Showing 51001 words to 54000 words out of 225640 words
yarda, dan namiji haka yake anjima zai iya ganin wacce tai masa ya canja ra'ayi”
Rahma ta kalli Momy tana ganin ta wulakanta ta ce wai wata rana Ataa zata fi ta, taya ma zata kai kamarta balle har ta fi ta.
“Momy ko dai dan baki san yarinyar ba ne, wata kazama ce marar daraja, taya za ki hada ni da ita? Ni fa matar dan ki ce”
“Da na hada ki da ita na yi sabo kenan? Ya yanzu kika gama fadin cewar haihuwa na Allah ba ne? Shi talaucin da arzikin ba na Allah ba ne? Ke bari na fada miki idan ma baki sani ba, arziki da talauci duka na Allah ne, wani lokacin talaka ma sai ya fika kima da daraja a gurin Allah, ba kwalliya ki ka yi wa Allah yasa aka haiho ki a gidan masu arzikin ba, ita kuma ba wani laifi tai ma Allah yai ta a haka ba”
“Na yi zaton kema kin dauki ni kamar yar ki ne za ki share min hawayena shiyasa na kawo kukana a gurinki”
Ta fada hawaye na sauko mata sannan ta mike tsaye ta dauki veil dinta ta fito Momy na binta da kallo. Haka ta fito hawaye na sauko mata amman bata damu da ta share ba, duk a maganganun da Momy tai mata ta fi jin zafin na haihuwa, taya Momy za tai mata wannan maganar kamar ba ta san Allah ne yake komai ba? Ta sani ita kanta bata da matsala Aliyu ma bashi da matsala so zata iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya so. Amman bayan Mama Fulani a yau ma Momy ta yi mata gorin haihuwa. A maimakon ta koma gida sai ta wuce family house dinsu gurin Mommy ta da Daddy su da take ganin kamar sun fi kowa kaunarta a duniya, domin tana da tabbacin da su ta kaiwa kukanta tun farko da basu mata bakar magana kamar yadda Momy tai mata ba. Daf da kofar shiga falon ta faka motarta sannan ta fita tana hawaye har lokacin ta shiga falon. Mutane ta samu da dama a falon suna ta hidimar canja decorations din Falon ko ba a fada mata ba tasan Mai gidan Daddybsu ne zai zo wato Alhaji Bashiru Muhammdu Sarkin Agades, domin ta san a duk lokacin da zai zo sai Daddy ya saka an yi gyaran gidan, kuma an gyara masa masaukinsa, daman tun gobarar da ta faru be zo ba kuma be aiko kowa ya yi ma Daddy jaje ba, kasancewar Daddy yayi hasarar dukiya mai yawa a Shopping mall din nan daya kone, domin shopping mall din ya yafi ko wane kawo kudi kuma shi ne wanda kudin Daddy zalla a ciki ba da na mai gidansa ba.
Mommy na zaune a falon tana kallon yadda ake saka labulayen Rahma ta shigo yadda ta ga fuskarsa da ganinta a wannan lokacin ta san ba lafiya ba, hakan yasa hankalinta yai mugun tashi har ta kasa hakura ta kawo kusa da ita ta tashi ta tarbeta.
“Ke lafiya?”
“Momy Aliyu wata yake so?”
“Wata yake so, wata wa? Waya fada miki”
A nan ta narke a kasa ta fashe da kuka wanda hakan yasa hankalin Mommy kara tashi ta rikata itama tana fashewa da kuka.
“Rahma ki fada min minene?”
Daker tai shiru har ta iya zanawa Mommy abunda ya faru, sai Mommy rika hannunta suka nufi part din Daddynta, Mommy tai masa bayanin komai a take shi ma ransa ya bace musamman da ya ga yadda yar lelensa take kuka. A take ya daga waya ya kira Aliyu ya ce ya zo ya same shi a gida, ba a dauki thirty minutes ba sai ga Aliyu zaune a falon daddy daman he used to respect his in-laws da kuma iyayensa da matarsa duk abunda ya shafi nan baya wasa da shi.
