Showing 171001 words to 174000 words out of 225640 words
daukar kiran da ba tai ba, wata kila ma hakuri zai bata kuma ya roki ta dawo dakinta ko kuma ya bukaci ta bashi dama ya zo ya tafi da ita, ta san irin rayuwar da suke da kuma yadda Aliyu yake da kyama da kin kula mata ba zai iya raba zuciyarsa da jikinsa wa mace biyu ba, mace ma kazama yar bara kuma yar aikin gidansa kamar Ataa.
“Hahaha yarinyar za ki ci ubanki ba dai mijina kika aura ba? Kina yar talakanki kika jawa kanki wahala Wallahi sai kin yi kuka da idonki kuma kin gwammace ba a taba halittarki duniya ba”
Ta fada yana shiga dakinta na da wanda ya kasance mallakin Muneera a yanzu, ita da Muneera suke sharing a yanzu.
Gaban madubi ta zauna tana kallon kanta a madubi ta mika hannu ta dauki wayarta ta kira Aliyu, ringing biyu a na uku ya daga sai yai shiru yana jiran tai magana kamar yadda ya saba idan dai kai ka kirashi ba shi ya kiraka ba ko da ma shi ya kiraka idan uzurin naka ne kyalewa zai yi sai ka yi magana da kanka.
“Aliyu”
Ta fada a shagwabe tana tana wani cream dake gaban madubi.
“Ka kira ni jiya”
“Lafiyarki zan tambaya”
“Ka damu da ni kenan? Amman ka auro wata”
“Wata aba kanki take ba, ke ma kuma ba akanta kike ba, idan kina da wata maganar ki fada”
Kasa cewa tai ya zo ya je da ita ko kuma yai hakuri tana son har sai shi da kansa ya bata hakuri ko kuma ya roketa ta dawo da kanta idan ma ba zai iya zuwa din ba.
“Dear kina bukatar wani abun ne?”
“Aliyu ba zaka ba ni hakuri ba? Na zaka ce komai a auren da kai ba?”
“Ina nufin kina bukatar wani abun kamar na ci ko na sha ko wani abun daya shafi lafiyarki?”
Ta ji haushi a take ta kashe wayarta tana buga kafa kasa, ta san halin mijinta da jin kai ai, ba zai bata hakuri ba tun da yana ganin shi ne da gaskiya, amman zata jira har nan da sati daya ko biyu idan ya be ce ta zo ba ko be biyota ba zata share shi, balle ma tasan yana yin hakan ne kawai dan ya bata haushi kamar yadda yake mata idan yana fushi da ita a gida, ta san Aliyu can't live without her shiyasa ya turo mahaifiyarsa ta bata hakuri ta koma wacan karon duk kuwa da ya san yana da gaskiya, yanzu ma saboda abunda Mommynta tai ne da yanzu ya sake aikowa ko kuma ya zo da kansa.
ALIYU POV.
ya sauke wayar, ya amsa wayar a gaban Ataa ne saboda Rahma ta kira shi kamar yadda zai iya amsawa wayar Ataa a gaban Rahma saboda dukansu matansa ne kuma wani uzurin zai iya sakawa wata ta kira, da dai ba daga daga cikinsu ba ne, sai kuma Momy ko Mama Fulani Daddy Abbah, bayansu sai ya ga dama yake daukar waya idan an kira ko da yana waje balle kuma yana tare da iyalansa. Aje wayar yai gefena yana kallon Ataa wacce ke ta motsi kamar bata jin dadin zaman, ta turo baki sai hawaye take a hankali.
“Ba kya jinddin zaman ne?”
“Zafi ni dai har yanzu”
Ya san abunda take nufi sai kawai yai yar dariya, ya mike tsaye ya dauke ta ya nufi dakinsa da ita.
“So kike a kara kenan?”
“Wallahi baka da tausayi kai mugu ne”
Ta fashe da kuka.
“Ni ne mugun?”
Ya tambaya yana cige baki yayinda yake sauke ta saman gadon. Sai ta kara fashewa da kuka shi kuma ya saka mata dariya.
“Kin cika raki, ba da gaske na ke ba, ruwa zan hada miki”
Bandakin ya shiga ya hada mata ruwan zafi, ya fito yana fada mata
“Kullum ki rika yin tsarki da ruwan zafi”
“Wallahi ko wuta na saka ba zai daina ba, ni kaina na san zafin da na ke ji, har ya fi na jiya ma, kuma har yanzu bana iya tafiya daidai”
Ta fada tana wani irin shan iska saboda kukan ya mata yawa.
“Na lura ai ba zan sake ba”
“Har abada?”
Yayi wata mahaukaciyar dariya sannan yaja kunnenta.
