Showing 12001 words to 15000 words out of 225640 words

Chapter 5 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

mika masa gaisuwa. Kai kawai ya daga musu ba tare da ya amsa musu ba sai kara hade fuska yake kar su ga damarsa.
Fitowa yai harabar gidan yana amsa kiran Rahma, da yai picking shiru yai har sai da ta fara magana cikin yanayin damuwa duk da irin faduwar da gabansa yai jin muryarta kamar tana cikin damuwa.

“Dear ina driving na kade wani”

“Hope babu abunda ya faru?”

“Ya ji mu a kafa da kai”

“Lafiyarki na ke tambaya”

Ya tambaya kamar maganar bata son fitowa daga bakinsa, sai dai tashin hankalin da ke zuciyarsa da burin jin lafiyar matarsa ya saka shi fidda numfashi kadan-kadan.

“I'm fine amman shi mutumen ya ji ciwo”

“As long as be mutu ba, ba wata damuwa ba ce, turo min address din inda kike yanzu”

Be jira abunda zata ce ba yai hanging, he don't mind ya tambayi inda zata je ko abunda ta je yi, saboda ya yarda da matarsa ko kasar zata bari bata fada masa ba ba damuwarsa ba ce indai zata je kalau ta dawo kalau. In few minutes ta turo masa sakon inda take sai ya forward massage din to the one of his bodyguard.

_Ka samu Madam a wannan address din, ka biya wanda ta kade ko dubu nawa ya ke so, and make sure matata ta isa gida lafiya_

Yana tura masa sakon ya mayarda wayarsa aljihu ya nufi motarsa yana wani shan kamshi.


ATAA POV.

Hankalina ya tashi sosai lokacin da na ga yamma ta gabato mahaifiyata bata ko matsa ba balle ta bude ido, ban san kan aikin asibiti ba, amman a yadda na ke jin ana cewa ko tiyata akai wa mutum indai ya kwana ya wuni yana farkowa sai dai tawa uwar shiru. Ina ji ina gani yunwa ta saka ni a gaba tana ta cina ni kuma na gagara kai ko da ruwa a bakina na natsu ina ta sauraren kukan da cikina ya ke min. Shiru shiru babu wanda ya sake leko dakin likitan be dawo ba, sai da yasa an aiko mana da abinci dare, a nan Lukman kawai ya ci ni kasa ko da kallon abincin balle na kai hannu na ci.
   Bayan na gama sallah isha'i ina ta kaiwa Allah kukana, sai na hango Nana na motsa har tana yawo da kanta, da sauri na mike na tsaye na rika gadonta ina kiranta cike da jindadi.

“Nana Nana Nana”

Shiru bata amsa min ba sai juya kan take yana dantsar baki kamar bata cikim hayyacinta, ban yi dabarar na je kiran nurse ba balle kuma likita sai kawai na daga zanen da aka rufa mata na ga inda aka mata dinki yana fitar da jini kadan-kadan  ganin hakan yasa na fita daga dakin da sauri na nufi wani dan guri mai kamar reception inda nurses da yawa maza da mata suke tsaye wasu kuma a zauna.

“Mama ta ta motsa amman bata magana kuma na ga jini gurin da aka mata aiki”

Na fada cike da damuwa, sai duk suka tsaya suna min wani kallo kamar na kyama, a nan na kalli tufafin jikina hakika na yi dauda sosai tufafin da ke jikina wadanda na saba sakawa ne kullum, kuma ba damuwa nai da na wanke ba, gashi dazu na ji girki da kara sun kara datti, sai dai ba da dauda na ke a yanzu ba ta lafiyar Nana na ke. Daya daga cikinsu taja tsaki kamin ta aje biron da ke hannunta ta nufo ni tana fadin.

“Ni Wallahi ba son irin kazaman patient din nan na ke ba, idan kuma ba ka kula su ba ace ba ka yi aikin ka ba”

Sai sauran suka saka dariya, sai duk na ji na muzanta na ji babu dadi amman hakan be hana ni binta a baya ba ita kuma tana gaba har muka shiga dakin.
https://chat.whatsapp.com/HlKVwXU1HwlIrs8jJeHHqZ

*Z A K I*

By Khadeeja Candy


6️⃣

ALIYU POV.

