Showing 132001 words to 135000 words out of 225640 words
har be janye yatsansa daga nuna Muhseen da yake ba sai rawa yatsan yake kamar zai da ki Muhseen da hannunsa.Wani irin abu yake ji yana masa yawo cikin jini wanda be taba jin irinsa ba, duk wani kishin Ataa da yake a can baya na yanzu ya ninka shi ninkin ba ninkin, ya yaba kyauta ya janyo gashinta kanta ya rika yatsanta, tunawa da irin kallon da yai mata da kalamansa na jiya sai ya ji kamar an yanga tsagen jikinsa an zubar a kasa, har lokacin Muhseen be iya cewa komai ba banda kallon kallon da suke da juna shi da Aliyu.
“Wai miye haka ne? Shikenan idan kuma abuja hankalin Fulani ya tashi idan kuma kuna nan nawa ya tashi? Wannan wace irin rayuwarce?”
Aliyu ya juyo ya kalli Momy.
“Ki fada masa ya daina shiga gonata”
“In daina shiga gonarka ko ka daina shiga gonata? What kind of nonsense is this, idan ina yaba kyau Ataa ko magana da ita ko taba ta miye matsalar ka da wannan?”
“Babu har sai ka sake”
Aliyu ya fada yana daga masa gira sannan ya fice daga falon zuwa bq.
“It's because tana gidanku?”
Muhseen ya fada a fusace yana bin Aliyu da kallon haushi.
“Muhseen nan mu ba gidansu ba ne, gidanku ne”
“To idan ba shi ba Momy miye ruwansa da ni? Naga dai ba shi da alaka da ita kamar yadda ni ma ba ni da, kuma son Ataa na ke son ta na ke be isa ya hana hakan ba... ”
Amina ta kalli Momy Momy ma ta kalli Amina kamin ita Aminar ta juya ta koma cikin dakinta.
“Na rasa gane kan Aliyu”
Muhseen ya sake fada.
“Ka yi hakuri Muhseen zan masa magana, ka yi hakuri dan Allah”
Maganar da Momy ta masa ce ta saka ya zauna saman kujera yana ta huci da mamakin yadda Aliyu yake son masa fin karfi.
ALIYU POV.
Tafiya yake yana kamar ba kasa yake takawa ba shi kan shi be taba jin kanshi a cikin irim wannan yanayin ba kamar yau. Ji yake kamar ba zai jure wani ya kara yabon kyau Ataa ba, ko da mace ce balle namiji. Yana shiga bq din Ataa ta daka tsalle tana ihu ta yi bayan Nana da ke zaune ta boye gabanta sai faduwa yake ta yi zaton ko dukanta Aliyu ya zo ya yi, duk da bata tsoronsa a yanzu amman tana tsoron yanayin da ta ganshi a yanzu. Yayi kokarin sauke fushinsa ya dan saki fuska sannan ya taka balcony din yana isa bakin kofar dakin da Nana take ciki ya tsaya ya cire takalminsa sannan ya shiga, risinawa yai har kasa kamar jiya ya gaishe ta ya mata ya jiki ta amsa masa fuska a sake Ataa na bayan Nana zaune tana dan lekoshi ta kawar da kai.
“Dan Allah Mama kar a sake bari Ataa ta fita tsakar gidan nan babu mayafi a jikin, kin ga akwai aljannu masu shiga jikin mutum gidan be rufe jiki ba, ko ka rufe ma ya aka kwashe balle kuma ba a rufe din ba? Yana da ta rika rufe jikinta da gashin kanta”
“In-Sha-Allah zai rega sakawa, muna goziya jiya kaya sun zo masu kyau Allah ya biya”
“Amin”
Yana amsawa da amin ya mike tsaye yana watsawa Ataa wata uwar harara domin mugun haushinta yake ji kamar ita tace Muhseen din ya kama hannunta ya rike, ita kuma ta murguda masa baki ta buya bayan Nana.ATAA POV.
Yana fita na fito daga bayan Nana na zauna daidai ina turo karamin bakina.
