Showing 66001 words to 69000 words out of 225640 words
koma gida tare”
Sakin baki tai kamar zata ce masa ba mu kare ba, sai kuma ta ga kamar be dace tai karya ba, dan haka tai murmushin yake.
“Ba matsala”
24
“Thank you, idan kin je gida ki fadawa Mama Fulani ni na areta kuma zan kawo ta nan ba da jimawa ba”
“Okay ayi shopping lafiya”
Taja kwandon daga hannuna tai gaba a abunta kamar tana jin haushi. Sai da ta wuce sannan ya dawo da dubansa gurina ya ce.
“Shiga ciki na turaki”
Ba shiri na bude baki.
“Aa mutane suna kallon mu, kuma mutane ba sa shiga cikin kwadon zuba kaya ai, za su mana fada”
“Ko?”
Ya fada yana murmushin kan na sake cewa wani abu ya dauke ni ya zuba a cikin kwandon yana dariya, ina kokarin fitowa ya girgiza min kai.
“Karki fito basa fada”
“Ni kunya na ke ji”
“Nan Abuja ce ba ruwa kowa da kowa”
Tura ni ya fara yi yana tafiya yana dauko duk abunda yake so yana sakawa a gwandon.
“Fada min abunda kike son na siya miki”
“Bana son komai”
“Kina son abun goge baki? Ko kadar mata ko turare?”
Na yi shiru ban ce komai ba sai yai murmushi ya fiddo wayarsa ya dauki ni hoto.
“Bari na taimaka miki na saka ki a status dina ko wani zai gani ya zo kawata”
“Kawarka? Mace?”
“Eh mana”
Saurin sauka nai daga cikin kwandon duk na san wasu sun gama gani na domin ya zaga wani bangare na shopping din da ni a ciki har wasu na kallona. Da kanshi ya koma yana tura kwadon duk wani abun kwadayi daya gani sai ya dauko guda biyu ya fasa ya ci ya bani rabi sai kuma ya saka rabi a cikin shopping basket din. A haka ya daukar min kadar mata da turare da man goge baki sannan muka zo gurin biya ya ciro kudi mai yawa ya bada sai suka saka masa kayan a leda wani daga cikin yaransu suka zo suka dauka suka kai masa a mota. A tare muka fito daga shopping din yana cin chocolate.
“Na jidadin zuwa shopping din nan kin ga na hadu da ke, jiya na aika kiranki waya hana ki fito?”
Nan ma shiru nai masa ban ce masa komai ba, sai ya bude min gidan gaba yana fadin.
“Shiga muje yau dai sai kin ba ni labarin abunda ya kawo ki garin Abuja”
Sai da na fara taka wani abu dake gefen murfin motar sannan na shiga cikin katuwar motar mai tuli sosai, sai shi ma ya zagoyo ta mazaunin direba ya zauna ya rufe motar yana kunna ac motar tare da kai hannu ya rage karar sautin da ke tashi sannan yaja motar muka hau babban titi yana ta kallona kamar ba driving yake ba.
ZAKI
By Khadeeja Candy
23...
Kamal na tsaye yana lasar wayarsa yana jiran fitowar Ataa sai ga Aliyu ya fito yana wani shan kanshi, bayansa Kamal ya rika kallon a zatonsa ko tana bayansa ne amman sai yaja gate din rufe bata fito ba.
“Kai kake kiran Ataa ne?”
“Eh nine Aliyu ya aiki, ashe ka dawo”
Kamal ya fada yana mika masa hannu.
“Yes, wani abun ta maka ne?”
Da mamaki Kamal ya sake kallon Aliyu sai kuma yai murmushi.
“Mi zata min bata min komai ba”
“Miyasa kake kiranta?”
“Mun saba gaisawa da ita ne kwana biyu, yau kuma ban ganta ba, shiyasa na aika a kira min ita, da wata matsalar ne?”
Aliyu ya tsaya kallonsa kamar ba zai yi magana ba can kuma ya ce.
