Showing 6001 words to 9000 words out of 225640 words
ya takani da mota ya wuce.
Yau kam ban dawo da wuri ba, domin a hanya magariba tai min, hango manyan motoci guda biyu a gidan da zan iya kiransa da hamu yasa ni hanzarin cira kafa na karasa ciki da sauri, Nana na samu risine a kasa tana rokon wani mutum kamar zata fasa kuka.
“Dan Allah ke yi hakuri Wallahi babu inda zai je, shiyasa ya laba nan shi da yaranshi”
Babban mutumen mai rigar arkin dake nuna isarsa da tarin dukiyarsa ta dakawa Nana tsawar da har sai da naji ciki raina.
“Babu ruwana da wannan, akan mi za ku zo ku bata min gida, ku san nawa na zuba na siye filin nan, an fara min gini sai kawai ku zo ki shige kuna lalata min guri”
A nan nima na zubar da kayana na shiga rokonsa kamar yadda Nana ta hade hannayenta tana rokonsa.
“Baba dan Allah kai hakuri Wallahi idan ka koreni daga nan ban san inda zamu je ba ba mu da kowa”
“Ba ku da kowa daga sama kuka fado? Daga ina kuka taso kuka dawo nan? Ku koma can ni bana son ganinku anan, ku bar min gida na fada muku idan na sake zuwa na tarar da ku a nan sai na wulakanta ku”
Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga, sauran mutane da suke tare da shi suka shiga dayar motar suka bi bayansa. Kallon mahaifiya dake kuka nai ina kwalla sai kuma na daga kai na kalli yar bukkarmu, miye laifin mu dan mun raba a wannan gidan tunda ba a ciki muka zauna ba, miye laifin bukkarmu mu dan kawai mun zauna a ciki.
“Yau ko mun shiga uku an koro mu can nan kuma an kore mu, yau ina za mu?”
Shine abunda mahaifiyata take fada ya yaren buzanci tana kuka. Zuciyata ta sosu sosai tana da gaskiya domin idan har kuma bar nan ban san wani guri da zamu iya rabawa ba, domin ba mu san wani gurin da zamu iya zuwa mu nemi taimakon gurin zama ba. Daga ni har Nana haka muka wuni cikin damuwa da rashin walwala har garin Allah ya waye, da safe Nana ta aika Lukman ya siyo mana waina ni da shi ita kuma ta gagara cin komai. Sai dai hakan be hanata fita bara ba, ni ce dai ban je ba, daman yau bana jin fitar saboda abunda ya faru jiya na laka min sata da kuma zancen barin gurin da muka raba, sai duk haka yasa ni jin kamar ma bani da lafiya, sai dai yau na samu yin sallah biyu a cikin lokaci tun a gida na wuni kuma bana aikin komai, wato azahar da la'asar ban da Asuba da da nai bayan rana ta gama bayyana.
Can da yamma Nana ta dawo har da biredinta a hannu, Lukman na bayanta da gorar ruwansa rataye a wuyansa. Biredin kawai muka ci muka sha ruwa sannan ya dauko kudin da ta zo da su da sauran kudin da suke rage mana idan mun siye abinci gaba daya kudin ba su wuce dubu uku da yan kai ba.
“Wadannan kudi ba zasu iya mu kama haya ba, ni ban san yadda za mu yi ba”
Magana take ina karantar tashin hankalin dake zuciyarta har yake bayyana kansa a fuskarta, ni dai na yi shiru ina ta tunanin sama mana mafita.
“Nana ko mu nemi gadi wani gida? Ta yadda zamu samu gurin zama”
“Wa zai ba mace gadi? Idan mu mun samu ni ina zan iya tare barawo?”
“Ai dan mu samu gurin zama ne”
“Hakan ba zai yi ba, sai dai na bincika wani gurin ko Allah zai sa mu samu”
Tun daga ranar kullum Nana cikin neman gurin da zamu koma mu raba take amman ba mu samu ba, yawancin inda muke samu duka filaye ne mu kuma muna tsoron zama a fili sai dai a kangon gidan da aka fara aka bari ko kuma ba a karasa ba ko ya kuma ginin daya soma zubewa.