“Wai shi baya son ya ga wani na min far'ah ko muna wasa ko magana, ya fi son ya gan ni cikin bacin rai, idan yaga wani ya sakar min fuska ji yake kamar an masa ruwan mutuwa a zuciya”
Da yaren buzanci na fada cikin mugun jin haushinsa. Dariya Nana ta yi tana kallona ta ce.
“Tunda ba ya so ai sai ki daina, namiji baya jindadi idan yana ra'ayin mace yaga wani namijin na kula ta”
“Wacan zai ra'ayina? Wallahi duk ya bi ya tsane ni ban san abu da nai masa ba, bayan ma ni na fi dacewa na natseshi”
“Ki tsane shi aka ce mi? Ai baki da wata hujja ta tsanarsa, domin ya gama mana komai a duniyar nan”
“Haushi na yake ji kila ma dan yaga na fi shi kyau ne, sai wani ji da kan banza, kuma sai na kula Muhseen din haka kawai sai na yi ta shiga kunci ina bakin rai kamar shi, haka jiya ya kori mai koya min karatun nan da ya zo, wai ya cika far'a ya fi son ya ga ina ta bakinciki, shi fa dariya ta bakinciki take saka shi mtchhhhhhh”
Na karasa ina jan tsake har ga Allah yau kan Aliyu ya ba ni haushi, ban san abunda na tsare masa ba yake bakincikin ganin dariyata, wani lokacin ma sai yai ta abu kamar ba shi ba, dazun da naje tambayarsa ai dariya yai min, jiya yai min siyayya har ina jindadi amman yau ya canja kamar ba shi ba.
Murmushi kawai Nana take tana kallona kamin ta koma murza yatsun hannunta.
“Yanayin yaron nan yana tuna min da mahaifinki, haka yake kishi a lokacin da yake so na, ni kuma ina kishinsa saboda kyausa, idan yayan manyan sarakai suka zo nema na ranar ba zai yi bachi ba, saboda yana jin kamar zai rasa ni”
Ta fada da yaren buzanci hawaye na sauko mata, sai na kara matsawa kusa da ita na kwantar da kaina jikinta, sai ta shafa kan nawa hawayenta na sauka a kumatuna.
“Mutuwa ba tai kyau ba”
Ta fada da hausa tana son fashewa da kuka. Nima hawayen na soma yi tunawa da Baba na na san da yana raye duk wannan rayuwar ba mu shige ta ba, balle har Aliyu ya nemi takura domin Babana yana so na sosai. Ganin ina hawaye yasa tai saurin share nata kukan tana dariya kamar ba ita ba.
“Yana can cikin rahamar Allah In-Sha-Allah”
“Eh Nana yana cikin Rahama Allah ya jikanshi”
“Amin”Sanye da uniform Siyama ta kawo mana abun karyawar mu bayan ta gaisa da Nana ta fito daga bangaren mu ni kuma na biyota ina tambayarta ko nima zan iya zuwa makarantar.
“A a yau ba a zuwa sai da yamma, ai ita Islamiya sai assabar da lahadi kawai ake zuwa da safe”
“Na sani, amman na ga wata islamiyar idan mutum baya zuwa makarantar boko sai ya tafi islamiyar safe”
“Wannan ba a zuwa”
“Sai kin dawo Allah ya tsare”
Na fada ina kallonta gwanin sha'awa, sannan na juyo na dawo bq din na soma cire uniform din ina tunanin maganar Nana ta dazun wai idan yayan manyan sarakuna suka zo sai yai ta kishi, lallai Nana ta yi farin jini tunda har da yayan sarakuna sukai nemanta.
MUHSEEN POV.
