Showing 198001 words to 201000 words out of 225640 words

Chapter 67 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

fargaba ko damuwa a rayuwar aure shi ne samun miji da baya baka kulawa ko kuma baya kaunarka, amman ni ina jin cewar na yi wannan dacen duk kuwa da ban san mi gaba zata haifa ba amman ina jin cewar Aliyu zai iya tsaya min a ko wane hali na samu kaina. Ta dayan bangarem kuma ida na tuna yadda Allah ya daukaka daraja da martabata a take ta ba kuma ta hanyar kowa ba sai ta hanyar mahaifiyata wacce kowa ke gani a wulakance yana raina mu. Lallai bayan tsananni akwai dadi a tafe wani a kusa wani kuma a nesa, a duk inda duhu yake a akwai haske, a tsoro na da rashin gatana na samu kwarin guiwa da gatan da ban yi tsammani ba. Idan na tuna farkon abunda nai ma Aliyu na fasa masa mota da ruwan da ya watsa min a tufafi sai abun ya bani mamaki kuma ya bani dariya, kamar ba mu ba, mutumen da ke kyamar talaka yana ganin kamar ba su da raja yau shi ne a gabana a matsayin mijina har yake yabona ya fada min cewar yana kaunata.
Hannuna na ji an kama wanda hakam yasa na dawo daga duniyar tunanin da ke, agogon hannu ya saka min mai kyau sosai sannan ya saka min wata tsarkar hannuna dake tare da agogon, sai yai ma hannun nawa kiss.

“I love you both”

Ya fada yana min wani lallausan murmushi mai kawata fuskarsa da siffar zatinsa. Goma saura muka fito tare da shi, ina rike da wani jakarta ta rayatawa shi kuma yana rike da karamin akwati kuma ya janyo babban, da kansa ya saka akwati bayan mota sannan ya bude min na shiga kamar yadda na sawa kaina a yanzu ko kuma na ce ya sabar min na bude min mota da kansa.
Tun kan yai horn ko yi ma motar key mai gadin ya bude mana gate.

“Za mu tafiya zuwa Nijar yau, ban san tsawon yaushe za mu kai a can ba, amman dai ba za mu dade sosai ba, ka kula da gidan da komai, kuma karka bar kowa ya shiga ciki”

Ya fadawa mai gadin daidai lokacin daya tsayar da motarsa a gurin da yake. Sannan ya bude wani guri a cikin motar ya dauko kudi masu dan dama ya mika masa.

“Ka siya abinci kuma ka yi wata lalurar idan ta taso”

Hannu biyu ya saka ya karba yana ta masa godiya sannan ya ja motar kuma nufi gidansu Mama Fulani, kamin mu karasa har Mama Fulani ta kira shi a waya wai ana jiranmu.
A harabar gidan ya faka motarsa ta cikin motar ya miko hannu ya bude min kamin ya fita, muma fitowa muka nufi bangaren Mama Fulani tare da shi, a falo muka samu Maryam da Rukaiya da Mama Fulani zaune, Aliyu ya fara sallama sannan ni ma nai, ta amsa mana ita da su Maryam sai dai bata kalli inda ake ba, na gaishe ta ban yi zaton zta amsa min ba na yi zaton yar jiya zata min sai na ji ta amsa min amman salaf da ita gishiri kamar ba ita ba, ta wani sukuku kamar marar lafiya.

“Ya jikin naki Mama?”

“Al-hamdulillah, Tun dazun ake ta jiranku Ammy ta aiko sau biyu tana cewa na kira na fada maka wanda zai dauke ku ma ya zo”

“Okay, Ki yi Mama bankwana”

“Mama ina kike karanta bankwana sai mun dawo”

“Allah dawo da ku lafiya ya tsare”

Shine abunda kawai ta fada bayan an fada mata haka sannan ya mike tsaye ta nufi upstairs, Aliyu kuma ya kalli Maryam da Rukaiya dake zaune a saman kujera suna satar kallon mu.

