Showing 216001 words to 219000 words out of 225640 words
shine likitan da ya cire kodar mahaifiyata ba tare da sanina ba ko saninta”
Daga haka suka fara karanto masa abunda ake kara akansa da kuma zarginsa da ake.
“Wannan yarinyar fa karya take ita ta siyar da kodar mahaifiyarta, kuma ta kai karata a gurin police ba ta ci nasara ba suka koreta shine yanzu take kokarin ganin ta bata min suna, wasu ne suke sakata saboda aci min zarafi”
Sai da suka tambayeni sannan na bayyana komai yadda ya faru ciki har da kulleni da akai gurin police, da suka tambayi ko ina da shaidu akan hakan sai na ce shukura ce ta san komai yadda ya faru.
“Fine na yarda a nemo shukura za ta fadi gaskiya ai, and zan kawo takardar da ta saka hannu akai za ku ga komai”
Yana fadar hakan na raya a zuciyata cewar akwai abunda yake kokarin shiryawa, wata kila ita ma zai siyeta kamar yadda yai ma polisawan da suka kama ni.
“Za mu cigaba da bincike, za mu gone gaskiyar lamarin idan har ba shi da laifi za mu hukuntashi, kuma zamu mika shi kotu domin ta hanke masa hukunci daidai da abunda ya aikata, ba zamu yarda wani likita ya bata mana aiki ko suna ba, ko kuma ya taka daya daga cikin dokikinmu, idan kuma ke muka samu da laifi yin masa kazafi za mu hukunta ki babu ruwanmu da kasancewar jikan Sarkin Agadaz babu ruwanmu da kudin kakanki ko babanki za mu hukunta kuma mi mika ki kotu domin a yanke miki hukuncin daidai da abunda kika aikata”
“Na yarda”
Ina fadar hakan Doc Asim ya maida hankalina a gurina, wata kila yana mamakin yadda nake da karfin hali ne wata kila kuma yana mamakin jin alakata da wani babban mutum nw kamar sarkin Agadaz da kuma zancen kudi da sukai ko da be san waye shi ba yana ji ya san ba karamin mutum, a take yanayinsa ya canja ya koma kamar ba shi ba rama yai ko lalacewa ba, yana nan yadda yake amman hankalinsa ne a tashe, domin ya san waennan likitocin ba kamar police ba ne da zai iya siye su ba. Ninkaina a yadda na gansu na san za su adalci ko da yake abun ba a fuska ba ne, da a fuska ne da Doc Asim ba zai min haka ba.
Dukanmu da farinciki muka dawo a mota na ke labartawa Hamma yadda akai yana ta kara kin kwarin guiwar cewar za su yi adalci domin gurin ba gurina na wasa ba, kuma ya san wasu daga cikin ko dab ganin abun ya fito ta bangaren Mai Martaba dole su kwatanta adalci domin ya nuna musu hakkin yarsa yake son a bi masa, abu na biyu kuma ba za su so wani likitan mai zaman kansa ya bata musu suna ba.
A gidan Momy na wuni ni da Mama domin bayan Hamma ya aje ni sai ya shiga gari, muka wuni muna ta maganar likitan har ake dauko zancen wasu likitocin masu taimakon da gaske da kuma wasu masu halin Asim sai dai su ba su kai shi ba ba domin na shi ya yi yawa ba kowane mai imani ne zai aikata haka ba. Daga bisani Mama ta dauko min labarin yayan Ammy da wasu yayan yayyunta ke so, wai magana har ta yi nisa ta kai gurin Mai Martaba ana zancen yin baiko. Na jidadin sosai jin cewar yaran Ammy ne duk dai Mama bata rike sunansu ba, amman ina ayyana cewar Humaira ce da Anty Zee, sosai na so ganin fuskar Mama Fulani da Maryam dan na san ba zata jidadi ba, saboda ba son shiri da Ammy take ba, kuma babu wanda zai so y'ar kishiyarsa ta samu jiki ta sa bata samu ba, balle Mama Fulani dake ta falako a cikin gida da nuna isa. Lallai Allah mai yadda ya so, kuma sai ya bawa Ammy surukai a cikin jikokin Mai Martaba yayan masu arziki wanda nasan Mama Fulani ce zata fi kaunar hakan.
Sai da dare muka koma gida, bayan Mai Martaba ya sake Kiran mama ya fada mata cewar an saka wani ranar Assabar mai zuwa wato nan da kwana biyu kenan. Kamar yadda ya saba yau ma sai da siya mana dan abun tabawa a baki sannan ya muka isa gida yana rike da hannuna kamar ba zai sake ki ba.
