Showing 174001 words to 177000 words out of 225640 words
ta zo bikonki kuma ki yi tsammani ba zai yi fushi ba? Haba dai ai Wallahi dole ma ne mahaifiyarsa ta saka ya kara aure, ni dai inda nake ganin rashin kyautawarsa na kin dawowa yai bikonki gaskiya be kyauta ba, sai dai idan aka aunanda tafiyarki Dubai ba ki fada masa ba sai a ga kamar hakan da yai ya dace”
“Ki daina tuna min abunda ya riga ya faru, ki ba ni shawarar abunda zan yi”
“Shawara kawai ki koma dakinki, ko da iyayenki sun nuna miki ba haka ba ki ce ke dai kina son mijinki kuma kina son ki koma dakinki, amman zamanki a nan ai matsala ce kawai domin za ki jawa kanki wata matsalar ne wata kila ma ki janyo ciwon ya dawo gashi har yanzu ba a samu kodar ba”
Shiru tai na wani lokaci sannan ya hade ya wu ta ce.
“Zan koma, idan an daura auren Amra gobe hankalin Daddyn ya kwanta zan masa magana, na san yanzu hankalinsa ba kwance yake ba saboda zuwan Mai Martaba Sarkin Agadaz”
Lubna ta wara ido, domin ita ma tana jin labarinsa saboda tashen kudi da siyen kamfaninika da yake.
“Laa ya zo? Ashe dai da gaske zai zo”
Rahma ta share hawayen.
“Eh ai bashi da girman kai, daman Daddy ya ce zai zo domin shi ya bawa walincin aurar da Amra, kuma daman yana bukatar zuwa da kansa yi ma Daddy jajayen rasa babban shopping mall dinsa da kuma duba wasu abubuwam tun yau ya zo ance yana Hotel yana hutawa sai gobe zai je daurin aure idan an daura zai wuce Abuja ya duba wasu abubuwan sannan yaje jigawa da Lagos sai kuma ya wuce, tun da yamma ma Mommy ta shirya masa abubuwa taje ita da Daddyn suka kai masa, hankalin Daddyn yanzu yana can gurinsa amman na san da zarar an daura auren ya wuce Abuja indai ba tare da Daddy za su tafi ba zan samu ganinsa hankali kwance idan ma da shi yaje ai dole Daddyn zai dawo sai na fada musu cewar ni ina son komawa dakina”
“Ba dole sai Daddy kai tsaye ba, idan dai hankali ya kwanta sarkin ya tafi an gama bikin sai ki samu Mommynki a daki ki fada mata ita zata fadawa Daddynku ai”
“Amman kara na same shi ni da kaina dan ya tabbatar da gaske na ke, saboda Mommy zata iya kin fada masa, tunda bata son komawar tawa”
“Ke dai ki gwada idan ka bata fada masa ba ai sai ki same shi da kanki ke ki fada masa daga baya”
Ta gyada kai.
“Zan yi hakan In-Sha-Allah na gode sosai Lubna”
“Karki damu, kuma idan kin koma ki nuna mata ruwa ba sa'an kwado ba ne, kin dai san ba lafiya ce ta ishe ki ba Wallahi ko bi tai kusa da ke ki fadi ki ce ta tureki dole ya daukar mata mataki ki tai mata bandar kasa”
“Ai ba sai kin fada min wannan ba, ke dai na koma gidan kawai tana yadda ake kula da mijin tana wata kazamarta komai bata iya ba, sai ya san banbancina da ita ai dole”
“Ina son ki kawata, ai kema na san baki da dama kina babbar mace karamar yarinya ta ce zata zubar miki da aji? No-no yanzu dai tashi muje gida ki shirya muje dinner ki cire komai a ranki yanzu mun samu mafita”
Murmushin jindadi Rahma tai ta mike tsaye tana dora mayafinta a wuyanta, tare da kallon kawarta.
“Bari na je na shirya ke ma ki shirya sai na zo mu tafi domin ni motata tana can gurin hadahadar biki ana yi da ita”
“Ba matsala bari nima na shirya”
Daga haka itama ta mike tsaye ya rako Rahma har gurin gate din gidansu suna ta kara tattaunawa kan lamarin kamin Rahma ta wuce gidansu domin shiryawa ita ma Lubna ta koma gida.
ATAA POV.
Kusan karfe ukun dare muka baro can kayan da muka tafi da su da zamu dawo sai mu dawo da jaka biyu, domin a lokacin da zamu je tufafina da na shi a jaka daya ya hade su, tsarabar da mukai a can kuma ta zama a dayar jaka ya zama mun dawo da jaka biyu a amaimakon daya da muka je da ita.