“Allah ya kiyaye ya tsare”

Ko wace su ta fada sannan muka fito daga bangarenta muka shiga bangaren Ammy, Mama da Ammy na zaune a falon da kuma Yusuf wato dan'uwana kuma jikan Mai Martaba wanda suka zo tare, Humaira ma na falon ita da Zee da ke ta aikin chatting. Mama na sanye da wata kamfala ja mai kyau sosai kana ganinta kasan mai tsada ce wacce na ke kyautata zaton Ammy ce ta bata domin bata zo da tufafin ba a lokacin da zata baro sokoto ta zo nan. Na gaisa da Ammy kamar yadda na saba Aliyu ma ya gaisa da ita sannan ya gaisa da Mama sai ya fita daga falon yana lasa waya, ni kuma na koma kusa da Mama na zauna.

“Ki gaishe shi mana”

Ta fada tana nuna min Yusuf da ke murmushi yana kallona, da yaren buzanci muka gaisa da shi yana amsa yana min wasar tabasai kamar daman can ya sani, ni dai ban rama ba domin ban san yadda na ke da shi. Tare da shi muka fito daga bangaren Ammy, hakan kuma be yi ma Aliyu dadi ba, na fahmcin hakan ne ta fuskarsa da na gani a daure yana ta aika min da harara kasa kasa. Kowa ya fito yana mana Allah ya tsare sai mun dawo ciki kuwa har da Maryam da Rukaiya abun babu ko kunya, kuma babu sha'awar gani, ina kyautata zaton sun yi hakam ne saboda kar Aliyu ya ga laifinsu ko kuma Mama Fulani ce ta cilasta su domin ta san Yaran Ammay ma sai sun fito. Aliyu ya zauna gaba ni da Mama muka zauna baya, Yusuf yaja motar muka kama hanya, tsakanin ni da Mama aka rasa wane ya fi wani farinciki da zumudin ganin yan'uwan, ita da ta shekara ashirin rabonta da su ko kuwa ni da zan fara gaduwa da su a yau? Tun da muka shiga motar ni da Mama da Yusuf ne kawai muke magana Mama da Yusuf na yi da yaren buzanci ni kuma sai na maida wata maganar da hausa saboda Aliyu, shi dai be ce uffan ba.

