukansu a wacan lokacin shiyasa a lokacin da Momy ta haife ni na isa yaye sai Mama Fulani ta yayeni, daga nan Daddyn ya samu aikin wannan kamfanin suka dawo a nan Abuja sai ta dawo tare da ni, kawaici irin na Momy ya sa ta kasa cewa a bata danta domin har tsawon lokacin da na fara wayo Mama Fulani bata samu ciki ba, sai daga baya aka haifi Muhseen daga shi kuma sai ta dade kamin ta sake haihuwa wanda hakan yasa Abbah ya auro Ammy, sai kuma haihuwar ta zo mata daga baya su kai ta yi tare da Ammy. Mama Fulani ta rike ni tsakani da Allah bata bari wani abun ya same ni ko nai kuka duk wani abun da nake so shi take min, kina da idonki idan wani abun ya shiga tsakanina da Muhseen ni take ba gaskiya, ko da shi ne da gaskiyar, bata taba yarda yaranta su rainani shiyasa na taso bana sake musu fuska saboda kar su raina ni din, har abun ya zame min jiki, kowa a gidan yana saunata ko yin wani abu a gabana ciki har da shi Muhseen din, hakan yasa ba mu jituwa da shi, ba ma san inuwa daya bama fahimtar junanmu, saboda shi yana ganin ina akan kuskure abubuwan da na ke yi ni ma kuma ina ganin yadda yake sakewa yana wasu abubuwan basa burgeni, a ciki kuwa har da tsanar talaka wanda na samu asalinsa daga gurin Mama Fulani, ban taba daukar cewar abunda Momy da Muhseen suke nuna min abu ne mai kyau ba sai haduwa ta da ke”
Yayi shiru sannan ya rumgume ya sumbaci saman kanta.
“Na san ba za ki taba son Mama Fulani ba, amman zan jidadi