Showing 204001 words to 207000 words out of 225640 words
saboda su suna takalawa ne, tare da Mama muka tafi da kuma wasu daga cikin yan gida, akwai tafiya mai nisa sosai tsakanin unguwar da Sarkin yake da kuma inda su suke. Ko da muka isa rana ta bude sosai a unguwar su har sun sauke sallah azahar. A hanyar mu ta zuwa ne na ke labartawa Aliyu jawabin da sarkin yai abubuwan daya fada, domin duka maganganun da yai da yaren buzanci yai shi wanda kuma Aliyu ba ji yake ba.
Sai da aka fadawan ta Mai Martaba ya hado mu da su suka shiga aka sanar sannan mu ka bi baya. Gidan kasa ne gaba daya gidan, sai dai irin ginin nan ne na mutanen da wanda ake na iyali da yawa, wanda zaka samu wani lokacin har da jikoki ma a gidan. A gidan muka wuni ni da Aliyu suna ta kiran mutane a zo a ganmu wai yar Ummaruje ce kamar yadda take fada, tsohuwar ko gani bata yi sosai Nene na ke jin suna kiranta, ta yi farinciki sosai da ganin mu kuma ta yi kuka ita da duka yan gidan jin cewar Baba ya rasu, ba su kadai ba ni kaina sai da nai kukan tunawa mutuwar tasa, yau ga ji a gaban iyayensa amman babu shi. Sai da dare muka baro gidan a can muka ci abincin rana da dare da za mu dawo aka tasa min nonon rakuma saboda an bani na sha na jidadi har na roka. Kallo daya za ka ma fuskokinsu ka fahimcin cewar suna cikin farinciki da jindadi ganinmu, ban yi zaton Aliyu zai sake jiki kamar yadda yai a yau ba, fuskarsa na nan a yadda take babu wani walwala sosai Murmushin ma ba komai yake ba, amman ya sake jiki ta hanyar cin abincin da aka kawo mana da har ma da Nonon ragumin wanda ya fada ai yana shansa a gidan Mama Fulani wani lokacin tana siye ta aje. Duk kuwa da kasancewar an aiko mana abincin daga masarautar suna ganin kamar ba za mu iya cin wannan ba, wani abincin ma na san saboda Aliyu aka girka shi irin tuwon shimkafa miyar Allayahu da akai da man shanu ga naman kaji da garo a ciki.
Ba tare muka dawo da Mama ba domin ita tana gama gaisawa da su ta dawo gida, wai bata son kowa da kowa ya zo ganta ta san ba zasu taba cire tabon abunda ta jawa musu na ja dansu su gudu ba, ballantana yanzu da ta kawo musu labarin mutuwarsa har a bada ba za su manta da ita ba, ba kuma za su yafe mata ba, duk wani so ko nuna mata kauna da za su yi ta ciki na ciki tana ganin kamar komai lafinta, saboda ita taje ta same shi da zancen guduwar kuma ya amince.
Na dawo ima jin kamar kar na baro na dawo nan ba, ba dan komai ba sai dan yadda tsarin gidan da kuma yadda suke haba haba da ni ya burgeni, har ta ginar gidan ana ta lekowa ana kallona, ba ma kamar lokacin da za mu tafi har da masu fitowa suna kallon motocin Mai Martaba.
A cikin unguwar na yi ta ganin zangon maza masu shan shayi da yar butarsu wasu sun yi gugun guri daya sun kuna kidan buzaye wasu kuma suna ta fira abunsu.
A lokacin da muka dawo gidan ma sai aka sake kawo mana wani abincin aka ni dai sai da na ci Aliyu ne kawai be ci ba saboda ya koshi, muna shirin kwanciya aka aiko kirana, har zan fita haka sai ya rike ni ya dauko min Hijab.
“Gidan nan har ya fi gidan mu yawan maza, bana son fitar ki haka Baby, kuma ya zama dole ki min alkawarin kula da kanki da jikinki da kuma babyna da yake cikin ki kamin na tafi pls”
“Taya mutum zai kula da kan shi? Da ma dai kula da wani ne ai zan iya”
Ya kama kunkuruna ya rike.
“Karki bar kanki da yunwa, ko kuma wani abun ya same ki, idan kin ji ciwo ko rashin lafiya ki yi saurin fada, kar ki bar jikinki haka nan sake har wani ya ga kyauki ko ya yaba, ki rika rufe jikinki kina tunawa cewar ke ajiyar wani ce”
Na gyada masa, sai ya sumbance ni sannan ya sake ni na fita. Bangaren da Mama take na nufo sai dai ban same ta a dakin dana same ta jiya ba sai wani dakin dabam,tana tare da mahaifiyarta da kuma wata mai kula da gidan da kuma wasu matan da aka nuna min dazun da safe aka ce matan yayyen mahaifiyata ne.
