Showing 201001 words to 204000 words out of 225640 words

Chapter 68 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*
*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
Daker Mama ta tsagaita kukan da take, har suka samu damar magana da juna.

“Babu wanda ya fada min za ki dawo, na yanke kauna daga ganinki na dauka kin mutuwa gaba daya, ko kuma kin tafi kin tafi kenan ba zan sake saka ki a idona ba”

Mahaifiyarta ta fada tana hawaye, Mama kan kasa magana tai sai hawaye take, wani da na ke kyautata zaton Yayan Mama ne ya ce.

“Dukan mu mun san da maganar kawai dai mun boye miki ne saboda Mai Martaba ya bukaci haka, mun san idan har kika sani za ki damu kanki sai kin ganta kuma ki katsa natsuwa”

Hannun Mama kawai take murjawa tana hawaye da motsa baki irin wadanda kuka yake cinsu.

“Nana Asma'u tana can ta kafa wata sabuwar rayuwar har ta yi ya ta aurar da yarta ba tare da sanin kowa ba, wata kila da Mai Martaba be ganta ba, da ba zata dawo garemu ba”

“Ina jin kunyar abunda na aikata, ina jin cewar ban yi daidai ba, shiyasa ba zan iya dawowa ko tunkarar kowa ba”

Mama ta fada sai Mahaifiyarta wacce zan iya kira da kakata ta daga kanta tana kallon inda na ke har tana girgiza kai alamar mamaki da takaici abunda aka fada mata a yanzu. Ba mutanen gidan kadai ba, har da wadanda na ke ganin kamar daga wata unguwar suke shigo duk wanda ya shigo ya ga Mama sai ya fashe da kuka kuma yai mamaki, hakan na nuna cewar an dade da shafe tahirinta a cikin gidan ne, wanda ya santa ya san wanda kuma be santa ba sai dai a bashi labari wata kila ma wanim ba za a fada masa cewar masatautar na da wata Gimbiya mace daya ba, sai abun bakinciki a alakanta Gimbiyar da guduwa saboda soyayyah. Mun yi awa biyu a gurin sannan aka kai mu masauki, na yi zaton dabam za bara mu sai gashi an sauke mu daya daya  a wani bangare na gidan ni da Aliyu.
  Sallah ce ta zame nana wajibi sai da muka sauke nauyinta sannan na fara shiga a bandakin da aka tanadar masa komai kamar an san da zuwanmu.

“Babyna”

“Na'am”

Na amsa daga can cikin bandaki sai kuma na leko domin na riga da na cire tufafin jikina, tawul ya miko min ban san da yayi gurinsa ba sai yanzu, karba nai ya turo kofar sannan na fara kunna ruwan, ban wani dade ina wa kam ba na fito, ko da na fito Aliyu ya hada min tea a cikin kayan tea da aka kawo mana da kuma abinci.

“Ki fara shan wannan kamin ki ci komai kar cikinki ya kumbure”

Sai da na zauna a bakin gadon da yake zaune sannan na mika hannu biyu zan karba, sai da ya shafi hannayen nawa kamin ya sakar min cup din ya nufi bathroom. Sai da na saka doguwar riga na gama shirya kaina sannan ha fito daga wankan.

“I can't wait na ganki da cinin cikin nan, abun yana burgeni fa”

Ya fada yana gyara daurin tawul din dake kogunsa, ni dai ban ce komai ba domin tuni kunya ya sauko min, ni wani lokacin har mamakin yadda Aliyu yake fadin wadansu maganganu nake ko aikata wani abun ba tareda kunya ba.

“Sauka kasa ki ci abinci”

“Kai ba zaka ci ba?”

“Zan ci mana, kin san dai ke a jirgi ba ki ci komai ba yunwa tana tare da ke, idan kuma ba kya bukatar wannan kalar abincin sai a siyo miki wani”

Na saka masa dariya jin irin karfin halin da yake da shi.

“Ka san garin ne da za ka siyo min wani?”

“Dole sai an san gari ake yawo? Ga waya kuma zan iya bin hanya ina kallon abubuwa ina karantawa har na isa, ko kuma nai ta tambaya har na dace”

“Idan kuma ka bace fa?”

