Showing 117001 words to 120000 words out of 225640 words

Chapter 40 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

kulolin jiya suka koma da su, haka nai ta rabon ido da rana ko Aliyu zai dawo amman be dawo ba, sai direban gidansu aka aiko da abincin rana ya kawo mana. Bayan wucewar direban tare da Labara dan tace zata fara zuwa gida ta gyara idan ta dawo sai ni na tafi na shirya. Nana na fara zubawa shimkafar da miyar ina ta bata tana ci a hankali har ta koshi na bata ruwa ta sha sannan na zubawa kaina na ci sai da na koshi sannan na zuba lemu na sha. Ina aje kofin wani mutum mai kamar masinja ya leko dakin mu.“Wai ance ana kiran Ataa”

“Wa ke kirana?”

Na tamabaya ina tashi tsaye na bi bayan mutumen da ya riga da ya fice. Hango inda ya bi yasa na bishi har muka isa wani dakin da nake zaton dakin likita ne muna shiga ciki zaton da nake ya zama gaskiya, domin kuwa dakin likitan ne sai dai macece tana hakimce saman kujerarta tana kallon laptop din gabanta tana murmushi.

“Hajiya ga nan”

Mutumen ya fada sai tai masa alama da ya tafi ni kuma ta nuna min kujera, bayan na zauna ya dauko wani katon wali ta miko min, sannan ta juyo da laptop din gabanta izuwa inda nake, Muhseen na gani a ciki yana zaune saman wata kujera mai juyawa da alama shi ma yana office din ne. Matar ta tashi ta fice daga dakin ta barni da laptop din da kwali a hannu, ban dauka da gaske na ke ganinsa a ciki ba har sai da yai min magana.

“Pretty ya jikin Mamana?”

Ya dan wara ido kamin na amsa masa.

“Jiki Alhamdulillah, da gaske kai ne?”

“Yes ba gani kina ganina ba, ta ji sauki sosai?”

“Eh bata manta komai ba”

“Ina iya kokari na hada da addu'a a gurin aikin dan an samu na yi aikin cikin nasara, na san yadda uwa take da muhimmanci musamman ke da kike bukatarta, ina son ki rayu da mahaifiyarki duk kuwa da kin nuna min ba kya so na, amman ba son ne a gabana ba samun lafiyar mahaifiyarki ne a gabana”

Ya fada yana murmushi ni kuma na yi kasa da kaina ina taba kwalin dake saman cinyata.

“Ataa.... ”

Na dago na kalleshi.

“Bude kwalin”

Na bude kamar yadda ya bukata wani kyakkyawan zobe na fara cin karo da shi, a kasanshi kuma cake mai zagayen zuciya.

“Ban san size din yatsunki ba amman na san idan be miki yawa ba, ba zai miki kadan ba”“Zoben minene?”

“Na zinari ne”

Wani tsoron na ji na kamani daman tunda naga yanayin zoben ma dauka cewar na zinari ne, sai dai rashin ranin hakikanin zinarin yasa ban yi saurin yake hukunci ba har sai da ya fada min.

“Ni ban taba saka zinari ba”

“Kin fara kenan daga yau, ke din ai matar manya ce Ataa, ba dan ina son ki nake son ki saka zoben ba, sai dai kar ki manta da ni, a duk lokacin da kika tuna da samun lafiyar Nana ki min Addu'a Allah ya bani mata irin ki”

“Amman....”

“Karki ce komai Ataa pls ki saka dan Allah”

Akwa girma da nauyin a hada ka da Allah kuma ka saka yin abun nan, ko be hada ni da Allah ba mutumen da yai ma mahaifiyata tiyata ta samu sauki ya cancanci ya saka wani abun nai masa balle kuma ya hada da mahaliccina. Bude akwatin zoben nai ya fiddo daga ciki, sai da na kalli Muhseen sannan na saka zoben ina hade yawu gabana na bugawa da mugun karfi. Wani irin abu na ji ya ratsa ni, wata irin daraja da daukaka suka cika min ido, saurin cire zoben nai hawaye na sauko min.

