Showing 87001 words to 90000 words out of 225640 words

Chapter 30 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

a kirjinka? Wane irin rayuwa ce wannan?”

“Momy ta ki aminta da ni ne, a duk lokacin da nai mata maganar mahaifiyarta sai ta fada min wata maganar dabam marar dadi, ta kasa yarda cewar taimakonta zan yi, a yanzu ma ina kokarin ganin ta aminta da ni ne kuma Mama ta koreta”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u amman wannan yarinyar tana ganin rayuwa”

Mama Fulani ta gyara tsayuwarta cikin yanayin da ke nuna bata jidadin boye mata da Aliyu yai ta ce.

“Baka taba fada min wannan maganar ba, baka taba labarta min komai ba, taimakonta da kake son da ma gaskiyar abunda ya faru duk baka fada min ba”

“Ba abu ne mai dadi da zan rika labartawa kowa ba Mama”

“Haka ne”

Ta fada sannan ya juya ta fice daga dakin. Saukowa tai downstairs ta nufi kitchen cikin wani yanayi marar misaltuwa, ko Muhseen da ke zaune a falon bata kula da shi ba har taje ta hada ma Abbah abinci ta fito ta fice ta kofar gaba zuwa part din Abbah, abincin ta kai masa ta zuba masa da kanta kamar yadda ta saba.

“Lafiya dai Hajiya Fulani?”

Abbah ya tambaya ganin yanayinta.

“Lafiya Kalau”

Bata fada masa komai ba duk kuwa da kasancewar fuskarta ta nuna hakan. Sai ya gama cin abinci ya tashi a uzurce ta rako shi har gurin mota ya shiga sannan ta nufo part dinta. Lokacin da ta shigo sai ta zauna a falo tana ta kallon su Rukaiya da Husnat dake gardama kan wani film, kallonsu kawai take amman hankalinta baya gurinsu, Aliyu ne ya sauko yana rike da wayarsa ya nufo inda Mama Fulani take zaune, sai da ya karaso daf da ita ya dan risina sannan ya ce.

“Mama ina ne unguwar su yarinyar nan, kuma daga ina aka akawo miki ita?”

“Ban san kowa nata ba, balle na san unguwarsu”

“Amman baya kawo miki ita?”

“Wacce ta kawo min ita ma ban san inda take ba”

Tana fadar hakan ta mike tsaye ta nufi upstairs ta barshi a gurin risine Muhseen da sauran yan'uwnas suna kallonsa domin sun ji abunda yake tambayar Mama Fulani sun kuma fahimci wacce yake tambayar, ban da Muhseen da be san abunda yake faruwa ba. Mikewa Aliyu yai tsaye ya fice daga falon, motarsa ya nufa ya shiga ya dauki hanyar gidansa cikin damuwa. A masallacin hanya ya tsaya yai sallah magariba da isha'i sannan ya shiga gida. A falo ya fara zaunawa ya dafe kansa yana ta yawo da idonsa, har ga Allah be jidadin korar da Mama Fulani tai ma Ataa ba, all his plan yanzu na taimakonta ne and yanzu be san ma inda zai sake samunta ba, tana kadunar kamar yadda wacan ta fada masa ko kuwa tana cikin sokoto? The way da yake ganin yanayin Mama Fulani ba lallai ta fada masa inda zai ga Ataa ba.

“Ban zata maganar zata haifar da wata matsala ba”

Cewar Rahma tana sauko daga stairs. Kamim ta karaso Aliyu ya mike tsaye ya wuce zuwa upstairs yana fadin.

“Ba shi ya dame ni ba yanzu”

Juyowa tai tana kallonsa.

“To me ya dame ka? Wata matsalar ce?”

Be ce mata komai ba ya shige dakinsa bakin gadonsa ya zauna yana kallon dakin kamar wani bakonsa. Rahma ce ta shigo tana tafiya a hankali ta zauna kusa da shi.

“Aliyu akwai wata matsalar ne?”

