Showing 210001 words to 213000 words out of 225640 words

Chapter 71 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

rasa wanda kake so a lokacin da ba kai tsammani ba, mahaifinta kan ya sha jinin jikinsa kamar ba shi ba, sai kallona suke ta yi daga shi har Mommyn Rahma.
  Bayan mun dawo daga gaisuwar ne su suka kama hanya, ni kuma aka bar ni nan a gurin Momy wai sai an gama karbar gaisuwa. Ina zaune saman carpet ni kadai a dakin ina salatin Annabina na ji shigowar mutum, ban waiga ba amman na san ko wanene tun daga kan kamshin turarensa, ta kuma yadda yake takowa zuwa inda na ke a hankali har ya iso. Ji nai an rumgume ni ta baya, sai na sauke ajiyar zuciya a hankali ni kaina na san na yi marmarin Hamma sosai tun a lokacin da na zo garin nan idona suke kai kayin ganinsa, amman ban saka shi a idona ba ko gaisuwar da su Mama da yan'uwanta suka masa ina kyautata zaton sai indai a can gidansa suka same shi ko kuma ya shigo ni ban ganshi ba ya fita domin tun shigowata gidan ban ji ko alamun motsinsa ba sai yanzu. Gafen kumatuna ya sumbata.

“Fada min kina nan lafiya?”

“Lafiya kalau, tun dazun muka zo amman ban ganka ba”

“Ina ta kokarin boye kaina dan kar na yi arba dake har sai idan ke kadai ce, saboda ina mararin na rumgume ki na jiki a jikina kuma ba zan iya haka abun a agaban mutane ba”

Ya fada ba tare da ya sake ni daga rumgumar da yai min ba.

“Mama ta tafi”

“Na sani na gode da ta bar min ke”

Mun dauki lokaci a haka yana rumgume da ni ta baya, sannan ya sake ni ya mike tsaye ya zauna bakin gadon Momy, juyowa nai na kalleshi sai wani irin kaunarsa da tausayinsa suka dirar min a zuciya lokaci daya, ya rame sosai kamar ba shi na har idonsa sun fada kamar marar lafiya.

“Hamma baka cin abinci?”

Kallona kawai yake ba tare da yace komai ba.

“Bari na saka Husna ko wata ta hada maka wani abu ko kuma idan akwai fura ka sha idan baka son abu mai nauyi”

Ina mikewa tsaye sai ya riko hannuna ya dawo da ni kusa da shi ya zaunar ya ja ni zuwa kirjinsa ya rungume ya lumshe ido, ina jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.

“Na gode Allah da be dauke min Rahma ba sai da ya ba ni ke, kuma yai min tukuici da wani dan ko ya, ni kada na san halin da na ke ciki kuma ni kadai na san iya abunda na ke ji a zuciyata”

Ya fada yana kara matseni a kirjinsa, rashi akwai ciwo sosai na san irin yadda Hamma yake ji a yanzu saboda ni ma na taba rasawa ba ma sau daya ba. Sai da ya ji kamar muryar wata a kusa da kofar dakin sannan yai saurin sakina ni kuma na mike tsaye cikin tsoron kar wacce ke maganar ta shigo ta gan mu a tare. Wata kanwar Momy ce ta shigo dakin da sallama ni na amsa mata sai ta miko min kofin fura.

“Ga shi inji Yaya ta ce ki sha”

“Na gode”

Na fada bayan na saka hannu biyu na karba, sannan ta juya ta fice. Zaunawa nai kusa da Hamma na mika masa furar wacce aka damata da kirdirmon nono.

“Ka sha”

Ba min musu ba, ya karba ya sha sai dai ba da yawa ba, ya mikon min sauran.

“Shanye”

Na sha rabin kofin sai na aje ina ta kallonsa, gaba daya ya koma kamar ba shi ba, so silent fuskarsa ma abun tausayi kallo daya zaka masa kasan cewar mutuwar Rahma ta taba shi ba kadan ba, ni ma da ban saba da ita ba ta taba na shiga damuwa kuma nai kuka balle kuma shi da yake mijinta kuma su kai rayuwa da ita.