“Saboda tafiyar safe zai yi ya kamata ki fada mana abunda yake bukata sai saffara masa da wuri kamin ya tashi”
“Wa? Wai Aliyu? Okay bari na tambaye shi”
Duk kallona sukai har Mama dakanta kamar na yi wani sabo ko fadin maganar da ba daidai ba.
Sai Mama da sauran matan sukai murmushi.
“Ina ruwan Ataa”
Mama ta fada.
“Mu a nan ai ba a fadar sunan miji, miji yana da girma sosai, kuma akwai kunya ka fadi sunan miji kai tsaye, ina ma laifin ki ce masa Hamma”
Cewar Mama Hajjo. Sai a lokacin na gane dalilin kallon nawa da suke, ashe dan na fadi sunan Aliyu ne kai tsaye.
“Ga ki da sunan Maman su Mai Martaba amman ba ki iya girmama manya ba?”
Na yi kasa da kaina alamar kunya sannan na fice. Lokacin da na dawo dakin ya same shi rike da waya a hannu, ina shigowa ya dago kai yana kallona.
“Hamma wai ance mi kake so a maka da safe kamin ka tafi?”
Na yi maganar da sigar zolaya ina dariya tare da lake kafada kamar karamar yarinya. Murmushi yai ya miko min hannunsa.
“Zo nan matar Hamma”
Sai na saka dariya na zo gunsa kamar yadda ya bukata. Sai ya dora ni kafafuwansa.
“Wace ki ce min Hamma”
“Cewa akai wai ba a fadar sunan miji, shine aka ce ina laifin na kiraka Hamma”
Na fada ina dariya, sai shi ma yai dariya.
“Ke kuma na rika ce miki indo”
“Eh na yarda, fada min abunda kake so aka dafa maka da safe”
“No bana bukatar komai zan karya idan ya sauka can, akwai kayan tea a nan zan iya hadawa na sha ai”
Haka na koma na fada musu baya bukatar komai, sannan na dawo bangaren mu muka kwanta.
Washe gari.....
Ina gama sallah asuba na kunna butar ruwan zafi na hada masa tea, ko da ya shigo ina saka masa sugar. Be sha ba sai da ya bani na fara sha sannan ya sha, sai ya tashi ya shiga wanka ya fito ya shirya nima na shiga nai wanka na shirya. Har airport na raka shi ina jin kamar kar ya tafi saboda na saba al'amurarransa kuma ina ganin kamar tafiyar tasa bata zame masa dole ba, wata kila saboda ya baro ni ya dawo ne tace wani bata da lafiya. A lokacin da zai fita motar sai da nai masa kuka domin har ga Allah ban jindadin tafiyar da zai yi ina jin kamar na bishi amman ba hali.
“Ki samu layin kasar nan ki saka a wayarki ki kirani kinji? Ba zan dade ba zan dawo matukar jikin nata da sauki zan dawo na ga sauran yan'uwanki”
Ya fada min murya kasa kasa, ni kuwa ina lafe a kirjinsa ina hawaye.
“I love u ki kula min da kanki pls”
Ya fada bayan ya bude motar ya fita sai na gyada masa kai ina hawaye.
“I love you”
Na fada masa kamar ba ni ba, dawowa yai cikin motar ya saka bakinsa cikin nawa na tsotse yawuna sannan ya cire ya sunbanci goshi sai kuma yai kasa ta hannunsa ya shafa cikina.
“I Love you More”
Haka muka rabu ina jin kamar idan ya tafi ba dawowa zai yi ba.
ALIYU POV.
Da zahar jirginsu ya sauka Lagos, hutun awa daya yai wanda hakan ya ba shi damat kiran Momy da Mama Fulani ya fada musu cewar ya dawo yana Lagos kuma zai kama hanyar sokoto saboda Rahma bata da lafiya, Momy ba tai mamakin jin cewar bata da lafiya ba daman ta san za a rina wai an sace zanen mahaukaciya, ta san inda ta ji Ataa na ta ciki kuma ga rufin asirin da suke takama da shi na kakanta ne dole ta kwanta ciwo.
Daga Lagos ya hau jirgi zuwa sokoto, daman tun yana nijar yayi waya da Nasir ya sanar masa a samar masa ticket a cikin jirgin da zai je sokoto yau, ta online Nasir ya masa komai.
