Showing 9001 words to 12000 words out of 225640 words

Chapter 4 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

kuka. Abincin na aje na shiga ciki na daukowa Nana riga da zane na saka a jakar da kudin suke ciki na jira Lukman ya gama cin abinci ya wanke hannunsa sannan na dauki abincin Nana muka fito bakin titi na tari Napep muka shiga ni da shi muka doshi asibitin.




ALIYU POV.

Bachi Rahama take ta yi tun bayan sallah asuba har goma ta gota, a saman wani katon gado mai tsada da katifa mai kyau take kwance, ta lulluba da blanket mai laushi kamar kada, ta saba da hutu da jindadi haka take bachi har sai ta gaji dan kanta ta farka.
A lokacin Aliyu na falo zaune saman wata lallausar kujera rike da kofin tea laptop a saman ciyoyinsa yana duba yanayin yadda aikin gas din kamfaninsu na Abuja yake tafiya. Sanye yake da short jean da farar vest, a gabansa wani katon tv ne mai dauki da farar baturiya tana watso labarai a channel din Al Jazeera. Wayar ce dake silent tai haske sai dai be lura ba, domin ya cire ringing din, baya so hayaniya ko kadan that's why he choose Abuja a gurin aikinsa to because its a quiet place for him, ko da wani meeting din ne ya taso wanda yasan za a iya hayaniya da cece kuce sai ya tura abokinsa Umar. Be lura da kiran ba har sai da ya gama abunda zai yi ya juya da zimmar aje laptop din sai ya hango wayarsa tana haske, hannu ya kai ya dauki wayar ganin Doc Asim yasa shi sauri picking.

“Hello Doc”

“Ranka ya dade ina ta kira baka dauka ba”

“Yeah ina wani aikin ne, sai yanzu na lura”

“Na kira na maka albishir ne cewar an samu Kidney din”

Kofin tea dake hannunsa ya aje ya mike tsaye da sauri cike da farinciki marar misaltuwa har ya saka shi kin yarda da maganar da Doc ya fara masa sai da ya sake tambaya duk kuwa da yasan be taba masa karya ba.

“Doc are you serious?”

“Wallahi da gaske nake, gani nan ma gurin Alhaji abunda muke tattaunawa kenan”

“Wow gani nan zuwa”

Yai saurin waje wayar ya nufi bedroom dinsa cike da farinciki, labulayen dake fuskarta gadon ya bude sai ga hasken rana yana haske gadon kasancewar gaba daya gaban dakin glass ne. Jin hasken rana yasa ta lunkumewa cikin blanket tana bata fuska, sai ya zauna bakin gadon ya yaye blanket din ya dagota.

“Dear wake up yau ranar farinciki ce”

“Ba yau na ke birthday ba sai next month”

Ta fada ba tare data bude idon ba.

“Ba maganar birthday za ki yi birthday cikin koshin lafiya In-Sha-Allah, Doc Asim ya kirani ya fada min yana gurin Daddy suna tattaunawa an samu Kidney din”

Ba idonta kadai ta bude ba har da baki da da hancinta duk a bude suke jin wannan daddan labarin, da sauri ta kama hannayensa.

“Dear da gaske”

Ya gyada mata kai yana kallonta da cat eyes dinshi sai ta rungume shi da sauri ta fashe da kukan dadi. Dan murmushi yai kadan ya shafa bayanta.

“Congratulations Dear you save me”

“I said i would”

Ya fada yana dagota daga kirjinsa yana share mata hawayenta.

“Tashi ki shirya zan kaiki gidanku ni kuma na wuce gurin Daddy na gana da likitan naji yadda za ayi”

“I love you”

Ta fada tana kuka, sannan ta daga daga jikinsa ta sauka ta shiga bathroom ta sauka cikin kankanen lokaci ta fito shima ya shiga yai ko daya fito har ta shirya, shima be dade gurin shiryawa ba dan ya matsu ya hadu da likitan.

“Idan munje can zaki karya promise?”