“Ina auna yadda kika rasa babanki da dan'uwanki ne, kuma ki kaita dawainiya da mahaifiyarki, gaskiya Ayusher kin yi kokari kuma ke jajirtacciya ce, wani lokacin ana jarraba bawa saboda a gwada imaninsa da kuma irin hakurin da zai yi, ban yi tsammanin tunanin Rahma zai addabe ni kamar haka ba bayan rayuwarta, amman idan na tuna ki da abunda yake cikinki sai na jidadi kuma nai ma Allah godiya”

Ya fada a hankali yana ta kallona da murmushi a fuskarsa sai dai ba murmushin farinciki ciki ko na jindadi ba irin murmushin nan na godiya ga Allah da kuma jin zafin wani abun a lokaci daya. Shigowar Momy ce tasa na dan ja baya shi kuma ya mike tsaye yana saka hannayensa aljihu ya fice, ni da Momy da kallo muka bi shi har ya fice sannan Momy ta karaso cikin dakin ta dauki kofin furar da ta aiko min tana dubawa.

“Ba ki shanye ba?”

“Eh na sha rabi”

“Ki daina barin kanki da yunwa, na san ba za ki iya cin abu mai nauyi ba wata kila shiyasa na tanadar miki da furar”

“To Momy”

“Zauna”

Ta nuna min kujerar da ke facing din gandon, bayan na zauna sannan ita kuma ta zauna bakin gadon.

“Ataa ki matar aure ce a yanzu ina fatar kin san da haka?”

Na gyada masa kai ina maida idona kasa.

“Ke yarinya ce na sani, amman daga lokacin da kikai aure zancen yarinta ya kare sai dai a kira ki yarinya saboda shekaru ko kuma wani abun da za ki na shirme ko rashin tunani, ballantana yanzu da kike dauke da juna biyu”

Na kasa yin kasa da kaina saboda kunya.

“Mijinki na bukatar kulawarki a yanzu fiye da ko yaushe, na san ba ki san wata dawainiyar ba, amman kula da abincinsa ya ci ko be ci ba yana wuyanki a yanzu, karki zamana shi kadai zai dinga damuwa da ke, mijinko ya rasa daya abokiyar rayuwarsa hakan kuma ba karamin jefa shi yai a matsala ba, sai da taimakonki zai iya dawowa dai da ya manta komai kamar be faru ba, ki shimfida masa kalar rayuwar da kike son yai kuka ya bi saboda yana tsananin son ki ni na sani, na san ke ma kuma kin san da haka, ki rika yi masa abunda zai kwantar masa da hankali da saka shi natsuwa, hakan ba karamin kara mishi son ki zai yi, a yadda yake damuwa da ke kuma yake son ki idan kina nuna masa damuwarki akan rashin cin abincinsa zai ci saboda gudun damuwarki kuma zai sa ya rage damuwar, tun da akai mutuwar bana jin ya saka wani abu a cikinsa har yau sai ruwa, sannan ki rika yi ma mijinki addu'a a duk sallah musamman a sujadar karshe da kuma bayan tahiya kamin ki sallame, mace mai aure ma ba akarbar addu'arta har sai idan tana yi ma mijinta da kuma iyayenta”

“In-Sha-Allah Momy”