Daddy ne ya fara kora masa da bayani kamin Mommy ta dora da nata cikin fada.
“Be ma kyautu ace ka fara son wata ba Aliyu, kasan halin da Rahma take ciki idan kace zaka mata kishiya da wanne kake son ta ji?”
Tun da suke maganar yake ta kallonsu har sukai suka gama sannan ya kalli Rahma ya ce.
“Lokacin da zan aureki na fada miki cewar da ke kadai zan zauna? Na miki wannan alkawarin ke kadai za ki zauna?”
Rahma ba tace komai ba sai kuka take, sannan ya kalli Daddy da Mommy ya ce.
“Ciyar da yarku shayarda ita nema mata lafiya abu ne daya rataya a kaina, kuma shi ya kamata ku tuhume ni da shi idan ban mata ba, ba wai zancen karin aure ko kin sa ba, wannan abu ne da ke tsakanin ni da ita, matsala da za mu iya gyarata a tsakaninmu, ku hukunta ni idan na tsallake daya daga cikin abunda musulunci ya ce nai mata na take na ki nai amman ba wannan ba”
“To rashin kunya za ka mana kanan ko?”
Mommy ta fada tana watsa masa wani kallo kamar ba sukurinta ba.
“Babu zancen rashin kunya a ciki Mommy, Rahma ta yi ba daidai ba kamata yai ku fada mana ku nuna mata abunda tai ba daidai ba ne, ba wai ku kirani ku tsare kamar haka ba”
Daddyn kan mamaki da kataici ya hana shi cewar komai sai wani kallo yake watsawa Aliyu ta cikin gilashin idonsa, ya manta da cewar Aliyu mai arziki ne dan mai arziki dan gin amsu arziki, da dai ace talaka ne yake auren yarsu da za su iya juya shi yadda suke so amman ba mai arzikin da baya jiran abun hannunsu kamar Aliyu ba. Jin babu wanda ya sake cewa komai yasa shi kallon Daddy ya ce.
“Akwai wata matsalar ne bayan wannan?”
“Lallai Aliyu wuyanka yai kauri wato ita wannan ba matsala ba ce ko?”
Daddy ya fada, Aliyu dai be ce komai ba sai kallon Rahma yake da idon da ke nuna ya fusata sosai.
“Daddy ka bar shi kawai zan yi magana da shi”
Rahma ta fada tana dagowa daga jikin Mommy ta dake kokarin riketa.
“Babu inda za ki bishi yaje yai ta cusa miki bakinciki a zuciyata ya akashe mana ke da ranki”
“Aa Mommy zan yi magana da shi, daman ban yi magana da shi ba ne na fada muku, idan abun ya gagara zan...”
Sai kuma tai shiru bata karasa ba, tana tsoron kar ran iyayenta ya bace su hanata komawa gidan sahibinta ko wata matsalar wacce ta fi wannan ta shiga.
“Sai da safen ku”
Aliyu ya fada yana mikewa tsaye ya fice daga falon, da sauri Rahma ta bi bayansa wanda hakan yasa ran Mommy baci son tai ta riketa a gidan har sai Aliyu ya gane kurensa. A tare suka iso gurin motarsa Rahma na ta kallon fuskarsa ko zai kalleta amman be kalleta har ya bude motarsa ya shiga ya danna horn aka bude masa gate ya fice ya barta a gurin tsaye. Da sauri itama ta shiga motarta ta bishi ko da ta isa gidan ta samu har ya shiga dakinsa yana kokarin cire tufafin jikinsa. Jikinta a sanyaye ta shiga dakin tana ta kallonsa amman ko inda take be kalla ba, har ya cire tufafin ya daura tawul ya shiga yai wanka ya fito tana a gurin zaune, so take ta masa magana kuma bata san mi zata ce masa ba, har ta gaji da zaman ta tashi ta koma dakinta ta shiga bathroom tai alwala ta gabatar da sallah isha'i, bayan ta gama ta hau saman gadon ta zauna, ta san ba zai shigo dakinta ba tun da yana fushi da ita, kuma idan taje can ba kula zai yi ba. A saman gadon tai ta juyi bachi ya ki daukarta, sauka tai daga saman gadon ta nufi dakinsa tana hawaye ta tura kofar ta shiga sai ta hango shi saman gado kwance. Bayansa ta kwanta ya kai hannu ta taba kansa.