“Ba zan iya sakawa ba Muhseen ka yi hakuri”

“Ba zan cilasta ki ba Ataa amman ki aje shi a gurinki”

Na gyada kai kamar yana gabana ina share hawayen.

“Upper week zan zo na yi ma wasu aiki, fada min abunda kike son na zo miki da shi, Mama Fulani ma ta ce na tambaye ki abunda kike so na zo miki da shi”

“Ni”

Na fada ina nuna kaina da tsananin mamaki.

“Yes baki yarda ba? Idan na koma zan fada mata ta kira ki da kanta”

“A a karka ce karka saka ta”

“To fada min abunda kike son na kawo miki”

Na yi shiru ina nazarin ban san mi zan ce masa ba.

“Kina son turare?”

“Eh ina so”Na amsa da sauri domin ya fanshe ni daga dogon tunanin abunda zan fada.

“To zan kawo miki, ki ci cake din kin ji?”

Na sake gyada masa kai ina kallon yadda yake kurba tea da ke gabansa. Murmushi ya sakar min kamin ya kai hannunsa ya taba wani gurin sai hotonsa ya bace bat. Mikewa nai tsaye ina rike da zoben da kuma cake din na fice daga dakin. Kadan kadan nake tafiya ina jim kalamansa kamar yanzu yake fada min su cewar Mama Fulani tace a tambaye ni abunda nake so, yafi komai bani mamaki da al'ajab, anya da gaske ma tace haka ko kuwa cewar Muhseen ne. Da wannan tunanin na shiga dakin da Nana take ina shiga na samu wata mace a tsaye tana sanye da yadi maroon da garin gyale, daga ganin yarinyar ka san budurwa ce ko da ganinta zata yi masifa.

“Ke ce Ataa?”

Ta tambaya tana zare min ido, gabana ne ya fadi har na kasa amsa mata na gyada mata kai kurum.

“To ki fita daga hanyar Aliyu domin ba makaskanci ba ne irinki, Aliyu ya fi karfin ko wace mace balle kuma ballagaza talaka irinki, yar bara a titi marar daraja....”

Yarinyar bata gama fada ba Nana ta daka mata tsawa da yaren buzanci tana zaburowa kamar ba tiyata ce a jikinta ba.

“Ke ya ishe ki”

Saurin karasa nai gurin Nana na dafata ina rufe mata baki. Sai yarinyar ta juyo ta kalli Nana ta ce

“Aniyar da biki idan ma wani abun ne kike karantawa ni na fi karfinki da duk danginki, kuma Wallahi Aliyu ma yafi karfinku duk wani abu yana muku shi a matsayin taimako amman shi kansa baya son kaskantacin mutane irin”

Mikewa nai tsaye ina nuna ta da yatsa na ce.

“Ke ce kaskantacciya domin da kina da wani matsayi a gurin Aliyu da kin hana shi taimakon ku ba sai kin zo kina mana ihu a cikin asibiti ba, jahilar banza wacce bata san darajar dan adam ba.... ”

Matsuwa yarinyar tai ya wanke min fuska da mari ta buge kwalin da ke dayan hannuna da zoben suka watse kasa.

“Lalala wato har da su zobe ya baki eh lallai zaki ci ubanki”

Ta nufi inda zoben yake ta dauka ni kuma na yi kanta na rama marin da ta min ina kuka sai juyo ta rikani ta buga da karfen gadon da Nana take kai a take kaina ya fashe da jini ya fadi zaune a gurin ina kuka, ita kuma tai ficewarta tana kwafa.
ZAKI

By Khadeeja Candy

36...