Yana zaune a falon har Aliyu ya fito daga bq ya shiga motarsa ya dauki hanyar gida. Tunani yake ta yi yadda Aliyu ya zo rana tsaka yake son hana shi kula Ataa, idan ma wai wani sonta yake to shi mai gaba daya zai yi idan take takensa kenan shi zai fito kai tsaye ya aureta ya ga yadda zai yi. Har Momy ta gama hada breakfast din ta zubawa Siyama ta kuma zuba na su Nana ta bawa Siyama ta kai musu Muhseen na zaune a gurin be huce ba, a dinning ta jera sauran ta fada masa ya tashi ya karya sannan ta wuce bangare Daddy dan kai masa na shi su karya tare. Bayan ta gama da Daddy ta sallame shi ya wuce gurin aikinsa ta dawo part dinta sai ta samu Muhseen zaune a dinning shi kai yana cin plantain a hankali kana ganinsa kasan hankalinsa baya jikinsa, shi kai ne a dinning din hakan na nufi Amina da Husna sun gama karya sun tafi shi kuma ko rabi be yi ba. Sai da Momy ta kai kulolin data dauko part din Daddy kitchen sannan ta dawo dinning din ta ja kujerar da ke fuskantar ta Muhseen ta zauna.
“Ba ka ci abincin ba?”
“Momy ina tunanin ya kamata na fadawa Abbah da Daddy zancen Ataa kara su san da maganar, idan ma karatun za tai ko wani abu sai tai a gidana, ko waje ta kama sai a fitar da ita ai”
Momy ta dan yi shiru na waji lokaci tana sauke ajiyar zuciya. Kamin ta kalli Muhseen a natse ta fara magana.
“Shekaranjiya na tafi gidansu Rahma gurin bikonta, wai ta yi yaji ta tafi gida saboda mijinta na kula Ataa, nemawa mahaifiyarta magani da zuwa dubata da yake sai Rahma ta dauka son ta yake, shi ne tai fushi ranar da na je bikonta ni da kawata babu kalar maganar da mahaifiyarta bata fada min ba saboda Ataa, tana kiranta da yar talakawa yar bara a titi wai yar su ba za ta yi kishi da Ataa ba”
Tun da Momy ta soma maganar Muhseen yake kallonta dan shi be ga ta inda wannan abun ya shafe shi ba, domin ba matsalar wani ce yanzu a gabansa sai ta shi.“Gaskiya Rahma bata kyauta ba, kuma be dace tai haka ba, cewa akai Aliyun son ta yake ne?”
“Ni kaina ban jidadin abunda mahaifiyarta da ita Rahma kanta su kai na tun farko, kuma ina tunanin tana wannan abun ne saboda tana ganin it kadai ce a gurin mijinta, shiyasa na yanke shawarar...”
Sai ta kasa karasawa kamar mai jin nauyi. Muhseen ya kashe kunne sosai ya maida hankali yana saurarensa, main reason din yake son ya ji domin ya fara fahimtar inda zancen Momy na dosa.
“Shawarar me?”
“Wata kila Fulani ba zata bari ka auri Ataa ba, ko kuma idan ka aureta ta gallaza mata, ko wani abun ya samu kyauta wanda zai iya sakawa wata rana ka sabu da ita ko musguna mata, amman ina da tabbacin Aliyu ba zai iya juya mata baya ba ko da baya sonta saboda ya san hakkin aure, kuma mutumen da ya zauna da Rahma zai iya zama da ko wace irin mace a duniyar nan, duk wani guri da fada na Rahma da mahaifiyarta akan Ataa ne shiyasa na yanke shawarar Aliyu ya aureta ko dan gorin da suke mata na kuma nuna musu na isa da shi...!”
Wani irin abu ya ji ya daki kirjinsa sai yai murmushi yaja numfashi ya sauke.
“Ya fada miki cewar son iskanci nake wa Ataa ke nan? Kuma kin yarda duk da kin san ni bana neman matan banza, dan na ce ina son Ataa saboda tana da kyau ai ban yi laifi ba, kina tabbaci idan bata da kyau Aliyu ma zai so ta? Kina da tabbacin shi din Mama Fulani zata bar shi ya aureta? Kawai dai kin nuna ke kika haifi Aliyu da kanki kuma kin nuna masa son kai, kuma Ina masa farincikin samun uwa kamar ki wacce zata so abunda danta yake so har ta fishi son abun”
Yana fadar hakan yaja kujerarsa baya ya mike tsaye. Tuni idon Momy ya cika da kwalla zuciyarta kuma tana mata babu dadi.
