Showing 54001 words to 57000 words out of 225640 words
kike yi ma aiki? Mama Fulani ko Ammy?”
“Dukansu”
Na amsa muryata na gargada.
“Ki daina jin tsoro ba wani abun zan miki ba. Ya sunanki?”
“Aisha”
“Ashe mamana ce ke, kina da kyau Aisha ke fulani ce?”
“Aa buzuwa ce”
“Shiyasa kike da kyau sosai ga gashi, an taba fada miki kina da kyau?”
Na shiru ina yin kasa da kaina sai yai dariya.
“Kar ki ce ban saba ganin kyawawa ba, na saba ganinsu ni ma ai kin ga na fiki kyau ko?”
Na dan dago na kalleshi sai ya shafa kansa yana dariya.
“Sunana Kamal Isma'il Isa, nan ne gidan mu kuma ni soja ne, idan kikai wani abu sai na kama ki, dan haka ki yi hankali”
Ya fada yana fiddo yar karamar bindigasa ya nuna ni da ita, aiko ba shiri na ranta cikin na kare cikin wani irin gudu da ban taba sanin ina da shi ba na zarce cikin gida, ina waigensa ya biyoni yana ta dariya.
*Littafin nan na kudi ne*
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
19.
Nasir ya fada masa a unguwar da ak fada masa ya sa an bincika amman ko fulani ba a samu a unguwarba balle wasu buzaye, zancen wani ja gini duk karya ce.
Jin wannan yasa Aliyu ya zabi ya cire nemanta da kokari fahimtar da ita idan ya ganta a ransa, tun da be san inda take ba, and gashi garin nemata har suna kokari mom samun matsala da Rahma, and idan ma yace dole sai ya nemota ya ai wani sabon aikine a gareshi, but he know one thing for sure tunanin zalincin da akai ma yarinyar nan ba zai taba fita a zuciyarsa ba, kyauta kuma ba zai taba gushewa a idonsa ba.
He keep himself busy these days saboda shirye shiryen da suke na zuwa Abuja ya san akwai aikin kamfaninsa yana jiransa, kamar yadda ya saba and Rahma ta masa complain cewar tana on ganin likita idan sun koma Abuja saboda matsalar haihuwarta. Da kanshi ya dauke ta suka je sukai Momynsa da Daddynsa sallama sannan naje gidansu Rahma suma sukai musu bankwana, domin tafiyarsu gobe ne. Farinciki gurin Rahma ba a magana tana ganin da zarar sun koma Abuja komai na damuwarta ya wuce, sun bar garin da Ataa take hakan zai saka hankalinta ya kwanta gashi kuma ta jin cewar idan ta je ga babban Likita kamar Doc Perry matsalar haihuwarta zata gushe, duk da acan din ma tana fargabar Mama Fulani saboda zancen haihuwa da take mata gashi kamar bata san Allah ne yake komai ba.
ATAA POV.
Ina ta gudu yana biye da ni a baya har na nufi garejin na boya sai kuma na wuce falon Mama Fulani a tunani ba zai iya biyo ni ya shigo ba, amman ga mamaki na sai ya biyoni har cikin Falon, mamaki ya hana ni cewa komai sai bin sada nai da iso, shi kuma yana ta murmushi kamar daman can mun saba irin wannan wasan da shi, zaunawa yai saman sofa yana maida bindigarsa aljihu.
“Ba ruwana idan suka zo suka maka fada”
“Ba za su min ba, sai dai ke su yi miki ke da kika kawo ni”
Ban sake wata maganar ba, gabana sai faduwa yake gudun kar Mama Fulani ta fito ta ganshi, gashi ban san mi zan ce mata ba, ban gama tunanin abunda zan yi ba sai ga Mama Fulani ta fito daga dakinta sanye da doguwar riga da alama wanka tai ta canja tufafi. A take hantar cikina ta kada tsoro duk ya bi ya cika min ciki, tana sauko ya mike tsaye a mamakina sai ganin nai ta sakar masa fuska tana masa murmushi.
“Kamal ne?”
“Ni ne Mama ya gida?”
“To ba dai Aliyu ya zo ba balle na ce, na san sai idan yana nan kake shigowa gidan nan”
Murmushi yai ya shafa kansa.
“Kawai dai yau na ce bari na zo na gaishe ki”
“Ato ka kyauta gaskiya, ka yi abun kai, ina Hajiya Uwani?”
“Tana nan lafiya kalau”
“Ke shiga kitchen ki dauko masa cup ki bude freezer ki dauko masa lemu”
Mama Fulani ta fada min, sai na juya da sauri na nufi kitchen din, ina shiga na duba inda kofuna suke na dauko tare da lemun na dawo falon na kawo a gabansa na dire.
“Mama ina kuka samu wannan mai aikin?”