“Sai Mai Martaba ya saka cigiyata, surikin masarauta ya bata kuma ga jikarsu da ciki”

Ya fada kamar ba shi yai maganar ba. Nikan dariya ce aikina har ya saka tufafinsa ya zauna kusa da ni, a tare muka ci abincin ba laifi ina sha'awar abunda aka kawo mana kuma na ci sosai, kamin a bugo kofar dakin wai na fito ana son ganina. A yadda yanayin Aliyu da fuskarsa suka nuna kamar be jidadin kiran nawa ba, domin a ganinsa mun yi tafiya mai nisa haka kamata yai ace mun huta musamman ni da yasan ina da cikin na san wannan baya rasa nasaba da abunda ya saka yake kin bari na nai wata tafiyar ni kadai. Ni na fara fita na gaisa da wasu da aka fada min cewar iyayena da kuma kawunnai na sannan aka saka na dawo na kira Aliyu shi ma suka gaisa da shi. Bayan sun wuce shi ya koma dakin da aka sauke mu ni kuma na bi wata buduwar gidan na ce ta kaini dakin da Mama take. Ban same ta a falon ba sai wasu yan mata da suka fara bachi akan kujerar, har cikin dakin Hajiyar aka kai ni a nan na samu Mama zaune mahaifiyarta kuma a tsaye tana rike da wata sandar karfe wacce na ke kyautata zaton tana taimaka mata ne a tsayin ko tafiya. Ina shigowa sai suka maida kallonsu gurina dukansu kana ganin su ka san suna cikin damuwa ba kuma damuwa ta bakinciki ko zullumi ba ta nadamar abunda ya faru da kuma ganin junansu ta inda ba su yi tsammani ba.

“Ace wai ki gina wata rayuwar a can har ko aurar da ya ba ki nemi familynki ba”

Mahaifiyarta ta fada tana kallona har na zauna kusa da Mama.

“Auren ya do mana ta inda ni da ita ba mu yi tsammani ba, kuma ko da ace an dauki lokaci kamin auren bana jin cewar zan ka kawo mijinta ko ita ta ganmu saboda na san abunda na aikata”

“Wa ake aikatawa laifi be yafe ba? Allah ma muka masaba daidai ba yafe mana balle mu? Na san kin aikata kuskure amman Mai Martaba ma bayan tafiyarki ya ji cewar be aikata daidai ba ta hanyar nuna cewar zai aura miki wanda ba ki so, shi kan shi abun ya dame shi domin da be yi hakan ba da duka komai be faru ba, da yanzu wannan ciwon zuciya da na ke fama da shi na ki be same ni ba, da yanzu kina nan cikin yan'uwanki ana yin komai da ke, a duk lokacin da kowa ya taru sai na ji kamar ace kema kina nan, idan jikoki suka taru sai na tambayi kaina ko ina nake suke wane hali kike a yanzu, a mace ko raye ko kuma a cikin wata mummunar rayuwa”

“Ba laifi ba ne dan uba ya zabawa yarsa ko dansa abokin rayuwa na gari, Mai Martaba ba aikata laifi ba, kuma be yi hakan dan ya jefa rayuwata a matsala ko damuwa ba, yayi hakan ne saboda al'adar gidan nan ce, ni kuma sai na bijire na gudu na bar muku abun kunya da magana a gari, soyayya da kurciya a wacan lokaci ta debi da yawa har na kasa gane cewar abunda na ke kokarin aikatawa babban abu ne kuma be dace na aikata hakan ba, a lokacin dana farga daga abunda na aikata kuma sai na ga lokaci ya kure min ba zan iya gyara komai ba, amman na gode Allah daya ba ni ikon neman yafiyarku a lokacin da na ke da rai kuma kuke raye, Wallahi ba zan iya kwatanta irin farincikin da jindadin da na ke ciki ba a tsakanin lokacin da nai arba da mai martaba da kuma ganin ki a yau”

Mama ta fada tana hawaye. Sun dade suna tataunar magana tun tana a tsaye har ta kai g zaunawa, tana sako labarin Babana wai ai ga fuskarsa nan a fuskata, a lokacin da Mama ta bata labarin cewar tana da wani dan bayan ni wanda ya rasu sai da Kakar tawa tai kuka, sai dai Mama bata sako mata labarin ciwon kodarta ba a cikin labarin da ta bata. Ban bar dakin sai da na fara jin bachi kusan ma a cinyar Mama na fara shi sai da ta tashi ta ce na koma wai na baro mijina can shi kadai. Sannan na tashi idona da kufan bachi na dawo inda aka sauke mu kamin na iso har na gaji domin akwai tazara sosai a tsakanin bangaren matan sarki da kuma inda aka sauke mu. Ban yi mamakin samun Aliyu a farke ba, daman ban kawowa raina cewar zai iya kwantawa ba tare da ya gan ni na dawo ya tabbatar ni na fara yin bachin ba, hakan kuma ba karamin dadi yake min ba. Na yi zaton ko zai yi magana ya ce yaje na zauna na barshi a gurin, sai na ji shiru be ce komai ba kamar ma hankalinsa yana wani gurin. Bandakin na shiga nai fitsari na fito ina hamma har da hawayen bachi na cika min ido na ce.