Da zahar muka isa lagos, wani kyakkyawan gida aka kai sauke mu, gida ne nadaidaicin mai kyau wanda aka kawata da shuke shuke gwanin sha'awa. A nan muka gaisa da Mai Martaba muka ci abinci muka huta sannan aka zo aka dauki mu aka tafi da mu wani gurin aka dauki hoton mu da tambarin yatsun mu akai wasu abubuwan da ban san ma'anarsu ba sannan aka dawo da mu. Bayan mun dawo Aliyu ya kira Momy ya ba ni muka gaisa har ta ke ce min na kula da kaina kuma na gaishe da kowa da yake can, ya bawa Mama ita ma ta gaisa da ita sannan ya kira Daddynsa shi ma muka gaisa kamar yadda ya fara gaisawa da shi, Abbah ya biyo baya shi da Mama Fulani sai a lokacin ya sanar musu mun iso lagos lafiya kalau.
Ba mu bar lagos ba sai da la'asar sannan muka shiga jirgin Mai martaba zuwa nijar, ni da Aliyu muna zaune a kujera daya daga can baya, Mama da Mai Martana kuma suna zaune a wata kujera mai kamar dinning wacce kowa ke iya kallon kowa ga wani dan karamin tebur a tsakani, bayan wadancan jikokin da ya zo da su wato Yusuf da kuma dayan da na ji Nana ta kira sunansa da Abdallah na ga su ma da ban san fuskarsu ba sai yau. Ban san awa nawa ne daga nigeria to Nijar ba, mota balle kuma a jirgin sama, sai dai na yi bachi a cikin jirgin a kafadar Aliyu sau biyu ina farkawa sai kuma nai bachin, abincin da aka ba mu a jirgin kin ci nai duk kuwa da kasancewar na mu ne irin wanda na saba ci yau da kullum amman sai naji bana ma kaunar warin abinci. Aliyu ma Ginger tea kawai ya sha sai wani biscuit na alkama, ni dai ko ruwa da ban sakawa cikina ba har muka sauka. A nan ma akwai banbancin lokaci da can kamar dai yadda mukai wacan tafiyar zuwa Las Vegas sai dai wannan ba tai nisa wacan ba ko kadar nisanta bata kamo ba, wata kila kuma saboda mun sauka da dare ne na ke ganin kamar lokacin da banbanci. Mama da Mai Martaba su suka fara fita daga jirgin tare da masu take masa baya wato fadawansa, sannan ni da Aliyu muka fito sai kuma sauran suka fito. Tun daga yanayin filin jirgin zaka fahimci ba a Nigeria kake ba, domin yawacan mutunen da suk can shigarsu daban ce da wadanda suke airport din Nigeria.
Motar biyar aka jera a filin jirgin ban yi zaton na Mai marta ne ba har da na ga ya doshi can wasu fadawan sun fito daga motar da sauri suna tarbarsa, motar da ya shiga dabam da wacce mu muka shiga. Duka motocin bakake ne masu bakim gilashi a hankali suke tuka motar har muka hau babbar hanyar garin. Yawacan mutanen da na ke kallo a titi da inda muke wucewa mafi yawansu suna sanye da rawani da ginuka su sum sha banban da na Nigeria domin su zaka ga wasu ginin na su tun na al'ada ne ba su zamanantar da shi ba, wasu kuma an kawata su kamar garin sokoto.

Tun daga unguwar da muka shiga na gane cewar ana yin sarkin a unguwar yadda na ga mutane suna tsayawa kallonsa da daga masa hannu da masa kirari a cikin yaren buzanci. Wata irin katuwar masarauta muka shiga mai haske kamar rana sakamakon kwan lantarki da aka saka ta ko'ina, ga kuma ginin da zanen masarautar irin an al'adar masarautar mai hawa biyu ce, wani bangaren kuma hawa daya ne, ga fadi kamar wata unguwa dukam wadanda suke cikin masarautar daga mai rawani sai mai hula manya da yara, mutane da dama suka fito daga cikon gidan zuwa inda aka faka motarmu suna mana lalle marhabun a cikin kuwa har da manyan mazan da nake saka ran yayun Mama ne, ganinta ya bawa kowa, sai Mai Martaba ya fito sannan ta fito, muma muka fito ni dai sai wara ido na ke abun ka da bakauyen mutum kuma mai son ganin masarauta. Kowa mamakin ganin Mama yake wasu kuma kallonta kawai suke wanda hakan ke nuna cewar ma su kallon nata ba su santa ba ne ko kuma sun manta, domin matasa me ko da yake a akwai manya a ciki, sauran kan mamaki ya hana su magana, ta yadda na ga suna mamakin ne ya fahimtar da ni cewar Mai marta be fada musu cewar ya hadu da Mama ba sai dai zuwan da yai da ita na ba zata. Tare da Aliyu muka karasa gurin da Mama take tsaye shi kan Mai martaba tuni yayi cikin fadarsa tare da manyan amsu take masa baya, Mama kuma ta fashe da kuka har sai da aka rakata a ka shiga da ita ciki.
Nima hawayen na ke har muka shiga cikin katuwar fadar wacce akaiwa ado da kwalliya irin ta mutanen da sai dai an zamanantar da adon ta yadda zai burge kowa gwanin sha'awa. Kwatatan fadin fadar da girma ta abu ne mai wahala ga mutum irina ne, domin kallon kwaliyar fadar ya hana ni tsayawa na lura da wadanda suke cikin fadar ma. Ban an kara da hakan ba har sai da masu yi ma Mai martaba kirarin cikin yalshen buzanci suka hankato da ni na dawo daga duniyar kallon fadar. Ashe tuni Mai Martaba yai gaba ni da Aliyu da wasu masu take mana baya tafiya muke zuwa wani bangare na fadar ban sani ba. Duk inda muka bi indai da mutane wasu kallon tausayi suke mana wasu kuma kallo ne akwai ma Mamaki, Mama kan sai aikin kuka take ni kuma ina taya ta da hawaye har muak shiga cikin gidan ni da ita da kuma Aliyu. Shi ka Mai Martana tuni ya kama wata hanyar dabam, Yusuf ne yake mana ja gaba har muka shiga inda Mata da yaya da yawa suke. A tsakar gidan Mama ta gurfana ta fashe da wani sabon kuka mai taba zuciya, matan gaba daya suka zagaye ta suna kallonta kamin wasu su kama ta su shiga da ita ciki ciki. A bangaren da ke farko aka shiga da ita wanda na ke kyautata zaton na mahaifiyarta ne ganin hoton Mai Martaba da wasu da ga kuma wati dattijiwa wacce tuni ta kawo bakin kofar falon tana kuka sosai har da saka hannunta ta dafe zuciyarta, Mama ta fadi a bakin kofar tana rike da hannun matar matar ma ta rike hannun Mama gam tana kuka sosai, ba ni kadai ba kowa da ke gurin sai da ya tausawa Mama da matar saboda kukan da suke da kuma wasu ma har da kukan sai da sukai.