Kamar kullum idan zai kwanta sai ya tsaya ya duba wasu abubuwan a laptop dinsa haka ma idan ya tashi da safe musamman abubuwan kamfaninsu na samar da gas wato Sky Global Resources, babban kamfani ne da babu irinsa a nigeria wanda ke samar da gas da man fetur da ma hako wasu ma'adanai na kasa da saffara su, kuma shi yake wakiltar babban reshensu da ke Abuja inda ake tura komai, hakan yasa dole komai rashin lokacinsa dole ya matse a haka ya kula da wasu abubuwan.
A dakinsa ya ke amman ko'ina n dakin kanshin expensive perfume din Rahma yake, yana daf da rufe laptop din Rahma ta turo kofar dakinsa ta shigo hannunta rike da mug, bakinta ya sha janbaki har kyali yake, wata rigar bachi ce a jikinta mai kamar rariya, komai na jikinta a bayyane yake kamar ma bata saka ba komai ba. Dagowa yai yana kallon yadda ta nufo shi tana wani irin taku kamar kwararriyar karuwa, da fuskarka ta miskilanci, a lokacin da ta karaso kusa da shi sai ta kurba ginger tea dake cikin mug din a bakinta ta saka dayan hannunta ta dauke laptop din dake jikinsa ta aje gefen gadon da yake zaune ta raba kafafunta biyu ta hau saman cinyoyinsa ta juye masa tea a bakin. Murmushi yai bayan ya hade tea ta karbi mug din hannunta ya aje kan bedside drawer ya wutsilo da ita saman gadon ya zama na shi ne a samanta yana ta kallon bakinta wanda ya sha janbaki.

“Kin san lafiyar jikinki bata ishe ki ba, amman sai neman fitina, idan kuma na biye miki ciwon ki ta shi ko?”

Ya fada mata kadan kadan kamar mai rada yana ta yawo da cat eyes dinsa a fuskarta. Murmushi tai ta san halin Ali Zaki baya wasa da wannan bangaren komai fushin da yake ko damuwar da yake ciki, duk miskilancinsa da jin kansa indai ta wannan bangaren nan na da nan za'ayi saurin kama shi.

“Ina ta tunanin abunda zan yi na saka maka ne, Aliyu kana kokarin kawarda duk wani abu da zai taba ni, a sadakar a lokacin da likitan nan ya fada min cewar kidney ta daya ta samu matsala, bayan kuma an cire daya, na dauka mutuwa zan yi amman gashi yanzu za amin dashen wata na samu lafiya”

“Komai zan miki Dear, na yi magana da Doc Asim dazu da rana har ya hada ni da likitan da za muje UK tare da shi, In-Sha-Allah within week din nan za mu gama duk wani shirye-shiyen sai muje can a saka miki, i will pay Doc Asim a huge of money saboda wannan abun da yai min, zan yi masa godiyar saving a billionaire naira wife”

Ya fada yana kissing din wuyanta, tare da saka halshensa yana wasa da gurin.

“I promise you idan kika samu lafiya ba zan raga miki ba”

Ya fada sound so sexy kamin ya shiga aika mata da sakwanni masu zafi.......



ATAA POV.

Lokacin da nurse din ta shigo ta dubata sai ta kalle a hartsine ta ce.

“Farkawa ne za tai, kuma wannan jinin ai dole ya fito tunda jiya akai tiyatar be gama bushewa ba”

Nurse din ta fada kamin ta kalleni.

“Ga ki kyakkyawa kin maida kanki kazama”

Ko kadan ban kula wata maganarta ba, wani dadi na ji ya lullube ni jin cewar farkawa ne Nana za ta yi, sai raina ya fara fari, wani irin shauki ya kamani na ji kamar na taba ta tai magana, ina ta kallon Nana kamin na maida dubana gurin Nurse din yadda ta saka tufafinta da yadda take aikinta sai ya burgeni daman na dade ina ganin sha'awar aikin likita ko unguwar zoma amman ba ni da wannan halin hali saboda ba ni da wannan gatan na karatu, wa na ke da shi da zai tsaya min nai karatu har na kai ga zama nurses ko likita? Ni da karatun secondary ma ya gagareni sai bara da aikin titi.
  Bayan ta fice na zauna a kujerar dake facing dinta Lukman kuma yai kwance kasa yana jin bachi, ido na kura mata tun ina kallonta da kyau har bachi ya soma sata na, shigowar likitan ce tasa na Nana tana bude idonta tana rufewa kamar bata san inda take ba. Ni nai saurin mikewa tsaye likitan kuma yai saurin karasowa kusa da ita ya shiga dubata sai na ga yana ta murmushi.

“Masha-Allah tiyata ta yi kyau, na sunanta?”

“Nana”

Na bashi amsa ina wani irin murmushi da ke bayyana irin farincikin da ke raina. Sai ya shiga kiran sunanta cikin ikon Allah da iyawarsa ta amsa muryarta can kasa kasa.

“Na'am”

“Sannu”

Ya ce da ita a lokacin da ta kalleshi. Sannan ni ma na fada.

“Sannu Nana”

Sai ta kalleni ta gyada min kai sai kuma ya dan dago kan kadan ta kalli cikinta da ke lullube da zane.

“Ina Lukman”

“Gashi yana bachi”

Na bata amsa da sauri.

“Waya kawo ni asibiti?”