“Yes har a bada”
Sannan ya fice daga dakin, falo ya koma ya zauna for a while sannan ya taso ya dawo dakin ya shirya cikin wasu tufafin, sai ga Ataa ta fito daga bandakin tana ta sauri.
“Ka ce zaka kai ni gurin Nana ko yau?”
“Ke fa baki da wyo ya za ayi Amarya da fita yau? Kuma da rana? Da ma da rana ne zan iya kai ki ki ganta sai dai kuma ba a yadda kike ba wannan abun kunya kawai zai sa na ji”
“Zan yi tafiya daidai”
“Ba kya iyawa ai, dole sai kin warke idan kin warke zan kai ki gida ki ga Mama da Momy”
Ya fada yana fesawa jikinsa turare sannan ya juyo ya sumbace ya saka bakinsa cikin nata bayan ya cire ya shafa kumatunta.
“I love you”
ATAA POV.
Da kallo na bi shi har ya fice sannan na zauna bakin gadon ina dan sake jikina ina hawaye, gaba daya satin haka nai shi cikin takura domin daga kafan da yai min na kwana hudu ne kawai, ranar da na cika sati daya ya kai ni da dare na ha Nana ranar ji nai kamar karna dawo gida, daker na shiga motar ina ta kuka yana jin ba dadi.
Muna kama hanyar gida ya mika hannu ya rika hannuna yana ta murzawa a hankali, kamin ya kwanta da ni jikinsa.
“Ashe ba za ki iya zuwa wata kasar ki barta ba? Gashe na shirya nan da kwana uku za mu dawo mu musu bankwana mu wuce”
Ni dai ban ce masa komai ba sai kukan na ke a hankali, da gangan na feshe masa majigina a jikin shaddarsa na yi tunanin ko zai yi magana ne, sai dariyarsa na ji ya shafa kaina.
“Kurciyarki na burge ni, dan kin yi hakan sai na ji haushi? Ko na miki fada? Ai ko ba amarya kike ba bana da irin wannan rayuwar balle kina Amarya ai ba kyan laifi ko kin kashe dan masu gida”
Nan ma ban ce masa komai ba, yana rikw da hannuna yana watsa da yatsuna har muka isa gaban wani mai siyarda kilishin ya siya mana sannan muka nufi gida.
Kamar yadda ya fada after three days muka koma gida dan yin bankwana da Momy da kuma Nana akan tafiyar da zamu yi Los Vegas, ya bada dama na zabi kasar da na ke son muje amman ban xaba ba saboda ban san komai akan wasu kasashen ba ni dai burina kawai na hau jirgi na san na taba hawa jirgi ko da sau daya ne a rayuwata. Rabar a gida na wuni a nan Nana take labarta min cewar ai kullum a falon Momy take wuni su yi fira saboda kadaici wani lokacin kuma idan zata kwanta Momy na turo mata Amina ko Husna su kwana tare, wani lokaci kuma ita kadai take bachinta.
Na jidadin yadda Momy take kula da mahaifiyata sosai, ita kanta tana jindadin haka. Washe garin ranar muka wuce Abuja daga sokoto, Nasir ne ya hada mana komai a yadda na lura Aliyu be fada min ba, amman na lura da yawan kiransa da yake ya tambaye ni ko shi abu har tafiyar ta hadu. Ya fada min bankwana zai yi ma Mama Fulani sannan mu wuce Lagos domin daga can ne jirginmu zai tashi, be takura ni kan cewar sai yaje da ni na ga Mama Fulani ba ko kuma yi mata bakwana, ni kuma hakan ya fi min sauki da dadi, ko ba komai bana son ganinta ita da Muhseen duk kuwa da ba ni da tabbacin ko zamu tarar da shi a gidan, kwananmu daya a Abuja sannan muka wuce lagos. Daga lagos jirginmu ya tashi da ina ta jin tsoro kamar yadda nai a lokacin da zamu taso daga sokoto zuwa Abuja da kuma zuwa lagos din, domin yadda na ke tsammani da marmarin jirgi sai na tarar ya fi karfin tunani da kuma hankalina, a lokacin da zai daga kana jin motsinsa sosai idan kuma zai sauka kana jin motsin dirarsa a kasa, sai dai idan kana sama baka ma gane tafiya ake sai idan kana kusa da windows, Aliyu a gurin windows ni kuma ina gefensa ya jingina na ni da jikinsa yana ta nuna min kasashe ta cikin wata yar karamar kwanfuta dake lake bayan kujerar da ke gabanmu, da map din yake fada min yanzu muna guri kaza, wani dan biscuit ne aka kawo mana da tea shi kuma ya ce coffee yake so, bayan mun gama sha wata mai uniform ta zo ta dauke sai Aliyu ya sake maida ni jikinsa yana ba ni ragowar biscuit din da ya dauka a plate din a baki ina ci a hankali kamar wata jaririya har bachi yai gaba da ni.