“Dan Allah ka yi hakuri ba zan sake ba”
Shiru be ce mata komai ba, ta sake fada be ce komai ba ko matsawa be yi ba sai da kwanta bayansa tana kuka, sannan ya tashi zaune ita ta tashi zaune tana kallonsa.
“Matsalar da ke tsakaninmu wacce za mu iya solving sai ace sai kin dauka kin kai gidanku? Idan ma zan kara aurene kina tunanin yin haka zai saka na fasa? Duk abubuwan da nake miki Rahma saboda ina son ki ne, kuma ina taka tsantsan da lafiyarki ne, ba wai dan ki juyani kamar dan ki ba”
“I'm sorry”
Ta fada da muryar kuka tana kama hannunsa, a sannan ya jimke hannunsa cikin nata alamar ya hakura kenan ya kai bakinsa ya sumbanci goshinta.
“Wannan ya zama first and last, dan ba zan dauka ba”
“Ba zan sake ba”
Ta fada tana ta kallonsa, sai ya jata jikinsa ya rumgume suka kwanta tare. After like one hour ta dan dago kanta tana kallonsa ta ce.
“Aliyu kana son haihuwa ko? Kana son yara right”
“Yes”
“Amman baka taba nuna min ba”
“Saboda karki damu ne, kuma ga lalurar da kike fama da ita shiyasa ban damu da ki samu cikin ba”
Hannu ta kai ta shafa fuskarsa.
“Zan samu ciki zan saka ka farinciki In-Sha-Allah, zan haihuwa duk inda haihuwa ta kai sai na samo ta, zan kashe ko nawa ne na haihu Aliyu just for you”
Murmushi yai ya sake sumbantarta.
“Allah ya bamu mai albarka”
“Amin”
Ta fada tana kara kankameshi.
“Amman ina son mu koma Abuja, hankali zai fi kwanciya idan muna can”
“Yaushe kike son mu koma?”
“Jibi”
“To ki fara shiri daga yanzu”
“Thank you, i love you”
“I love you too”
Lumshe ido tana sauraren sakwannin da yake aika mata masu zafi.
ATAA POV.
A lokacin da na shiga Bathroom din sai da nai fitsari a bandaki sannan na wanke shi, na fito na gyara bedroom din na fesa turare kamar yadda aka fada min, haka na bi duka dakunan na gyara ko wannen sannan na sauko da kayan mopping din na nufi inda na daukosu na aje.
“Ke je ki cire Hijab din nan karna sake ganinki da shi sai idan fita za ayi, a cikin gidan ki yi ta saka mana Hijab kina watsa mana kora”
Mama Fulani ta fada tana kallon cike da kyama daga can saman dinning da take zaune ita da yaranta suna karyawa, ba musu na nufi garejin na cire hijab dina na saka dankwali a kaina wanda hakan ya bayyana gashin kaina da na yi masa tsoro daya ya sauko har gurin mazaunaina. Da na tashi ban dawo part din Mama Fulani ba sai na wuce part din Ammy da alama ita ce da girkin tsakanin jiya da yau, domin ban same ta a falonta ba sai Anty Zee tace min Ammy tana part din Abbah amman ga abincin nan ta aje min, farfesun kaza ne a wani karamin plate sai wainar kwai da dankwalin turawa a plate daya da kuma katon burodi, da tea a wani babban kofi, duka an hade su a tray daya. Daukar tray nai zan fita sai Anty Batulu da ke murzawa fuskarta wani farin mai mai kamar sabulu ta ce.