“Yarinyar da tai mana aiki wacce aka kirewa mahaifiyarta koda aka saka miki, ta zo nan Abuja tana aiki gidan Mama Fulani and yau Mama Fulani ta koreta”

Da Mamaki Rahma ta kalleshi tasan ba mutum ne mai yawan magana ba lallai ya fada mata cewar yarinyar tana aiki a gidan Mama Fulani ba, amman bata ga abun damuwa a cikin lamarin ba, akan mi zai damu da an koreta? A take zuciyarta ta soma raya mata son ta Aliyu yake.

“Miye abun damuwa dan Mama fulani ta koreta? Wata kila ta mata ba daidai ba ne shiyasa ta koreta”

“Ba lallai sai ta mata wani abu ba, and ba ni da wani plan a yanzu daya wuce taimakon yarinyar saboda halin da muka saka ta”

“Ba mu saka ta cikin ko wane hali ba Aliyu, ba laifin mu ba ne, da muka ce a nemo siya mukai kuma ka biya kudi ba a hanya ka kareta ka cire mata kodar ba, ban ga dalilin damuwa ba sai idan son ta kake!”

Ta fada da kamar fada idonta na cika da kwalla. Aliyu ya kalleta da kyau

“So ne abunda ranki ya kawo miki? Ba ki yi tunanin ya kamata mu taimake ta ba? Ba ki duba irin zalincin da akai mata da irin rayuwar da ta shiga?”

“Ba mu muka saka ta a cikin wata rayuwa ba Aliyu, idan ma zalinci ne b mu muka zalince ba”

“Amman sanadin wa? Tun farkon da aka samu kodar nan ya kamata na bincika daga gurin wa ta fito ban yi ba, gashi abunda ya faru, yanzu kuma na gane gaskiya sai na ce zan hau gado na kwanta nai rayuwata na kyaleta? Abunda ya faru da ke Rahma ishara ce, wata kila da ba a zalinci yarinyar nan ba da yanzu kodar da aka saka miki bata kone ba”

Hawaye ne ya sauko mata tana kallonsa.

“Mommy ta yi gaskiya, tun ba mutu ba ka fara gajiya da ni, da ada ne baka iya yin maganar wata mace a gabana Aliyu kuma ba za fada min wata magana da zata bata min rai ba, gaskiya ne maza ba su da tabbas, korar da akai wa wata ita ce damuwarka ba lafiyata ba? Saboda ni ina daf da mutuwa ka auro wata ko?”

Mikewa tai tsaye ta fice daga dakin Aliyu ya bita da ido yana jin kansa kamar zai rabe biyu, gaba daya yau komai na duniyar nan ya hade masa, rumtse ido yai gam kamin ya bude ya mike tsaye ya bi bayan Rahma, yayi zaton zai same ta tana kuka sai ya same tana hada wasu tufafin nata cikin akwati tana hawaye. Kusa da ita ya zauna yana kallon yanayinta ya kai hannu ya rika hannunta ya soma magana a hankali.

“Lafiyarki ta dame ni Rahma, amman hankali ya fi karkarta akan yarinyar ina zan same ta har na taimaka mata wata kila idan na taimaka mata Allah zai dube mu ya ba mu haihuwa kuma ya baki lafiya”

Mikewa tai tsaye ta nufi wardrobe ta rufe sannan ta juyo tana share hawayenta ta kalleta.

“Mommy ta fada min gobe da misalin Goma na safe za mu wuce, ina son na kwanta da wuri saboda na samu bachi”

Kallon kawai yake har ta zagayo ta hau saman gadon ya lullube da bedsheet ta juya masa baya. Mikewa yai shi ma ya kashe wutar dakin ya dawo bayanta ya kwanta ya rumgumeta ta baya, lumshe ido yai ba dan bachi ba sai dan tausayin Ataa daya cika masa zuciya a yanzu ya fi tausayinta fiye da Rahma, sai yanzu yake ji da ma ace Kamal be dawo fa ita ba da Mama Fulani bata koreta ba, wata kila ma ba zata iya gane hanya ba amman an tura zuwa garin be san ina take ba, maybe tai hadari ko ta gadu da wani abun be sani ba. Wannan tunanin ne ya hana shi bachi har asuba, for the first time yau ya kwanta gado daya da Rahma kuma rumgume da ita amman zuciyarsa tana gurin Ataa. Sai da yai sallah asuba sannan ya kwanta dakinsa shi kadai saboda nauyin da idonsa da kansa suke masa wai ko zai samu yin bachin da be yi ba jiya.