“Allah shine shaidata, ban aikata hakan dan nuna son kai ba, sai dan ganin kamar Ataa zata fi samun kwanciyar hankali idan ta aureshi, kuma Rahma ta raina kanta gudun yar talaka sai ta ga ta aure mata miji ma gaba daya, idan har bana son ka ba zance Amina ta aureka ba, ba zan baka yar cikina ba Wallahi ban rike wani dabam ba, kai da Aliyu duka daya ne a gurina, na dauke dana wanda zan iya sakawa na hana, na zaba masa ko na canja masa zabi”
Juyowa Muhseen yai ya kalleta.
“Ashe kin dade da yanke hukunci kika barni ina da lalabe cikin duhu, ni da Aliyu ba daya ba ne a gurinki da ni ma kin dauke ni da da kin hana Aliyu son Ataa ko da zai mutu kin ba ni, domin na fishi sonta kuma na fi cancanta na aureta fiye da shi ita kanta idan kika tambaye ta zata fada miki ni take so, kin sani Momy na tun yau ba ina son Ataa amman yau ni za ki zauna a gabana ki fada min gaskiya cewar kin ba danki ita, good luck wish you all the best”
Yana fadar hakan ya fice daga falon a fusace, ya bar Momy tana aikin hawaye.Sai a yanzu take jin cewar bata kyauta, sai a yanzu take jin girman kuskuren da ta aikata, da tasan cewar Muhseen ba zai fahimce kamar haka ba da bata aikata ba tun farko. Fashewa tai da kuka a gurin ta tashi da sauri ta shige dakinta, Husna da Amina suka fito suka bi bayanta jin kukanta hankalinsu tashe.
“Momy lafiya?”
Husna ta tambaya tana zama kusa da ita.
“Sam be dace nai haka ba, yayan fulani ba su cancanci komai a gurina ba sai farinciki da goyon baya, ban za ci cewar Muhseen zai min fahimta baibaiye ba ban tsammaci zai dauki haka ba, Wallahi ban yi wannan abun dan son kai ba sai dan dukansu su samu farincikin”
“Kema kin sani Momy ba zai taba fahimta ba, tsakani da Allah fa ya riga Ya Aliyu sonta, kuma shi Ya Aliyu ba ma cewa yai yana son ta ba kawai dai kina son yin hakan ne saboda Rahma, kuma ya dace ki yi hakan amman za ki iya yi da wata dabam ba dole sai Ataa ba”
Momy ta dauke kanta daga barin kallon Husna wacce take maganar ta dafe kanta tana hawaye.
ATAA POV.
bayan mun gama karyawa, Nana ta ce na je na taya Momy aiki domin yau ko yar sharar da na ke ban mata ba, ni kuma na ki zuwa domin a tunani Aliyu yana nan kuma idan har na je sai Muhseen ya kula idan kuma ya kula ni Aliyun zai iya cewa zai min fada ko ya dake ni ma wata kila.
“Zan je Nana amman sai Aliyu ya fita”
“Tau idan dai za ki tafi sai ki saka mayafi”
Na dan turo baki domin ni dai a cikin gida a ce ka saka mayafi yana takura min sosai. Muna haka ni da Nana na hango Muhseen tsaye a balcony yana kallon kofar dakin mu.Da sauri na tashi tsaye na fito daga dakin domin yanayin fuskarta ya nuna akwai damuwa sosai a tattare da shi.
“Ya Muhseen lafiya?”
“Mamaki kike ba ni yadda kika yarda ki auri Aliyu”
Ba zan iya cewa wani mai maganar ba Muhseen ba, domin sautin muryarsa ne bakinsa ne yake motsu kuma shine tsaye a balcony din dakinmu, amman ta ina wannan maganar ta fito mai kamada almara, dan lekawa nai ina kallon fuskarsa to ko wani abun ya sha ko kuma bachi yai ya tashi yana mafarki? Idan ba haka taya zai furta irin wannan maganar da hankali ba zai dauka ba balle har ta zauna a kwakwalwa.