“Ina za ki je?”
“Waje zan je na zauna na ci?”
“Zauna a nan ki ci?”
“Ammy ba zatai fada ba idan na ci a nan? ”
Sai duk suka saka min dariya.
“Hala Mama Fulani ta miki fada da kika zauna a falonta?”
Anty Zee ta tambaya sai nai kasa da kaina ban ce komai ba.
“Ammy ba ruwanta, idan ma muka saba sai ta fi son ki da mu,ba kamar wacan bakar matar ta ke ba”
Anty Zee ta fada sai Anty Batulu ta kalleta.
“Anty Zainab Ammy ta ce ki daina cewa haka”
“Ke na fada tashi kije ki Fadawa Ammy ki ce na ce Mama Fulani mai bakin hali, munafuka kawai”
Tana fadar hakan ta tashi ta nufi upstairs tana jan tsaki. jin hakan yasa na zauna a kasa na soma cin abincin hankalina a kwance har na ci na koshi, rabon da na ci abinci da naman kazan tun asibiti lokacin da Doc yake siya mana na restaurant, duk sai na ji babu dadi ina ma ace Nana na kusa da ni da na bata naman ta ci, sam bana son na ci wani abu mai dadi ba tare da Nana ba, hakan yasa na yanke shawara na shanya naman idan ya bushe sai na tarawa Nana idan naje sai na sake dafa mata shi ta ci.
“Anty Batulu zan iya shayawa idan na koshi”
“Eh to sai idan Garden za ki shanya shi, inda kowa ba zai gani ba”
Tana bani amsar na tashi tare da ragowar naman na koma gareji na dauko wani dankwalina na nufi garden din na shimfida daga inda rana take haskawa na baza naman sannan na dawo part din na gyara ko'ina kamar yadda nai a part din Mama Fulani. Bayan na gama gyaran Ammy ta shigo part din jin kamshi na tashi yasa ta murmushi tana ta yaba min.
“Kai haka na ke son yarinya da kuzari kazar kazar da ke, ai to za mu shirya kuwa idan kina son aiki ba kamar yaran gidan nan ba, manya da su amman sai dai a gyara suna zaune”
“Ai daman Anty Zainab ta fada cewar nan da kwana biyu sai kin fi son ta da mu”
Anty Batulu ta fada tana dariya, ni ma nai murmushi sai Ammy ta nufi upstairs tana fadin.
“Eh mana to me ake da mu”
Bata dauki lokaci ba ta fito rike da tufafi kusan kala biyar ta miko min.
“Ungo idan kin yi wanka sai ki canja naga jikinki sun dan tsufa”
Cikin wata irin murna da jindadi na saka hannu biyu na karbi tufafin ina godiya.
“Allah ya saka da alheri na gode sosai”
“Ba komai”
Cike da jindadi na nufi garejin dan ajewa, kasa hakuri nai har sai na yi wanka na saka sai na soma gwadawa ina ta jujjuyawa rabon da wani yai min kyautar tufafi har na manta, kana ganinsu ka san masu tsada ne, na san ba zai wuce na Inteesar ba, domin ita ce kamar ni ganin yadda tufafin suka min cif kamar daman can nawa ne. Sam na manta da zancen gyarawa Ya Muhseen part dinsa har sai da na koma Part din Mama Fulani sai ta rufe ni da fada tana ta zagina kamar wacce bata san inda na fito ba.
“Gidan uban wa kika je kika zauna? Ba na ce ki je ki gyarawa Muhseen part dinsa ba? Shine dan kin maida ni shashasha kika tafiyarki ko? Zo nan”
A tsawa ce take min fada kamin ta ce na zo, ni kuma duk tsoro ya kamani jikina nata rawa kamar nazari idona har ya fara hawaye, domin na fahimcin kiran da take min dukana za tai.
