Showing 21001 words to 24000 words out of 225640 words
tiyatar ne?”
“Aa cewa sukao maganin da kika sha ba shi ya kamata koli sha ba wai likitan be kware sosai ba”
A take naga hankalinta ya tashi, har fuskarta ta kara boyewa, nasan da na fada mata gaskiyar cewar kodarta aka cire wata kila zan iya rasata ma a nan take. Matsawa nai kusa da ita ina kokarin kwantar mata da hankali.
“Nana ki kwantar da hankalinki zan samu kudi zan biya a baki magani, kuma za ki warke za ki tashi, domin sun ce idan aka ba ki maganin za ki iya jin sauki a take”
Hawayen idonta ta share tana sauke ajiyar zuciya tare da saka dayan hannunta ta dafe gefen hakarkarinta.
“Nawa ne kudin maganin?”
“Dubu takwas ne kuma akwai ragowar dubu biyar a hannuna, kin ga dubu uku kawai za mu samo”
Na mata karya saboda hankalinta ya kwanta. sai ta lumshe ido hawaye suka sauko mata, ashe zubar hawayen mahaifiya yana da zafi da daraja a idon 'ya'yanta, domin a take na ji duk wani kuka nawa da na ke kokarin tarewa ya tafi sai na nemi rashin kuzarin na rasa, wani karfi da shaukin neman mafitar inda zan tsayarda da zubar hawayenta ya cika ni. Mikewa nai tsaye na juya da zimmar tafiya sai na ji Lukman ya kira ni.
“Ataa zan biki ni ma zan yi baran”
Hannuna mika masa ya mikon nasa na rika muka tafi daga ward din zuciyata cike da karsashi.
Babban titin Gawon Nama muka fara yin baran, ganin ďan abun da muka samu ba mai yawa ba, yasa na ja hannunsa muka nufi titin gadar Alu ganin can din kamar ya fi manyan motoci, misalin karfe daya muka isa gurin bani da agogon da zai tabbatar min da hakan, sai dai ganin yadda rana ta soma budewa tana yin zafi yasa na fahimci hakan, gashi kuma wasu masallatan har sun fara kiran sallah karfe daya. Muna tafiya Lukman na ta bata fuska da alama ya gaji da tafiyar da muke a kafa, daga ni har shi sai gumi muke na wahala.
Muna isa na nufi gurin wasu motocin shi kuma ya doshi wasu yana mika musu hannu, ba zan iya fadar abunda ya faru ba, iyakar abunda na sani an saki traffic motocin sun fara wucewa sai kuma na jiyo ihun Lukman da dukan karfinsa sai kuma na ji kaurar karafuna. Juyo nai a firgice ina kallon mutane da ke nufar gurin da sauri, wani irin kara nai da muryar da ban taba sanin ina da irinta ba, na saki kudin da ke hannuna na n ruga a guje ina haniniya kamar wani doki...
ALIYU POV.
Yana zaune sitting rooms dinsa yana duba wasu takardu da Nasir ya kawo masa tun daga Abuja domin ya saka hannu.
“A nan ma kai za ka wakilce ni Nasir, ba zan iya barin Matata a nan na tafi saboda aikina ba”
“Amman miyasa ba zaka dauke ga kuje can gaba daya, ai zaka iya kula da ita a can din ma”
Shiru yai few minutes kamar ba zai ce komai ba, sai kuma yai maganar cike da gundira kamar wanda ya shekara yana magana da wani.
“Yeah ita ce ta ki ta yarda wai ta fi son kusa da Familyn ta har sai ta ji sauki sosai sannan ta koma”
“Amman ai zaka iya convince dinta ta yarda ta bika”
Aliyu be sake ce masa komai ba, wayarsa da ke aljihu tai kara alamar sako, fiddo wayar yai ya duba.
_Na shirya kuma ina son ruwa_
Cikin sauri ya saka hannu ya mike tsaye yana kallon Nasir.