“Babu, idan gaisuwa ne, ba sai ka kara aikawa nemanta ba aiki take, aikin da aka kawota dan shi”
Aliyu na fada masa haka be tsaya jiran abunda zai kara cewa ba ya juyo ya dawo cikin gidan, cikin wani irin jin haushi da be san dalilinsa, a dayan bangaren kuma yana jin idan har ya kyale rayuwar Ataa zata iya shiga wani hali domin kyanta zai rudi samarin su fara jan ra'ayinta ga wata hanyar da dabam wacce bata dace ba. Cikin falon ya dawo ya zauna sa dai be samu Ataa a falon ba sai Mama Fulani da Maryam da Rukaiya suna wata magana ganinsa sukai shiru.
“Lafiya yake nemanta?”
“Lafiya kalau, wai zuwa yai su gaisa”
“Su gaisa?”
Mama Fulani ta tambaya da mugun mamaki.
“Shi Kamal din? Kuma ya tsaya a waje?”
“Ai ba zai shigo ba dan kar mu dauka gurin Maryam ya zo tunda gurinta ya saba zuwa shiyasa ya aiko a kira masa wannan kazamar”
Rukaiya ta fada tana yatsina fuska, Mama Fulani ta ce.
“Ni fa tun ranar na ke ta mamakin ganinsa har cikin falon nan, domin abu ne mai wahala ya shigo cikin gidan nan idan ba Aliyu ya zo nema ba, sai kuma Maryam wani lokacin idan yana son su gaisa”
Aliyu ya kalleta kamar ya ce wani abu sai kuma yai shiru ya maida hankalinsa gurin tv. Rukaiya da Maryam kuma suna ta kallon juna alamar gulma na cikin cikinsu tana cin su. Wayarsa yai jit alamar kira sai ya cirota daga aljihunsa ya duba number Rahma ce, hakan yasa shi picking ba tare da bata lokaci ba.
“Dear karfe tara za mu je mu ga Doc Perry, idan baka gida ka same ni a asibitinsa idan kuma ka dawo da wuri sai ka same ni a can”
“Kun yi magana da shi ne?”
“Eh mun yi karka bata lokaci ka ji?”
“Na ji make sure kin ci abincin dare kamin ki tafi”
“Okay i love you”
Be amsa ta ba ganin cewar yana a gaban Mama Fulani sai kawai ya kashe wayar ya tura mata ta sako. Ko be fada ba Mama Fulani ta san da Rahma yai waya, sai dai abunda bata gane ba ta ci abincin kafin ta tafi.
“Ina zata ta fi?”
“Zamu je mu ga Doc Perry ne”
“Ciwon ya tashi ne?”
“Aa akan matsalar haihuwa ne”
“Hmmm haka za ku yi ta bata lokaci da kudin a banza ba ku samu mafita ba, na sha fada maka idan ba aure ka kara ba ba zaka taba haihuwa ba”
“Ni da ita duka likitoci suna cewa ba mu da wata matsala za mu iya haihuwa a ko yaushe, wata kila lokacin ne bai yi ba”
“Idan lokaci be yi a yanzu b yaushe zai yi? Shekara takwas fa, haba abun nan yayi yawa”
“To ya za'ayi haka Allah ya kaddara”
“Aa Wallahi ba za mu gane haka Allah ya kaddara ba, sai ka kara aure mun ga ita ma wacce ka aura bata haihu ba tukuna sai mu san yin Allah ne, amman dan ance za ku iya haihuwa a ko da yaushe ai ba abun dogara ba ne”
Yai dan murmushi
“Mama Rahma fa bata son kishiya”
“Ni son kishiyar na ke da aka min ita? Ko kaunar Ammy na ke aka ce maka? Amman a haka na hakura na zauna da ita gata nan ta zuba zuri'a arzikina ma bata haifi namiji ko daya ba, sai ita wannan dan ta auri sarkin soyayya zai ce ba zai kara aure ba dan bata so ko? To baka isa ba, ni ba zan dauka ba idan kai baka son ganin zuri'ar ka ni ina so”
Juyowa yai ya kalleta da kyau.