“Ni na kawo ki maciji ne ya tsare ki, shine wannan likitan ya taimaka ya miki tiyata ya cire miki dafin kuma yai miki allura ya siya miki magani”

“Allah ya saka da alheri”

Ta fada daker tana kallonsa. Sai ya cire mata wasu abubuwan da ke jikinta ya kalli Lukman.

“Bari a samo muku abunda za ku rika kwana ko, ba ki san ana dauka cuta kasa ba da za ki bar shi ya kwanta”

Na yi shiru bance komai ba, shi kuma ya juya ya fice daga dakin. Be jima ba ya dawo tare da wasu masu sharar asibitin su hudu ko wannensu dauke da abubuwan bukata, tabarma ce da babban bargo da filo da kuma buta da carpet din sallah, dayan kuma abinci ne ya kawo mana. Wallahi sai na rasa da wanne baki zan yi ma likitan nan godiya da irin dawainiyar da yake da mu ko da shi ya haifi Nana iyaka kenan yadda yake kashe mana kudi sai ka ce ya sanmu.

“Za a kawo muku kayan tea gobe, ai kin iya gada shayi ko? Sai ki rika hada mata tana sha da fruits”

Ya fada bayan mutanen masu shara sun fita.

“Dan Allah ya sunanka?”

Na tambaya cike da fargabar yadda zai amsa min.

“Ina son na rika saka ka a addu'a ta ne idan nai, irin alherin da kake mana yayi yawa kana ta dawainiya da mu kamar ka san inda muka fito”

Kallo yai n wasu yan mintuna kamin ya dauke kansa tare da wani guntun numfashi ya ce.

“Ba komai ba sai kin min addu'a ba, Allah zai ba ni lada ai”