“Matata tana da muhimmanci a gurina i can't choose my work over her, kar ka sake min irin wannan maganar”
Yana fadar hakan ya jefar da takardun saman center table din dake tsakanin shi da Nasir din ya bi ta kofar ciki ya fito ta baban falon. Kai tsaye freezer ya nufa ya dauko robar ruwa ba mai sanyi sosai ba da cup ya nufi upstairs. Tana zaune bakin gado ta cancanda ado kamar wacce zata je gurin biki sa kanshim turare take.
“Princess you look cute”
Ya fada yana kokarin aje ruwan kasa tare da kai hancinsa ya shimshina gefen wuyanta.
“Kun kare meeting din?”
Ya gyada mata kai yana zuba ruwan a kofa.
“Nasir ya tafi?”
Ya daga kafadunsa alamar be sani ba, sannan ya kai mata ruwan a baki, kadan ta sha ta kawar da kai.
“Mu tafi yanzu”
Ta riga shi mikewa tsaye kamin shi ma ya mike ya riko hannunta suka sauko downstairs. Kadan kadan take tafiya kamar mai tausayin kasa har suka isa gaban motar ya bude mata ta shiga, ganin babu motar Nasir na tabbar masa da cewar ya fice. Front seat ta shiga shi kuma yaja motar tun kan ya juyo da motar mai gadin ya bude masa gate. Kai tsaye Family house dinsu Rahama ya fara isa ya aje, sai suka bude motar suka fito tare, tana gaba yana bayanta har suka shiga cikin falon yadda ta tararda fuskokin my siblings dinta ta san ba lafiya ba.
“Miya faru na ga fuskokinku a haka?”
Ta fada cike da faduwar gaba, tana kokarin zama kusa da kanwarta Razinatu.
“Wallahi one of those big shopping mall din Daddy da ke kano ya kone, ya ma tafi can tun da safe shi da Mommy”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”
“Saboda wannan tashin hankalin na ki yace kar a fada miki baya son ranki ya bace”
Cewar Razinatu sannan ta shiga sahun yan'uwanta da ke mikawa Aliyu gaisuwa, shi kuma gaba daya hankalinsa yana kan Rahma ganin kamar ta tashi hankalinta sosai.
“Dear”
“I'm okay, idan ka je ka ce ina gaishe da Momy kuma na mata naganar mai aikin”
Kai kawai ya gyada mata sannan ya juya ya fice wani shan kamshi. Yana shiga motarsa ya dauki hanyar family house dinsu daman yana jin cikinsa babu nauyi.
Ko da ya shiga falon ya tarar Momy na tattara littafan da jikokinta suka watsar wato kanenen Aliyu da akaiwa aure suka haihu.
“Momy barka da safe”
“Safe yanzu 12:13pm?”
Ta fada tana kallon katon agogo dake falon. Shi ma kallon tsadadden agogo hannunsa yai kana ya zauna yana fadin.
“Ban san ta yi ba, gaske na ji cikina ba nauyi”
“Matarka bata nan?”
“Tare muka fito da ita na aje ta gidansu”
Momy ta cigaba da tara books din ba tare da ta kara cewa komai ba, shi kuma yana ta kallo yanayinta.
“Anything Momy?”
Sai ta kalleshi.
“No nothing kawai ina tunani ya kamata ace ka ci abinci ne kamin ka fito”
“Momy yadda kike tunanin Rahma fa ba irin waennan 'ya'yan talakawa ba ne, duk wani aiki mai nauyi Rahma ba za ta iya ba, ko da can ma balle yanzu, kuma dacan Rahma tun da ta tashi a gidansu ba ta aikin komai bayan hutu saboda ciwon kidney din da take”
“Kuma bata iya zuwa gidan sukukanta ta gaishe su ba ko? Gidansu kawai ta sani sai gidan kawaye sai fita waje idan ta gaji da kasar”
Ya shafa kansa yana ta neman kalmomin da zai hada ya fahimtar da mahaifiyarsa ko wacece Rahma.