Da magariba ya sauka sokoto, sai da ya kira Husna ta kawo masa mota sannan ya nufi masallacin gurin yai sallah, after ya gama sallama ya sai da ya dan jira sannan Husna ta iso, daga airport din ya wuce asibitin Uduth, kamin ya isa ya kira wayar Rahma wata daga cikin yan'uwanta suka dauka suka fada masa dakin da take.
Ya shiga asibitin a lokacin da ba a shiga sai dai sanayyarsa da wasu likitocin ciki har da Doc Bukar ya saka an barshi ya wuce tare da Husna. Daga Rahma sai kanwarta Zulfa da mahaifiyarta ne a dakin. Hankali a tashe Aliyu ya shigo domin tun jiya jikinsa na bashi ba lafiya ba. Idonta a rufe suke amman tana jin muryar mijinta ta bude ido tana kallonsa, Mahaifiyarta na amsa gaisuwar Aliyu ta fice daga dakin. Sai ya rage daga kanwarta Zulfa sai Aliyu sai Husna.
Cikin sanyin jiki Aliyu ya karasa inda take ya zauna a saman kujerar yana kallonta, gaba daya bakin idonta ya bace bat, sai farin kawai shi ma kuma kamar ba daidai take kallo da shi ba, fuskarka da fatar jikinta sun bushe sosai kamar wacce ta dade bata da lafiya.
“Mi ke damunta?”
“Ciwon kodar ne, sun ce idan ba a canja mata ba a yan kwanakin aka mata dashen wata zata iya mutuwa, amman Mommy tace zata bada tata daya, gobe da maraice ma za a fita da ita zuwa inda za ayi aikin a London”
Juyowa yai ya kalli Zulfa cikin bacin rai.
“Akan me ba za a kirani a fada min bata da lafiya tun a aka kawo ta asibitin? Da ban kira ba da ba za a kirani a fada min ba kenan? Ni fa mijinta ne ina da hakki da yawa akan ta, kuma hakkina nema mata lafiya ba na iyayenta ba”
Zulfa ta yi shiri bata ce komai ba, sai ma saurin ficewa da tai daga dakin ganin yadda ran Aliyu ya bace sosai. Husna ma ficewa tai gudun kar ita ya shafe ta dan tasan halin yayanta be iya bacin rai ba.
Hannunsa ya kai ya kama hannunta, kamar jira take sai ta jimke hannunsa da karfi tana ta kallonta hawaye na sauko mata. So take ta masa magana so take ta nemi yafiyarsa kuma ta fada masa wasu abubuwan amman bata da wannan damar domin an iyakance mata maganar tun daga lokacin da tai wacan faduwar, ashe furta magana ma ba yin bawa ba ne na mahallincinsa ne sarrafa halshe ka iya fadar abunda kake so ma ba ikon mai shi ba ne iko ne mahallincin halshen da mallakin jiki gaba daya. Hannunsa ta ja ta rumgume a kirjinta Aliyu yai saurin ciro wayarsa ya kira Muhseen.
“Muhseen dan Allah ka taimaka min ka zo yau if possible ka duba Rahma kamin a wuce da ita tana jin jiki sosai”
Shiru Muhseen yai na wani lokaci kamin ya ce.
“Gaskiya ba yau ba, sai dai gobe idan an samu jirgi”
“Da safen pls”
Aliyu ya fada idonsa cike da kwalla. Sannan ya kashe wayar, so yake Muhseen ya zo ya duba kamin aje da ita waje, domin ya san Muhseen ya kware a wannan bangaren. Taso yai daga saman kujerar ya dagota ya rumgumeta a kirjinsa sai ta lumshe ido ta sauke wani irin ajiyar zuciya.
“I love you so much”
Ya fada mata hawaye na sauko daga idonta suna sauka saman kanta.
“Za ki warke Rahma In-Sha-Allah, zaki ji sauki ki tashi mu koma gida mu yi rayuwa tare da Ataa In-Sha-Allah”
Shine abunda ya fada mata a hankali yana kara hugging dinta tightly. A asibitin yai isha'i sannan ya dawo dakin ya zauna, shi ya taimaka mata ita ma tai sallah, misalin nine Momy ta zo tare da abincin da Siyama ta duba jikinta ta mata fatan sauki sannan suia tafi. Aliyu kan a asibitin ya kwana rike da hannun matarsa, sallah asuba ce kaiwa ta fitar da shi daga dakin ita yana gamawa ya dawo.
A nan ma shi ya taimaka mata tai sallah, sai dai yadda jikinta yai sanyi ya bashi tsoro sosai. Da kanshi ya hada mata tea da ruwan zafin daya gani a filas da ya kai mata tea a baki sai ta ki sha ta kawar da kanta.
“Ba kya so ne?”