*Khadeeja Candy*
Mun sauka a gajeye domin tafiyar jirgin ta dauke mu awanin masu yawa, na yi zaton idan mun sauka can dare zan gani ko yamma amman sai muka samu safiya ce da alama akwai banbanci yanayi da kuma lokaci.
Muna fitowa daga cikin jirgin Aliyu ya cire jacket din jikinsa ya saka min saboda yanayin sanyin garin, daman doguwar riga ce a jikina sai dan karamin mayadi daya rufe iya kaina ya sauko zuwa wuyana kadan.
Kasa ce ko kuma na ce gari domin tun a jirgi Aliyu ya fada min cewar ba kasa ce gaba daya ba, gari ne dai kamar yadda kasata take nigeria da gari kala kala. Garin da zan iya kira da kasa, kasa ce yanayi mai kyau mutane kowa hada hadarsa yake babu ruwan kowa da kowa ga bin ka'idodi da dokoki ba kamar kasata nigeria ba, hannu ya daga sai ga texi ta zo ya bude min na shiga sannan aka saka kayanmu a bayan motar shi ma ya zagoyo ya shiga inda na ke, ya jani zuwa jikinsa. Ni kan idona na can jikin windows ina ta kallon tituna da kuma manyan binaye da kwaliyar garin gwanin sha'awa har muka isa wata kyakkyawar hotel mai haske da dagon bene mai kyau da daukar hankali.
Na yi zaton irin kudin kasata zai bawa mutumen a lokacin daya ciro wallet dinsa, sai ga shi na ga wasu kudin ne dabam ba irin namu ba.
Bayan ya gama mika masa kudin ya kama hannu muka shiga cikin hotel din shi kuma yana janye da luggage. Da yalshen nasara yai magana da su ya mika musu wani dan karamin kati da nake zaton na banki ne kamar yadda ya fada a lokacin fa yake nuna min passport din da akai min a gida Nigerian a gurin jami'in immigration da ke sokoto, da kuma na dan kasa da shi ma ya saka aka min, mayar masa da katin sukai su ka bashi wata yar takardar da makulli sannan ya juyo muka nufi wani bangare na hotel din, wani gurin ya taba sai wani dan daki ya bude mana mai kamar kumbu muka shiga ni da shi sannan ya taba wata number sai abun ya rufe ya fara tafiya da mu sama, shi kuma ya ciro wayarsa yana ta daukata hoto har muka isa abun ya bude muka fita, ni dai ina rike da hannunsa gaba daya tsoro ya gama kamani domin na lura da gurin tsif yake kamar babu kowa ga shi dakuna ne aka jera masu yawa sosai ko wane da number shi, numbobin dakunan ya rika dubuwa har muka isa gurin wanda aka ba shi key sa, budewa yai ya ya fara shiga sannan n shigo, an share dakin fes kamar wani ne a ciki komai a tsara shi gwaninb sha'awa, ac dakin ya fara kunnawa da wuta sannan ya maida kofar ya rufe ya aje kayanmu a gefen gadon. Bandaki ya shiga yai wanka da alwala ya fito sannan ni ma na shiga, bayan na gama wankan na nufo kofa abunda ban sani ba ashe Aliyu yana nan jikinn kofar labe yana jiran fitowata ina budewa sai yai cikina yana bani tsoro ai ko da gudu na koma ciki sai da yai saurin shigowa ya dauko ni ya fito da ni. Kuka na saka masa na buge masa fuska sai ya aaka min dariya wai daman ya lura da ina jin tsoro. Sai da muka lissafa sallah da ba mu yi tsakanin tasowar mu daga can zuwa nan muka rama su sannan muka dora da suba din da muka tarar a garin.
Bayan mun gama ya taba telephone din gefen gadon yai magana, ba bata lokaci sai ga wani mai uniform ya kwankwasa kofar dakinmu ya miko mana abinci, Aliyu ya karbo ya kawo mana komai a cikin kwali yake sai wata yar miya ce a cikin kwankwa mai shegen ja. Ni dai ban iya cin wasu abubuwan saboda ban saba ba ban ma tana ci ba, Aliyu kan cin abunsa yake da alama ma sun fi masa dadi. Pizza na ci da shawarma sai kuma miyar da na lasa kadan sai na ji bata min dadi ba.
Bayan mun gama mu kai hauk gado mukai bachi gajiya ni da shi, yadda na ke kwana a jikin Nana haka na kwana a jikinsa, ko da muka farka lokaci ya ja sosai bayan mun yi sallah ya cire layin wayarsa ya saka wani layin dabam ya kira Momy yace ta kaiwa Nana muka gaisa sai kuma Mama Fulani ita ya kirata ta daga ya fada mata ya isa lafiya.