“Yana da wahala ka ga kafar Rahma a gidan nan sai idan wani abun ake muhimmi, shin bata san zuwa gida sukurukai gaishesu yana da muhimmanci ba? Ko ta dauka Fulani ce Real Mother dinka? Bata taba fada mata cewar ni na haife ka ba? Ko kuma tana ganin kamar bana jin zafin abun ne? Idan zaku zo hutu daga Abuja wani lokacin har ku kuma ba zata tako kafarta gidan nan ba, sai idan za ku tafi shi ma idan kuna tare,, balle kuma ta dauko wani abu ta kawo min ko ta aiko min, ba dan ina da bukata ba, amman kowa yana son kyautatawa”
Momy ta fada mishi with serious face. Mikewa yai tsaye ya nufi dinning ba tare da kalma daya ta sake fitowa daga bakinsa ba sai dai yadda yaga fuskar mahaifiyarsa ta cikinsa yasa shi jin babu dadi be taba daukar abun nan da Rahma take wani abu ba, a ganinsa Rahma ta riga ta saba da rayuwar turai ne, ita kuma Momy ta kasa hakan, ba kamar Mama Fulani ba da bata taba damuwa da shiga safgar Rahma ko da kuwa zata taka ta ta wuce ba dan komai ba sai dan tana ganin daga Rahma har ubanta ba su kai matsayin da zata iya kallonsu ba, domin ita bata huldu da duk wani mai kudin da baya isa amsa sunansa a birnin Abuja.
____________
Assalamu Alaikum.
Kwana biyu ban yi posting ba hakan ya faru ne saboda rashin lafiyar Kakata, amman yanzu Alhamdulillah, In-Sha-Allah posting babu kama hannun yaro.
And ina son nai amfani da wannan damar na sanar da ku cewar da zarar mun kai page 12 za mu tsayar da Free pages, hakan na nufi sai mutum ya biya sannam ya samu cigaban labarin, daman na fada tun a ZABIN RAI cewar littafin ZAKI na kudi ne, wadanda suka sani sun sani domin na fada, and ina yin littafi free, wanda zai zo bayan shi na kudi, kamar dai yadda RAI BIYU ya zo free HAFSATU MANGA (yarinyar K'auye) na kudi, haka ma ZABIN RAI free ZAKI na kudi.
Ga wanda suke son fara biya tun yanzu za su iya turo 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank. sai ku turo shaidar biyan wato screenshot ta wannan number 08036126660, 'yan nijar za ku tura 500f na line orange ko zain ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta wannan number 08036126660 Za'a saka ku Paid Group.
Thanks 🙏🏻
https://my.w.tt/PWohUhlPv9.
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
1️⃣0️⃣
Kamar wata mahaukaciya haka na rika ratsa mutane ina cusa kaina har na karasa inda yake, ihu yake ta yi yana rike da jafarsa yana jiran sunana.
“Wayyo Allah Ataa kafana wayyo ni kafana”
Babu jini a kafar amman yadda yake ihu cikin magagi ya fahimtar da ni irin ciwon da kafar take masa, ga gefen kansa sai jini yake yana ta wani jujjuya ido kamar zai shude.
“Ai wallahi Allah ya kara mutanen ba su da godiyar Allah, kullum cikin bara, da sun hango mota har sauri suke su mikawa mutane hannu, yara kanana an koya musu bara”
Shine abunda mafi akasin mutanen da suke gurin suke fada, masu ganin tausayinsa kadan domin sauran ta'alaka abun ne da rashin wadatar zuci irin na mu, na raba a titi da kaskantarta kai.