Ina zaune a gurin ina ta aikin rare kukana a hankali marar sauti sosai Nana na samam gadon ita tana hawaye, jini nata min zuba sosai har jiri na ke gani na kasa tashi a gurin kuma na kasa daga muryata na waje ya ji ya kawo min taimako. Sai bayan sallah la'asar Laraba ta dawo dakin tana ganin halin da nake ciki ta bugawa Momy a waya ta sanar da ita cikin tashin hankali. Ba a dauki lokaci ba Momy ta iso asibitin ina da Amina, tana ganin halin da nake ciki hankalinta ya tashi da sauri ta rikani ta fita da ni zuwa inda za a wanke min ciwon. A gaskiya ta nuna min kulawa sosai bayan sun wanke gurin suka ba ni magani ta biya kudin komai, ba ta dawo da ni dakin da Nana take ba, sai ta nufi motarta da ni, tana rike da ni har muka isa a gidan baya ta saka ni ita kuma ta shiga a front seat Amina ke tukawa, tun kan mu isa ta kira wayar Aliyu ta fada masa tana nemansa cikin fushi.
Da muka isa sai ta wuce ciki Amina ce ta rika ni muka shiga ciki, a saman kujera ta zaunar da ni ta cire min hijab babu nuna kyama ko gazawa a tare da Amina da mahaifiyarta, ruwa Momy ta ba ni mai dan zafi da lemun tsami a ciki a na sha sai ta dauki kofin na kwantar da kaina saman kujerar na lumshe ido ina sauraren yadda take fadawa su Husna da Siyama abunda ya faru cikin fada kamar yarta a aka taba.Mutanen nan biyu sun koya min wani darasi na rayuwa, kyamar talaka da Mama Fulani da 'ya'yanta da suke ra'ayi ne kawai na kansu ba dan talakan ya musu wani abun ba. So da kauna da kulawar da Momy ke nuna min ya karantar da ni wani halin dabam na dan adam. Momy ma masu arziki ne sosai amman bata taba nuna min kyama ba, ta san darajar talaka ba dan zata amfana da ni ba, sai dai tausayi da jin kai da ya cika zuciyarta, halin ne na dan'adam wani da dadin zama wani babu, wani da sanin darajar dan'adam wani babu, haka rayuwar take tafiya kowa da irin ra'ayinsa da halinsa da kuma tarbiyarsa, domin kuwa Husna da Siyama da Amina suna bin tarbiyar da Momy ta dora su akai ne, yayinda Yayan Mama Fulani suke bin tarbiyar da ta dora su akai, ban ce Muhseen da yake da wata rayuwar ta dabam wacce ta fidda shi dabam a cikin yayanta, yatsun hannunmu ma ba daya bane ta ita halin kowa zai zama daya.
Ina kwance na a gurin na ji kamshin turaren Aliyu wani irin turare mai kwnatar da hankali da saka nishadin ruhi, ina jindadin shakar kanshin sosai fiye da komai a yanzu.
Da sallamarsa ya shigo Momy ta ki amsa masa sai Husna ce ta amsa masa wanda hakan ke nuna cewar Momy tana cikin fushi sosai, tashi Husna tai ta nufi kitchen daman ita kadai ta rage a falon Siyama da Amina tuni suna shiga dakinsu dan yim wani sha'anin.

“Aliyu ka fadawa Matarka cewar kana son Ataa ne?”

Kallonta ya tsaya yi kamin ya tantance abunda ke fitowa daga bakinta.

“Son ta kuma? Kamar ya?”

