Showing 138001 words to 141000 words out of 225640 words
sai naga ya faka motarsa gefen titi ya kalleni ido cikin ido ya ce.
“Saboda Ina son ki....!”
Waigawa nai na ga ko wata aljana ce a baya da yake gani ba ni ba, sai na ga babu kowa, to ko dai shi ma ya sha wani abun ne kamar Muhseen? Anya ma dai Aliyun ne ko waninsa.
“Ni ce Ataa ce”
Na fada dan na tunatar da shi idan na manya wata kila ya dauka wata ce dabam ba ni ba ko kuma Rahma. Idonsa na raurau ya ce.
“Ki zargi duk abunda za ki zagar Ataa, ki fada min kalamai masu zafi da da ci irin kalaman da kika san za su taba kwakwalwata, ki tsane ni adadin tsanar da kike tunanin na cancanci samu daga gareki, amman karki zabi wani bokin rayuwa bayan ni”
Da gaske kalaman nan daga bakin Aliyu suke fitowa, mutumen da baya kaunar talaka da talauci shi ne ya zaunar da ni gaban motarsa yana fada min irin maganganun nan, sam ban yarda a gaske ne ba wata kila wata gadar zanen yake kulla min idan na aureshi ya rika cin ubana kullum ko kuma wani abun ne dabam, amnan idan ba shi ba taya ma Aliyu zai ce yana so na? Taya ma zai so ni da gaske? Ina da kyau ai wata kila shiyasa na canja ra'ayi ya ji yana so na.“Ban taba jin ina son ki dan wani abu na jikinki ba”
Ya fada yana girgiza min kai, ashe a fili nai maganar ban sani ba.
“Suna nan da yawa wadanda suka fiki kyau da komai a duniya, amman da ke Allah ya jarrabe ni, a tsakanin jiya da shekaranjiya da yau na kasa tantance irin kaunar da na ke miki, da gaske son ki na ke Ataa amman ban sani ba sai da Momy ta dora ni a hanya, sai na gane son ki ne yake ta wahalar da ni ya hana ni sukini, ban taba jin abunda na ke aji a yanzu ba, ban taba jin cewar idan wata ta zabi wani ba ni ba zan iya shiga matsala sai a kanki Ataa, ban taba jin kishin mace ba sai a kanki Ataa, ki yarda da ni ki bani dama na bude miki duniyarki, na maye miki gurbin Abubuwan da kika rasa, zan inganta rayuwarki Ataa zan nuna miki ko wanene Aliyu, ta aurenki ne kawai zan nunawa mahaifiyarki da ke kanki wanene ni, yanzu haka bana son na hada ido da Mahaifiyarki, ki taimaka min Ataa idan Momy ta tambaye ki kira sunana, ko da ba zaki so ni ba ki taimaka min ki aureni, Wallahi ina son ki Ataa... ”
Saurin bude motar nai na fita sam ban yarda Aliyu bane, idan kuma shi din ne to ba kalau yake ba, da kafa na karasa gidan na bar a gurin cikin mota zaune. Gaba daya rikewa nai tunanin ma na rasa ta ina zan fara, sai nuna kai na ke ni kadai ina tambayar kaina.
“Wai ni ni fa”
Nana ma ta lura da hakan har ta tambaye ni abunda yake damuna, ban boye mata komai ba domin a halin da nake ciki a yanzu ina bokatar abokin da zan fadawa damuwata.
“Wanene Kamal?”