“Kuma ke ma ki kula da kanki, wani abun ba sai ance ki yi ba, ya kamata ace kin san aure kike a yanzu, kuma ke ce kadai a gurin mijinki, mijinki na bukatarki a yanzu fiye da ko yaushe, ina fada miki wannan ne saboda na san zaki iya kuma ke kadai na ke da tabbacin za ki saka shi cikin walwala a yanzu, mijinki be iya so ba, be iya ki ba, ba kuma iya sakawa rai abu ba, idan yana so gaba daya yake so baya ganin aibun abun har sai yayi zurfi a ciki, idan kuma ya tsane abu gaba daya yake tsanarsa baya iya ganin kyaun abu har sai yayi nisa a tsanarsa, idan kuma ya sakawa rai abu yana sakawa sosai ta yadda rashin abun nan zai yi ta damunsa yana cinsa a rai, daga ke har shi ni duk kallon yara na ke muku wani abu dole sai an nuna muku, saboda mun fi ku tunani da hangen nesa, na san ba ki yawance a komai ba, sai dai ke din jajirtacciya ce saboda gwargwarmayar rayuwa da kika sha, da kurciyarki kin fuskanci kalubale kala kala na rayuwa kamin yanzu, kuma da Allah ya tashi miki sakamako sai yai miki duka a lokacin da kike bukatar hakan, hakuri yana da kyau kuma yana da riba sosai duk wanda yai hakuri be ga riba ba to kadan yayi”

Sosai na jidadin magangannun Momy, a natse ta fada amin komai kuma na fahimci manufar da nufi, daga lokacin na sakawa kaina zan iya, kuma na fara jina a matsayin mace mai aure mai daraja wacce zata iya kula gidanta da mijinta da kuma yayanta duk kuwa da irin karancin shekaruna. Idan na waiwaya baya kadan na tuna abunda ya faru da ni irin halin rayuwar da muka shiga da fadi tashi da nai sai na ga wacan rayuwar kamar labari aka ba ni ba ni ce na wanzu a cikinta ba.

“Tashi ki bi mijinki ku kwana a can”

Maganar Momy ta katse min tunanin da nake.

“Ba ki bukatar komai dai ko?”

“Babu”

Na fada ina mikewa tsaye na dauki Hijabina na saka, sannan na fara takawa a hankali har na fito falo.

“Matar yaya ina za ki je?”

Siyama ta tambaya tana kallona da murmushi a fuskarta.

“Gida zamu je”

“Ba anan za ku kwana ba?”

“Eh”

Na amsa mata muryarta da kamar damuwa. Sannan na karasa kusa da Mama Fulani na dan risina na ce mata.

“Mama za mu tafi gida sai gobe”

“To Allah ya tsare”

Ya mayar min tana kallona, sannan na karasa gurin Ammy ita ma nai mata sallama da wasu kannen Momy da yan'uwan Daddy sannan ya fito harabar gidan. Na yi mamakin ganin Muhseen tsaye jikin motar Hamma yana magana da shi, ban san mi yake fada masa ba na ga dai Hamma ya gyada kai sannan ya bude min gaban motar tun kan na karaso.

“Ataa”

Kiran da Siyama tai min ne yasa na juyo sai ta nufo ni da yar karamar dogowar kular silba a hannunta.

“Ga shi wai Momy ta ce ku tafi da shi”

“Mun gode”

Na fada bayan na karba, ko da na juyo ban ga Muhseen ba balle mafarinsa sai Hamma tsaye yana ta kallona har na karasa, hannu ya kai ya karbi kular hannuna sannan ya matsa daga jikin motar wanda hakan ya bani damar shiga ciki na zauna shi kuma ya rufe motar, ya zagaya bangarensa ya shiga yai ma motar key.
  A hanya ya rika tambaya ko ina son wani abu, sai na ce masa bana bukatar komai, amman duk da haka sai da ya tsaya ya siya min gassashiyar kaza da yoghurt.

“Bana jin yunwa fa”

“Za ki iya bukata da dare ai, kuma ba dan ke kadai na siya ba”

“Dan wa?”

“Babyna”

Ya fada min fuskarsa babu walwala. Har muka isa gida ban sake ce masa komai ba shi ma kuma be ce min ba, har sai da ya faka motar na kai hannu zan bude.

