Showing 207001 words to 210000 words out of 225640 words
da kai, ka yi hakuri kuma kai hamdala ga wanda ya baka ita kuma a yanzu ya karbe ta”
Aliyu ya gyada kai tare da hade wani abu daya tsaya masa a makoshi ya mike tsaye yana share hawayensa, yana kallon Muhseen sai ga fuskar Rahma a fuskarsa, a take rayuwar da kai a da ta fara dawo masa, iyakar kokarin da yai na kawar da kansa daga barin kallon Muhseen ya fara takawa yana jin kamar ba tafiya yake ba saboda nauyin da kafafuwansa sukai masa, hannunsa ya kai ya rika ginin gurin yana maida numfashi a hankali wani abun ya tsaya masa a zuciya ya tokare masa. Da sauri Muhseen ya rika shi ya bude wani dakin da ke kusa da su ya shiga dashi ya zaunar da shi saman kujera. A take Aliyu ya lumshe ido ya bude bakinsa saboda samun taimakon numfashi, know one can express yadda Aliyu yake ji saboda be taba losing wani important person a rayuwarsa ba kamar yau, mamanshi tana raye, Mama Fulani na raye Daddy da Abbah duka suna raye, yana rayuwa da Rahma and he pray for Ataa Allah ya ba shi, bayan tarin dukiya da lafiya da Allah ya bashi, ga kuma samun cikin Ataa Allah ya bashi Allah ya hada masa goma da ashiri na farinciki duk shi kadai, be taba jin yadda ake jin zafin rasa wani ba, be taba sanin haka zafin rashi yake ba, be taba jin zafin rasa wani abu ba sai yau.
Muhseen ya fito da wayarsa ya kira Momy da Mama Fulani ya fada musu halin da ake ciki.
Cikin firgici da rudewa mahaifiyar Rahma ta shiga dakin da Rahma take ciki, ba kuka take ba domin ihun da take ya wuce a kira shi da kuka sai dai hargagi da kuwa.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, na shiga uku na lalace Rahma ta tafi ta bar ni, La'ilaha illallahu”
Ikram da wata gwaggonsu na rikonta amman ta kasa yin shiru sai ihu take, har da tsalle tana direwa kasa, kaico mai rai bakon duniya, yau Rahma ta tafi kamar bata taba wanzuwa a duniya ba. Babu mai iya bayyana yadda Aliyu da mahaifiyar Rahma suke ji sai wanda ya taba rasa uwa ko uba miji ko mata, saboda sune the most important abu a rayuwar ko wane dan'adam. Cikin wani irin karfi Mahaifiyar Rahma take wai ko zata tashi, amman ina mai rai ya aiko an tafi da abunsa, daman can aro aka ba kowa, kuma ranar tafiyar tana nan zuwa komai daren dadewa. Ji take kamar ace tana da ikon dawo mata da rai da ta dawo mata da shi, da ace kudi suna maganin mutuwa a yau da ta cire ko nawa ne an bawa Rahma ranta ta dawo su yi rayuwa kamar da, ina ma tana da yadda za tai Rahma ta sake rayuwa. Fitowa akai da ita daga cikin dakin Ikram da Gwaggonsu suna ta kuka, ga Rahma kwance kamar tai magana amman babu numfashi ta zama gawa.
Kan kace kwabo kofar emergency ta cika da sisters din Rahma kowa sai kuka yake, ciki har da Momy da wasu yan'uwanta da ta dauko su rakota, ba mahaifiyar Rahma ce kadai abar tausayi ba har da yan'uwanta da Aliyu, domin kana kallonsu kasan suna cikin damuwa marar misaltuwa. Momy kan ciki ta wuce gurin Aliyu har lokacin yana nan zaune a dakin da Muhseen ya shiga da shi yana zaune baya kuka kuma ba hawaye idonsa sun yi ja sosai ga wani gumi da har yanzu be daina zubo masa ba.
Momy na shigo Aliyu ya kalleta da sauri kuma ya mike tsaye kamar zai yi magana da ita sai kuma ya kasa cewa komai. Karaso tai kusa da shi tana hawaye tana kallonsa. Sai ya rikata ya zaunar da ita ya zauna kasa ya dora kansa a kan cinyarta, auna rashin Rahma yake a ma'auni mai nauyi amman idan ya hada da Momy sai yaji nauyinta ya koma kamar bashi, da Momy ce ta mutu a yau da be san iya halin da zai shiga ba.