“Idan kuma na kara aure ya zama matsalar daga ni ne fa?”
“Sai mu a cigaba da neman magani, amman ai yanzu ba za a gane ba sai ka kara auren, ba fa zan yarda ayi ta tafiya a haka ba har mu zo mu mutu ba mu ga yayanka ba”
Tana kaiwa nan ta mike tsaye ta nufi upstairs. Da kallo Aliyu ya bita har ta haye sannan ya kawar da kansa ya sauke ajiyar zuciya daman ya san Mama Fulani bata masa da sauki idan aka tabo bangaren haihuwa shiyasa ko da yaushe yake kokarin ganin ya kare Rahma, amman a yanzu dole yai ma tufkar hancin ko dan saboda Mama Fulani a yanzu yake ganin ya dace yai amfani da shawarar Nasir na maida matsalar a kansa shi kadai, sai da ya shafa kansa sannan ya mike tsaye ya fice daga falon zuwa part din Ammy domin ya gaisa da ita.
ATAA POV.
Dana soma tsarguwa da yadda suke kallon suna aybanta ni ne yasa na tashi na tashi na bar musu falon na dawo garejin na zauna na karasa cin abincin, sai da na cinye shi tass na koma ina tsude kwanon da kuma hannuna abincin ko dadi babu dan kawai ina jin yunwa ne domin abincin Ammy ya fi na Mama Fulani dadi, da na gama sai a dauki plate din da cup din na nufi garden na wanke tare da tara wasu ruwan na sha sannan na dawo garejin na kife su guri daya da wacan plate din da Mama Fulani ta bani da farko, ni ina ruwana da kymarta ai na kara samun wani plate din da cup, sai da na jerasu sannan na kwanta a gurin ina jin gajiya na sauko min. Kamshin turaren Aliyu da na ji ne yasa na dago kaina na kalli kofar shigowa garejin sai na ganshi a tsaye yana kallona fuska a hade kamar na masa wani abun, har harara na watsa masa na turo baki kamar yadda na saba idan ina fushi na juya masa baya na kama tsorona ina ta watsa da shi.
“Idan Kamal ya sake zuwa nemanki a gidan nan sai na bata miki rai”
“To ni na ce ya zo nemana? Ni ina ruwana”
Yana fada a take na bashi amsa ba tare da na juyo ba, har sai da na ji kamshin turaren na shi na kara matsoni alamar ya baro gurin kofar ya nufo inda na ke kenan, sai nai saurin tashi zaune still bakina a ture ina kallonsa har ya karaso.
“Kar na sake ganin kin yi wanka a garden”
Ya fada yana zare min ido, ni ko kuwa be san bana jin tsoronsa ko kadan a raina ba.
“To ina kake son naje nai? Idan na yi wanka a wani gurin sai ga a ce na yi ba daidai ba dake ni ko? Ni ba zan iya wanka a bandakin wani kato ba ace kullum zan yi wani abu sai dai na je bandakin mai gadi nai ni ba zan sake yin komai a can ba”
“Tashi ki koma bq a can za ki rika kwana”
“Ba zan koma ba, ni babu inda zan je, matar gidan a nan ta aje ni dan haka a nan zan zauna ba zanje ko ina ba”
Na bashi amsa kai tsaye ba tare da fahimtar inda yake nufin naje ba. Matsowa yai kusa da ni ya kai hannunsa ya rika gashin kaina ya matse shi sosai ya mikar da ni tsaye da shi yana kallon idon cikin wani irin bacin rai ya ce
“Idan ina magana kina ba ni ko wace amsa sai na ballaki”
“Ka balla ni mana, ka balla mahaifiyata ai, ka gama da ni daman, kadan ya rage kuma sai ka karasa ni a yadda kake so ai, ba zan taba tsoron ka ba Aliyu, ba zan taba kaunar ka ba, ba kuma zan taba kyale ka ka fada min magana daya marar dadi ba, ko wace magana da zaka fada min ina da amsarta, ba zaka cutar da mahaifiyarta kuma ka sake cutar da ni ba, azzalumi kawai kai da yan'uwanka ba ku iya komai ba sai zalinci sai danne hakkin wanda kuka fi karfinshi sai cin amana, Wallahi Allah sai ya saka min a ko wane zalinci da kuka min, kuma matarka ba a zata taba lafiya ba har abada”
Ina fada yana matse min gashi da dukan karfinsa har sai da na fashe da kuka sannan ya sake ni na fadi a gurin na fashe da kuka.