“Promise”

Ta fada tana saka bakinta cikin nashi, musanyar yawu sukai halshenta da nashi suka hada auratayya sannan ta sake shi ya rika hannunta suka fito tare. A tare suka sauko kasa hawayen farinciki tana cika idonta, har ya bude mata motar ta shiga sannan ya zagaya ya shiga ya yai mata key tun kamin yai horn mai gadin ya bude masa gate suka kama hanya gidan Alhaji Nasiru Gobir.
Cikin kankanen lokaci suka isa gidan nan ma horn daya yai aka bude masa gate, tun kamin yai parking Rahama ta bude motar ta fita ta shiga cikin gidansu da sauri, shi kan sai da ya faka motar sannan ya fito ya rufa mata baya. A falo ya sameta tana zaune kusa da mahaifinta.

“Daddy naga kamar kana cikin bacin rai”

“Wallahi wasu wulakantaccin mutane suka shige min a gidan da nake ginawa a Clapperto road, ance sun janyo har macizai suna shiga gidan, amman na ce a korasu”

Hannunsa ta kama.

“Daddy kar wannan ya dame ka yau rabar murna ce na Doc Asim ya kira wai an samu kidney din”

“What”

Gaba daya suka amsa har kanenenta suka taso ta sauri suka rumgume ta suna ta murna. Alhaji Nasiru ya kalli Aliyu irin kallon ganin kima da kauna ta suruki da surukinsa.

“Mun gode sosai Aliyu Allah ya saka da alheri”

“Karka damu Alhaji aikina samawa Mamata lafiya ko ta hali yaya, zanje gida san na samu ganawa da likitan”

Daga haka yai musu sallama ya fito ya shiga motarsa ya dauki hanyar family dinsu wato gidan Alhaji Garba Fayau...



_________________

Wayyo Ataa 😪
https://chat.whatsapp.com/DaDP34cM3s5FMfaQOtFM9Y

*Z A K I*

By Khadeeja Candy


5️⃣

Ko da mu ka isa asibitin ana ta mopping ko'ina, ni da Lukman muka rakube kamar sauran talakawa irinmu, wadanda suka tsaya suna jira a gama mopping din sannan mu wuce, masu hannu da shuni kan da masu galihu wucewa kawai suke ba tare da n tsayar da su ba, masu aikin sai mika musu gaisuwa suke.
Mu kam mu kai tsaye har aka gama mopping din sannan na mika kafata na taka sai wata daga cikin Nurses din da suke tsaye a can babban kofar shiga ta daka min tsawa data saka hantar ciki ta kaďawa.

“Ke ki ka fi kowa a nan ne da za ki tsallako ki wuce gurin be gama bushewa ba”

Da sauri na koma baya na tsaya gurin da na ke tsaye dazu, sosai tsawar nurse din ta firgita, da alama idan na sake taka gurin zuwa za tai ta mareni. Ina rike da hannun Lukman da jakar dana sakawa Nana tufafin dana dauko mata, Lukman kuma na rike da taliyar da ke cikin kula mai murfi dabam kular ma dabam. A haka muka tsaya a gurin kamar wasu marayu har gurin ya gama bushewa, da na ga wasu sun fara takawa sannan muka taka muka doshi ciki, sai kuma muka tarar dan cikin ward din be gama bushewa ba wani gurin ma a yanzu ne ake mopping din.
  Dan Albarkar likitan nan yana tsaye da wasu nurses suna masa wani abu a takardu, yana hangomu ya ce mai mopping din ta tsaya mu wuce, cikin sauri ta tsaya muka fara takawa zuwa inda dakunan suke, wani dadi na ji ya lullubeni ko ba komai ya nuna min karamci da kulawa a matsayina na ba kowa ba, a take na ji kimarsa da darajarsa ta karu a idona. Sai da na gaisheshi sannan na wuce dakin da Nana take ciki, nurse din nan ta jiya na tarar wacce ta ce rika girgiza min kai lokacin da zan saka hannu a takardun da aka yi wa Nana aiki.

“Ina kwana?”