Yana fadar hakan ya juya ya fice, ni kuma na bishi da kallon kauna kauna irin ta wanda ya taimake ka a halin da kake da bukatar taimakon. A dare Nana ta dan ta6a fira da ni tana tambayar abubuwan da ke mana ina ta fada mata ita kanta tai farinciki sosai kuma tai masa addu'a sannan ta sha kankana kadan kamar yadda ya umarta, ni ko a daren sai da nai tas na ci na koshi sannan na kwanta kan shimfidar da ya kawo mana ni da Lukman, kusan sai na ce ban taba kwanciya akan wani abu mai dadi makamancin katifa ba irin yau.
Tun daga lokacin kullum Nana cikin kara samun lafiya take, ni da Lukman kuma ba mu kara zuwa bara ba, kudin daya bani tun a karon farko ma ban sake taba su ba domin komai na ke bukata yi mana yake babu abunda muke yi da kanmu tun kama daga abinci magani da duk wani abun bukata. Sai dai abu daya yake ta bani tsoro, yadda Nana ta gagara komawa daidai, motsi kadan sai ta rike kirjinsa ko gefen cikinta ta ce ciwo yake mata kuma tana yawan fadawa likitan amman sai ya ce ba wata matsala ba ce zata ji sauki nan gaba kadan. Mutanen da muka zaman arziki da su suna ta zuwa suna duba Nana, kusan sai na yi sati ban leka gida ba idan ma wanka zan yi sai na yi a bandakin da ke dakin, daman can kuma wanka ba damu na yai ba, iya kar kokarin da na ke a yanzu na tsayar da sallah a kan lokacij ne ganin bana aikin komai a nan asibitin sai zama, Nana ma ina kokarin ganin na saka ta yi duk kuwa da irin kin son taba ruwa da take ko da na zafi ne yanzu sai ta ji jikinta ya kara rashin karfi, ganin hakan yasa na samo mata kasa na koya mata taimama kamar yadda aka koyar da mu makarantar islamiya lokacin da na ke zuwa.
Kullum cikin yi ma likitan nan da ban san sunansa addu'a muke ni da Nana, yana kulawa da mu sosai, ba dan rashin lafiyar Nana da ke cikin raina ba da Allah kadai yasan kibar da zan yi akan abubuwan dadin da muke ci, sai dai Nana kan ta kasa komawa yadda take a da, walwalarta kuzarinta da kuka sakewa ta kasa yi kusan kullum sai rama take daman can ba wani jikin ne da ita sosai ba.
Wasa wasa muka kwashe wata daya a asibitin, har zaman ya fara gundirata ita kanta Nana da ke ciwon sai ta fara gajiya, kullum addu'ar Allah ya bata lafiya mu bar asibitin, kowa mamaki yadda dafin macijin ya zame mata haka ake yi, ko da yake likitan ya fada mana cewar dafin ya warke ciwon cikin cikinta ne kawai ya rage ya warke. kusan sai na saba da nurses din da ke dan shigowa duba wani lokacin amman masu sake fuska a cikin, sauran kan sai dai su yi min kallon banza, da kuma mutanen da ke zam waje harabar asibitin suna jinyar wasu, domin idan na gaji da zama cikin dakin da take sai na dauko tabarmar nai shimfida a waje ni da Lukman mu zauna, har ita wani lokacin Nurse Shukura tana fitowa da ita ta sha iska, duk a cikin Nurse din Shukuwa ta fi sake min sai dai a yadda na lura kamar shi likitan baya son shirinmu da ita, wata kila akwai rashin jituwa a tsakaninsu ne ko kuma wani abun oho, domin na lura da ita ma kamar bata jindadin yadda muke yabonsa muke saka masa albarka da addu'ar alheri.
Haka nan kawai wani lokacin idan bata aikin komai sai ta shigo dakinmu mu yi ta fara kamar mun saba, ta haka har na san unguwar da take zama wato tudun wada da kuma inda ni ma nake zama har take ce min tana da wata kawa a kusa da mu, akwai ranar da take fada min cewar tana tausayina ni da Lukman jin cewar ba mu da kowa a nan Nigeria ko ma muna da su ni ban sansu ba, domin Mahaifina be tana fada min ba Nana ma bata nuna fada min ba, har take ce min ya kamata na nemi yan'uwa ko'in suke saboda wata rana. A lokacin na samu Nana na tisata a gaba ina tambayar wasu daga cikin yan'uwanta har take fada min harma da na Babana ma.
Misalin karfe biyu da yan mintuna na fito daga dakin na nufo gurin da muke zama a harabar asibitin inda shuke-shuke na zauna. Ban yi minti hudu da zama gurin ba sai ga kawata Farida ta zo, na jidadin zuwanta domin yau harabar babu mutanen da muka saba fira wasu an sallame su wasu kuma suna ciki gurin kula da masara lafiya, wadannn bakin fuskar kuma sun tsare ni da idonsu, dukuwa da nasa wannan kallon baya rasa nasaba da irin kyauna da kuma manyan idanuwan da Allah yai min haka zalika gashin kaina, shiyasa ba kasafai na ke son yin alwala a waje ba sai gaka hankali kowa ya dawo kaina duk da kasancewar gashin nawa a cinkushe yake guri daya har wani warin tsami yake, domin ba kitso nake masa ba idan am anyi kitson sai warware saboda sulbin gashi, kuma ba damuwa nai da na wanke ba balle har na shace shi ko na gyara.
Dambun da suka na masara ne ta riko mana, duk da kasancewar bana jin yunwa amman hakan be hana ni ci ba domin ina son dambu kusan duk wani abu da za a sarrafa shi da masara ko shimkafa ko dawa ina sonsa. Na ci dambu da yawa saboda yajin da aka cika a ciki domin ni ma'abociyar cin ya ji ce sosai, bayan mun gama fira ta shiga ciki ta duba Nana tai mata ta jiki sannan ta fito na rakota har bakin titin ringin sambo ina ta jin kamar na bita dan har ga Allah zaman asibitin ya fara ci min rai. A hanyata ta dawowa ne na hadu da Nurse Shukura tana sanye da uniform dinta amman ta dora bakar abaya sama ta rataya jakarta da alama ta tashi daga aikin ne zata tafi gida.

“Anty Shukura kin tashi ne”

“Eh sai kuma gobe, na kika fito?”

“Wallahi kawata na raka ina jin kamar na bita, zaman asibitin nan na ishemu”

Na fada ina yar dariya kadan, sai tai murmushi ta ce.

“Zama kan ai yanzu kuka fara tunda har kika ga Doc Asim ne yake kula da ku, in ma kina son mahaifiyarku ta samu lafiya to ki dauke ta daga asibitin nan ki kaita wata ko ku koma a gida, idan ba haka ba Wallahi za ki iya rasa mahaifiyarki asibitin nan ballantana yana ganin ba ku da kowa kin ga asirinsa rufe ba wanda zai san dalilin mutuwar mahaifiyarku”

Hankali na tashi da ji kalamanta har ya kasa boyuwa a fuska ta.

“Me kike Nufi Anty Shukura?”

“Bana nufin komai kawai baki ganin ciwon mahaifiyarki na ki ci ya ki cinyewa kullum kuna nan, ai ya kamata ki yi tunanin canja mata asibiti, kuma karki ce ni na baki shawara idan kin tashi kawai ki ce ke kin gaji gida za ku koma, Wallahi da masu kudi ne ku ko masu yan'uwan da yanzu an yi tunanin wata hanyar daban amman ba zama haka nan ba har kuna kokarin shiga wata na biyu asibitin nan, akan saran maciji kawai haba Ataa ke ma ai ya kamata ki yi tunani”

Tana gama fadar hakan ta yi wucewarta ta bar ni nan tsaye ina ta nazarin maganganunta, gaskiya ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login