A kullum da fargabar zuwan Alhajin muke kwana mu tashi muna ta zuba ido ko zai zo amman shiru be sake zuwa ba har aka kwashe kwana kusan goma shabiyar, hakan yasa muka koma muna rayuwarmu ta yau da gobe cikin kwanciyar hankali. Musamman ni da ban sake saka wannan bakin mutumen a idona na ba. Yau ma da gari muka karya duk kuwa da kasancewar bana sonsa amman babu yadda na iya dole na ci ko babu dadi, bayan mun gama sha ne na tashi nai alwalar isha'i na kabbatar sallah. Ina cikin sallah na ji ihun Nana waccw ta kewa a bandaki kasa karasa sallar nai jin ihun yayi yawa na dauki fitilar hannu dake dakin na fito waje da sauri ni da Lukman muka nufi kewan ina Haskawa sai na hango katon maciji ya nade gurin daya yana ta zuro mana kansa, Nana kuma ta fadi gefe daya tana ta murje murje da alama cizonta yai ko kuma sara, Lukman ya saka kara ni kuma na saki fitilar a firgice na ruga izuwa titi cikin hudun hangon gidan ina neman masu taimaka mana, daman na san ba za a rasa irin wadannan abubuwan ba a guri kamar wannan, musamman da dare ba hudu yake zageyemu har sai idan mun kunna kara ko fita ko kuma hasken farin wata, wutar nepa kan sai dai mu hangota a manyan gidaje. Da ihu da karaji na isa titin gawon nama ina ta neman wadanda zasu taimaka mana, mazan da suke zama a gurin titi suka yo kaina da sauri ni kuma na shiga gaba ina gudu suna gudu har muka dawo cikin kangon gidan dake cike da hudu, masu wayoyi suka kunna wayarsu suka haske bandakin sai Nana aka gani babu macijin babu labarinsa, motsin kirki ma bata iya yi da sauri wani yace a bashi kyale sai ya daure inda yake zaton macijin ya tsareta wato kafar data rike.
“Ku nemo Napep? A kaita asibiti”
Daya daga cikinsu ya fada ni da Lukam babu abunda muke sai kuka ni ina rike da ita Lukman kuma yana tsaye bayana, a gurin wasu samarin ke kallo domin yau babu wannan bakin gentleman n a fuskata mai hana kowa ganin ainahin kyawo na. Ban san wanda ya kira Napep din ba nadai ga an shigo da ita har gurin Bukkarmu samarin suka rikata suka sakata ciki ni Lukman na shiga gaba ni kuma na zauna baya tare da ita ina hawaye kamar ba gobe.
Ko wane motsi nata jinsa nake cikin kashina ji nake kamar ciwon a jikina yake, mahaifiyata ita ce duniyata, na gwada kokarina akan tsagaita kukana sai na gano ashe ni ba ba Jaruma ba ce a gafen dauri. Wata asibitin kudi mai zaman kanta Mai Napep din ya kaimu a lokacin da muka isa emergency sai suka karbe mu da gaggawa aka wuce da ita ciki Mai Napep ya juya yai tafiyarsa ni da Lukman sai muka yi tsaye waje. Har sai da Nurse din ta dawo kirana ta dauki sunan Nana ta bukaci naje wani guri na karbo kati sai na tuna da babu sisi a tare da ni, adole na bar Lukman a gurin na fita na hau achaba na je na dauko kudinta gaba daya na dawo naje na biya kudin katin sai kuma aka ce likita na son ganina. Da sauri na nufi inda Nurse din ta nuna na tura kofar office din na shiga hankalina a tashe fuskata duk hawaye ya bata ta, hannuna rike da yar jakar da Nana take zuwa da ita bara wacce kudin suke ciki.
“Nurse tace kana son ganina”
“Ke ce wa?”
Likitan ya tambayata yana min wani kallo daga sama zuwa kasa, duk wanda ya kalli sutura baya bukatar na fada masa cewar ba mu da shi, tufafin da nake saye da su kawai sun isa su isarda sakon talaucin da muke tare da shi.
“Mamata na kawo wacce maciji ya tsara”
“ina Babanku?”
“Babanmu ya rasu”
“To ina yan'uwanku da ke zan yi Magana”
“Ko minene likita ka Fada min mamata bata da kowa a nan sai ni, duka yan'uwan mu suna nijar”
Na Fada idona na sake cika da kwalla. Kallo yai sai ya sake kallona sannan yace.
“Okay wannan allurar za ki siyo naira dubu ashirin da daya za ki kashe”
Ya Fada yana mika min wata farar takarda. Ina karba na juya jiki ba kwari zan fice sai na ji ya ce.
“Kina da kudin ne? Idan ba ki kawo maganin nan da wasu hours ba Mamaki zata iya mutuwa”
Juyowa nai idona na zubar da kwalla ma girgiza masa kai dan bana ko iya magana.
“Babu?”
Na gyada masa kai.
“Bude baki kiyi magana wannan asibiti na ce zan iya taimaka miki idan baki da su”
“Wallahi ba ni da su ban san inda zan samo ba, bara mu muke kamin mu saye abincin”
Shiru yai kamar mai nazari, sannan ya kalleni ya ce.
“Shikenan zan mata allurar kuma zan ya mata tiyata na cire dafin macijin”
Da sauri na risina kasa ina masa godiya wani irin jindadi ya rufe jin za a ceci mahaifiyata sai dai ban taba jin inda akai wa wani tiyata aka cire dafin maciji ba sai dai allura.