“Tsaya ba ri na bude miki”

Fita yai ya zagayo gefena ya bude min motar na fito sannan ya rufe, ina gaba yana bayana har muka shiga cikin falon, sai ya zauna saman cushion yana ta kallona.

“Na hada maka ruwan wanka?”

“Zo nan”

Zuwa nai na zauna saman kafafuwansa kamar yadda na bukata sai ya rumgume yana sauke ajiyar zuciya a hankali sai dai hakan be hana ni jin saukarta. Mun dade a haka kamin ya barni na daga jikinsa mu shiga daki, rumguma a cikin abunda Hamma ya ke so kuma ni ma nake so domin ina jin natsuwa sosai idan ya rumgume ni hakan kuma yana kara min jin son kusanci da shi sosai. Cikin jikinsa na kwana kamar kullum sa'a daya nai ban farka cin abincin dare kamar yadda na saba ba. A lokacin da muka gama sallah asuba kuma sai na nufi kitchen na bar a dakin yana karatun qur'ane ni kuma na shiga na kunna gas din na sarrafa dan abunda na iya na ruwan zafin tea da suya wainar kwai da dankali sai kuma doya, sannan na bude kular da Momy ta ba mu jiya, farfesun kayan ciki ne a ciki, sai kawai na dora su akan wuta na dumama na juye a wata kular.

“Wow da kanki kike girki, na fada miki bana son wahalar nan da kike miyasa ba ki jin magana”

“Dan na yi aiki ba komai cikin zai yi ba, kuma ni bana son abincin waje”

“To amman sai ki bari idan na gama karatu Quranen na hada ko?”

“Bana son girki na namiji”

Wannan karon yayi kokarin fadada  fuskarsa da abunda ya rasa daga lokacin da akai mutuwar nan zuwa yau wato murmushi shi ma kadan.

“Kin taba jin inda da zai ce baya son abincin babansa”

“Haka dai yace wai babansa be iya girki ba, idan ma yayi babu dadi shiyasa nake turo min shi nai amai”

Na fada ina yatsina fuska, sai ya kara matsowa kusa da ni ya rika hannayena.

“Karki masa karya, na san ba zai ce haka ba, ta ina ma kika ji ya ce haka? Yaushe kika iya karya”

“Yanzu”

Na fada da kamar kunya, sai yai murmushim gefen fuska yana aje numfashi. Shi ya taimaka min na karasa hada komai, sannan muka karya, be wani ci da yawa ba shi ma kuma dan na matsa masa ne, ni kan na ci abincin sosai kamar wacce ta kwana da yunwa, ni kaina har mamakin yadda na ke cin abinci sosai na ke kamar ba cin lafiya ba.


***  ***   ***

Har akai zaman makokin aka gama Mommyn Rahma bata koma normal yadda take ba, damuwa ta taru a ranta ta tsaya mata, ba ita kadai ba gaba daya gidan babu wanda mutuwar Rahma bata taba shi ba, yau duk wani abu da Rahma ta mallaka na jindadi da dangi da kaunar iyaye da miji yau ta tafi ta barsu, mutuwa ta ishi kowa wa'azi, yau iyayenta sun ga Abunda kudi ko iko ko milki ko isa basa badawa wato rayuwa, komai ikon ka da isarka da milkinka baka isa ka hana mutuwa daukarka ba, kamin mutuwarta sun ga abunda ya kamata yace ya zame musu ishara, na juyarwar al'amarin da ba su taba zaton zai zame musu haka ba, duk wani abu da Daddyn Rahma ko mahaifiyarta ko ma ita Rahma da kanta take takama da shi na familyn Ataa ne yarinyar da suka wulakanta suka maida ba komai ba, a karkashin inuwar kakanta suke takama ta gidansu ce, ita din da suke gani ba komai ba Allah ya mayarda ita saman su, wani karin bakinciki ma ta zama ita kadai a gidan Aliyu babu yarsu a gidan balle tai kishi da ita. Yau sun koma sune kasa ta ko wane bangare.