“Mugu”
Daf da zai fice na fada masa haka sai ya juyo ya kalleni da cat eyes dinsa, sai kuma ya juya ya fice ba tare da ya sake cewa komai ba. Be yi minti biyar da fita ba sai ga Inteesar ta shigo garejin.
“Ataa wai Ya Aliyu ya ce ki taso ki koma bq acan zaki rika kwana”
“Idan naje ai Mama Fulani fada zata min”
Na fada cikin kuka ina murja idona.
“Ba zata miki ba tun da danta ne ya saki, mi akai miki kike kuka?”
“Ba komai”
Na fada ina turo bakina tare da mikewa tsaye nadauki jakana da plates din da tabarmar da na nade na bi bayan Inteesar, tana gaba ina biye har muka isa wani bangare na can gefen part din Ammy, an zagaye gurin da wani dan karamin gate, ciki muka shiga ni dai ina ta jin tsoro daman can gida mai fadi sosai tsoronsa na ke ji, wasu kanann dakuna na soma hangowa gefen dakunan an kawata su da fulawoyi gwanin sha'awa, da muka isa gurin dakunan sai na tsaya na ki na karasa ciki har sai da Inteesar ta hau saman dan karamin matakalin ta tura kofar daya daga cikin dakunan da suke gurin.
“Ke karaso ba komai”
Nake kafada nai alamar ni ba zan zo ba, dan ina jin tsoro taya zan iya kwana a nan ni kadai. Dage labulen tai hakan yasa na karasa kusa da ita ina kallon dakin, katuwar katifa ce a kasa an lullube ta da zanen gado mai kyau da filo har biyu a kai, a gefen dakin kuma wata kofa ce wacce nake saka ran bandaki ne a can.
“Ki shiga”
“Ni ba zan kwana a nan ba”
“Ba komai fa kuma kin ga akwai fanka da katifa”
“Ni bana so”
Ta saki kofar taja kofar ta juyo ni ma na juyo na biyota har sauri nake kar ta barni baya. Muna fito daga bangaren muka hango Aliyu tsaye jikin wata kyakkyawar mota yana kokarin bude ganin mu ya yasa shi tsayawa yana kallonmu.
“Ya Aliyu ta ce wai bata so ba zata zauna a can ba”
Kallona kawai yai ya dauke kai ya shiga motarsa aka bude masa gate ya fice daga gidan. Ni kuma na koma garejin na shimfida tabarmar ta na aje kayana na kwanta a gurin hankali ya fi natsuwa da nan din duk da a nan ma ina jin tsoro amman gwara nan da can din. Ina kwance na ji ana kira na.
“Ataa”
Muryar Anty Rukaiya ce hakan yasa ni saurin amsawa na mike da sauri na nufi part din Mama Fulani, a bakin kofar falon na same ta tsaye.
“Ance ki je ki gyara part din Ya Muhseen ashe ba ki gyara shi ba ko?”
“Wankin da aka saka ni yasa na manta”
“To yanzu an tuna miki”
Ta fada tana yatsina fuska, sannan ta kauce jikin kofar ni kuma na raba gefe na shiga na dauko tsintsiyar da mopper da robar da nake zuba ruwan mopping din ciki na hada komai sannan na dauko na nufo part dinsa, ina isa bakin kofar na kai hannu na tura kofar falon na shiga na yi zaton ko baya ciki sai na same shi cikin falon a zaune yana video call da wata, ganina yasa ya katse video ya kalle ni fuska a hade wai shi har yanzu fushi yake da ni, yana kallona nai saurin gaisheshi ina risinawa.