*** *** ***
Gaba daya al'amarin duniya ya koma mata sabo kuma ya zo mata ta inda bata zata ba, bayan daukakar da Allah yai ma Ataa akansu ya daukakata fiye da su sai kuma Allah ya kawo ma yaya Ammy miji daga cikin zuri'ar da tai kwadayin yayanta su samu, har magana ta fara karfi ga nata yayan babu wanda ya taya ban da Kamal shi ma Kamal din ma tun da akai fada da shi akan Ataa be sake kula Maryam ba. Balle Rukaiya ita ko zancen ba a ayi yadda kasan ta kasa kashi haka take, ga shi ba kyau ne babu ba amman babu mai gani ya taya kamar wanin abun amai. A yadda take so ita bata ki an hade su da auren Muhseen da za ayi ba, ita ta wanke su gaba daya ta huta ya zamana baby ce kawai ta rage mata.
Fitowa tai daga kitchen ta nufo inda Maryam take zaune tana lasar waya ta fara mata masifa kamar mai jin haushinta.
“Ai dole ku rasa mijin aure, ina can ina aiki kina nan kina lasa waya, idan safiya ta waye dakinku kawai kuka iya gyara kamar ku? Ace ba za ku iya aikin komai ba? Idan ma kun yi auren ai ba duka namiji ne zai dauki haka ba, dan ba ko wane namiji na kamar Aliyu ba da zai yarda da hali irin na Rahma wanda yai kama da halinku, su yayan Ammy haka suke? Indai auna nan ai su suke mata komai ku gyara ko'ina girki ne kawai nata shi ma wata rana su suke yi, gashi nan ai Allah ya basu maza a cikin waenda nai muku burin samu saboda ku ba ku san ku yi tausayina ko idan ina abu ku rika min ba, duki ki ga yarinyar Ataa haka ta zo tana aiki a gidan tai nan ta yi a can gurin Ammy duk akan mahaifiyarta kuma da Allah ya tashi bata gashi nan har Muhseen da Aliyu sai da sukai fada akanta, kuma yanzu gashi nan Aliyu take aure, mai taimakon uwa ai baya faduwa amman ku kullum kuna kan waya sa kan gado sai ka rantse kujera sai idan na gama ku taso zuwa dinning room dan ba ku da kunya”
Maryam ta kalleta cikin jin haushin fadan na ta ta ce.
“Oh Mama yau kuma duk wannan fadan a kan mu? Kamar dai kin gaji da ganinmu”
“To wace uwa ce zata so yayanta kamar ku su zauna a gida suna jera tsawo da ita? Yanzu idan an wanke Zainab da Humaira ai kubkadai kuka rage domin na ji Abbah ku na zancen har da Batula zai aurar tunda tana da mijinta amman ku ko mai sallama babu, balle mai zancen aure ko a wayar nan da ake haduwa da maza ku ban ku, ace kuma tausayina da yanzu kuma Allah ya tauyasa muku ya baku inda za ku huta ku jidadi”
“Mama kin san aikin nan fa ba mu saba ba, taya jiki irin nawa zai iya aikin wahala dan girman Allah? Kara dai a nema wata nai aikin”
“Wallahi ba zan dauko wata mai aikin ba, wato n dauko wacce Aliyu ya aure yanzu kuma na dauko wacce ubanki zai aure ko? To ba za a koma ba”
Mama Fulani na rufe bakinta Rukaiya na shigo cikin falon makkale da waya a kunnenta baki har kunne tana wasa da keys din motar hannunta, zaunawa tai kusa da Mama Fulani a lokacin da ta sauke wayar ta rumgume Mama Fulani tana murna kamar wacce akai ma albishir.
“Mama ke dai wani ne na hadu da shi, ya hadu Mama ga motarsa yar yayi”
“A'ina?”
Mama Fulani ta tambaya baki a sake Maryam kuma ta tashi zaune tana jin kamar ita ce.
“A gidan mai shi ya biya min kudin mai aka cika min motata tam, sannan ya karbi number wayata yanzu haka ina isowa yana kira wai na ji na isa lafiya, yana ta tambayar gidanmu”
“Wow Allah yasa mijin ne yanzu nan Mama take ta fada sai ka ce mu muka dorawa kan mu bakin jini”
Cewar Mama. Rukaiya ta kyalkyale da dariya tana kara rumgume Mama Fulani da ke murmushi cikin jindadi.
AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.Kamar yadda aka aje cewar Assabar za a koma, haka kuwa akai duk kuwa da kasancewar ranar ba a aiki amman a haka muka tafi ashe su suna shiga office saboda irin wannan case din har sun fi son ya fada weekend saboda kowa ya samu halarta. Kamar yadda akai wacan karon wannan karon ma haka kai daga gurin zama har mutanen su dai.
Sai dai mun samu karin Shukura wato nurse din da fada cewar ita ce shaiduna. Ko da wasa Doc Asim be kalli inda take ba, sai dai ni da Mama yana ta kallonmu kamar be taba ganinmu ba, ya rame sosai ba kamar wacan lokacin ba idonsa har sun fito saboda ramar da yai.
‘Ai baka ga komai ba tukuna’
Na fada a raina ina kallonsa cikin jin haushinsa da kuma jindadin abunda zai same shi. A bangare daya kuma ina dan jin tsoron kar Shukura ta ki fadar gaskiya wata kila ma ya siye ta ballantana a asibitinsa take aiki. Sai da suka gabatar da wasu abubuwan sannan suka fara da tambayar ko Shukura ta san ni, haka ta tsura min ido tana ta kallona kamar bata gane ni ba, na san na yi kiba na kara kyau jiki da sura saboda samun jindadi da kwanciyar hankali da nake samu a yanzu, amman ba zai iya zama wani canjin siffa da zai saka Shukura ta kasa gane ni ba.
“Eh na santa”
“Kin san sunanta”
“Ba zan iya tuna sunanta ba, amman kamar Ita ne ko Aita na manta dai”
“A ina kika santa?”
“Asibitin da tai jinyar mahaifiyarta”
Sai da suka tambaye ta a wace Asibiti ne kuma ko ta san wanda ya kula da mu da kuma ciwon da yake damun mahaifiyata.
“Asibitin Doc Asim, na yi kula da ita a lokacin idan ina duty kuma Doc Asim shine likitan da ya duba ta”
Sannan suka bukaci na ta fada musu gaskiya tsakani da Allah abunda ta san yana damun mahaifiyata.
“Ciwon koda ne”
“Me kika sani a gake da Doc Asim?”
“Litane kwarare mai asibitin kansa wanda na ke aiki a ciki”
“Mun kira ki a nan ne saboda ki bada shaidar akan zargin Doc Asim da ke na cire kodar mahaifiyar Ataa ba tare da saninta ba, har ma tana ikirari ke kika bata shawarar ta dauke mahaifiyarta daga Asibitin ta kai ta wata idan ba haka ba zata iya rasa ta, kuma kina ta yi mata alama da kada ta saka hannu a takardun”
Kallona tai ta hade gayu kamin ta kalli Doc Asim sai kuma ta kalli masu yi mata tambayar ta gyada kai.
“Na bata shawarar ta dauke mahaifiyarta ta kai wata asibitin saboda samun lafiyarta, kuma tabbas Doc Asim ya cire mata koda domin tare da ni akai tiyatar kuma a gaban idona Ataa ta saka hannu a takardun, sai dai ba zan iya bada shaidar cewar ba da saninta aka cire kodar mahaifiyarta saboda ba a gana aka yi wannan maganar ba”
“Amman miyasa kika girgiza mata kai?”
“Ina girgiza mata kai ne, saboda karta saka hannu a takardun da bata masaniyar komai a kansu”
“Ba mu fahimta ba ki mana bayani dalla dalla yadda za mu ga ne”
“Takardun da Ataa ta saka hannu ba ita ce ta farko da take saka hannu a akan irin waennan takardun ba, ita ce ta uku daya an yi gabana na ta ma anyi a gabana dayan kuma labari aka ba ni”
“Mi takardun suka kumsa”
“Siyar da wani bangare na jikin dan'adam”
“Kina nufin Ataa ta siyarda kodar mahaifiyarta kenan?”
“Ba ni da tabbacin wannan, idan ma ta siyar ko akasin hakan ba a gabana akai komai ba, sai daia gabana Doc Asim ya rika hannunta ya saka hannu a takardar saboda bata iya sakawa kasancewar bata san komai a boko ba”
“Taya akai kika san cewar bata san komai a boko ba?”
“Ita ta fada min kuma a lokacin daya bata takardar ya ce ta saka hannu sai ta fada masa bata iya komai ba bata san inda zata saka hannu ba, wannan shine kawai abunda na sani”
“Miyasa kika ce ta dauke mahaifiyarta daga asibitin?”