*** *** ***
A haka Mama Fulani ta kwana cikin rashin sakewa wanda ya bawa kowa mamaki ciki kuwa har da Momy da bata sake ganin walwalarta ba, gaba daya aka hadu dinning gurin cin abinci har Muhseen amman ban da Mama Fulani da ta gama shirya abinci ta koma dakinta tana karyawar.

“Husna kui yi ku gama mu shirya da wuri kusan 10 jirginmu zai tashi”

Momy ta fada tana mikewa tsaye ta daga dinning din ta koma falo ta zauna tana kiran wayar Aliyu dan ta tambayi jikin matarsa. Muhseen ya kalli Maryam.

“Wai ina Mama?”

“A dakinta take karyawa wai bata jindadi”

“Ataa fa? Yau ba tai shara ba ban ma ta shigo ba, kuma tun jiya da dare na duba ganta a gareji ba ban ga kayanta ba”

“Mama ta maida ita gida”

Muhseen ya kalli Rukaiya da sauri wacce ke bashi amsar.

“Saboda me?”

“Ta gaji da ita, kuma abunda ya faru daman Mama ta ce ba zata kwanar mata a gida ba”

Sai a yanzu ya abunda Aliyu yake tambayar Mama Fulani jiya har take ce masa bata san inda take ba. Jan kujerarsa yai baya ya nufi dakin Mama Fulani. Kishingide ya same ta tana cin fruit tana duba wayarta.

“Mama kin kori Ataa? Mi tai?”

“Ba tai komai ba, na gaji da aikinta kar kuma ka sake min maganar abunda ya shafe ta last warning”

Ta fada masa sannan ta cigaba da abunda take, sai da yai kamar zai sake ce mata wani abu sai kuma yarfar da hannunsa ya juya cikin rashin jindadi ya fice daga dakin.



ALIYU POV.

Be farka sai sha biyu saura na rana, ya dade kwance a saman gadon idonsa biyu yana kallon silin sannan ya unkura ya tashi zaune ya sauko da kafafunsa daga kan gadon, agogon dakin ya fara kallo yana ganin sha biyu ta kusa yai hanzarin mikewa tsaye ya fice daga dakin zuwa dakin Rahma, be same ta a ciki ba sai yar takardar da ta bar masa saman gado.

_Kana bachi bana son na tashe ka, Mommy ta kirani zan je na same ta a gidansu sai mu wuce see you soon_

Yana gama karanta takardar ya cikawa bakinsa iska ya busar cike da rashin jindadin yadda yau Rahma tai masa, be taba damuwa da fita ba tare da ta tambayeshi ba sai yau, yana ganin kamar ta wulakanta shi. Hannu ya kai ya dauki wayarsa da ya bari a dakin jiya sai ya ga miss calls din Momy da Husna da Maryam misalin tara da wani abu na safe kiran wayar yai sai ya ji bata shiga, hakan yasa ya kira wayar Maryam din sai ta shiga.

“Hello Ya Aliyu daman Momy ce ta ce na kira domin ta yi ta kira wayarka bata shiga”

“Ina Momy take?”

“Ta wuce tun ten suka tashi”

Ya kashe wayarsa yana fadin.

“Jirgi daya suka shiga da Rahma kenan”

Fitowa yai daga dakin zuwa dakinsa dan yin wanka ya shirya yaje gurin Mama Fulani, kamin ya shiga dakinsa ya kira wayar Nasir ring uku tai sannan Nasir ya daga.

“Na kira wayarka baka daga ba ya jikin Rahma?”

“Tana hanyar sokoto”

“What ta jin sauki ne ko kuma wani ciwon ne?”

“Sun sallame ta jiya, mahaifiyarta ta ce da ita za su je, and yau bata ma jira na tashi ba kuma bata tashe ni ba suka wuce”

“Kun samu matsala da Rahma ne?”