Ta tambaye ni domin ban sakoshi a duniyar labarin da na bata ba wacan karon a zamana Abuja. A lokacin da na gama bata kabarinta bata ce min komai ba, bata sake tambaya wani abu ba, har aka kawo mana abincin dare muka ci muka kwanta. Washe gari kamar kullum na tashi da wuri na yi sallah ni da Nana sannan na koma na kwanta ina ta tunanin abunda ya faru jiya sai komai ya zame min kamar mafarki kamar ba gaske ba.“Amman Nana Aliyu fa.... ”
“Aliyu ya aikata kwatankwacin abunda na aikata a lokacin da kaddara ta rubuta min haka, yana da zuciya mai kyau Ataa tunda har iya taimaka mana ke ki samu ilmi kiji dadi rayuwa ni kuma na samu lafiya, be yi kokarin boye abun ya rufe a gidan yan sanda kamar Asim ba, mahaifiyarsa ta kyautata mana kuma ta yi fatan ki samu rayuwar jindadi shiyasa ta nemi ki auri danta, indai har mutum mai daraja mai ji da kai da kudi kamar Aliyu zai yada kansa ya bude ba ki ya roke ki ki so shi to ko ya cancanta ki so shi Ataa, ina jin a rai shi ne mijin da nake miki rokon samu kuma nake miki fatan samu, ba zan cilasta ki ba domin ni kaina cilastawa bata min amfani ba, ina baki shawara ne a matsayi na uwa kamar yadda nawa iyayen suka shawarce ni na ki”
Hawaye na sauko min maganganun Nana na ratsa ni, amman har gobe zuciyata Kamal take kauna.
“Karki kalli abunda Aliyu ya aikata a matsayin cin amana, domin be zalince mu ba, fada Ataa wace ya ce zata gudu ta bar iyayenta kuma ta ce zata ga kyau? Ta yi sammani komai ya zo mata da sauki? Kaddara ce a haka na gode Allah ya abun ya zo min ta nan kawai na gode ma Allah, Ataa ina son tun ina da rai na ki samu mijin da zai aure saboda Allah uwarsa ta dauke ki kamar yarta, domin ni na san mutuwa tana zuwa gobe ko anjima, ina son kamin na tafi na san na barki a cikin jindadi da farinciki, ina tsoron kar amin azaba biyu hakkin biyewa iyayena da kuma hakkin kin zaba miki miji na gari, yarinya ce ke Ataa ba ki san komai a yanzu wanda yake miki dariya yana yaba ki shi kike daukar cewar yana sonki wanda kuma yake nuna miki illar abunda kike shi kike yana kokarin kare miki mutuncin ki shi kike dauka a matsayin makiyinki, wanda kashi saba'in cikin dari na mutanen duniya haka suke, kar duniya ta rude ki kamar yadda ta yi min a lokacin da nake da kurciya, duk wanda zai so ki dan kyauki zai iya gudunki idan kyau na ki ya guje, wanda kuma ya guje ki dan talaucinki zai iya son ki idan arziki ya same ki kuma ya sake guje miki idan talauci ya rabe ki, amman wanda zai so ki dan ya gyara rayuwarki ba dan kyau ki ba, be kuma dubi talaucin da rashin danginki ba ya so shi ya fi cancanta ki so fiye da kowa Ataa, miyasa Muhseen be duka ya roki ki so shi ba? Sai ya nemi tada hankalinki? Miyasa Kamal be biyo ki har nan ya nemi ba, sai ya zabi ya kyale ki yai wata rayuwar, idan kika samu wani anjima ya ba ki abinci da kudi yai miki dariyar fuska shi za ki ce kina so, Ataa ba ki san so ba, wani be taba zowa ya ce a sallamo masa ke ba, bara kawai kike sani mu yi baran na yau da na gobe shi kawai kika sani, yadda za a baki nera ki saffarata ki ci abinci shi kawai kika sani, hakkina ne idan babanki baya raye na baki ilmi na ciyarda na shayar da ke na nema miki magani,amman ban yi ba ban koya miki komai ba sai bara Ataa, da ban gujewa dangina ba da duk haka be faru ba, shin kin samu wanda zai fanshe ni ya baki duk wannan miyasa ba za ki karba ba?”
Da yaren buzanci ta jera min komai a kwakwalwarta ta karasa tana fashewa da kuka.
“Guduwa kika yi Nana?”