“Wata taje ta taki akanka ta fada mata cewar idan bata fita daga sha'aninka ba sai ta mata illa, ta mareta kuma ta fasa mata kai”

“What”

Ya furta yana karasowa zuwa inda na ke ya duba kan nawa, tashi nai zaune ina kallon yadda fuskarsa ta canja ganin bandeji a goshi idona har ya kumbura saboda kukan da nai na gaji.“Ba zai yiyu ba, yarinya kamar wannan ace zata sake shiga wani halin kuma, ta wanne zata ji da jin mahaifiyarta ko da kishin matarka? Kishin ya kai har ta saka aje a fasa mata kai? Wannan wane irin rashin mutunci ne? Idan ma sun ta kake yin hakan zai saka ka fasa ne? Shi kenan dam tana talaka ba da daraja da kima a gurinku? Idan yar wani Minister ta ce Rahma ta isa ta dake ta ma balle har ta nuna mata yatsa? Da ace ita ce ta yi ma Rahma haka ina da tabbacin yau Ataa a gidan yari zata kwana saboda ta taba yar gata, to ya bata fi ya ba Rahma dan ta tana yar masu arziki bata fi Ataa ba dukansu mutane ne, suna zamansu lafiya cikin rufin asiri za su tashi hankalinta da na mahaifiyarta, ita Rahma idan mai tunani ce ai kamata yai ta kama Ataa ta rike ta martaba ta kodar mahaifiyarta ce a cikim cikinta fa, tasan bata da lafiya idan Allah ya ga dama sai ta fadi ta mutu a take amman sai neman wulakanta wata take? Idan ma son ta kake ta isa ta hana ne? Wallahi ka jawa matarka kunne idan ba haka fadan a tsakanin mu zai dawo domin ba zan zuba ido su cewa Ataa mutunci ba, idan ma ai kake goya mata baya to ko kuma ka kwashi matarka ku koma can Abuja.....!”

Tana kawai nan ta tashi a ficewa ta nufi dakinta ba tare da ta tsaya sauraren abunda Aliyu zai fada ba. Tun da take fadan na ke kallonta ina hawaye cike da kauna marar misaltuwa, wata uwa bata taba tsaya ta shigar min fada ba bayan Nana amman a yau na samu wata mace da ta rike ni 'ya har ta take fada da danta akan abunda surukarta tai min, ciwon kan da zazzabin da suke son rufe ni a take na neme su na rasa, wani irin kaunar Momy ya cika min zuciyata, hakika ta uwa Momy uwa ta gari ce mai iya kula da yayan kowa kamar yayanta. Risinawa Aliyu yai gabana yana kallon fuskata a hankali ya shiga min magana.

“Sannu”

Na gyada masa kai tare da saka hannu na share hawayena.

“Wacce ta dake ki cewa tai Rahma ta turo ta?”

Na girgiza kai.

“Bude ba ki yi min magana mana”

Kasa nai da kaina haka nan kawai na samu kaina da kasa bude baki na ce masa komai har na tsawon lokaci. Tashi nai tsaye na soma takawa da zimmar shiga bathroom din Amina saboda fitsarin da suka cika min mara, sai na ji ya kira Husna da ke kitchen ta fito da sauri.

“Rika ta ki kai ta daki”

Sai da ta kalleshi sannan ta zo ta rika ni ta nufi dakinta da ni a maimakon dakin Amina.“Kwantawa za ki yi?”

“A a fitsari zan yi”

Bandakin ta nufa da ni sai da muka shiga ciki sai ta fito, bayan na gama abunda zan yi na fito sai na zauna kasa na jingina da gadonta, murmushi na ke abunda Momy ta yi min ya faranta min rai sosai, Husna na shigowa dakin ta saka na tashi daga kasa na koma saman gadonta na kwanta, nan da nan bachi yai gaba da ni.





ALIYU POV.

Da kallo ya bi Ataa wance Husna ke rike da ita har suka shige dakin. Yana ta mamakin abunda Rahma tai bayan yau da ita ya wuni saboda ita ne be je ko'ina ba. Mikewa yai tsaye ya fice daga falon zuwa motarsa, yana shiga ya dauki hanyar gidansa. Harabar gidan ya faka motarsa yana kallon wata bakuwar mota da ke fake a gafen ta Rahma, ya fito yana rike da keys din motarsa a hannunsa ya tura kofar falon ya shiga. Rahma ya samu zaune ita da Muneera a kujera daya, da alama fira suke yi ko kuma wani abun Muneera take fadawa Rahma sai dai ganinsa ya saka sun yi shiru.