Bata ce masa komai ba tana ta kallonta duk inda yai, hakan yasa ya dawo ya zauna ya rike hannunta, sai kuma ya koma saman gadon ya zauna ya dora kanta saman jikinsa ya rike hannunta yatsunsa cikin nata sai ta jinke yatsun nasa ta rumtse ido. Da dayan hannunsa ya karba wayar da Nasir ke masa sannan ya amsa ta Momy da Mama Fulani da kuma Daddy kamin ya kira Muhseen, jin number sa ba ta shiga yasa yai tunanin wata kila yana cikin jirgi ne ko kuma ya kashe wayar ne. Number Mama Fulani ya kira ya tambaye ta idab Muhseen yana nan sai ta fada masa cewar tun da dare Muhseen ya fada mata zai je sokoto kuma ta ji lokacin da ya fita tun da safe. Kashe wayar Aliyu yai ya jinginar da kansa ya lumshe ido. Sai ga wata likita ta shigo hakan yasa ya sauka daga kan gadon amman Rahma ta ki sakin hannunsa har likitar ta saka mata oxygen ta saita numfashinsa da na'ura mao kwakwalwa, sannan ta fita, sai ya Aliyu ya dawo saman kujera ya zauna yana rike da hannun na Rahama, ya dauki lokaci a haka kamin ya maida hannunta gurin fuskarsa ya Lumashe ido, ya dauki awa daya a haka kamin ya ji hannun Rahma da ke jinke da na shi ya sake ya zamana shine kadai yake rike da hannunta. Da sauri ya dago ya kalleta sai jin karar tsayarwar numfashinta ya ji a computer da ke nuna tafiyar numfashinta. Girgiza ta ya fara yi da sauri a rike kuma a rude bakinsa har rawa yake.
“Rahma Dear... ”
Ya fada a lokaci daya, sai kuma ya sake ta da sauri ya nufi kofa kamin ya karasa Muhseen ya turo kofar dakin ya shigo. Da sauri Aliyu ya rike hannunsa sai kuma ya kasa ce masa komai sai wani numfashi yake sama saman kamar zai fice daga jikinsa gaba daya, kansa ya dora a kafadar Muhseen har sai da ya samu relief na few seconds sannan ya dago ya nuna masa Rahma.
*Ina mata son rage kiba? Ina mazan da kiba ta hana su sukuni? Ina masu jikin yai kyau kamar na yarinya? Ina masu fama da kujera ko wani ta bo a fuska? Ina masu fama da hawan jini? Masu diabetic? Ag cera an gwada yayi an tantance ingancin babu shakku ko kadan. AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*
*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
Da sauri Muhseen ya nufi inda Rahma take ya shiga dubata. Fita yai da sauri ya kira wasu likitocin suka shigo, sai ya ja hannun Aliyu ya fitar da shi waje, ya koma ciki shi da sauran likitocin biyu suka shiga bata taimakon gaggawa, amman ina rai yai halinsa mai abu ya karbi abarsa a lokacin da yake so kuma ya ga dama.
Aliyu na tsaye wajen kofar dakin ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai safa da marwa yake jikinsa na zafi, gumi sai karyo masa yake zuciyarsa na bugawa da mugun karfi har ya kasa daidai ta numfashinta. Yana ganin Muhseen ya fito ya nufo shi da sauri ya tsaya a gabansa sai kuma ya kasa tambayarsa tana raye ko a mace, saboda yana tsoron irin amsar da Muhseen zai ba shi, shi ma Muhseen din sai ya kasa ce masa komai, be taba jin tausayin dan'uwansa kamar yau ba, be taba fargabar fada masa wata magana kai tsaye ba sai yau, be taba jin cewar idan yana da ikon da zai ma Aliyu wani abu da zai saka farinciki ba irin yau, ji yake kamar ace ikon dawo da rai a hannunsa yake da ya dawo da ran Rahma saboda Aliyu.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”
Shine abunda Aliyu ya furta ya risina a gurin ya dafe kansa, ya san Rahmarsa ta tafi kenan, domin da ace tana da rai Muhseen ba zai yi fargabar fada masa ba. Muhseen ma risinawa yai ya dafa shi
“Aliyu”
Sai kuma ya kasa cewa komai, a lokacin da Aliyu ya dago ya kalli shi sai hawaye Muhseen ya gani a fuskar Aliyu ga wani kadewa da idonsa sukai su kai ja sosai.
“Allah be halicce kan Rahma ba, kuma be halicce Rahma dan kai ba, ba za a kara maka wa'adin mutuwarka ba idan lokaci yayi balle kuma a karawa Rahma dan ta rayu