“Baka kwanta ba?”

“Ba zan iya bachi ba sai na tabbatar ke kika fara yi”

Hawa saman gadon nai ba tare da na ce da shi komai ba.

“Ba za ki canja tufafin jikinki ba?”

“Bachi na ke ji sosai”

“Na canja miki?”

“A a ka bar su hakan nan”

Tashi yai yaje ya rufe kofar falon sanna ya dawo ya tura ta dakin sai kuma ya kashe wutar ya bata bayana ya rumgume hannunsa a kan ruwan cikina.

“Babyna gobe zan koma”

Ya fada min kamar mai rada bakinsa daidai kunne na.

“Miyasa baka son zaman nan ne?”

“Ina son na ga yan'uwanki su san ni na sansu, amman tafiyar ta dole ce”

“Miya faru?”

“Rahma bata da lafiya, ina bukatar na je na dubata”

A take bachin da nake ji ya wartsake wani abun na ji ya soke ni a cikin zuciyata wanda ban taba jin irinsa ba.

“Ko kadai kana neman wani uzurin ne daman?”

“Ko kusa, tafiyar ta zame min dole ne tun da ciwo ne ke damunta, ya kamata na je na dubata”

Shiru nai ban ce masa komai ba, sai dai ban jidadin ko sunanta daya ambata ba balle kuma zancen dubata, wata kila shi ya kitsa haka saboda na bishi mu koma ni kuma bana jin zan yi haka, ko kuma yayi hakan ne domin ya koma wata kila kuma ita ce ta tsara hakan saboda ta samu damar da zai dawo ya baro nan ko kuma ta hargitsa mana tafiya ko wani abun da dabam da ban san ma'anarsa ba. Ni kan har na manta da yana wata mata wai Rahma ashe fa Aliyun ta ne nake aure, ko tana ina ma iho ban sani ba, kuma ban ji zan iya tambayarsa ba domin bana son ji wani abun daya shafi sunanta ma balle kuma ita din da kanta.

“Ki min alkawarin kula da kan ki pls”

Ya fada yana sumbatar saman kaina, sannan ya juyo da ni ya shiga aikawa ko wane bangare na jikina da sako. Mun farka da wuri sakamakon kiran sallah asuba da ya tashe mu wanda ake yi aciki masarautar, sai da ko wannen mu yai wanka sannan mukai alwala shi ya fita zuwa inda yake jin karar loudspeaker masallacin na fito ni kuma nai tawa sallah a cikin dakin, ina ta tunani ta inda ya ji cewar Rahama bata da lafiya bayan ma layin Nigeria ba yayi a wata kasar kamar yadda ya fada min, kwata kwata zancen tafiyar nan be min dadi ba, wata kila saboda na saba da shi ne ko kuma saboda Rahma zai je gani yasa na ke jin ba dadi oho ba dai zan iya fadar dalili ba.
  Bayan an gama sallah da kamar minti talatin sannan ya shigo inda na ke.

“Good Morning”

Ya gaishe ni tun kamin na mika masa tawa gaisuwar, nikan kasa amsawa nai sai kawai na gaishe shi da halshen hausa sai ya amsa min yana kissing goshina.

“Lafiya kalau, kin tashi lafiya?”

“Lafiya kalau”

Hannunsa ya miko ya kama nawa.

“Ta so mu kwanta ina son kiji dumi jikina kamin anjima”

“Da rana zaka tafi?”

“Ban sani sai an bincika min idan akwai jirgi”

“Wa zai bincika maka? Taya ina ma ka ji bata da lafiya?”

“Na kira wayarta ne, sai Yayarta ta dauka ta fada min”

“Amman ka ce layin Nigeria ba yayi a wata kasar”

“Yeah ban da Airtel na can yana yi a nan, har daga saudiya ma ina kira da Airtel, na saka Nasir ya bincika min, ke kuma yanzu ina son ki fada musu zancen tafiyar idan mun shiga gaishe su”

Na gyada masa kai kawai ba tare da na ce komai ba. Kamar yadda ya fada na ji dumi jikinsa sosai ta a kuma wanin abun mukai ba bayan dogon bachin safe normal sleep, sai dai yadda ya shigar da ni jikinsa ya rumgume ya saka na jidadi kuma na ji dumi da yake fada.