“Taso muje ki saka hannu a file”
Da sauri na mike tsaye ina share hawayena, yana gaba ina binsa har muka shiga wani daki mai cike da nurse da yawa ya dauko wata takardar ya miko tare da nuna min inda zan saka hannu. Hannunsa ya dora saman nawa yana yimin sigh din yadda zan hi daidai, ina daho kaina nai arba da wata nurse tana girgiza min kai alamar kai, sai dai ban gane abunda take nufi ba na tausayi ne ko kuwa na kar nai yi ne oho ni dai fatana a ceto mahaifiyata....
https://my.w.tt/GuQH5GZKb9
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
4️⃣
Misalin goma aka shigo da ita tiyata amman basu fito ba sai karfe uku da wani abu na dare.
Anyi mata tiyata cikin nasarar Allah da iyawarsa, saidai a halin da naga mahaifiyata sai na kara matso da maraicin mu kusa ni da Lukman. A wani dakin mai kyau aka ajeta kamar matar wani babban mutum ko kuma wata hajiya, a jikinta an manna mata wasu na'urori har a hancinta a wani abu mai kamar kwanfuwuta nake kallon tafiyar numfashinta, sai dai tana kwance a gurin kamar gawa jikinta babu tufafi sai wani zanen asibiti da aka saka a lulluba mata.
Ina tare da ita har asuba ban runtsa ba, gani nake kamar zata iya farkowa ta bukuci wani abun ko da yake babu komai a tare da ni wanda zata iya ci ko ta sha, lukman ne kawai ke ta bachinsa hankalinsa kwance.
Misalin takwas da rabi likitan ya shigo cikin shiga ta kananan kaya da rigar likitoci a samansu fuskarsa a sake yana ta min murmushi kamar mun saba.
“Ina kwana?”
Na gaisheshi cikin girmamawa. Sai ya amsa min kamar be gane ni ba, ba kuma kallon rashin ganewar bane, wata kila sai a yau ne yake tantance irin hallittar da Allah yai ta kyau mai daukar hankalin mace balle kuma namiji.
“Miye sunanki?”
“Aisha amman ana kirana Ataa”
“A nan kuka kwana?”
Ya tambaya yana kara tantance kyawun surar jikina.
“Eh”
“Ayyah ban sani ba ai da na kawo muku abun shimfida ko kina da shi”
Na girgiza kai alamar aa a cikin yanayin dake nuna dukan hankalina da damuwata tana gurin mahaifiyata ne.
“Da gaske baki da kowa a nan Nigeria? Ku yan nijar ba naga akwai wadanda suke da yan'uwa a nan ba?”
“Ni ba mu da su, ba a mu da kowa a nan”
Na fada masa cike da gundira da tambayoyinsa. Sai naga yayi murmushi kamar wanda jin hakan yai masa dadi, sai ya saka hannunsa aljihu ya nufi mahaifiyata yana dubata.
“Ki samo riga ki saka mata da zanen da zai iya rufe kafafunta, na bada a siyo mata maganin dubu dari da bakwai manyan magunguna ne masu tsada yadda mahaifiyarki za tai saurin jin sauki kuma an mata allurar bayan na mata sai nai mata operation na cire mata dafin macijin”
Wani irin dadi ne ya lullube ni sai na rasa ta inda zan fara masa godiya, hawayen farinciki suka cika ido har naji kamar na dauke shi na hade, a rayuwata ta duniya tunda Nana ta haife ni ban taba karo ko ganin mutum mai tausayi da jinkan masarasa irinmu ba kamar wannan likitan.
“Na gode Allah ya biyaka ya saka mata da alheri, Allah ya daukaka asibitinku Ya saka maka da aljanna ka taimaki rayuwata sosai ba zan taba manta ka ba”
Murmushi yai yasa hannunsa aljihu ya ciro kudin da za su kai dubu goma ya miko min.
“Ga wannan, ki je ki siya abinci ki yi duk abunda kike bukata, kuma idan mahaifiyarki ta farka ki kirani karki bata komai”
Wannan karon addu'ar gamawa da duniya nai masa, domin a tunani ita kan aljannah da duniyar duka ya sameta, domin mutum mai taimako mai share hawayen masara shi Allah yai masa alkawarin aljanna kamar yadda Annabi yace shi da mai taimakon maraya kafada da kafada za su shiga aljanna da shi. Babu abunda nake hangowa sai matarsa tabbas tayi dacen miji domin samun miji mai taimakawa al'umma har su yi masa addu'a ta yi babban dace.