A lagos muka sauka kamar yadda muka tashi a can, na yi zaton ko Aliyu zai bari sai idan mun huta a lagos din sannan mu wuce Abuja ashe duka rana daya ne banbancin awa biyu ne kawai na jiran da mukai, tun da muka sauka a Abuja na soma jin kamar ba ni da lafiya kaina sai ciwo yake jikina yai zafi wata kila saboda canjin yanayi ne domin yanayin can ya fi na nan dadi sa sanyi, wata kila kuma saboda gajiya ne domin ban saba irin wannan tafiyar ba.
Yamma ta yi a nan domin karfe uku ne har yan mintuna a nan Abuja. Muna sauka airport Aliyu ya kira Nasir ya fada masa, ba bata lokaci sai gashi ya zo da motarsa ya dauke mu. Dan kwantawa nai a kujerar baya wai ko zan samu walwala da sakewa kamin mu isa gida, amman sai karuwa na ke jin abun na yi sanyin ac motar ya sa ina jinsa ba dadi kamar nai amai, yawuna ma daker na ke iya hadewa.
Lokaci lokaci Aliyu ya ke dan waigo baya ya kalleni sai na masa murmushi ina kokarin nuna kamar bana jin komai amman hakan be hana shi ya gane ba.
“Baby za muje gurin Mama idan mun huta a can sai mu wuce gidanmu kin ji?”
Na ji ba dadi domin ba son ganin Mama Fulani na ke ba domin bana sakewa da ita kuma na san ba so na take ba har yanzu.
“Amman ba za mu fara zuwa gida mu huta ba, idan mun huta sai muje mu gaishe ta?”
“No na riga na saba indai na yi tafiya mai nauyi irin wannan idan zan dawo gidanta na ke sauka zata shirya min abubuwa masu kyau, idan kuma a sokoto ne gurin Momy na ke sauka, amman ba za mu dade ba tun da ba ki da lafiya”
Babu yadda na iya tunda ya fada min haka akidarsa take amman har ga Allah bana son ganin Mama Fulani gabana har faduwa yake.
“Ba ta da lafiya ne?”
“Eh nima yanzu na lura”
“Ayyah Maybe gajiya ce”
Nasir ya tambaya yana juyawo ya kalleni. Sai Aliyu yai masa wani kallo.
“Ya zaka leko ka kallar min mata? Ni fa bana son haka”
“Kallon ta kawai nai fa”
Nasir ya fada yana dariya.
“Ato ko kallo ai ba zan jidadi ba, yanzu nan sai shedan ya raya maka wani abu, kasan mata masu kyau hadari ne”
“Kai Allah ya kiyaye wannan abun”
“Ato kodai cewa kai tana da kyau a zuciyarka ai na ji haushi”
Ban da dariya babu abunda Nasir yake har nima nai murmushin. Kamar yadda ya fada a gidansu Mama Fulani Nasir ya sauke mu, sai dai na lura kamar suna da baki domin na ga manyan motoci na alfarma da bansan da su ba a gidan har biyu, wata kila kuma na Muhseen ne ko mahaifinsa wadanda ban san da su ba. kin fitowa nai daga motar har sai da Aliyu ya fita ya zo ya bude min sannan na fito cikin yanayin da ke nuna bana jindadin zuwa gidan ba kuma dan fargabar komai ba sai na abunda zai iya biyowa baya.
“Ki kwantar da hankali ina tare da ke ai ko?”
Na gyada kai, ina tuna zama na a gidan a matsayin mai aiki yau kuma na shigo a matsayin matar Aliyu daraja ta dagu, sai da ya rufe motar sannan ya rika hannuna babu ko kunya muka shiga ciki. Da sallama ya shiga yana janye da hannuna da nake kokarin kwacewa ya ki ya sake. Ina jin yadda Mama Fulani ta amsa masa ita da su Maryam cikin far'ar da jindadin ganinsa.
“Maraba maraba da dan tafiya ka dawo lafiya?”
Ta fada ba tare da ta kalleni ba, Aliyu kawai take kallo. Tana sanyi da wata tsaddadiyar shadda ga yan kunnen gol da sarkarsu ta zuba a wuyanta Maryam da Rukaiya sun ci kwaliya kamar masu zuwa biki. A kujerar dake fuskantar tata ya zauna yana murmushi har lokacin yana rike da hannuna sai ya tangwarani ni ma na zauna.
“Mun dawo lafiya Mama fatar mun same ki lafiya?”
“Kai kadai na tambaya ai kai da wani kai tafiyar ne?”
Ya yi shiru be ce komai ba ni kuma nai kasa da kaina ina mika mata gaisuwa.