“Ka yi hakuri haka Allah ya so, haka yake a sadda ya so ga wanda ya zo babu wanda ya isa ya hana shi balle har ya tambaye shi dalilin yin haka, kai ma zaka mutu balle abunda ka mallaka ko ka aje”
Be ce komai ba bayan Lumshe ido da yai yana ta hade yawu ko abunda yake jin ya tsaya masa zai tafi. Sai kusan sha daya na safe suka bar asibitin tare da gawar Rahma suka nufi gidan iyayenta da ita. Babu wanda zai ga gawar Rahma ya ayyana cewar ta mutu har sai idan an fada masa ko kuma ta taba ya tabbatar, mai rai bawan Allah iyakar iskancin dan'adam idan yana da rai ne daga lokacin da aka zare rai daga jikinsa ya zama gawa yan'uwan ne za su saffara shi har a kai shi masaukinsa na gaskiya. Kowa ya yaba karfin halin Aliyu na yi ma matarsa wanka kuma yai mata surura kamar yadda addini.
“Allah ga Rahma nan, baiwar ka ce Allah yau ta dawo gareka aron ran da ka bata yau ka karbe abun ka ya Allah, Allah ina son matata ka sani, ita kuma tana so na, mun yi zaman aure da ita na shekaru tsabanin da muka samu atsakanina da ita na rashin jutuwa ko fada ko bacin rai da gangan ko cikin rashin sani Allah ka shaida na yafe mata, Allah kai ma ina rokon ka yafe mata, Allah jinyar da tai kasa ta zama sanadin tsira, Allah ka sadata mala'ikunka na Rahma ka sadata da Annabin Rahma, Allah ka hada ni da matata Aljanna”
Wannan karon be iya rike kansa ba ya fashe da kuka sosai kamar mace, har sai da aka shigo aka fita da shi, hankalin kowa be kara tashi ba sai da aka fito da ita akai mata sallah aka dauki gawarta zuwa makabarta inda gidanta na gaskiya yake kuma gidan kowa. Muhseen ne rike da Aliyu har aka kai makabarta aka saka ta cikin kabarinta, wa zai iya fadar yadda cikin kabari yake? Babu iyakar abunda ido ya gani ko ya ji a duniya ne kawai, the first thing da aka saka bayan gawar Rahma itace sannan aka saka tukane sai haki da ciyayi ya biyo baya, haka aka lullube kabarinta da kasa sai aka tabbatar babu wata kusurwa da wani abun zai iya shiga sannan aka kewaye kabarin ana mata addu'ar neman Rahma. Sannan aka taso aka baro ta can ita kadai daga ita sai aikinta. Gida aka kawo ana karbar gaisuwar, Momy kuma ta bukaci Aliyu ya koma gida su a can su yi na su karbar gaisuwar. Har lokacin Mama Fulani da Nasir ba su iso ba saboda mota suka biyo ba su samu jirgin da zai taso yau.
Aliyu na kusan shiga motarsa Ikram ta zo ta miko masa wata wasika, idonta yayi ja sosai.
“Minene?”
“Ita ta rubuta ta, a lokacin da ka kirata bata iya magana ta miko min, na tambayeta ta waye tai min alamu da kai zan bawa”
Kallon takadar Aliyu ya rika yi na few minutes kamin ya kai hannu ya karba jikinsa na ta rawa. Sannan ya nufi motar ya shiga, Muhseen ne ke tukawa har suka isa gida sai taba takardar yake ya kasa budewa. A can gurin Momy ma an cika da mutane yan'uwan Daddyn da Momy, har Daddyn da kansa da wasu abokansa da suke kusa da kusa suna tare, har da yan'uwan Mama Fulani da suke yola wadanda suka zo ta jirgi. duk wanda ke gurin tausayin Aliyu yake, sai da magariba Mama Fulani ta iso ita da su Maryam da Ammy gaba daya gidan aka kwashe ba a baro kowa ba.
After Sallah isha'i Aliyu ya shiga bangarensa da ke cikin gidan ya kulle kansa a cikin dakin ya bude takardar cike da fargaba ya fara karantawa.
_Zaka karanta wasikar nan ne wata kila, bayan ba raina domin na san ba sakan cewa ina asibiti ba, da farko zan fara taya ka murnar samun haihuwa da kai, kuma nai maka godiya na rufa min asiri da kai da hakurin zama da ni na tsawon lokaci, ina jin a jiki kamar ba zan rayu ba wani lokaci ba, amman ina rokon yafiyarka kuma ka nema min yafiyar Ataa da yafiyar Momy da duk wani wanda ka san na taba alaka da shi, ka nuna min soyayyar gaskiya Aliyu ta hanyar yi min addu'a bayan raina, Allah ya hada fuskokin mu a aljanna. I love you so much ina maka fatar alheri a sabuwar rayuwar da ka fara da Ataa, na san ka nuna min so, amman ni yanzu tawa ta kare, ka yafe min Aliyu kuma ka yafe wa mahaifiyata so na ne ya saka ta aikata maka komai, ka yi hakuri na san kana so na amman babu wanda ya iya kaucewa mutuwa, tarin dukiya ko lafiya bata amfani mai ita ba matukar mutuwa ta kusance shi, ka yafe min Aliyu_
Fuskarsa shakaf da hawaye ya gama karanta wasikar. Kansa kamar zai bare idonsa ya kumburo kamar ba na shi ba.
