Showing 90001 words to 93000 words out of 225640 words

Chapter 31 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

na juya sai na ji an fisgo ni da mugun karfi an juyo da ni.

“Wuce ki shiga na ce”

Ya fada cikin muryar dake nuna bacin ransa yana zare min ido.

“Bana shiga gidan da matan gidan ba sa nan”

Cikin daga murya na yi maganar har Mai gadinsa daya koma gurin gate ya zauna sai da ya kallemu. Matsowa yai da fuskarsa yana fitarda numfashi da karfi.

“Haka Muhseen yake miki ko? Shiyasa kike dauko ko wane namiji dan iska, mahaukaciya kawai”

Yana fadar hakan ya sake ni da karfi har yana ture baya kamar zan fadi, sannan ya juya ya koma ciki ya bar ni a gurin tsaye. Juyowa nai na dawo gurin mai gadin na ce masa.

“Dan Allah ka kira matar gidan ka fada mata yanzu”

“Ba kun yi magana da shi ba?”

“Be ce min komai ba sai bakin fada, ni dai dan Allah ka kirata”

“Wallahi Alhajin ne ba a iya masa yanzu zan iya kiranta ya zama ganin laifi”

Na marairaice masa fuska tare da dukawa kasa ina rokonsa.

“Ka taimaka min dan girman Allah, Wallahi ina cikin matsala sosai”

“Gaskiya tun da ya nuna ba ya ra'ayi kara ki hakura kawai, ko kuma na baki number ta kina da waya?”

“Ba ni da waya Wallahi amman dan Allah ka taimaka min”

“Zan kirata amman sai mai gidan ya fita, domin ni bana iya magana kadan idan kuma nai karai ya ji zai iya korata dan ya fada min baya son hayani”

“In tafi zaka kirata kenan?”

“Eh zan kirata In-Sha-Allah”

Daya bani tabbacin zai kirata ne yasa na taso na fito daga gidan, cikin rashin jindadin domin haka ta bata cin ma ruwa ba, daman nasan indai shi ne za ko zai siya sai ya wulakantani tunda dan wulakanci ne. Har na kama hanya sai kuma ya juya na koma saboda bacin ran daya same ni gate din gidan na buga da karfi mai gadin ya sake leko ganina ya bude min karamar kofar.

“Dawowa kikai?”

“Eh”

Na fada da kamar Fada sannan na wuce zuwa bakin kofar falon na taka na kai jikin kofar na buga kofar da karfin tsiya.

“Eh daman ai na san ba zaka siya ba, amman idan ta zalince ce kana so ko? Idan a hanya ka hadu da ni zaka iya sakawa a danne a min tiyata a cire a sakawa shegiyar matarka, mugu kawai duk halin da mahaifiyata ta shiga kai ne sanadi kuma ba zan taba yafe muku ba azzalumai masu.... ”

Ban karasa ba ya bude kofar falon sai nai shiru na kawarda fuskata ina hawaye. Farin jean ne jikinsa da bakar riga mai kwalliya sai fararen takalmi hannunsa rike da waya da kuma keys din mota, kamshin turarensa duk ya cika gurin shi kuma ya min fadi a ido tsoronsa ya cika zuciya, ba kuma tsoro na kar ya dake ni ba, yana da wani irin kwarjinin da ke saka mutun tsoro na rashin dalili. Yana tsaye jikinnkofar daga ciki ni kuka ina daga waje kaina na wani gafen shi kuma idonsa a kaina kamar yana hararata kuma ba harararba. Juyowa nai na sauko daga gurin na nufi gate na fice abuna ba tare da na kara cewa komai ba, shi ma kuma be ce min ba, hanya na biyo ina ta tunanina kala kala ciwon nana neman maganinta da kuma abunda mutumen nan da matarsa suka min. Da karfi aka faka mota gabana sai na ga an turo ganbun motar an bude shi, dana leka sai na ga Aliyu ne a ciki yana kallon wani gurin, ba zai iya cewa na shigo ba saboda bakin girman kansa, idan ma na shiga ban san inda zai kai ni ba, sai akwai nai gaba abuna na barshi a gurin. Sai ya kara cin gabana da motar ba tare da ya min magana ba nima na kara yin gaba abuna, sai ya fito daga cikin motar ya biyo bayana ya fisgo kafadar hannuna ya dawo da ni ya saka ni da karfi a front seat ya rufe motar ya zagayo gefensa ya shiga ya hau titi ba tare daya kalleni ba.