“Barka da yamma Mama Fulani”
Sai tai kamar ba ta san da zamana a gurin ba balle har ta amsa min sai magana take ma Maryam wai ta dauko ma Aliyu fruits din data yanka masa. Idona ne ya cika da kwalla ina kallon Aliyu sai ya girgiza min kai alamar kar nai kuka, a dole na maida kukan ciki.
“Biki ake ne Mama na ga kun yi kwalliya”
Ya fada bayan Mama Fulani ta miko masa ruwa mai sanyi.
“Eh baka ga motoci a waje ba? Mai gidan Abbahku ne ya zo, ya so ya sauka hotel Abbah ku ya dage ya roke a akan ya sauka gidanshi idan ya huta sai su shiga ya duba kamfanin har da surukin ka aka zo ai baban Rahma”
Aliyu ya sha ruwan sannan ya miko min har zan karba sai ta daka min tsawa.
“Karki kuskura ki taba min kofi, wai ba na fada maka karka kuskura ka kawo ta a gidana ba? Ban gargade ka ba?”
Karbar kofin Aliyu yai yaje.
“Mama idan kina takura mata ba dadi zan ji ba yanzu fa ita matata ce, Wallahi ko lafiya bata da”
“Ni ma saka mata ciwon kenan? Ka dauki yarinya kanta na cikin keji ka ta ka kaita har Los Vegas, ai Wallahi ka gama da turawan can ka gama ci musu mutunci”
Aliyu be sake cewa komai ba sai kallona yake domin tuni hawaye sun fara wanke min fuska, ina da dannar kukana domin ina daf da fashewa da kukan. Maryam da Rukaiya dai ba su ce komai ba na san hakan baya rasa nasaba da ganin Aliyu a gurin.
“Ai Wallahi ba dan zuwa Sarki Agadez a yau ba, ina cikin farin ciki da Wallahi abunda zan mata ba zata sake marmarin gani na ba balle har ta dawo gidan nan”
“Sarkin Agadaz?”
Na tambaya da sauri ina dago kaina na kalli Mama Fulani jin sunan sarkin yasa na manta da kukana a take.
“Sarkin ubanki, idan na sake magana kika saka min baki sai na saka Rukaiya ko Maryam sun fitar miki da jini a baki”
Ta fada tana aiko min zagi da hannunta. Ban damu ba ya koma gurin Aliyu.
“Aliyu sarkin Agadaz yana nan cikin gidan kenan? Ko kuma garin nan yanzo?”
“Yana nan cikin gidan yana part din Abbah”
Ya fada yana kai hannunsa ya share min hawayena.
“To sarkin soyayyah ai ban san kana son ta ba sai ka dauke wannan kazamar ka hade, sai na san kai din baban soyayya ne ko kuma kana son ta, wai ko kunya baka ji Aliyu kalle ka ace ka kare a wannan abun, ai Wallahi Rahma bata cire haushi ba”
Shine abunda Mama Fulani ta fada ni kuma na mike tsaye jikina na rawa na ce.
“Aliyu ina son na ganshi ina son na ganshi Aliyu dan Allah”
“Ai dole ki so ganinsa kan ki kafa tarihin ganin mai arziki a rayuwarki yar matsiyata”
Ban kula maganar Mama Fulani ba na soma fashewa Aliyu da kuka.
“Ina son na ganshi Aliyu dan Allah”
Mikewa yai tsaye yana kallona ganin da gaske kuka na ke.
“Lafiya minene?”
“Ina son ganinsa yanzu yi sauri ka kai ni dan Allah”
“Karka kuskura shiga da ita ita Mai Martaba baya son damuwa, ganin yarinyar nan ma zai iya sa masa tashin zuciya”
Tsayawa yai kallona sai na bar shi a gurin ya nufi kofa da sauri ina kuka duk ban tana shiga bangaren Abbah ba yau zan je na shiga, ina fitowa na ji ya riko ni ya juyo da ni.
“Baby lafiya kike?”
“So na ke na gani idan shi ne da gaske idan ba shi ne zan fada maka”
“Okay”
Ya ja hannuna sai ya nufi wata hanya da ni mai kamar corridor duk zamana gidan ban tana binta ba sai yau. Wani gurin muka kullo sai ga wani dan karamin guri mai kamar mai yar rufa da wata babbar kofa a ciki, ta kofar ya murda ya shiga da ni ciki sai da mukai yar yafiya kadan sannan ya tsaya da ni gurin windows falon a nan ma wani a tsaye yana kokarin tare window.
“Kalla ki gani shine mi yai?”