“Ba wani matsala kawai dai na mata maganar Ataa ne kuma taga laifina, Wallahi Nasir tunanin yarinyar nan hana ni bachi yai, Mama ta koreta tun jiya yanzu ban san halin da take ciki ba”

“Garin ya miya faru?”

Aliyu ya labartawa Nasir abunda ya faru sannan ya dora da.

“Mama ba zata fada min inda zan same ta ba, domin jiya konda na baro gidan ranta a bace yake, amman yanzu ina son ka nema min jirgi zan je sokoto gobe, zan koma gidan nan na sake bincikawa”

“Ko ba ka je da kanka ba za ka iya sakawa ayi maka Aliyu”

“Yeah ina son na je da kaina ko dan Rahma”

“Okay idan an gama komai zan sanar da kai”

Kai ya gyada kamar ance Nasir yana gabansa sannan ya kashe wayar.

Misalin biyu da rabi ya shiga part din Mama Fulani sai ya samu bata nan Baby ce kawai a gidan ita bata dade da dawowa daga scul ba. A saman Sofa ya zauna ya kira Mama Fulani a waya ringing tai sai da ta kusa katsewa sannan ta daga.

“Mama na zo ba ki gida”

“Eh munje gurin kamu ni da su Maryam kuma za mu shopping kamin mu dawo”

“Mama ina son magana da ke”

“Idan na dawo za mu yi”

“Yaushe za ku dawo sai da yamma”

Daga haka kai hanging wayar. Sannan ya nufi kitchen ya hadawa kansa Lipton ya sha ya fito shiga bangaren Ammy, a harabar gidan ya samu Batula tana fira da wani saurayi tana ganinshi ta sha jinin jikinta saurayin kuma ya gaishe shi Aliyu ya amsa mishi ciki ciki sannan ya wuce falon Ammy. Sai da suka gaisa sannan take koro masa da zancen tafiyar Momy.

“Ko da suka wuce ina bachi, Ammy ba ki san gidansu yarinyar nan Ataa ba?”

“Wallahi ban sani ba Aliyu, bata fada min ba nima dazun nake jin zancen tafiyarta gurin Muhseen yana tambaya wai ko na san inda take”

Aliyu yai shiru kamar be ji ba sai kuma ya mike tsaye yana saka hannayensa aljihu dan be son Ammy taja zancen da tsawo.

“Zan leka office”

“To Allah ya tsare”

Ko da ya fito part din Ammy wayarsa na vibration kiran Nasir na shigowa picking yai yana bude motarsa ya shiga.

“Aliyu an samu jirgin da zai tashi da yamma nan zuwa Kebbi idan kana so, daga Kebbi sai ka shiga mota zuwa sokoto, domin gobe babu jirgi sai jibi shi ma kuma da safe zai tashi na san kuma ba son tafiyar safe kake ba”

“Karfe nawa jirgin zai tashi?”

“5 idan kana so sai a siya maka ticket”

“Siya min gani nan zuwa office din ma”

“Okay sai na iso”

Yana kashe wayar ya shiga motarsa ya dauki hanyar kamfaninsu. Be bar kamfanin ba sai da ya rage minti talatin jirginsu ya tashi duk kuma jiran da yai na Mama Fulani ko zata dawo da wuri ne yai magana da ita dan be gane wannan fushin da ta soma yi da shi ba. Amman hakan be samu ba sai dai a waya ya kirata ya fada mata zai je sokoto tai masa Allah ya tsare.


ATAA POV.

Ina ta tunanin samun mafita har garin Allah ya waye, ban samu bachi ba saboda tunani da kuma nishin da Nana take yi. Bayan na gama sallah na dauki kofi naje na siyo mata koko da kosai da suga na saka mata na bata kokon kawai ta sha shima dan ina bata ne, ta ki ta ci kosan ni ma na kasa cin komai. Sai da na tabbatar ta koshi sannan na fito da ita na gyara mata jikinta na sake gyara dakim na saka Hijab dina na nufi titi, Napep na tara na hau na kama hanyar gidansu Rahma, da kudirin da ke zuciyata duk da kasancewar na san bata nan ina son naje ne na bar wa mai gadinsu sako ya fada musu domin na san ba zai rasa number da yake kiransu ba. Bakim gate din gidan Mai Napep ya aje ni na bashi kudinsa sannan na buga gate din mai gadin ya leko ya ganni sai na ga yai murmushi.