“Wallahi ni ba zan yarda ka cutar da ni ba, wacan zalincin da kuka mana ya isa cin amanar da muka min kai da Mama Fulani sai Allah ya saka min”

Na fada ina saka dayan hannuna na murza inda ya rikani cikin kukan dana fara tun a lokacin daya rikoni ya saka ni motar domin ba karamin riko yai min har yanzu ina jin ciwo a guri. Wayarsa ya ciro ya shiga wani guri yai dannen dannensa sai na ji karar kiran waya yana fita ta speakers din motar.

“Hello Ranka ya dade idan ka kira ta samu, idan ba ta samu ba sai dai mu kira mu gaishe ka”

“To ta samu Bukar kana ina?”

“Ina gida tare da iyalina”

“Ina da patient ne ambulance nake so”

“Subhanallahi waye ba lafiya?”

“Baka santa ba”

“Wani guri zan saka a turo maka yanzu”

Sai yai shiru be ce komai ba, ni yake jira nai magana ni kuma ban sammaci hakan ba tun da naga ko kallona be yi ba.

“Ko ba ki ji ba?”

Ya fada still be kalleni.

“A Clapperto road house number 11 amman ta bayan gidan zaka shigo kananan gidanjen da suke nan”

“Okay”

Yana fadar hakan sai Aliyu ya katse kiran ya dauki wani farin Bluetooth ya saka a kunnesa ya kara gudun da yake. Cikin kannnen lokaci muka isa Clapperto road, wani abun mamaki har kofar gidansu Farida ya faka motarsa ina ta mamakin yadda akai ya san gurin kai tsaye ba tare daya tambaye ni ba. Fita nai daga motar na nufi dakin na kwano ba tare da rufe masa motarta ba. Wasu tufafin na canja mata na saka mata Hijab, sannan na zauna kusa da ita tana ta kallona kamar bata gane ni ba har yanzu. Ina jin lokacin da motar asibitin ta tsaya sai na ji muryar maza biyu sun doso dakin kwanon da muke ciki.

“Ina marar lafiyar take?”

“Gata nan”

Na fada da sauri ina mikewa tsaye sai suka shigo suka dauki Nana suka fita da ita zuwa cikin motar asibitin Farida da Mahaifiyarta suka fito suna kallo har da wasu makota da ke kusa.

“Ni ina zan shiga?”

Na tambayi mutanen da suka shige cikin motar. Sai na ji muryar Aliyu yana fadin.

“Nan za ki shiga”

Da sauri na nufi motar na shiga daman ban rufe ba, shi ma kuma jin kai ya hana shi rufewa. Da na shiga motar sai yai mata keys muka bi bayan mutane sai da muka fara nisa sai na ga sun bi hanyar Uduth shi kuma ya dauki hanyar arkilla da ni.

“Kai ba fa ita za a cirewa koda ba ni, ita ba kasa an cire mata daya ba, idan aka kara cire wannan mutuwa za tai”

Na fada ina shirin fashewa da kuka.