Bayan ya fice ne na kama hannun Lukman muka fita zuwa gida, sai dai abunda na tarar a gidan sai yafi tada hankalina fiye da ciwon mahaifiyata. Yar bukkarmu ce aka hankade can gefe aka cire kwannon da maihaifiyata ta saka domin zagaya yin fitsari ko ba haya, kayan abincinmu da tufafinmu an watsar da su can gefe gaba daya an watsar da komai. Tsaye nai ina kallon yadda kayan idona cike da kwalla, ba komai yasa ake mana haka ba sai rashin, rashi kuma na kudi saboda talaucin da yake tare da mu da kuma rashin kowa a kusa da mu. Lallai muhalli babban abu ne, da ace haya muke ko mallakinmu ne da wani be isa ya wulakanta haka ba saboda kawai mun raba a gidansa dan mu zauna.
“Ataa waya maka mana?”
Lukman ya tambaya yana bata fuska kamar zai yi kuka, ban da jansa jikina na rumgume babu abunda nai domin ina jin idan har na bude baki nai masa magana kuke kawai zai fito domin shine cike a zuciyata. Waiga nai banga kowa ba, da alama ba aikin yau ba ne idan kuma har yau akai shi tabbas tun da farar safiya aka zo aka mana haka aka tafi. Bani da wani zafi daya wuce na share hawayena na shiga hada tarkacen mu ni da Lukman babu inda zan kaisu gashi ni kuma ban iya hada bukkar ba balle na sake yin wata, Nana ce ta iya hadawa ita kuma tana asibiti, ance zuciyata tana ga mai kudi idan aka masa abu sau daya ba za akara ba, domin zai dauki mataki wanda bashi da shi kuwa sai ayi ta maimata masa kuma ya shanye yai hakuri saboda bashi da shi, ganin babu inda zan kai kayan yasa na hada komai na je can cikin wani daki da yake a kangon gidan da ba a karasa ba na saka su ni da Lukman sannan na fito waje na samo duwatsu na hada murhu na dauki jaran bukkarmu na saka na aiki Lukaman ya siyo mana ashana da taliya da cefanen dafa taliyar. Ni kuma na wanke tukunyar da mike girki da ita sannan na gyara tarugu da albasa na nufi gidansu kawata Farida dan na jajjaga, da nai sallama mahaifiyarta na ji taki ta amsa min a zatonta rokin wani abun na zo kasancewar wani lokacin idan ba mu da ashana ko gishiri tana aikawa tace ta sammata, har take yawan cewa wai mun cika roko, ni ko a ganina duk wanda zai mika maka hannu yace ka bashi tabbatas oa fishi kuma dan kana da shi ne ake zuwa nema a gareka amman mutane da yawa ba su fahimci hakan ba. Sai da na karasa har bakin kofarta ina sallamar sannan ta amsa min na gaisheta ta amsa ciki ciki.
“Dan Allah turminku za ara min zan jajjaga tarugu ne”
A tsaye ta bar ni a gurin na kusan minti biyar tana ta kallon arewa 24 a karamin tv ta sannan ta dago ta kalleni.
“Gashi can gidan kin gama ki dauraye”
Ta fada min a cikin yanayin da ke nuna alamar bata son ara min kamar yadda take yawan yi min idan na zo nema abu, shiyasa bana son zuwa idan ba Farida ce a gidan ba ita ce mai min maraba wani lokacin har ta tayani dakawa duk kuwa da irin fadan da mahaifiyarta take mata na kin jinin abotarmu da take. Ni kuma babu wani gida da zan iya zuwa na roki abu kamar irin gishiri ruwa ko ashana ko daka wani abu kamar wannan gidan, domin duka gidanjen da suke kewaye da mu na manyan mutane ne, a ina zan iya shiga roko ayi min kallo banza wani gidan ma ko gate din su ka taba sai mai gadin yace maka basa nan saboda kawai anga yanayinka na masu bukata ne.
Daf da zan gama jajjagen ne take tambaya wai ance maciji ya tsari mahaifiyata, ni kuma na amsa mata na kuma bata labarin yadda abun ya faru har ma da taimakon da aka mana a asibiti, sannan na kwashe jajjagen na wanke mata turminta kamar yadda ta bukata na yi mata godiya na juyo na fito.
Hura wutar na fara yi na dora tukunyar na zuba mai da sauran abubuwa a take saboda tsananin yunwar da nake ji, haka nai ta bankawa girkin wuta har ya dafu na zubawa Nana a wani kwanon mai murfi Lukman kuma na saka masa a nasa kwano na zubawa kaina, na kwashe saura a wani kwanon na rufe, sai na zauna na tisa abincin a gaba na kasa ci babu komai a zuciyata sai kewar mahaifiyata da tunanin ruguje mana bukka da akai, a take na nemi yunwar na rasa, kuka ya maye min gurbinta har sai da Lukman din ma ya fashe da kuka ganin yadda nake ta