“Ahh wannan na manta sunanki ke ce”

“Ni ce”

Na amsa masa cikin damuwa. Sai ya bude min gate din na shiga ciki.

“Dan Allah so na ke ka kira matar gidan nan da mijinta a waya ka fada musu cewar akwai wata koda ta siyar idan suna so, ko kuma ka bani number wayarsu”

Ya daki kirji yana kallona

“Koda?”

“Eh”

“Ina kika samu koda?”

Na yi shiru ban ce masa komai ba.

“Allah yasa ba taki ce ba, kin abunda kike kuwa?”

“Na sani ni dai ka kirasu kawai”

“Sai dai a kira matar a waya amman Alhaji yana nan cikin gidan ai jiya da dare ya dawo”

“Ba suna Abuja ba?”

“Eh shi jiya da dare ya dawo bari na miki sallama da shi”

Ya fada yana nufar cikin gidan. Ni dai ina tsaye kusa da gate din har ya shiga ciki sai na hango Aliyu ya fito sanye da Jallabiya daga can ya tsaya yana kallona kamin ya sauko ya doso inda nake tsaye.

“Za ki siyar da koda?”

Na gyada kai ina matsa yatsun hannuna.

“Waya ce miki muna bukatar koda?”

“Na san ai kodar matarka ta kone, dole wata za ku nema”

“Saboda mi za ki siyar da kodar ki?”

“Saboda na nema ma mahaifiyata lafiya”

“Idan kuma ke kika mutu fa ko kika samu matsala?”

“Kara ni na mutu ita ta rayu da ta muti ta barni, jiya ba tai bachi ba saboda azabar ciwo, bata iya tashi komai a inda take take yinsa bata gane kowa ni ma da nake yarta bata gane ni ba, kuma ba mu da inda za mu babu wanda zai taimaka mana ina son mahaifiyata bana son ta mutu”

Na karasa cikin kuka mai karfi daman tun da na soma maganar hawaye ke sauko min. Shi ma hawayen na gani a idonsa sai yai saurin daga kansa sama ya zuba hannayensa aljihu.
ZAKI

By Khadeeja Candy

29...

Dukawa nai a gurin saboda kukan da ya ci karfina. Sai ya bar ni a gurin ya nufi cikin gidan be dade ba sai ga shi ya fito rike da gorar ruwa da cup dayan hannunsa kuma rike da tissue, ya nufo inda nake, tissue ya fara bani ba tare da ya ce min komai ba, na karba na share hawayena sannan ya bude gorar ruwa ya zuba min a kofi ya miko min. Karba nai na sha rabin ruwan sai na risina na aje kofin kasa dana dago sai na ga ni yake kallo ba ko kyaftawa, dan kawar da fuskata nai ina goge hancina.

“Ina Mamarki ta ke?”

“Tana can gida”

“Wane gida?”

“Gidansu kawata”

Shiru yai be ce komai ba har na wani lokaci idonsa na kaina ban san abunda yake kallo a jikina ba.

“Shigo ciki ki zauna kamin na shirya”

Yana fadar hakan ya juya da zimmar komawa ciki sai kuma ya juyo ya kalleni ganin na tsaya a gurin na ki na bi bayansa.

“Ni ba zan shiga ciki ba”

Na fada ina turo baki ba tare da na kalleshi ba. Matsowa yai kusa da ni sosai kamar zai hade jikinmu gabana ya shiga faduwa kamshin turarensa ya cikani sai dan matsa baya na kalleshi ido ya zare min.

“Idan na ce ayi yi ake ba a min gardama, wuce ki shiga ciki”

Yadda yai maganar is like yana bani umarni ne kamar wani boss. Kara tubo masa baki nai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login