Na gaisheta cikina cike da tsoro gani nake kamar ita tsawar zata daka min kamar waccan nurse din. Sai na ga ta amsa min da lalama tana min kallon tausayi.

“Lafiya kalau, wannan matar mamarki ce”

“Eh mamata ce”

“Ina Babanki ya ke?”

“Baba na rasu?”

“To waya kawo ta asibiti?”

“Ni na kawo ta”

“Ba ku da kowa nan ne?”

Na dan yi shiru ina nazarin irin tambayoyin da take min da suka yi kama da wadanda likitan can yai min dazu, ban san dalilin da ya saka suke son yi min irin wadannan tambayoyin ba. Har na bude ba ki na bata amsa sai ga likitan nan ya turo kofa ya shigo yana waya baki har kunne sai dariya yake, sai dai ganina da wannan nurse din yasa yai hanzari katse wayar ya hade fuska kamar be taba dariya ba.

“Me kike a nan?”

Sai nurse din ta sha jinin jikinta ko motsin kirki bata yi.

“Na na na... Zo duba... Ta..”

“Ke duba ta ke kika aje ta? How dare you? Fita ki ba ni guri”

Kamar zata 6ace 6at a gurin haka tai saurin ficewa jikinta sai rawa yake kamar mazari, a nan nima na shafawa kaina lafiya fahimtar cewa yana da fada sosai na koma gafe ni da Lukman muna kallonsa. Yana kallona sai ya sake fuskarsa yai min murmushi yana kallon jakar hannuna.

“Miye a ciki?”

“Kudin da ka ba mu ne, da tufafin da ka ce a daukowa Nana”

Na amsa cikin tsantsar ladabi da kuma muryar da ke nuna babu ruwana.

“Wannan fa”

Ya sakw tambaya yana kallon kular da ke hannun Lukman.

“Taliyar da na dafa ce na kawo ma Nana ko za ta ci”

Dariya yai yana kallon murfin kular da ke daban da kular wacce ta soma koredewa wani 6angare na jikinta ma har ya tsage.

“Ya ma sunanki?”

“Ataa”

“Ataa karki sake kawo abinci a nan asibiti, zan sa a rika kawo muku na safe da na rana da kuma na dare ke da kanenki da kuma Mahaifiyarku idan ta farko kinji?”

“Da gaske?”

Na fada ina kara girmama kirmarsa lallai a cikin dubu samun mutum kamar wannan likitan mai tausayi da taimako sai an tona.

“Yes”

Har kasa na kai idona cike da hawaye ina masa godiya kamin na koma yi ma Allah godiya daya hada mu da irin wannan mutumen. Karasa yai ya duba Nana ya canja mata wasu abubuwan na na'ura sannan ya juyo ya kalleni.

“Ina tufafin suke?”

“Ga su”

Na mika masa da sauri a zatona saka mata zai yi sai naga yai baya da sauri kamar mai kyama.

“No no bari na kira wata ta saka mata”

Daga haka ya juya ya fice, ni kuma na kuma kusa da ita na tsaya ina ta kallon fuskarta ga ta a kwance kamar ta mutu, amman fuskarta na kyalli kamar zata bude baki tai mana magana.

“Ataa yaushe Nana zata tashi?”

Lukman ya tambaye ni yana kallonta.

“Ni ma ban sani ba”

Na amsa masa idona taf da hawaye tausayin mahaifiyata ya cika zuciyata, na san Allah ne ya kaddaro mata haka amman macijin nan be kyauta min ba. Ina tsaye wata mata mai zubin marasa mutuncin ta turo kofar ta shigo fuskarta ta tsage tana sanye da uniform din nurse sai wani kallo take watsa mana a hankade.

“Ke kamar ki za ki ace ba ki iya sakawa mahaifiyarki riga?”