“Wallahi wata wacce ta saba kawo mana mai aiki ta kawo ta mana ita”
“Okay ni kan na ce ban san da zamanta a gidan nan ba”
“Bata dade da zuwa ba”
“Okay”
Ya fada yana mikewa tsaye ba tare daya sha lemun ba yai mata sallama ya fice yana ta kallona kamar zai yi magana sai kuma be ce komai ba har ya fice.
“Zo ki dauki kayan nan ki maida su kitchen”
Mama Fulani ta fada tana daure fuska. Kamar daman umarni na ke jira sai na nufi lemun na dauka na kai kitchen na aje sannan na fito na dawo falon na zauna inda na sabawa kaina da zama na kurawa tv ido. Misalin sha biyu na rana da yan mintuna Mama fulani ta fito ta shiga kitchen ta dora abincin rana, guraren karfe biyu ta kammala abincin sannan ta fada min na dauko plate dina ta zuba min abinci a ciki, sai na tashi da sauri na nufi garejin na dauko abincin safe da ban ci ba na nufi garden na siyayarda tea Wainar kuma na cinye, daman ni ba soyayiyar dankali bane dan haka na shanya shi a inda na sanya ragowar kazar nan ta dazun. Sannan na kunna fanfo na wanke plate din na dawo part dinta na kawo mata.
“Aje kasa”
Sai na risina na aje da alama kyamata take da har ba zata iya rika plate din ba, debo abincin tai ta zuba min a plate sannan ta zuba min miyar bata saka min naman da ke miyar ba ta ce na dauka, ni kuma na dauka da sauri na fito balcony na zauna ina cin abincin a hankali. Ina daf da cinyewa Ya Muhseen ya shigo gidan da motarsa, inda manyan motoci suke yai parking sannan ya bude motar ya fito yana matsa remote din motar tana kara.
“Pretty nan kike cin abinci?”
“Eh sannu da zuwa”
“Yauwa”
Ya fada sannan ya shiga part din Mama Fulani be dade ba ya fito ya nufi wani bangare na gidan inda nake saka ran a can dakinsa yake, sai da na gama cin abincin na je na wanke plate din na maida shi gareji na aje sai na kwanta a gurin, ina ta tunanin yadda zan iya da zaman gidan, anya zan iya juye wulakanci irin na Mama Fulani? Amman ya zan yi tun da na riga na zo, Sai da la'asar na fito daga garejin nai alwala na koma nai sallah sai na nufi part din Ammy, tambayar ta nake son yi domin ita ce mai far'a da son mutane ba kamar Mama Fulani ba. Da sallama na shiga sai ta amsa min tana zaune kasa tana cin abincin.
“Tun dazu na ke nemanki ba ki shigo ba”
“Je kitchen ki dauko tuwon ki ga shi can kina cin tuwo da rana dai ko?”
“Eh ina ci”
Na gyada mata kai sannan na nufi kitchen din, sai na samu tuwon shimkafa da miyar yauki a rufe cikin wani plate an saka min har da man shanu, ga wasu manyan tsokoki a sama. Daukowa nai na fito sai na koma can kusa da kofar shigowa falon na zauna na soma ci, ba wani da yawa zan bi ba ni kaina na san cikina ya cika da shimkafar da Mama Fulani ta bani amman ina son tuwo sosai ga kuma manshanun da aka saka a sama da namomi ba zan iya barinsu ba. Ina cikin cin abincin wayar Ammy tai kara alamar kiranta akai, picking tai ta kara a kunne ban san mi aka ce mata ba na ji dai ta yi amsa da okay, sannan ta kalleni.
“Mamana kin iya zuba tuwo?”
“Eh na iya”
“To shiga kitchen ki samu plate ki bude fula gata can dinning ki zubawa Muhseen ki rufe sai kije ki kai masa kin ji”
Sude hannun na yi na tashi na nufi kitchen da kuzarina na dauko plate din sannan na dawo dinning na zuba nasa miya a wani plate din sannan na saka tuwon a dayan plate din na rufe na dauka na nufi part din Mama Fulani, Ya Muhseen kadai na samu a falon yana shan kankana da fork, ganina yasa shi murmushi ya mika hannu biyu ya karbi abincin.
“Yauwa thank you, ke kin ci abincin ki?”
“Shi na ke ci ka karani”
“To dauko ki zo nan ki karasa”
“Zan fi jindadi ci a can”
“Saboda Mama tana miki fada a nan ko?”
Ya fada yana bude tuwon.
“Kin ga kin fini cin abinci yanzu na ganki kina cin shimkafa yanzu kuma kina cin tuwo”
Murmushi nai har na soma jin kunya na baibayeni.
“Dauko min ruwa”
Na nufi kitchen din an bude freezer na dauko gorar ruwa da cup na kawo masa. Kamar daga sama na ji muryar Mama Fulani tana masa fada.