Sai da akai aka gama karbar gaisuwa sannan Mama Fulani da Ammy suka koma Abuja tare da Abbah daman shi Muhseen kwana biyu kawai yai ya koma saboda yanayin aikinsa. Nasir ma da matarsa sai da suka kara kwana daya saboda Aliyu sannan suka wuce. Aliyu da kansa ya raka su har airport lokacin da za su tafi, Nasir yayi ta bashi hakuri da kuma kalaman da za su karfafa masa guiwa su akan rashin Rahma.
  After ya raka su ya dawo gidan Momy duk ya zama wani silent kamar ba shi ba, lokaci lokaci Rahma take fado masa a rai, idan ya tuna cewar be cutar da ita a zamantakewar su da aure ba sai ransa yai fari tas domin babban abunda yake gudu a rayuwarsa zalintar wani ko danne masa hakki da ikonsa, and wani abun godiya ga Allah da Allah ya saka ba Ataa ce ya rasa a yanzu ba, domin da ita ta tafi a yanzu maimakon Rahma wata kila da zai fi shiga damuwa sosai fiye da Mutuwar Rahma, duk wani abu da yake game da Rahma sabo ne kawai da kuma tuna irin rayuwar da akai ko makinyin ka ne ya rasu sai ka ji babu dadi balle kuma matarka, yana yawan ayyanawa kansa wata rana zai mutu Rahma ma zata mutu saboda matsalarta tun daga kan cire mata koda da akai na farko da ta biyun ta lalace aka canjin mata wata da ta mahaifiyar Ataa ta zo ta kone abun ya soma ba shi tsoro. Wata kila ta kone ne saboda Allah ya nuna musu ikonsa akan abunda suka aikata sai dai hakan be zame ma Rahma da iyayenta ishara sai ma kokarin aikata wani suke, yanzu kuma da mahaifiyarta zata bata nata sai Allah ya gwada musu ikonsa ya karbe abarsa a lokacin da suke tsananin bukatarta kuma babu yadda suka iya da ikon Allah. Yar da suke kishi da fada akanta mai abu ya karbi abarsa kuma ya maida wacce suke kishin da ita asaman su sai kuma ya?

ATAA POV.

kamar yadda Momy ta fada min ina kokarin ganin Hamma ya ci abinci ko da ba da yawa ba, kamar yadda ni ma yake tsare ni na tisani a gaba dole sai na ci na koshi a cikin satin sai ya zama ni da shi muna bawa junanmu kuwawa ta musamman da kuma ganin tausayin junanmu, yana ganin tausayin cikin da na ke dauke da shi da kuma tausayi Rahma sai ya dawo kaina ni kadai daman can kuma ga kaunata a ransa, yadda yake tallalina kana ganin abunda yake min kamar mai tsoron ya rasa ni ne, ni kuma tausayinsa ya cika raina sosai na rashin Rahma da yai da kuma yadda baya iya bawa kansa kulawa ta musamman amman yana kokarin kula da ni. Wanda ya rasu shi ya tafi babu abunda za a canja daga rayuwar wani ko kuma duniya gaba daya, daga lokacin da rayuwarka ta yanke shikenan kai na manta da ka taba wanzuwa a wata duniyar ma, kana ciki kabarinka kana fuskarta abunda ka aikata idan alheri ka fara gani idan kuma akasin hakan ne shi ma zaka gani. Na karu da abubuwa da dama a mutuwar Rahma a ciki akwai na tunatar da ni cewar saboda na samu jindadi da kwanaciyar hankali a yanzu ba shi yake nufin mutuwa ta manta da ni ko kuma ni na manta da ita. Abu na biyu kuma na yarda wanda ya mutu shi ya mutu duk kuwa irin son da ake masa, domin Hamma ya dan fara sakewa ba kamar da ba, daman kuma ai ba zai dawwama a cikin bakincikin mutuwarta ba kamar yadda take tsammani saboda Allah ya musanya masa da ni, wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login