“Aa ni nace ta bari sai gobe”
Ya Muhseen ya fada yana kashe min ido daya, kasancewar duka yan 'uwansa basa nan daga ita sai shi ne a dinning din.
“Ko?”
Sai na gyada kai.
“Eh haka ne, shi yace na bari sai gobe”
“Yaushe ka ce mata haka?”
“Dazu, dauki ga abincin ki can”
Ya karasa yana nuna min kasa kusa da Mama Fulani. Sai na kasa zuwa na dauka ina ta jin tsoro shi kanshi ya lura da hakan.
“Mama gaskiya tsoron ki take”
“Tsorona dodo ce ni?”
Ta daka min tsawa. Sai na amsa mata da sauri ina girgiza kai.
“Aa”
Ya Muhseen ya tashi ya nufi inda abincin yake ya dauko ya miko min yana dariya tare da fadin.
“Ko ni da kika haifa a tsoronki na ke balle kuma ita”
“Aa ni ban haife ka ba, dana ya can sokoto Aliyu dan albarka”
Mama Fulani ta fada tana mikewa tsaye daga dinning din. Sai Ya Muhseen ya saka dariya
“Kowa ya ganshi ai yaga danki halinku daya Mama, har ya fiki rashin tausayi”
“Kanka ake ji”
Ta fada tana tabe baki sannan ta nufi kitchen, shi kuma ya miko min abinci ina karba tana fitowa daga kitchen din tana fadin
“Idan kin ci abinci ki aje wannan plate din da cup din a gurinki, da shi za a rika saka miki abinci”
“To”
Sannan na juya na fita, tea a cup din sai wainar kwai da dankalin turawa a plate din da burado kadan, ban ci komai ba kasancewar na riga na ci na bangaren Ammy na koshi, sai kawai na aje a garejin na kwanta a saman tabarma ina ta tunanin Nana, ko a wane hali take yanzu oho, gashi ba ni da waya balle na kira ta ji muryarta.
After like one hour har bachi ya fara daukata na ji an taba garajen ina dagowa sai na ga Ya Muhseen cikin shiga ta kananan kaya ya dora rigar likitoci a sama, kayan sun karbe shi sosai ga fuskarsa da far'a yana aiko min da murmushi, ni ma murmushin nai masa kadan na tashi zaune.
“Zo ki bude min gate”
“Ba akwai mai gadi ba?”
“Ke nake son ki bude min”
Na tashi kamar yadda ya bukata ina gyara daurin dankwalina na fito daga garejin na nufi gate din, sai da na wuce gate biyu sannan na iso a babban gate din nai ma mai gadin magana ya nuna min yadda ake budewa na bude sannan na hango shi ya taso motar ya nufo inda nake tsaye da gudu kamar mai shirin kade ni, ni ko na ratse gefe na rufe ido ina jiran ya kade ni sai kawai na ji ya saka min ya jefeni da chocolate. Murmushi nai na duka na dauki chocolate din ina kallonsa.
“Sarkin tsoro, daman saboda na gwadaki nai kuma na ga gashin nan na ki”
Ya fada sannan yai gaba abunsa, ni da mai gadin muka bi shi da kallon mamaki, ni dai ina jin son barkwancinsa da yadda yake da son wasa da ni. Mai gadin ya riko dayan gate din ni kuma na riko dayan za mu rufe na ji an ce.
“Ke”
Juyowa nai sai na hango wani fari saraurayi tsaye jikin wani katon gate da ke facing din na su Mama Fulani yana sanye da uniform din sojoji. Ba musu na saki gate din na nufi inda yake tsaye cikin mugun tsoro domin Allah ya zuba min tsoron soja fiye da dan sanda.
“Ina wuni”
“Ina kwana dai”
Ya gyara min yana murmushi.
“A can gidan kike?”
“Eh"
“Gurin wa kika so?”
“Aiki na ke a gidan”
“Aiki?”
Ya maimaita, yana kallona kasa da sama.
“Wa