Misalin tara aka kawo mana abincin karyawa tun daga kan shigar masu kawo abinci za ka tabbatar da cewar bayin gidan ne, domin sukansu suna sanye ne da tufafi kala daya sun jero kamar tururuwa. Duk yadda ya so na ci abinci sosai sai na kasa, sakamakon dadin da raina baya min kan tafiyar da zai yi.
Sai dai na yi kokarin boyewa domin ni ma ban ga abun damuwar akan zai tafi gurin matarsa ba. Daya daga cikin yan matan gidan aka aiko wai na shirya na fito ni da mijina za mu je mu gaishe da Mai martaba da matan gida. Ni ce kawai nai wanka na shirya shi Kan Aliyu tun kamin mu fara karyawar yai wanka ya shirya.
  Rana ta fito sosai ko da muka shiga bangaren Mai Martaba tare da mai mana iso, na yi zaton wani gurin dabam za a kai mu inda Mai Martabar yake kebe sai ga mu a fadarsa ta jiya duka iyalansa da hakimansa suna ciki ban da shi. Muna shiga sai idon kowa ya dawo kan mu

“Zo nan ki zauna”

Wani Dattijo ya fada yana nuna min inda zan zauna din a kusa da shi. Ni da Aliyu muka zauna a kasa sai ya fara nuna waenda zan gaida sune iyayena da kuma abokiyar zaman kakata, da kuma sauran da suke yan'uwana  wasu dai ban ga fuskokinsu a jiya ba, sai yau ina kyautata zaton zuwa su kai a yau, sai haba haba suke da ni da kuma Mama. Duka zuri'ar Sarkin farare tas wasu ma har sun fini fari da jar fata, ga kyau kamar larabawa daga mayan har yara da matashi farare ne, sai dai wani ya fi wani farin, a cikin hakimansa kuma akwai fafaren da bakeke, matanyen na sanye da shadda ga wani uban ginari a hannu da wuya ko wacce ta saka gwanin sha'awa.
A lokacin da sarkin ya shigo sai da kowa ya mike tsaye masu kirari ta bude rigunansu suna tare masa gaba da baya suka fara wasu kuma na fita da katon mafecinsu. Yadda ake ma sarkin sai da abun ya burgeni kuma ya kara min jindadi. Sai daya zauna sannan kowa ya zauna, da dai daya masu rawanin suka fara zuwa suna mika masa gaisuwa baya amsawa sai dai badawansa su amsa a madadinsa har suka gama gaisuwar.
  Sai da yao gyaran murya sannan yai dan jawabi akan dawowa Mama da kuma zancen yafiyar da yai mata, sannan ya sallami wadanda ba familynsa ba ya bar iyalan gidansa kawai ya sake gabatar musu da jawabi tare da nasiha da kuma jan kunne akan al'amurran rayuwa, fada musu abubuwan da ya samu Mama na bijire musu da tai a ciki har da zancen cire mata koda wanda kowa be san da maganar sai a yau. Babu wanda be girgiza ba da jin lamarin kuma aka tausayawa Mama, duk na san ba za a rasa wadanda a zuciyarsu za su ce Allah ya kara ba domin ita ta jawa kanta. Hankalin kakarmu ya tashi sosai jin cewar an cirewa Mama koda sai dai Mai Martaba ya shaida mata ya jaddada mata kuma ya tabbatar mata da cewar za a kwato mata hakkinta domin tuni elya mika abun ga kungiyar likitocin kasar, ko zuwan nan da zai yi sai da ya roke su akan su daga mana kafa ta samu zuwa ganin danginta kamin su gama tattara bayanai.
   Yayi takaici kuma ya nuna bakincikin akan abunda ya faru da kuma gina mana rayuwa da tai ba tare da yan'uwanta ba. Sai dai abun jindadi kuma mai muhimmanci dawowarta a yanzu wanda hakan zai ba ni damar sanin yan'uwanta da kuma yan'uwan mahaifina kamar yadda sarkin ya fada.
  Bayan ya gama jawabinsa ne aka sallami kowa, ni kuma sai na raba kusa da Mama na fada mata cewar Aliyu yana son na koma yau saboda Rahma bata da lafiya, ita kuma ta fadawa yayanta yayanta kuma ya samu Mai Martaba ya fada masa a take, Mai Martaba ya sa a bincika masa idan za'a samu jirgi da a yau, aka tabbatar masa da babu sai dai gobe, saboda haka dole Aliyu ya aje tafiyar har gobe.
  A ranar aka kai ni gurin kakannina na bangaren uba, ganin cewar Aliyu zai tafi ba masanar ko ya dawo yanzu ko kuma sai nan da kwana biyu ko wani lokacin, su kansu ba za su jidadi ace ya tafi ba tare da sun ganshi ba, kuma za su iya daukar cewar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login