“Sannu da zuwa”

Rahma ta fada sai yai mata banza ya nufi upstairs.

“Ranka ya bace saboda an gargadi wata banza”

Ta fada tana mikewa tsaye, shi kuma ya juyo ya kalleta.

“Akan me za ki nemi takurwa yar mutane? Ce miki nai ina sonta? And what makes you think abunda kika saka ka mata zai sa na canja na fasa taimakonta ne? Wallahi abunda kika yi be kara min komai ba sai tausayinta, yarinyar da ke jinyar mahaifiyarta saboda ke a maimakon ki tausaya mata ki taimake ta sai neman saka ta kike a cikin wata fitinar, matace ke ina martaba ki ina mutuntaki ba zan bari wani ya zaga miki rigar mutunci ba, kamar yadda ba ba zan bari ki yagawa wani ba wanin ma kuma wacce ta taimake ki rayuwarki”

Ya fada cikin daga muryar fuskarsa a hade kamar bakin hadari.

“Abunda kake yi abun kunya ne Aliyu namiji mai daraja mai kima da mutumci kamar ka ace yana bibiyar wata banza yar talakawa yar bara a titi wacce bata san mutuncin kanta ba, namiji nawa na kwanta da ita lokacin da take bara baka sani ba, amman abun kunya har ka dauki robe da cake ka bata zobe ma mai tsada wanda na yi imani bata taba ganin irinsa a rayuwarta, ka yi kuskure Aliyu kuma kana shirin aikata kuskure idan har ka ce zaka hada ni kishi da wata kazama wacce ba a san ubanta ba balle asalinta, wannan ne kuskure mafi girma da zaka aikata hada ni kishi da yar talaka, abunda za ka yi ka burgeni ka nemo yar wani minister ko yar wani mai ji da kansa ka hada ni shi da ita amman ba yar iska yar gantali a titi ba, wacce ta kwana a titi yan sanda suka gama amfani da ita Doc Asim ya gama amfani da ita kai kuma yanzu kake son kawota cikin gidanka”

Tana fadar hakan ta juya sai Aliyu ya juyo da ita da dukan karfinsa yana kallonta naman fuskarsa har rawa yake saboda bacin rai.

“Idan zan so Ataa ba zan so ta dan wani abu nata ba, kamar yadda ke ma ban so ki dan wani abu na ki ko na gidanku ba, ban taba son mace dan wani abu nata ba kin fi kowa sanin wannan”

“Ba haka ba ne, ka so ni a yadda na ke saboda ka san cewa baka haihuwa saboda kai juya ne, so that sai mu taru mu mutu a haka, yanzu kuma kana ganin ka gaji da ni mahaifiyarka ta saka ni a gaba shine zaka fara son wata ko? Watan ma yar titi wacce kai da kanka kake nuna mata kyama amman mahaifiyarta take kokarin gyarata saboda kana sonta, daman na sani yan'uwanka gaba daya ba so na suke ba”

“Ba ki da kunya Rahma, kina magana kamar ba ki san da wanda ki ke magana ba, mi yake damun ki ne?”

“Abunda yake damunka Aliyu, abunda ya saka ka canja ka koma kamar mahaukaci akan wata dabba can, shiyasa na gano matsala da kai idan har zaka iya runtse ido a halin da muke ciki ka ce zaka min kishi to sai an bata guri ta zo ta zauna da kai fa haihu na gani”

“Za ki yi nadama matukar kika ce Zabin Rai za ki bi, ina daga miki kafa ne saboda sanin abunda yake tare da ke, ina tausayin ranar da za ki yi nadama Rahma, wulakanta dan 'adam ba shi da kyau musamman wanda ya taimaki rayuwarka”

Wani kallon mamaki tai masa

“Haka ka fadan to sai kaje ka aureta ka zauna da ita, daman ai haka halin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login