Kallonasa nai sai na hango zaune saman kujera tsohone sosai amman ba irin tsufan nan na marasa karfi ba, irin tsufan nan da jindadi da wadata wanda tsufan sai ya tsufa sosai a jikinka yake bayyana kansa, farin waganbari ne a jikinsa ya hade fuskarsa da rawani wasu matasan samari na zaune kusa da shi a kasa, mahaifin Rahma da Abbah na zaune kasa suna masa fira a hankali da alama wani abun Abbah yake nuna masa Daddyn Rahma na kara masa bayani. Tsufansa be hana ni ganin fuskar Nana a fuskarsa ba, kuka ne ya zo a take na kalli Aliyu ina fadin.
“Shine Aliyu shine Mahaifin Nana”
Ina fadar hakan nai saurin kufar inda na ke hango dogarai masu wasu kalar tufafi da ba kalar na dogaran nan ba da zimmar shiga sai suka tare. Ashe kofar ma ta cikin gida su suke tsaronta har da wasu masu shigar gida da nake kyautata zaton yan sanda ne amman ba su saka uniform ba. Dawowa nai da gudu gurin windows din na tura bakina da inda muryata zata shiga cikin falon.
“Mai martaba ina son na ganka sun hana ni”
Na fada cikin daga murya da yaren buzanci, sai mutane da ke tarun kofar da tagar suka yo kaina da sauri za su rike ni, Aliyu yai sauri jana ya maida bayansa.
“Kar wanda ya taba min mata cikinki”
Ya fada yana nuna su da yatsa.
“Mai Martaba”
Na sake kiransa sunansa da yaren buzanci ina kuka. Sai ga Abbah ya fito tare da Daddyn Rahma.
“Miye haka?”
Abbah ya fada yana tambaya da hannu cikin bacin rai, har Aliyu ya bude baki yai magana sai ga daya daga cikin samarin da ke tare da sarkin ya fito da hanzari yana kallona.
“Wacece ke?”
“Ni jininsa ce ni yar Asma'u ce ni yar Nana Asma'u ce dan Allah ku bar ni na ganshi?”
“Wace Asma'u?”
“Gimbiya Nana Asma'u yarsa dan Allah ku bar ni na ganshi”
Duk da yaren buzanci muke magana da saurayin, kamin mamaki ya kamashi sai yai min wani kallo daga kasa zuwa sama sannan ya juya ya koma ciki da sauri. Be dade ba ya dawo ya ce a shigo da ni, da sauri na shiga gaba wajen shiga cikin falon. Sai dai ina shiga sai dogaransa suka hana ni isa kusa da shi.
“Wallahi ni jininka ce Mai Martaba ni yar Asma'u ce ba cutar da kai zan ba”
Na fada cikin yaren buzanci ina kuka, kallo yake daga can inda yake zaune, har na wani lokaci sai ya daga musu hannu sai suka bani guri na nufi inda yake da sauri, ina isa na fadi kasa na rike kafafunsa na fashe da wani irin kuka.
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
*AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*
*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
Wani irin kuka na ke bai ban tausayi da taba zuciya ni kaina ina jin wani yanayi da ban taba jin irinsa a sai yau, taya zan iya bayyana ganin farinciki? Farincikin mahaifiyata? Kakana? Kai tsaye kuma a saukake ban taba kawowa raina haduwa da shi a nan kusa ba. Ban taba tsammani abun zai zo da sauki kamar haka ba. Ji nai an shafa kaina sai na dago da saurin domin tantace mai taba nin shi din ne ko wani? Shi ma kwalla ce a idonsa irin da tsufaffin da basa son bayyana kukansu. Daga cikin wanda yake tare da su ne suka zo za su rikani su raba ni da kafafuwansa da na rike sai an kara rike su da sauri na fashe da kuka, a take ya daga musu hannu Alamar su kyale ni. Wani irin kuka nake kamar dacan an halitto kukana dan zuwan wannan ranar ne kawai, tun ina a hankali har muryata ta fara shakewa, sai Aliyu ya matsa kusa da ni ya dafa yana kokarin raba ni da jikinsa.
“Ayusher ya isa haka”
Kai na girgiza masa na sake rike kafarsa, dadi na ke ji yau na ga wani daga dangina, yau na ga mutumen da Nana take ba ni labarinsa, ban tana gani wani dan'uwa daga jinin Nana ko jinin Mahaifina ba, sai yau taya ba zan yi kukan dadi da farinciki da tausayi da takaici a lokaci daya ba? Hannu ya daga wa Aliyu kamar yadda yai ma sauran, a dole Aliyu ya kyale ni yana ta damuwa da kukan da na ke, ni kuwa na samu damar yin kukana iya son raina har sai da na ji an samu natsuwa sannan nai shiru dan kaina amman ban sake kafar ta shi ba. Sai a lokacin na lura da