“Karki sake min maganar kodar nan karki sake”

Shine Kawai abunda ya fada min ba tare daya kalleni ba ya cigaba da tukinsa ni kuma na cigaba da rare masa kukana har muka isa arkilla, wata hanyar ya biyo inda manya gidaje na alfarma, bakin wani katon gate ya tsaya wanda saman gate din duk iccen fulawa ne da yai rassa ya sauko har gurin gate din. Da karfi zai saka a cire min kodar ya sakawa matarsa ni ya kyale ni shine kawai abunda zuciyarta take raya min. Da muka shiga harabar gidan sai na ga manyan motoci uku a fake kusa da ta farkon ya faka tashi motar ya bude ya fita ba tare da ya ce min komai ba. Nima na bude na fito na tsaya gurin motar ina hawaye gaba daya tsoro ya gama kamani dan a nawa tunanin wata kila ma tsafi yake. Da kai yai min alama da na wuce ciki ni kuma na lake kafadata ta alamar ba zanje din ba, gaba yai abunsa ya bar a gurin ina karewa gidan kallo ina hawaye, gidan be min kama da na yan yankan kai ba amman ba ni da tabbacin ba cutar da ni zai yi ba, gashi kuma ya saka an tafi da Nana waya sani ko sani abun za a mata. Karar bude kofar falon naji kamar yadda na ji lokacin da zai shiga, sai na hango wata farar mace ta fito daga falon ta doso inda nake tsoro ne ya kamani a zatona wani abun zata min sai ta kusan karasowa kusa da ni sai na ga ashe matar da na taba gani gidan Mama Fulani ce wacce ta ba ni cake, fuskarta da tausayi ta karaso inda nake ta kai hannunta ya rika fuskata sai na ga idonta da hawaye.

“Alhamdulillah Allah mun gode maka, sannu kinji”

Na gyada kai ina hawaye sai tasa hijabina ta goge min fuskar.

“Daina kuka kinji zo muje ciki”

“Ina nan ya kawo ni?”

“Ya kawo ki inda za ki samu gata ki samu jindadi a nuna miki kauna”

“Mamana tana asibiti ya saka an tafi da ita ban san abunda zai mata ba, bana kwanciyar hankali har sai naji halin da take ciki”

“Ba cutar da ita zai yi ba, shi ma ya dade yana nemanki da inda kike ni da shi, ban san cewa ke ce ba sai bayan da Fulani ta koreki, ki aminta da mu Wallahi ba za mu cutar da ke ba”

“Mahaifiyata fa?”

“Ita ba zai mata komai ba”

Matar ta fada tana hawaye sai ta rumgume ganin ina kuka. Shi kuma ya fito daga falon ya nufo inda muka na yi zaton ko wani abun zai fada min sai na ga ya bude motarsa ya shiga.

“Dan wajen Fulani komai ake ciki ka kira ni saboda hankalinta ya kwanta”

“Okay Momy”

Ya fada yana kallona daga cikin farin gilashi motar. Sannan taja hannuna ta nufi hanyar falon da ni, da muka shiga ciki sai sai yan matan nan da na gani idan Mama Fulani su Biyu Siyama da Husna da kuma wata wacce ban sani ba suka ce min

“Sannu”

Kai kawai na gyada musu na zauna a kujerar da matar ta zaunar da ni. Sannan ta zauna kusa da ni ta rike hannayena.

“Dan Allah ki daina kuka Wallahi raunana min zuciya kike idan kina kukan nan sai ki saka nima nai”

Sai kuma ta kalli Siyama tana share hawayenta ta ce.

“Shiga ciki ki hada mata ruwan wanka”

“Aa ba zan yi wanka ba, na fi son naje asibitin kusa da ita hankalina zai fi kwanciya”

“Za a kula da ita za a mata duk abunda take bukata idan ma kinje ba wani abun za ki mata ba, kuma ba cutar da ita zai yi ba taimakonta zai yi”

Kai na girgiza.