“Jama'a ku taimaka min kar ya mutu”
Shine abunda ya iya fada cikin kuka, sai daya daga cikin mutanen da ke tsaye ya zo ya dauke shi ya saka a mota wanda na ke kyautata zaton shi ya kade shi. Gidan baya ya bude min na shiga gurin da Lukman yake sannan ya bude mazaunin direba ya zauna na fisgi motar muka doshi specialist hospital wato asibitin daji. Muka isa aka wuce da shi layin yan hadari ni kuma na bi bayansu hankalina a tashe, sai da suka fada min cewar na je na karbo kati na tuna da kudin da suke hannu, ba ko tantama sun fadi tun a lokacin da hadarin ya afku, da sauri na fita emergency din zuwa neman mutumen ko zan ganshi ya taimaka min, sai na nemesa na rasa, wata kila shi kuma ya tafiyarsa. Komawa nai ciki ina rokonsu su taimaka su kula da shi kamin na kawo kudi sai suka ce min wai sai na zo da police za su iya taba shi, haka suka kyale Lukman a wulakance cikin gurin da duban mutane suke sai ihu yake. Ji nai kamar na je na dauke shi nai tafiyata idan kuma na dauke shi ban san inda zan kai shi ba, ba ni da wani magani da zan iya masa.
Tasowa nai na fito daga cikin gurin ina tafiya hawaye masu zafi suna sauko min, yanzu yan kudin da suka rage min da kuma wadanda mukai bara muka samu na zubar saboda kidima, ga shi Lukman ya bugu da mota ga Nana tana asibiti tana jiran na kawo kudin maganin da hoto. Wani abu na ji ya tsaya min a zuciya yana neman numfashina, a take tsayuwa ta gagareni, ba zan iya fadar inda na ke ba, iyakar abunda na sani na ji na zauna saman wani abu mai kamar kaya, sai kuma duhu ya rufe min ido har na soma jin kamar babu sauran numfashi a tare da ni.
Ban san iya awanin ko mintuna dana dauka a gurin ba, kamar wacce aka sakowa numfashi daga sama haka na farka firgigit ina maida numfashin wahala, baren kaina na ji yana min ciwo, gurin da na ke zaune sai sukana ake, hakan yasa na unkura na tashi tsaye sai na lura ashe saman fulawoyin na ke zaune masu kaya, da na soma tafiya sai na ji jiri na ďibata idanuwana kuma suna ta lumshewa kamar mai jin bachi. Haka na fito bakin gate din asibitin ina tafiya kamar marar lafiya, bakin titi na tsaya na tari wani mai Napep yana tare da wata mace a baya, yana tsawa na duka har kasa na hade hannayena ina rokonsa.
“Dan Allah ka taimaka min ba, kanene yai hadari mutumen daya kawo shi asibiti ya gudu ya bar mu, su kuma sun ce baza su duba shi ba sai na kawo police kuma ba ni ko kudin siyen kati”
“Yanzu me kike so?”
Matar da ke baya ta fada tana dage nikab din dake fuskarta.
“So na ke ka taimaka min na dauko shi na saka a ciki na kai shi gida”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, mutane suna ciki hali, ke yanzu kudin Napep din ma ya gagara? Allah ka ba mu karfi da ikon da za mu iya taimakon bayinka marasa shi”
Ta fada tana miko min dubu daya yan dari biyu guda biyar, sannan ya ciro dari biyu ta mikawa mai Napep din.
“Je ka kaita ni zan tari wata na shiga”
“Na gode Allah ya saka miki da alheri”
Tana fita na shiga zauna a ciki mai Napep din ya janyo ta ciki muka shiga har bakin kofar emergency. Da sauri na fita daga napep din na shiga ciki sai na same shi a inda na barshi, sai dai baya motsi babu alamar numfashi a tare da shi.
“Kun kasheshi, kun bar shi nan ba ku taimaka masa ba, ya mutu kun ji dadi”
Shine abunda na fada ina kallon nurses din ina hawaye kamar ba gobe, sannan na duka na saka hannuna biyu na tallabo shi na juyo na fito da shi mai Napep din ya taimaka min ya saka shi a ciki ni kuma na shiga, ina ta shafa fuskarsa ko zai farka amman shiru, can na kai hannuna gurin hancinsa sai na ji babu numfashi ba alamunsa.