“Wai Muhseen baka kyamar yarinyar nan ne? Ka cika shige mata fa bana sin haka”
“Miye a jikinta?”
Banza tai masa tana jin haushin tambayar da yai mata, sai gyara tsayuwar jikar da ke hannunta take da alama fita za tai. Ni dai ban ce komai ba ina tsaye ina jin umarninsa ko zai sake bukatar wani abun ne, ban ji ya ce komai ba hakan yasa na fice na barsu ita da danta na koma part din Ammy. Da sallama na shiga kamar dazun, wannan karon kishingide na sameta tana kallo tv.
“Mamana amman ku fulani ne ko?”
Ta fada tana kallona.
“Aa ni buzuwa ce”
“Wane gari kike?”
“Sokoto”
“Tare da iyayenki kike zaune?”
“Babana ya rasu mama ce kawai”
“Allah sarki, ita ta turo ki aiki a nan kenan? Ina kika san Maman Salma ko yar'uwarku ce?”
“Aa ba mu da alaka da ita zaman unguwa ne kawai”
“Allah sarki, amman kina da kanen ko? Ke ce ta nawa gidanku?”
“Ni ce ta farko ina da kane amman ya rasu”
“Ayyah Allah ya jikanshi”
“Amin”
Daga nan bata sake magana ba har na gama cin abincin na tashi na maida plate din na wanke hannuna na dawo na zauna. Gefen kujerar muka cigaba da kallon a tare, sai ga Ya Muhseen ya shigo rike da plates bakinsa kunshe da nama ya miko min plates din.
“Kai kitchen”
Na karba da hannu biyu na nufi kitchen din na aje. Ban san abunda ya fadawa Ammy ba kallona kawai take tana dariya. Kamar yadda shi ma yake dariyar har na soma tsaguwa, ma tashi na bar musu falon na dawo gareji na zauna ina turo baki kamar an min wani abu. Tun da na dawo ban koma fita ba sai da magariba, shi ma sai da na sauke farilla sannan na fito harabar gidan na zauna ina ta kallon fitilun da suka haska gidan gwanin sha'awa. Ban tashi daga gurin ba sai da aka kira isha'i sannan na nufi garden da tsoro nai alwala na dawo garejin nai sallah ta sai na kwanta a gurin ina ta jin tsoron da ban san ta ina yake fito min ba, kamar jiya ba ni kadai na kwana ba, yau kan tsoro ya kamani sosai ko iska ya kada sai na ji kamar wani aljanine zai kama ni, da naji na kasa natsuwa da gurin ne na taso na koma Part din Ammy na zauna, ina ta kallon Anty Zee Inteesar da ke cin abinci a plate daya.
“Shiga kitchen ki dauko na ki”
Inteesar da fada min, ni kuma na tashi na shiga kitchen din a inda na samu abincin dazu nan aka sake aje min wani yanzu ma tuwo ne kamar dazun sai dai wannan miyar ganye ce ba kamar dazunda taie miyar yauki ba. Dauko abincin nai na fito waje falon na zauna na ci sai da na koshi sannan na tashi na maida plate din na wanke hannuna.
Haka rayuwata ta cigaba da tafiya a gidan kullum Mama Fulani da Yayanta cikin nuna min kyama suke, a gurin Ya Muhseen kawai na ke samun sakewa har dadi nake ji idan yana nan, tun ina kin sakewa da shi har na soma sakewa kwanan biyu da nai a gidan sai na ji kamar daman can na basa da gidan, sai na fara sabawa da halin Mama Fulani da kuma Ammy da bata nuna min kyama, sai dai abu daya ke damuna kwana a gareji da kuma wanka idan zan yi sai naje garden na boya a bayan itace sannan nai wanka, da sabulun da Ammy ta ba ni, idan kuma ba haya zan yi sai dai na raba a dakin mai gadin na shiga nai.
Yau ma na yi aikina kamar yadda na saba, bayan na gama da bangaren Mama Fulani na je sashen Ammy nai mata nata sannan na shiga bangaren Ya Muhseen shi ma na gyara masa nasan dakin da falon na goge komai kamar yadda na fara yi masa a jiya na fito na dawo bangaren Mama Fulani, kowa na falon kasancewar Weekend ne Ya Muhseen da Anty Maryam na zaune a kujera daya tana nunawa Ya Muhseen wani abu a wayarta, Mama Fulani kuma na zaune kasa tana mulka fulawa, sama sama nake jin tana firar dan ta nan tafe dole ta dafa masa abunda ya ke so, sai da ta gama mulka fulawar sannan ta kalleni.