“Ba shi da amfani, tun da babu komawa har a bada babu wannan zancen”
Ta fada tana share hawayenta.Ban leka sashen Momy ba sai misali goma har da rabi na safe, a lokacin har mun karya ni da Nana sai dai daga ni har ita ba mu wani ci abincin sosai ba, na yi zaton idan na ce zan je bangaren Momy zata hana ni ne amman bata ce min komai ba har na dauki kayan da muka ci abinci na nufi part din. Amina na samu a kitchen tana kuna gas da alama abincin rana zata dora tun yanzu maimakon Momy. Na gaishe ta cikin mutunci da girmamawa ita ma ta amsa min tana murmushi.
“Ina Momy”
“Sun tafi Abuja”
Sai na ji ba dadi da amsar da ta bani wata kila abunda ya faru ne yasa suka tafi abuja, ita da wa ma suka tafi oho.
“Ita da yaya Aliyu”
Amina ta karasa maganar tana maida hankalinta gurin dora girkin. Juyowa nai na dawo bq ina ta tunanin dalilin tafiyar ta su, sai dai gaskiya na ji ba dadi na rashin dalili, daga tafiyar Momy har Aliyun ma, ina shigowa dakin sai Nana ta jefo min wani zance.
“Mi zai saka ki zabi Kamal? Mutumen da be tana biyowa ya nemi inda kike ba?”
Na zauna kusa da ita ina murza yastun hannuna na ce.
“Yana da kirki sosai Nana kuma yana so na”
“Yana da kirki kamar Muhseen ko kamar Aliyu?”
Na yi shiru ina nazari.
“Muhseen ba shi da kirki Ataa to har zai iya tunkara a matsayina na uwarki ya fada min magana irin wannan ko da ko ya san na sani, irin wannan wata rana zai iya ci miki mutunci a gabana”MUHSEEN POV.
Kamar yadda yai wacan tafiyar hakan yai wannan, domin kuwa yana baro bq ya kama hanyar Abuja cikin bacin rai be taba nadamar yin wani abu kamar yadda yai nadamar zuwa sokoto ba a yau ba, domin ba be so ba da duk wannan be faru ba da be ji wata maganar marar dadi daga Momy ba, balle har yau Ataa ta ce ta tsane shi.
Ya isa Abuja cikin dare kamar wacan karon sai dai yau da 11 ya shiga gidansu tsabanin wacan zuwa da ya dira karfe ukun dare.
Hango wuta a falon Mama Fulani yasa ya nufi can kai tsaye domin labarta mata abunda ya faru har lokacin ya kasa sauke fushinsa. Tura kofar falon yai ya shiga sai ya same ta zaune bakin saman kujera tana kallon tv. Karasa yai kusa da ita yana wani bata rai shi ala dole fushi yake yana kuma son nuna mata damuwar, kusa da ita ya zauna, ganin bata kalleshi ba yasa ya kira sunanta.
“Mama....”
Tana juyowa ta tsinka masa mari mai zafi da bayan hannunta ta mike tsaye a fusace tana kallonsa ta ce.
“Sha sha sha marar tunani sakaraiz ashe Muhseen baka da hankali ban sani ba sai yau? Waya kai ka taba Momy? Wa kake a cikin Familyn mu da zaka fadawa Momy marar dadi wa ke? Da? Da? Dan da zaka iya mutuwa yau gobe na haifi wani? Ka taba kowa ka yi ma kowa amman ban da Momy ban aminta ba, ban aminta ko inuwarta ta kata ba, balle har ka fada mata ba dadi idan ka taba uwar Aliyu uwarka ka taba tashi ka fice min daga falon, daman kai nake jira dan sannan za ka zo, get out....!”
Ta furta a tsawace tana nuna masa kofar fita. Hawaye shar suka wanke fuskar Muhseen tuni yai mutuwar zaune a gurin.
ZAKI
By Khadeeja Candy
41...