“Na yafe miki Rahma na yafe miki, Allah ma ya yafe miki”
Ya furta sannan ya mike tsaye ya shiga bandaki ya wanke fuskarsa ya fito harabar ya memi Abbah, can gefe ya koma da shi ya karbi number Mai Martaba saboda yana son kiran Ataa ya nema ma Rahma yafiyarta. Dakinsa ya dawo sai da ya fara gaisawa da Mai Martaba sannan ya gabatar masa da bukatarsa, sannan ya kashe wayar bayan Mai martaba ya tabbatar masa da za a fada mata, after like thirty minutes aka kira shi da line orange na can nijar wata bakuwar number wacce ba ta Mai Martaba ba.
Yana yin picking ya ji muryar Ataa kasa kasa kamar marar lafiya, sai da suka gaisa ya tambaye ta ko bata jindadi ne ta fada mishi lafiyarta kalau.
“Ya jikin Rahma?”
“Babyna jiki da sauki sosai ta ce a fada miki tana gaishe ki kuma na nema mata lafiyarki, tsabanin da kuka samu a baya”
Aliyu yayi kokari wajen ganin yayi magana da ita normal ba tare da muryarsa ta canja kuma ba tare da nuna akwai damuwa a tare da shi ba, sai dai kana jin muryar kasan baya cikin walwala. A maimakon Ataa ta tace ta yafe mata sai kawai ta fashe da wani kuka da cikin wayar har Aliyu ya kasa saurare ya kara wayar a kirjinsa yana hawaye.
Mutuwa....! 💔
Allah kai mana kyakkyawan karshe, Allah ka jikan Babana da Rahma😭😭😭😭💔
*AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
Kuka na ke sosai jikina na raya min cewar Rahma ta rasu daman tun a lokacin da ya tafi na ke jin ba dadi, yanayin yadda na ji muryarsa ma na san ba lafiya ba, domin alamu ya nuna ba ya cikin walwala duk dai ban san ainahin abunda yake damunsa ba, sai dai jin cewar Rahma na neman yafiyata na san mutuwa ce kadai zata saka ta neman yafiyata, idan kuma ba haka ba, wata kila kuma Aliyun ne ya nema mata da kansa saboda ta mutu.
“Babyna kukan ya isa haka”
“Hamma ba a boyon mutuwa, idan ma ta mutu da gaske ba zan iya dawowa da ita ba, kuka ba ya dawo da wanda aka rasa, da yana dawowa da ya dawo min da Babana da Lukman, amman duka na rasa su kuma kuka da bakinciki be dawo da su ba, zan yi kuka saboda tausayinta ne da kuma kai”
“Bana son kukan ko tunanin ya janyo miki wata matsala, ke kadai kika rage min a yanzu sai abunda yake cikinki, idan na kara wani rashi ban san ya zan yi ba, rashi akwai ciwo sosai gashi ba zaka iya dawowa da wanda ka rasa din ba, akwai ciwo sosai ka rasa wani abun da kake so a lokacin da kake tsananin bukatarsa, akwai ciwo rabuwa da abokin rayuwa da ka shirya yin rayuwa da shi”
Hannu na kai na share hawayen fuskata, na san yadda Hamma yake ji saboda be taba rasa kowa ba a rayuwarsa sai yau, mahaifiyarsa mahaifinsa duka suna raye, wani karin gatan ma sai Allah ya kara masa da Mama Fulani da Abbah duk shi kadai, ni ko na san zafin rashi saboda na rasa mahaifina da dan'uwana kuma na san zafin babu saboda ana tashi a cikin babu din, shi ko be san babu ba sai akwai kuma be san zafin rasa komai ba a rayuwarsa sai yanzu.
“Fada min kina nan lafiya kalau”
“Lafiyata kalau, kuma na yafe mata abunda tai min wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ya jikanta yai mata Rahma”
“Amin na gode, cikinji fa yana lafiya?”