“Nana ce ta dawo, Nana ce, Nana, Nana”

Shine abunda yawancin matan da ke gurin suke fadi tare da wasu dattijan mazan, wadanda suka tsaya rumgume da hannunsu suna kallon Mama. Sai da akai ta ba su hakuri sannan Mama ta tsagaita kukan da take ta shiga cikin katon falon wanda sanyin ac da kamshin turare ke maka lale marhabun. Muma shiga cikin falon ni da Aliyu sai aka dawo kan mu ana ta kallon mu wasu har da bude baki, ina jin lokacin da wasu ke fadar ni da Aliyu duka yayanta ne wai Aliyu ne yaya ni kanwa, wasu kuma su ce rakota mu kai. A lokacin da Dattijiwar ta zauna a falon sai ta daga kanta sama hawaye nata mata zuba sai girgiza kai take.

“Mama ki yafe min, Mama ban kyauta miki ba aikata daidai ba, kuma ban kyautawa kaina ba na sani, kuma na cancanci ko wane irin hukunci ko fushi daga gareki”

Mama ce take fadin haka tana daga kasa zaune rike da hannun matar tana kuka, matar ma kukan take irin na tsofi gwanin ban tausayi da taba zuciya, ta hanyar kalaman da Mama take na fahimci cewar dattijiwar Mahaifiyarta ce duk kuwa da kasancewar ba a su yi kama sosai ba domin Mama ta fi kama da Mai Martaba.




RAHMA POV.

daga idonta har makoshinta da fatar jikinta abushe suke kamar wacce. Ta shekara ashirin a gadon asibiti, kallo daya zaka mata ka fahimce akwai damuwa sosai a cikin zuciyarta, tun daga lokacin da aka kawo ta asibiti ta farka bata ce da kowa komai ba, ciki kuwa har da mahaifiyarta da ke kai da kawo tana yawan tambayarta idan tana bukatar wani abun, sai dai ta gyada kai ko ta girgiza, likitan da ya zo dubata ma sai dai ta girgiza masa kai ko ta gyada kai, rashin maganar ya damu kowa domin an kasa gano matsalar rashin maganar tunda tana ji maganar ce kawai bata furtawa, wata kila damuwarta da ke ranta ce ta hana ta magana da kowa ko kuma wani ciwon ne, na daban ya same ra a yanzu.