Kasa cewa komai Muhseen yai sai kallon Mama Fulani yake hawaye na sauko masa kamar ba shi ba. A fusace ta bar masa gurin ta haye sama dakinta. Ya dade zaune a gurin sannan ya mike tsaye ya nufi part dinsa, keys bude dakin ma daker ya iya sakawa ya bude yana shiga ya zube a falo zaune saman kananan cushion dinsa.
Abunda ya faru ne ya tsaya masa a rai, ta ina ne be kyautawa Momy ba? Miye illar abunda yai? Har ga Allah be ga da inda yake da wata matsala ba, Momy ta nuna masa son kai, kuma maganar da ya fada mata babu laifi a ciki, ta sani sarai yana son Ataa taya zata juyar abun akan Aliyu saboda yana danta? Ya sani be kyautawa Ataa na fada mata maganar kai tsaye a gaban mahaifiyarta ba, sai dai be san cewa mahaifiyarta bata sani ba da be aikata abunda ya aikata har ta furta kalmar tsana a gareshi ba, wannan babin kam ya yarda yayi kuskure amman da wanne zai ji rashin goyon bayan Momy ko kuwa yanke masa hukunci da mari da Mama Fulani tai, ko kuwa auren Ataa da Aliyu zai yi? Anya ma zai iya zai iya kallon Ataa da Aliyu a guri daya bayan shi ya fi cancanta ya zauna da ita? Domin shi ya ce yana son ta kuma yana da tabbacin tana son sa.
A daren be yi bachi ba duk kuwa da irin gajiyar da ke tattare da shi na tafiya mota amman tunani ya hana shi bachi kamar wacan karo, ta ina yake da matsala ina zai samu mafita? Ta ina zai shirya da Ataa? It's necessary ya koma sokoto ko gobe? Asubar fari ya fita daga gidan zuwa masallaci be dawo ba sai takwas da wani abu na safe, kamar zai wuce part dinsa sai kuka ya shigo part din Mama Fulani ita ya samu tana share falon da kanta Maryam da Rukaiya na zaune sai aikin danna waya suke.
“Mama ina kwana?”
Ta yi kamar ba ta ji shi ba sai cigaba tai da aikinta.
“Mama Muhseen na gaisheshe ki”
Maryam ta fada a zatonta bata ji abunda Muhseen yace ba ne.
“Na ji ai”
Ta fada ba tare da ta kalleshi ba. Shi kuma ya mike tsaye cikin rashin jindadi ya fice daga falon.“Gaskiya Mama be kamata ki ga laifin Ya Muhseen ba, har ga Allah Momy be kamata tai supporting Ya Aliyu ta bar Ya Muhseen ba”
Mama Fulani ta dago tana kallon Maryam wacce tai maganar tana nuna ta da tsintsiya.
“Baki san komai a kan rayuwar yara ba, babu ruwanki a ciki duk wanda zai ce kushe min Momy zai yi to zai jawa kansa bakin jini ne kawai, ai Aliyu ya fi cancantar karin aure yanzu fiye da Muhseen ko dan saboda Rahma, sannan Momy mai zaba masu matar aure ne, waya sani ko ta zaba masa wata ne shi Muhseen din ya ce baya so sai ta Aliyu, ai Amina ta fada min mafarin fadan duk akan wata yarinya ne”
“Haka ne kuma, su ma dai ban da abun su miye abun fada kan mace ga mata nan da yawa a gari, dama Ya Aliyu ya bar masa ko wacece ya zo ya auri Rukaiya”
“ai na ga kamar bata masa ne shiyasa ban matsa ba bana son abunda zai jawa Aliyu matsala, kuma namiji kara dai ka jira har kawo maka wacce yake so da wacce kai kake so, kin san dai duk yarinyar da Aliyu zai so classic lady ce, ai ko dan ya ba wa wannan yar iskar Rahma haushi zan zo ya aure ta”
Rukaiya ta yi kunce tana danna wayarta ta ce
“Uhmm ni jikina na ba ni Ataa ce suke wannan rigimar akanta Wallahi, kin san fa tun tana gidan nan suka fara wani zafi zafi akanta”
Mama Fulani ta dan yi shiru kamin ta kalli Rukaiyah.