“Komai lafiya kalau, zan fadawa Mama yanzu”
“Okay ki kula min da kanki pls”
Na gyada kai kamar yana gabana sannan na aje wayar akan gadon na zauna bakin gadon ina ta kuka, ban taba tsammanin jin labarin mutuwar Rahma zai sakani shiga damuwa ba balle har nai kuka, amman sai ga ni ina kuka kamar wacce na rayu da ita na tsawon lokaci na shaku da ita, a yau duk wata kiyayya da kishi da jin haushi ta kare, mai rabawa ta raba. Kaico mai rai ba abakin komai yake ba, lokaci daya idan Allah ya so kama ka sai ka raina kanka har makiyinka ya tausaya maka. Sai da na ci kuka na koshi sannan na fito falon Hajiya wato kakana idona a kumbure da kuma sauran hawaye na nufi inda Hajiyar take zaune na mika mata wayarta wacce ta ara min na kira Hamma da ita.
“Lafiya kike ko?”
“Rahma ce ta rasu”
“Wace Rahma?”
“Matar Hamma”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”
Shine abunda ya fito daga bakin Mama tana dafe da kirji, na san ta ji mutuwar kamar yadda na ji, abun kamar daga sama kuma babu dadi ko kadan. A nan suka shiga tambayar wacece ita, Mama ce ta fada musu ni kan sai wani sabon kukan ya kubuce min, har ga Allah ban jidadin mutuwarta ba, dan tsabanin da muka taba samu da ita sai ya dawo min sabo ina ta ganinta a fuskata. A cikin dare aka fadawa Mai Martaba halin da ake ciki na mutuwar Rahma, a waya ya kira Daddyn Rahma yai masa gaisuwa da kuma Abbah da sai aka sadashi da Daddyn Hamma shi ma yai masa gaisuwa sannan yai ma Hamma din, mu kuma aka ce mu shirya domin zuwa gaisuwa, a daren ban yi banchin kirki ba saboda tunanin Rahma ina ta ganin kamar ba da gaske ne ba, sosai na ji mutuwarta kamar wani ginshike nawa na rasa, har na soma jin ciwon kai na kama ni, da safe sai ga ni da mura, tun da nai sallah ban koma ba bachin ba, saboda tunani ashe Allah be yi zamu zauna a guri daya ba, balle ma na ga kishinta domin ni dai bana jin ina da kishin ma amman na san nata na musamman ne a yanayinta da yadda na karanci halinta.
Ko da goma tai dukan mu muna airport, wani abu sai kudi, babu zancen siya mana tickets na zuwa Nigeria, da jirgin Mai Martaba muka tafi, ni, Mama sai kuma wasu cousins dinta mata biyu, maza biyu wadanda Mai Martaba ya turo su walkice shi su yi masa gaisuwar.
Mun sauka sokoto cikin lokaci wani abun burgewa muna sauka motocin da za su dauke mu suka iso, a wani gidan suka so su kai mu mu huta kamin muje gaisuwar sai Mama da kanta ta ce a sauke gidan Momy su kuma Mazan sai su tafi can din su huta, haka kuwa akai ni da ita da wasu yayyunta mata aka sauke mu gurin Momy su kuma mazan aka wuce da su. Mun tarardar gidan da taro sai dai ba taro irin nan farinciki da walwala ba, domin kana kallon fuskarta duk wanda ke gurin kasan ba taron jindadi ne ya tara su ba. A cikin gidan kuma mata yan karbar gaisuwa, ganin taron ya karya min guiwa na san nima wata rana haka za'ayi nawa, ayi na kowa.
Husna da Siyam su kai mana lale marhabun duk da kasancewar suma basa cikin walwala sosai sai dai sun yi murna da ganina suna ta dauki ba kuma murna na marmari na kawai ba har da murnar cikin da na ke da shi. Mama Fulani kan ba wani sakewa sumi sumi da ita kamar ta Allah, Ammy da duka yaranta suna nan, har ma da su Maryam da Rukaiya duka suna nan.
Kar ka so ganin yadda Momy taks ta kokarin dawainiya da ni, sai kace wata mai tsoron ciki ko kuma wacce bata iya komai, abinci ma idan za a kawo min sai an tambayi wanne na ke so gudun kar a kawo min mai saka ni tashin zuciya. A ranar kawunai na da Mama suka koma da kuma cousins din da suka rako Mama, bayan sun yi gaisuwar a can bangarensu Iyayen Rahma, ban za ci Mama zata iya zuwa tai gaisuwar rasuwar Rahma ba, sai gashi ta maida komai ba komai ba, kana kallon mahaifiyarta zaka san a firgice take, irin figirtar nan na