“Aa ni ban yarda ba, wacan karon ma cewa aka yi taimakona za ayi ashe koda za a cire mata a bar mu da lalura, kuma mutanen da sukai wacan aikin sune a yanzu, a gabana ya kira wani likita ya aiko da mota aka tafi da ita ni kuma ya kawo ni nan, hankalina be kwanta ba, zai iya cirewa ya sake kasawa matarsa, dan girman Allah ku tauyasa min ba ni da kowa a duniyar nan sai Nana ban san kowa ba a cikin danginmu Wallahi idan ta mutu ban san inda zan je ba”

Ina rufe baki matar ya saka a kirjinta ta rumgume ta fashe da kuka sautin kukanta har ya fi nawa dagawa. Husna da bakuwar da ban san sunanta ba suma suka saka kukan dakin yai tsin ba ka jin komai sai sautin kukan mutane hudu, ni Matar, Husna da bakuwar ban da Siyama da ita hawaye kawai take. Mun dauki lokaci muna kuka duka aka rasa wanda zai bawa wani hakuri balle kuma har ya rarrashi, Siyama ce ya shiga daya daga cikin dakunan ta hada ruwan wankam sannan ta fito tana fadin.

“Momy ga su can na hada dakina”

“To”

Wacce aka kira da Momy ta amsa cikin muryar kuka, ni dai ina rumgume a kirjinta ina fitarda numfashi a hankali, na jidadin rumgumar da tai min rabon dana kwanta jikin Nana a haka har na manta amman yau wata uwar ta rumgume ni na yi kuka a jikin rigarta ba tare da ta nuna min kyama ba. Ko da yake ba a fuska da hali ake gane mugun mutum da na kwarai ba, domin da a fuska ne da Doc Asim be mana haka ba, daga nai daga jikinta ina jan majina sai ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

“Ta so mu shiga ciki ki yi wanka”

“Momy bari na kaita mana”

Bakuwar ta fada tana mikewa tsaye gaban tv dana tarar da su suna game ta nufo inda nake, wata kila ita ma yar gidan ce domin ta yi kama da Momyn sosai. Hannuna ta rika na tashi tsaye taja har cikin dakin dan madaidaici mai gado daya da yar karamar kujera da teburin karatu an kawata shi iya gwargwado.

“Nan za ki cire kayanki ko sai kin shiga ciki”

“Ciki zan cire”

Ta min murmushi.

“Ya sunanki hala?”

“Aisha”

“Ni kuma sunana Amina, jin ga a girme na girmeki dan haka ke kanwata ce”

Bance mata komai ba sai ta nuna min bandakin.

“Shiga ciki sai ki yi wankan bari na kawo miki wasu tufafin da za ki saka”

“To”

Na nufi bandakin cikin tsoro domin ni har yanzu zuciyata bata natsu da su ba, a dayan bangaren kuma na kasa aminta cewar Aliyu ba cutar da Nana zai yi ba. Ban wani dade gurin wankan ba na gama na dauki zanena na daura na fito tsoron gashina har gadon bayana. Ko da na fito Amina tana zaune rike da kayan tana jirana.

“Wow”

Ta fada tana kallona sai kuma ta aje kayan hannuna ta nufo bayana tana taba gashina.

“Ke da gaske gashinki ne? Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kamar aljana ko dai kari kikai”

“Gashi na ne”

Na fada cikin rashin sakewa.

“Ki shafa mai ki saka rigar”

Ta fada tana fita daga dakin. Abaya ce yellow da under wears sai dan karami dankwali baki. Sai da na fara saka kayan ciki sannan na saka abayar na daura dankwalin a fito da tsorona sai na zauna kasa, gudun kar na zauna a saman gadon ya zama laifi komai ban shafa ba duk kuwa da tulin kayan kwaliyar da suke dakin tsoro nake ban sani ba ko suma kamar Maryam da Rukaiya suke. Kofar dakin aka turo sai ga Momy ta shigo dauke da plate da kofi.

“Aa ya kika zauna kasa? Tashi ki zauna saman gadon mana”

“Nan din ma ya ishe ni”

“Aa tashi ki zauna ya za ki zauna kasa”

Saman gadon ta aje plate din da ke rufe sai ta mika min kofin hannunta ashe tea ne a ciki.