“Ke je kitchen ki yanka min kabeji, yana nan a roba”
Na amsa da to ina mikewa tsaye na nufi kitchen din, yana jiyo lokacin da Ya Muhseen ke fadar cewar ina da gashi, har Mama fulani na masa fada wai yana ta abu kamar be tana ganin kyakkyawar mace ba. Karamar kujera na samu na zauna na dauko daya daga cikin wukaken da suke hade guri daya na soma yanka kabejin, ban ankara ba na yanke kaina sai jini, ban san lokacin da na kwala wani uban ihu ba na mike tsaye da sauri jikina nata rawa abun ka da mao tsoro ga shi ban saba da amfani da wuka sosai ba, rabon da naji ciwo har jini ya fito haka har na manta.
Cikin sauri Ya Muhseen ya shigo kitchen din.
“Daman na san yankewa kikai”
Ya fada yana kallon yadda jinin ya samu hanya sai bulbulowa yake, ni ko ina ta kuka kamar hannun ya cire gaba daya, wanda hakan yasa Anty Maryam shigowa kitchen din tana tambayar ba'asi. Wani dogon tsaki taja ganin ganin a yatsa ne kawai na yanke amman nake wannan ihun. Hannun nawa Ya Muhseen ya riko muka fito daga kitchen din ina ta kuka sosai muka nufi kofar fita jinin nata zuba. Bangarensa yaje da ni ya dauko wani dan karamin akwati ya bude ya saka ruwan nan masu shegen zafi ya goge min gurin ya saka min wani maganin sannan ya saka min kada ya rufe min yatsan.
“Sarkin raki”
Ya fada yana kallon yadda hawaye suka bata min fuska, na turo baki waje kamar yadda yara suke idan sun ji ciwo.
“Kadan ne fa kika ji ciwon amman kin cika mana gida da ihu ke sagartacciya ko?”
Na yi kasa ta kaina ina kallon yadda yake aiko min da murmushi.
“Shikenan zaki iya tafiya”
Ina juyowa shi ma ya tashi tsaye muka fito tare, ina gaba yana bayana har muka shiga part din Mama Fulani.
“Muhseen karka sake shiga safgar yarinyar nan”
“Mi akai?”
“Na dai fada maka? Ba ita ba kai daga yau, ke kuma dauko Mopper ki goge jinin nan”
Ta karasa tana kallona, sai na nufi inda mopper take na dauko na goge duk inda jinin ya diga sannan na koma kitchen din, zan cigaba da yanka Anty Maryam ta shigo wai na zubar da wannan kabejin basa son sa na yanka wani sabo. A kwandon shara na zuba kabejin na dauko wani a freezer dake kwance na soma yankawa, a hankali nake har na gama sannan na aje mata shi na fito na nufi part din Ammy. A lokacin da na shiga falon ita kuma tana kitchen tana hada fruits salad, a falon nai zamana har aka yi azahar sannan ta fito ta miko min plate da spoon.
“Ga abincin ki”
Hannu biyu na saka na karba ina mata godiya. A gurin na zauna na ci sannan na aje mata plate din a kitchen, na fito na nufi garden na wanke hannuna da fanfan gurin, nai zamana gurin ina ta kallo wasu kananna tsuntsaye dake cikin keji suna cin giďa, ina jin lokacin da motacin har biyu suka tsaya a habarar gidan amman ban tashi ba sai da na gaji da zaman na fito na ratsa motocin zan shiga part din Mama Fulani sai na soma jin kamshin wani turare mai dadi, da na taba ji sai dai ba zan iya tuna inda na ji shi ba. Tura kofar falon nai na shiga da sallamata babu wanda ya amsa min sai Ya Muhseen, Anty Maryam da Anty Rukaiya duk sun sha jinin jikinsu ko motsin kirki basa yi, Mama Fulani kuma na zaune a kujera daya da wani saurayi tana bare masa abaya ba tana mika masa, da na kalleshi da kyau sai na ga she mutumen da nai ma aiki kamin na dawo Abuja hakimce a kujera yana kallona da mugun mamaki.
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Idan ba ki biya ba karki karanta hakkin wani. Idan kuma kin ji zaki iya Bismillah.
20.
Ba ni kadai yake kallo ba, gaba dayan jikina da duk wani motsi takun da nake na karasa gurin da na saba zama na zauna yake kallo. Nima idona na kansa ina ta mamakin abunda ya kawo shi gida, da alama yana da kyakkyawar alaka da mutanen gidan, domin yadda na ga Mama Fulani na bare ayaba tana bashi yana ci kamar wani karamin yaro ya nuna yana da muhimmanci sosai a gareta duk da ban san alakarsu ba.
“Ke bana son kallo”
Ya fada yana kallona, sai duk suka juyo suka kalli inda na ke kokarin zama.
“Haka ta ke da shegen kallo kamar yar kauye”
Anty Maryam ta fada tana watsa min harara. Ya Muhseen yaja