“Wane irin aure kuma? Wane Aliyu?”
“Kin fi kowa sanin abunda na ke nufi, amman tabbas Ataa kin ba ni mamaki ashe ba ki da tunani ba ki da zuciya kuma ba ki kishin mahaifiyarki da har za ki yarda ki auri mutumen da aka hada ba ki da shi aka cire mata koda ya dasawa matarsa? Mutumen da ya wulakantaki irin wannan mutumen za ki aura?”
Mutuwar tsaye nai wacce ta fi ta kwance hadari da rikitarwa. Sam ban gane inda ya soba ba amman na gane abunda yake kokarin furtawa.
“Ba ka san abunda kake fada ba Muhseen, ni Aliyu be taba nuna min so ba balle har ya furta min, kuma ba zai taba so na ba har abada saboda ya tsani talaka, ni ma kuma ba zan taba son sa ba saboda na sani dan masu arziki, babu wannan a tsakanin mu idan ma wani yai maka karya to karya ce kawai ba gaske ba”
Na fada ina girgiza masa kai, tuni Nana ta taso ta fito daga dakin ta kawo bakin kofa tana kallon Muhseen. A tsawa ce ya ce
“Gaskiya ne Ataa Momy ta fada min Aliyu za ki aura, mutumen da ya cirewa mahaifiyarki koda ta yi wata da watanni tana jinya, saboda kawai ya dauke ta ya kaita asibiti ya kawo ta nan be isa ya goge tabon abunda yai mata ba, domin har abada kodarta ba zata taba dawowa ba, ta koma rabin mutum ba cikakkiyar mutum ba”
“Ni Ataa ni a aka cirewa koda? Ni?”
Nana ta tambaya cikin yaren buzanci tana juyowa da ni dan na fuskance ta, tuni hawaye suka gama wanke min fuska a yau Muhseen ya tona abunda Nana bata san da shi ba, a yau Muhseen zai saka Nana cikin wani halin na damuwa da tunani da zullumin mutuwa a kullum.“Na tsane ka Muhseen na tsane ka, bana kaunar ka, idan ma ka burge ni kai to baka burge ni ba, kai da Aliyu duka na tsane ku, bana son ka bana son sake ganin fuskarka karka sake shiga rayuwa ta”
Na fada da iya karfin muryarta ina hawaye, matsowa yai kusa da ni yana girgiza min kai sai na kada masa tsawa.
“Dukan ku kuna juya rayuwata yadda kuke so saboda ina talaka, Nana bata taba sanin wannan maganar ba ayau ka tona ta ka bude komai, na tsane ka Muhseen na tsane ka”
Ihun muryata ne ya fito da Momy da Husna da Amina suka shigo bq din hankali a tashe. Nana kuka take tana dafe da cikinta ni ma kukan na ke ina rike da dayan hannunta, idan ma zan mata bayani ta ina zan fara? Ya za ayi tai fahimta? Har ta kwamtar da hankalinta.
“Ataa....”
Muhseen na kiran sunana na daka matsa tsawa ina nuna shi da yatsa.
“Karka ce min komai, ka riga ka gama fada mata cewar an cire mata koda sai me kuma? Ka riga ka fada mata abunda bata sani ba, bana son ganin fuskarka na tsaneka na ce na tsane ka”
Kallonsa Momy tai ta kalleni sai kuma ta sake kallonsa.
“Me ka ce mata?”
“Ai ke kika bata komai Momy ke kika ja koma... ”
Be kai Ayaba Momy ta tsinka masa mari, har sai da Husna tai saurin zuwa ta rike mata hannu.
“Muhseen kai ba mutum ba ne, ba ka da tunani irin na mutane, kai sakare ne sha sha sha”
Tana fadar hakan ta juya ta