“Miyasa ka canja liyin?”
“Ai na nigeria baya yi a kira shi a wata kasar ko wace kasa da kayinta, daman na dade da siyen wannan ba yau na fara zuwa kasar”
Na yi mamaki sosai jin cewar abubuwa da dama ba irin na kasata ba ne, wasu kuma dole sai an canja mutanen da yanayin ma ba daya ba.
Kwanan mu biyu a hotel din muna huga gajiya sannan muka fara fita yana nuna min wasu abubuwan da kuma wasu guraren, har da gurin shakatawa ya kai da gurin da ake hawan abubuwan wasanni kala kala, sai dai fa komai sai an biya kuma ba a jefar da abu kasa sai dai ka kasa a inda aka tanada dan zuba shara
Sannan babu mata masu saka manyan Hijab ko gyale kowa ka ganinda karamin mayafi yake indan musulmi ne wasu ma musulman ne amman ba mayafa haka suke ta yawa, na ga bakar fata da dama a garin. Ba cikin Los Vegas kawai muka yi yawo ba, har ma da wasu guraren da ke kusa da ita, idan Aliyu ya nuna min wani gurin sai ya min browsing a wayarsa ya fada min gurin da irin muhimmancinsa sannan kuma yai min hoto.
Gaskiya tafiya mabudin ilmi na karu da abubuwa da dama na ga abubuwa da dama kuma na san wasu abubuwan da a da ban san su ba, mun ci abinci a restaurant dabam dabam, ido ya bude sosai da tafiyar kuma na jidadinta lallau idan dai haka honeymoon yake gobe ma a kara muje wata kasar dabam su ma muga abubuwansu. Tafiyar da mukai ba kadan ta karamin kaunar Aliyu ba, domin ya nuna min kulawa sosai da kauna, duk inda za mu je yana rike da hannu duk kuma wani abun da yasan idan n saka zai min kyau sai da ya siya min, idan kuma na ci har sai na ture, kullum sai ya kira min Nana da Momynsa mun gaisa Mama Fulani ce kawai be yaba ba ni mun gaisa ba, I love you shine furuncinsa a gareni kullum, ko numfashi nai da karfi sai ya tambaya idan lafiya nake, abun har mamaki yake ba kamar ba Aliyu ba ashe dai waje ne wannan bazaranar take a gidan kuma yafi kowa iya tarairaya da nuna kulawa, sai dai idan abun nashi ya motsa na kin magana sai ya share ni nai ta tambayarsa abu sai dai yai min murmushi ko ya ja kunne na ko hanci ya ce nai shiru idan mun koma gida zai fada min. Satin mu hudu a can sam ko mamari komawa gida bana yi domin kullum muka fita wani gurin dabam yake kai ni mai nishadi da shakatawa idan ma ta kama wani lokacin ba za mu kwana a hotel din ba sai dai mu kwana a wata. Ranar da za mu bar Los Vegas mu koma gida sai da na ji kamar nai kuka domin na fara sabawa da garin da ba nawa ba, Aliyu yana ta rarashin na yana fada min wata rana ai za mu dawo.
RAHMA POV
kowa yana ta hada hadar zuwa dinner da za'ayi a yau ta kanwarta Amra ita kan tana makota gidan su Lubna ta boye kanta abun duniya ya isheta, daman tun da ta ji zancen Aliyu ya tafi Honeymoon da Ataa sai ta ji gaba daya kamar bata da lafiya a jikinta yar walwalar da take sai ta daina. Kullum tana cikin damuwa da bakinciki kuka kan babu ranar da bata yinsa, tun tana ganin laifin Aliyu har ta koma dorawa Mommynta laifi a ganinta da bata yi mahaifiyarsa wannan cin mutuncin ba da yanzu be kara auren ba, kuma da yanzu tana can dakinta. Wannan tunanin shi ya hanata sakewa kuma ya hanata sukuni balle har tai murna ko walwala a cikin yan'uwanta da yan biki.
“Rahma kina ta sakawa kanki damuwa dubi ki ga yadda kika koma, kowa yana can yanashirin zuwa dinner ke kina nan kin ware kanki dabam kina ta saka damuwa a ranki saboda da namiji”
Rahma ta kalli Lubna wacce ta dafata tana wannan maganar.
“Lubna idan ban yi kuka na yi damuwa ba dariya kike son nai na yi murna Aliyu yayi aure? Ina son miji taya zan jure ganinsa da wata?”
Ta fada cikin kuka.
“Indai kina son mijinki Rahma dole ki yi hakuri ki koma dakinki, ba dole sai kin tsaya ya zo bikonki tunda dai kin san laifi na ki ne, kin dawo gida kin zauna kina fushi kin bar shi can shi kadai kuma mahaifiyarki ta hana shi ke lokacin da mahaifiyarshi