“Ina wuni”
“Ban sani ba, ba na ce karki sake min magana ba?”
“Yi hakuri”
“Fice ki ba ni guri”
“Mama Fulani ce ta na zo na gyara gurin”
Na fada ina dan turo baki idona na kokarin cika da hawaye. Maida kansa yai gurin wayar ba tare da ya kula ni ba.
“Ya Muhseen kai hakuri ka daina fushi da ni ba zan sake boye maka komai ba daga yanzu”
Na fada cikin da damuwar yadda ya ke min tsakanin jiya da yau, domin har ga Allah na damu da rashin kulani da yake yi. Kallona yai sai ya sakar min murmushi.
“Na ji”
“Na gode”
Na fada nima ina murmushi tare da daukar ruwan mopping din ma nufi bedroom dinsa. Shara na fara yi na kawo ta bakin kofar falon sannan na soma mopping, ina cikin mopping din ya zo bakin kofa ya tsaya yana kallona wayarsa a hannunsa.
“Pretty karki sake wanka Garden kin ga ke macece ba namiji ba, i'm sorry dazun na kasa dauke idona akanki kina da kyau gaskiya ba zan boye miki ba kina da abun da ake so a jikin mace kin san ni bana gani nai shiru, amman dai karki sake wanka a garden”
Kunya ce na ji ta rufe ni, ni har na manta da zancen ya ganni ina wanka dazun amman yanzu ya tuna min sai na ji babu dadi.
“Bana son wanka a bandakin mai gadin ne shiyasa”
“Be ma dace ki yi wanka a can ba, shi ma ai namiji ne, idan za ki yi wanka ko wani abu ki shiga bangaren Mama ki yi”
“Ai kasan Mama Fulani ba zata yarda ba, dukana ma za tai”
“To ki shiga bangaren Ammy ko kuma ki zo nan idan ina nan zan fita naje part din Mama Fulani har ki gama, amman karki sake wanka a garden”
“Tau”
Na fada a ladafce sai yai murmushi.
“Good girl”
“Aisha.... ”
Kamar daga sama na ji kiran da muryar Aliyu, yadda ya kiran sunan sai ka rantse da Allah shi ya rada min shi, juyawa Ya Muhseen yai yana kallonsa ni kuma na saki mopper na nufo kofar dan ganin mai kiran duk kuwa da muryar mai kiran na karantar da cewar a hasale yake. Aliyu ne tsaye a kofar falon fuska a hade.
“Fito”
Ya fada a tsawace.
“Mama fulani ce ta ce na gyara part din Ya Muhseen”
“Fito na ce kar na sake ganin kin zo nan”
Ta fada da kakkausar murya.
“Kamar ya?”
Ya Muhseen ya tambaya, sai Aliyu ya watsa nasa harara.
“Haka kawai zata zo nan ta kebe da kai da sunan wani sharan daki”
ZAKI
By Khadeeja Candy
24...
Kadan-kadan yake tuka motar yana ta kallo har na soma tsarguwa na takure guri daya, sai yai murmushi ya kai hannunsa ya bude wani dan gurin ya dauko wata yar karamar kwalba mai kamshin gaske ya miko min turare a cikin mai shegen kamshi na kamfanin Awwaba scent ya miko min.
“Wannan turaren tun da na siye shi ban yi amfani da shi ba, amman dai kanwata ta fada tace yana da kyau sosai”
Ina karbar turaren kamshi ya baibaiye tun kan na bude.
“Yana da dadi?”
Na gyada masa kai alamar eh sai yai murmushi.
“Miyasa baki son yawan magana ne? Ni fa labari na ke son ki ba ni”
“Labarin me?”
Na tambaya ina dago kai na kalleshi sai ya sakar min murmushi.
“Mi ya kawo ki aikin