“Ai ko kowa zai yi ban da Aliyu, ai sam ba zai taba son wannan banlagarar yarinyar ba”
“Mama tana da kyau fa sosai, kuma nan zai iya rudarsu, shi dai Ya Muhseen tun da a nan ai ya furta”
“Ai yau Momyn zata zo za mu idan ita ce din, amman ni nasan Aliyu ba zai taba son irin wannan yarinyar ba”
“Uhm Mama ba ki sani ba kenan, ai Wallahi Ya Aliyu zai iya jin cewar zai gyarata ya zauna da ita”
“Yarinyar da ke bara a titi dan Allah ki bar ma wannan maganar bakinki ya sari danyen kashi amman dai ba akan yayana ba Wallahi”
Mama Fulani ta karasa tana tofarda yawu, a take ranta ya bace domin ko maganar Ataa bata son a mata a yanzu sam ta ma manta da ita a duniyarta.Misalin goma na safe Momy da Aliyu suka sauka Abuja, suna sauka yai ma Nasir waya ya zo da mota ya dauke su zuwa gidan Mama Fulani, a motar ne Nasir yake karantar damuwar Aliyu domim tsakanin jiya zuwa yau har wata rama yai idonsa sun dan fada kana ganinsa kasan akwai damuwa a tare da shi, sai dai fuskarsa na nan a daure kamar ko yaushe. Suna isa gida Aliyu ya fara bude motar ya zai fita sai Nasir ya hana shi ta hanyar ce masa.
“Aliyu ina son mu yi magana da kai”
Jim hakan yasa shi zaunawa a motar Momy kuma ta bude gidan baya ta fita zuwa cikin gidan sai da ta shige sannan Nasir ya kalli Aliyu ya ce.
“Wani abun ne kuma ya sake faruwa?”
“Babu komai Nasir”
“Ga fuskarka nan ta nuna damuwa”
“Ina jin zaman jirgi ne”
“Zaman jirgi daga sokoto zuwa Abuja zai saka cikin damuwa”
“Babu wata damuwa a tare da ni Nasir kai ne kake ganin haka”
Yana fadar hakan ya fice daga motar zuwa cikin gidan, yana jin cewar matsalarsa da Rahma private matsala ne da ba lallai sai aminnsa ya ji irin zaman da suke ba, matsalarsa da Muhseen ma yana jin ta su ce ta cikin gida da wani be kamata ya ji ba, balle kuma na son Ataa daya hana shi walwala wata kila ma idan ya fada masa dariya zai masa.
Ko da ya shiga Momy na falo zaune ita da Mama Fulani ta jera mata fruits domin abincin rana be kai ba kuma bata jin zasu fito ba su karya ba. Kusa da Mama Fulani Aliyu ya zauna yana murmushi karfin hali.
“Mama ba ki fada min maganar Kamfanin nan ba sai a gurin Momy na ji”
“Ai da gangan na ki fada maka, wai ka tashi ta wuce sokoto ta waya ma kake fada min cewar ka wuce sokoto kai mai mata duk inda take kafarka na nan”
Dariya yai ya ahafa kansa yana kallon Maryam da Rukaiya da suka dauko kular farfesu Maryam kuma ta dauko plates da spoons. Maryam ce ta fara gaishe shi kamin Rukaiya ta dora da nata sai ya amsa musu fuska a hade kamar yadda ya saba.“Oh to sai na zuba masa ido yai miki rashin kunya kuma na kyale shi? Dan kin zaba masa mata ma ya isa ya ce ba zai aureta ba balle kuma dan kin zabawa Aliyu ita, yau ba ni burin da ya