Ta fada tana fisgar rigar a hannuna sannan ya karasa gurin Nana, yadda ta saka hannu ta tallafota sai ta tsikar jikina ta tashi dan zaka rantse da Allah ka ce karamin yaro ta dauka, a gabana gaban Lukman ta janye mayafin da aka rufe Nana da shi ni da Lukman muka ganta tsirara haihuwar uwarta ga dinki a cikinta gurin yayi ja sosai kamar jini ya kwanta, da sauri ya juyar da fuskar Lukman ni ma na juya muka ba ta baya hawaye na sauko min, ban juyo ba sai da na tabbatar ta gama ta rufe mata zane har na watsa min wata magana marar dadi jin.

“Tufafin ma duk ďoyi suke yi mtswwwww”

Ni dai ban ce mata komai ba na karasa gaban Nana ina kallon yadda yake ya mutsa fuska duk da kasancewar bachi take ko kuma ma na kira shi da suma, da alama taji zafin yadda nurse din ta motsa ta, ji nai kamar ace ina da wata dama da zan bawa ciwon umarni ko kuma na saka hannu na dauke mata shi ta farka ta tashi mu bar asibitin nan, ga dukan alamu likitan nan ne kawai mai mutumci sauranka ko kallo ba mu ishe su ba. A kujerar da ke gaban gadon na zauna ni da Lukman sai ya kwanto jikina kamar wani maraye yana ta tabe baki alamar zai yi kuka, ni kan daman hawayen kawai na ke ina jin wani abu ya tsaya min a zuciyata.
  Kamar yadda fada haka kuwa akai misalin uku saura na rana aka aiko mana da abinci irin na manyan restaurant mai dadi har da naman kaza, a take Lukman ya hau murna jikinsa har rawa yake ya dauki naman kazan ya kai baki, ni kan sai na ji bana son cin komai duk kuwa ni da irin kwadayina. A bandakin na shiga nai alwala nai shimfida dankwalina nai sallah azahar, babu komai a sujida ta sai rokon Allah ya bawa Nana lafiya.
  

ALIYU POV.

  Yadda ya ke driving sai ka rantse da Allah ba jiransa ake ba, hankalinsa a kwance yake tukin motar yana tafiya kadan-kadan duk kuwa da irin son ganin Doc Asim da yake. A ka'ida ba ya danna horn sau biyu sau daya ya ke yi amman wannan karon sai da ya danna har sau uku sannan mai gadin ya bude masa gate, tsayawa yai dai-dai gurin mai gadin ya sauke gilashin motarsa yana watsa masa wani kallo na marasa ganin talaka da daraja ya ce.

“Kar ka yarda na sake danna horn har uku ba ka bude min gate ba”

“Ayi hakuri ranka ya dade, Wallahi na dan zagaya ne”

Dattijon mai gadin ya fada jikinsa na rawa.

“An aje ka nan ne dan ka zagaya?”

“Ina nufin bandaki na shiga”

“Kai ya shafa ni dai na fada maka next time korarka za'ayi”

“In-Sha-Allah hakan ba zai sake faruwa ba, ayi hakuri Zaki”

Uffan be sake ce masa ba ya faka motarsa a harabar gidan sannan ya fito yana ta kanshin turaren da ke sanar da zuwansa ya shiga falon. Khaleesat da Hauwa na zaune a falon ko wace rike da waya, ganinsa yasa sukai mugun shan jinin jikinsu suka natsu sosai ko kallon inda yake ba sa yi gudun kar ya su hada ido da shi ya ce sun masa ba dai-dai sun san shi sarai ya tsani kallo.
Ganin Momy da Daddynsa yasa ya saki fuska ya cire talkamin kafarsa ya karasa kusa da su da sallama. Dukansu fuskarsu dauke take da murmushi da alama suna cikin jindadi da farinciki.

“Dan wajen Fulani ka yi lattin zuwa likitan kuma ya ce yana da aiki da yawa a asibiti be tsaya jiranka ba ya tafi”

Momy ta fada tana kiransa da sunansa da ta saba kiransa.