“Ya kamata a sanar da mijinta Mommyn wannan abun, tun da ta tashi ba tai magana ba, idan kuma aka takura da magana ta fara hawaye wannan abun yayi yawa”

“Ya san da ita ai, tun da yai aure be waiwaye ba, idan ma ya zo ba wani maganin zai mata ba, koda ce take bukata kuma ta mu In-Sha-Allah”

Mahaifiyarta ta mayarwa da Ikram amsa cikin hawaye, kallonsu kawai Rahma ke yi ba tare da tace komai ba.

“Ko jiya ya kirata amman ban daga ba saboda ban san mi zan fada masa ba, amman kyaleta a haka ba shine mafita ba, ya kamata ace ya san matarsa tana asibiti ko da ba zai mata komai ba”

“Idan ya kira ki daga ki fada masa cewar matarsa bata da lafiya tana asibiti”

“To Mommy”

Mommyn ta fice daga dakin cikin damuwa tana share hawayenta. Rahma ta bita da kallo, irin kallon na tausayin mai jinya idan yana jinyar kansa, tana son mahaifiyarta kamar yadda mahaifiyarta take sonta, zata mata sadaukardar da take jin ba lalle ne ta rayu bayan an dasa mata kodar ba, zata iya mutuwa bayan cirewa mahafiyarta kodar an sada mata ya zama an yi ba ayi ba kenan! Abu daya take da bukata a yanzu mutuwarta kamin a cire kodar mahaifiyarta a dasa mata, domin ta san zata bar duniyar komai daren dadewa, and mutuwarta zata fi mata rayuwarta a yanzu, domin bata da tabbacin idan an dasa mata wata kodar za ta rayu.
Abu daya take fata kuma take ta jira a yanzu zuwan mutuwarta kamin jibi da mahaifinta ya fada mata za a fita da ita waje ayi mata aikin kodar a can.


“Rahma?”

Ta juyo ta kalli Ikram tana hawaye kamar yadda yar'uwata take yi.

“Dan Allah ki cire damuwa a ranki ki yarda da duk abunda ya same ni daga Allah ne kuma babu mai iya miki maganinsa sai shi”

Kai kawai ta gyada mata ta hade yawun bakinta. Alama tai maga da ta bata wayarta sai ta ciro wayar daga jakarta ta mika mata. Kamar hadin baki tana karbar wayar kiran Aliyu na shigowa wayarta da layinsa na Airtel. Kara wayar kawai tai a kirjinta ta lumshe ido tana hawaye.

“Ki dauka mana idan ba za ki iya ba ki ba ni”

Mika mata wayar tai ita kuma ta koma ta kwanta saboda numfashin da taji yana yin sama sama kamar zai fita daga jikinta. Ikram ya dauki kiran ta saka wayar a hands-free tana kokarin danne kukanta.

“Hello Dear”

“Ba ita ba ce, Ikram ce”

“Ina Rahma?”

“Tana asibiti tun shekaranjiya”

Ikram ta fada cikin kuka.

“Mi ya same ta?”

“Ciwonta ne ya taso har bata iya magana”

Sai kawai ya kashe wayar, Rahma har lokacin kuka take marar sauti tana dafe da zuciyarta gwanin ban tausayi, ga jikinta babu sauran karfi.



*Ayi hakuri a gafarce ni, dukan wani tsaikon da ke sakani typing da dare na gama shi yau, Al-hamdulillah. In-Sha-Allah posting din dare ya kare da yarda Allah.*

*Ina mata son rage kiba? Ina mazan da kiba ta hana su sukuni? Ina masu jikin yai kyau kamar na yarinya? Ina masu fama da kujera ko wani ta bo a fuska? Ina masu fama da hawan jini? Masu diabetic? Ag cera an gwada yayi an tantance ingancin babu shakku ko kadan. AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login