Har muka isa Clapperto road kuka kawai na ke ina rike da Lukman, mai Napep din ne ya fito ya saka hannunsa ya dauko shi ya kai shi gurin da na nuna nasa wato cikin kangon gidan nan ya aje min shi sannan na saka hannunsa aljihu ya ciro dari biyar ya miko min.
“Gashi ku kara Allah ya muku mafita”
“Na gode”
Na Fada cikin muryar kuka. Sai ya juya cike da tausayawa ya fice, ni kuma na zauna a gurin ina ta kallon Lukman wai ko zai motsa amman shi, har hannuna na kai na dan matsa gurin kafar inda na ga yana riko dazun ko zai motsa amman shiru. Kaina na daga saman ina hawaye cikin daga murya irin da masu neman dauki nan cikin gaggawa na ce.
“Allah kai ka so haka a garemu, komai ya samemu da saninka ne da yardarka, Allah ka sani ba ni da wata mafita sai ta ka, Allah kana ganin halin da na ke ciki Allah ka kawo min dauki”
Sannan na tashi na je nai alwala nayi Sallah, ban tashi daga gurin ba, sai da na gabatar da sallah la'asar, sannan na mike tsaye ina murza kudin da ke hannuna zuciyata sai wani abu take min babu dadi, da kafa na taka zuwa asibitin uduth wannan karon babu masu gadin dakunan kasancewar la'asar, cike da nauyin kafa na ke taka ward din ina sakesaken abunda zan fadawa Nana, idan ma na boye mata dole zata san gaskiya, idan kuma na fada mata zata iya shiga wani hali sai na kasa za6a tsakanin fada mata da kuma akasin haka.
Kwance na sameta ba kamar dazun da na bar ta jingine ba, ban san hawaye na min zuba ba har sai da ta nuna fuskar tawa.
“Miya saka kike kuka Ataa? Wani abun ya samu Lukman ne?”
Saurin share hawayen nai ina girgiza mata kai.
“Aa babu abunda ya same shi”
“Karki boye min, fada min babu abunda zan iya da lamarin Allah”
“Mota ta kade shi Nana, kuma an kai shi asibiti amman baya motsi na dauko shi na dawo da shi gida, kuma kudin da na samu da ragowar duka sun fadi”
Kamar wacce aka yi ma allurar karfi da kuzari, haka ta tashi zaune kamar ba ita ba.
“Lukman din ya mutu ko?”
“Ban sani ba amman dai baya numfashi kuma yai ta ihu lokacin da aka kade shi ya rike kafarsa yana da kuka sosai”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u ”
Ta fada tana mikewa tsaye har mamaki ta bani dan zaka rantse da Allah cewar ba ita ce ke kwance malala dazun ba.
“Mu tafi”
Ta fada tana jan dayan zanen da ke saman gadon ta rufe jikinta. Ni kuma nai saurin rikata n zaunar.
“Ba za su bari mu tafi ba sai mun biya kudin gado Nana, ki zauna zan je samo wasu kudin na biyasu sai mu koma gida”
Zaunawa tai a saman gadon sai ta fashe da wani irin kuka mai taba zuciya. Ni kuma nai saurin fita daga gurin ina sauri kamar zan halde kafafun.
Lokacin da na fito bakin kofar asibitin sai na rasa abunda zan yi, wace hanya zan bi na samu kudi? Baran zan sake komawa ko kuwa sata zanje na yi ko mutuncina zan siyar, idan ma sata zan yi ina kudin suke da har zan sata? Ina mai siyen mutuncin yake da har zai siya, a nawa zai siya, mi zai biyo bayan wannan?
Wani tunanin ya zo min, da sauri ma tari Napep na shiga na ce