“Ya ce min an samu kidney din”

Ya fada yana mikawa Daddy hannu su gaisa. Sai Daddy ya dora da

“An samu, na masa magana ya ce zai hada ku da wani likita da za ku je London ayi mata dashen”

“Samun Kidney ba abu ne mai sauki a yanzu ba, gaskiya likitan nan ya cancanci komai daga gurina, at long last Rahma zata samu lafiya”

“Ba daga gurinka ya cancanci komai daga garemu ma gaba daya, amman ina fatar ba ta wani ya cire ba, domin ba kowa zai yarda ya bada kodarsa ba”

Aliyu yai shiru kamar mai nazari can kuma ya kalli Mommy ya ce.

“Ba lallai ya zama haka ba, kin san Nigeria ce, akwai talakawan da ba su san darajar kansu ba, za su iya siyarwa saboda kudi”

“Amman ko talaka sai wanda talaucinsa ya kai makura gaskiya, ai sai da lafiyar ake neman kudi”

Momy ta fada with doubt. Aliyu yai murmushin kasaita.

“Momy kenan ba ki san talaka ba, na san Doc Asim zai iya siye zuciyar talaka da kudi ya samu abunda ya ke so, domin ya san shi ma zai fanshi fiye da haka a garemu, shi fa talaka wawan mutum ne, indai za ka nuna masa kudi to zai maka komai na duniyar nan”

“Wato ďan wajen Fulani kai da Maman ka Fulani ban san wanda ya fi wani kyamar talaka ba, su ma fa mutane kamar mu duka daya muke a gurin Allah”

Ya kalli Momy cike da mamakin yadda take hakikancewa idan ana maganar talaka.

“Momy kenan, ai Mama Fulani gaskiya ta ke fada, tsakanin mu da talaka sai dai akwai mu amfana da shi shi ma kuma ya amfana da mu ta hanyar biyansa hakkinsa, amman ni ko abota bana fatar ta hada ni da talaka”

Daddy yai murmushi yana dafa kafardar Aliyu ya mike tsaye.

“Sai ka yi hanzarin samun Doc Asim ku tattauna, kasan matsalar matarka ita dayar kodar na daf da daina aiki”

“Yeah haka za ayi, san same shi mu tattauna, Thank you Dad”

“Your Welcome”

Daddy ya fada yana nufar hanyar da zata sadashi da part dinsa. Momy kuma ta mike tsaye tana fadin.

“Talaka ba shi da kima a idonka kai da uwarka Fulani”

“To ai ba shi da kimar ne Momy ki ce kin ki gane sai hada shi kike da mu, bayan kuma ba daya ba ne, as long as ba da ganganci Doc Asim ya cire kidney din nan ba babu abunda zai dame ni, ni zalince ne kawai ba na so, indai na san na biya ka to dole ka min aiki ba wani uzuri da zan dauka, so indai siyenta Doc Asim yai ni ya kyauta min wlh kuma zan bashi fiye da abunda zai tambaya”

Ya fada yana mikewa tsaye ya nufi dinning area, wani kebantaccen guri ne da ya kusan ayi babban falo da shi amman ba a zuba komai a gurin ba sai kato dinning table da freezer, daya daga cikin kujerun dinning din yadi aja ya zauna yana kallon Momy wacce ta taso ta nufo shi tana fadin.

“Ba ka ci abinci ba ka fito? Matar ta ka har yau ba ta iya girkawa ta baka ba?”

“Momy kin san lafiya be isheta ba, kodar ďaya da ke jikinta ma ance ta fara lalacewa, so ba komai na ke bari tai ba, and Momy kin san wahala ai sai talaka”

“Au ni da nake shiryawa Daddynku fa?”

Murmushi yai kadan yana dora duka hannayensa saman dinning din.

“Ai ke Momy saboda kin kwana biyu ne, ke da kina da kurciya ai Daddy ba zai bari ki yi girki ba, i rather na yi oder a restaurant da nai forcing dinta ta girka min, besides ba komai ta iya girkawa ba ita a gidansu ba aiki take ba”

Momy ta tabe baki tana saka masa sikari kwaya biyu a kofin tea. Bayan ya gama karyawa ya sauko daga dan stairs din dinning din yana taba wayarsa ya nufi kofar fita kanensa na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login