“Ki ci abinci kinji ki kwantar da hankalinki ki yarda da mu ba zamu taba cutar da ke ba, kuma mahaifiyarki zata samu lafiya ta warke In-Sha-Allah”

“Bana jin yunwa bana iya cin komai a yanzu”

Na fada ina aje kofin tea a kasa sai ta dafa ni ta zaunar da ni kusa da ita saman gadon.

“Na sani an miki zalinci kuma an miki rashin kyautawa, tabbas Dan wajen Fulani ya yi kuskura ban sani ba ko za ki yarda cewar ba da saninsa aka aikata miki hakan ba?”

“Idan ba da saninsa ba ya za ayi a sakawa matarsa? Kawai sun yi amfani da rashin ilmina ne suka saka na saka hannu a takardun da sunan taimakona za ayi ashe kodarta za a cire, saboda ya tambayi ne na ce masa ba ni da kowa sai yai amfani da wannan damar ya cire mata koda kuma ya saka a kulleni har kwana hudu gidan yan sanda, wai na bata masa suna”

Na karasa ina hawaye.

“Wallahi ba da wanin sanin sa akai miki haka ba, kudi aka bashi aka ce ya siyo ba mu san cewa zalinci zai yi ya cire kodar mahaifiyarki, kuma tun daga lokacin da abun ya faru muke ta neman ki da inda za mu ganki mu taimaka miki amman ba mu samu ganinki ba, ban san cewa ke ce kike aiki a gidan Fulani ba sai daga baya, shi kuma ya fada min cewar kin ki bashi hadin kai ne shiyasa be taimaka miki ba”

“Ina tsoron taimakon kowa ballanata na shi, Wallahi Aliyuna nan bashi da imani da tausayi kansa kawai ya sani”

Wasu yawu ta hade da karfi tai min murmushi.

“Ba ki fahimce shi bane, amman za ki sanshi nan gaba kadan”

Ban sake cewa komai ba bayan hawayena da na share ina murza yatsun hannuna na rasa yadda zan yi zuciyata ta aminta cewar ba cutar da nana Aliyu zai sake yi ba.


ALIYU POV.

Daga Arkilla ya koma uduth din, duk wani abu da ake ma patient kamin a shiga da shi ganin likita shi yai kama daga karba kati da kaiwa a bude file. Sannan ya kira Doc Bukar ya fada masa cewar ya kawo ta har an shiga da ita ciki, ba bata lokaci Doc Bukar ya iso asibitin sai da Aliyu yai masa bayanin cewar matsalar koda ce sannan ya shiga dakin da aka kaita ya soma bata taimakon gaggauwa shi da wani likitan. Bayan sun fito Doc Bukar ya saka wasu nurses din suka kaita akai mata hoto a aka debi jininta sannan ya canja mata daki aka kaita wani dakin na musamman.

“Aliyu ya akai aka bar matar nan haka? Ciwon nan yana kokarin cinye ta?”

Lokacin da suka jero suka fito daga emergency ne Bukar ke masa wannan tambayar.

“I can't tell yanzu fada min ba zata samu sauki ba?”

“Zata samu mana, amman dole sai mun jira Doc Muhseen ya zo shi kadai zai mata aikin nan tun da Doc Mustapha yana waje, daman sune likitocin da suka fi kwarewa wannan fannin”

“Ka kira shi?”

“No na yi request a kira shi dai, ai ba mu muke kira ba, kuma ko bayan nata ai zai zo ya duba wasu patients daman amman sai next week”

“Kana tunanin zata kai gobe?”

“Yes zata iya kaiwa next year ma a haka, daman yanzu jini da ruwa ne abunda ta fi bukata, to mun saka mata ruwa jinin kuma na saka a bincika idan kawai wanda yai daidai da nata ko kuma zai iya zama a jikinta”

“Ka gwada nawa mana idan zai yi”

Doc Bukar ya kalleshi.

“Seriously?”

“Yes ina son rayuwar matar nan Bukar, ko me za ayi dai i need her alive”

“Then ka kira dan uwanka ka fada masa idan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login