“Saboda waenda suke jin irin nata daga karshe suna rasa ran waenda aka cirewa koda cikin asibitin”
“Su wa da su waye?”
“Akwai wata Hadiza Salisu wacce take unguwar mabera, da kuma Faruk Abubakar da ke unguwar Minannata sai kuma wannan Ataa din da ke unguwar Clapperto road”
“Za mu je da ke mu taho da su sati mai zuwa, au bada shaida a gabanki kin yarda”
“Na yarda”
Daga haka aka bawa Doc Asim damar magana sai ya sake nanata cewar shi saiyar masa da kodar Mama nai. Sai dai sun tuhumi she da siyen koda ba tare da neman yan'uwan masu ita ba, taya zai siye koda a gurin yarinya kamar ni bayan mahaifiyata bata cikin hayyacinta ba tare ya nemi yan'uwanta ba, kuma ya kamata ace akwai shaidu a tsakani.
Ni kaina sai a lokacin na kawo wannan tunanin a raina, lallai ya kamata ace ko a iya yan'uwan suka kai ya nemo su indai har da gaske ne, tun daga nan kowa ya san akwai cutar da yake shirin yi.
Mun dawo gida tare da Mama kamar yadda muka saba a gidan Momy muka wuni sannan muka wuce gida. A ranar Hamma yai min ba zata da wani form na makarantar koyon girki da ke nan cikin sokoto, ni ban taba sanin cewar akwai wata makaranta ta koyon girki ba na sai yau ashe abun na manya ne wai har certificate suke badawa ga wanenda aka koya musu suka iya. Babban abun jindadi daya fada min cewar sati mai zuwa zan fara zuwa domin yayi magana da malamar har ya kai mata hotona da sunana da duk wani abun daya shafe ni. Na jidadin sosai da yai wannan tunanin ni kaina na san akwai abubuwa da yawa da ban sani ba kuma ban iya ba ta fannin girki abunka da wacce bata saba ba hasali ma ba ya na ke ba a can baya sai idan an samu ganima, wacan lokacin taliya ce muke ci sai kanzo da shimkafa idan ta yi afki. Sai dai an san shiga wannan makaratantar koyon girkin zai taimaka min sosai.
Bayan sati daya da wacan taron muka sake komawa sai da wannan karon bayan Shukura har da mutanen data fada cewar su ma an cire musu wani bangare na jikinsu, sun bada shaida kamar yadda Shukura ta fada, kuma dukansu kodar aka cire musu da alama dai Doc Asim ya kware a bangare cire koda ko samar da kodar a gurin masu nema a biya shi ta hanyar kwarai ko akasin hakan. Da aka tambaye su shin suma ba su da ilmi na kamar ne dayar wacce ta kasance matar aure ce kuma babbar mace ta amsa da eh. Ta saka hannu ne saboda bata san komai a kai ba, kuma ta fada mata yayarta na da ulcer dole ai an mata tiyata ashe dan ya cire kodar ne. Namijin ma be saka hannu a takardun ba an likitan ne ya saka hannu da kansa sai ya bashi dayar ya saka hannu wacce ita ce akai wa mahaifinsa aiki akai da sunan kodarsa daya ta lalace zai masa aiki a kyauta. Ba karamin mamaki sukai da jin lamarin ba, da aka nemi jin ta bakin Doc Asim sai ya amsa da cewar shi dayar ce kawai ta siyar masa da koda sai kuma ni amman sauran duka akan ciwonsu yai musu aiki. A lokacin da aka tambayeta ya akai ta san koda aka cirewa Yayarta sai ta amsa da cewar ita ma dai ta yi gwaji a wata asibitin kamar ni su suka fada mata cewar an cire mata kodar, sai dai ganin cewar ba su da inda za su sake kaita a karbetaa bata magani mai tsada da zata ji sauki yasa suka dawo da ita asibitinsa har ta rasu a nan, dukansu su ukun nan sun rasa majinyantansu shi namijin ma sai a yanzu yake gane cewar an cire wa mahaifinsa koda, sai dai biyun kamar ni ne wato talakawa masara galihu waenda ko za su ihu su nuna fushinsu da bakincikin da bacin rai ko son daukar mataki babu mai kawo musu dauki ko kula balle har ya shige musu gaba gurin karbar hakkin na su, ni ma din ba dan da Mai Martaba ya shiga ciki ya mika lamarin a gurinsu ba da ni da su duka ba za a karbo mana hakkin mu ba, babu wanda zai san da zancen an yi mana haka din idan kuma har mu kai unkurin