Showing 141001 words to 144000 words out of 225640 words

Chapter 48 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

wuce na Aliyu ya kara aure”

“Wannan dalilin ne yasa na so Aliyu ya aureta amman ai Muhseen ya kasa fahimtata, kwana biyu da suka wuce Rahma dai fushi...... ”

Momy ta labartawa Mama Fulani abunda ya faru ciki har da jawabin da Mahaifiyar Rahma tai mata, a take ran Mama Fulani ya bace

“Uban me suke takama da shi a duniyar nan? Su har suna da bakin yi ma mutane iskanci? Ai shiyasa na ke son ya kara aure mu nunawa amaryar kauna in yaso ita sai ta mutu, ya yana bukatar aure ko Allah zai ba shi haihuwa ma, ta san da maganar auren ne? Amman zan cen ba aza ayi kishi da talaka ba kam tana da gaskiyarta wa yake son rabar talaka”

Momy ta hade yawun bakinta kana ta ce.

“Bata sani ba, yanzu haka tana dubai taje hutu”

“Ahhh hutu ko? Aiko kamin ta dawo za ayi auren nan, idan ma ni Aliyu zai dauki shawarata ya aika mata da saki kawai ni fa bana son rai ni”

“Ba sai ya sake ta ba, kin san halinndan ki ai ba lallai ne ya ce zai yarda ya sake ta ba, amman ko auren ya kara ai sai samu saukinta, amman yanzu ni na janye maganar auren ma kara dai ta zaba tsakanin shi da Muhseen duk wanda take kauna sai a aura mata shi idan ma wani take so ba shi ba sai a aura mata?”

“Wacece wai?”

“Ataa”

“Ataa”

Mama Fulani ta maimaita tana kallon Momy baki sake.

“Kam uban nan”

Ta daki kirji ta buga kafa da kasa.

“Dan Allah idan wasa kike ma ki daina”

“Babu zancen wasa a ciki Wallahi gaskiya na ke fada miki, Ataa ce”

“Ataa dai wacce tai aiki a karkashinmu? Ita ta samu wannan damar da har Muhseen da Aliyu suke ribibinta ko kuwa dai wata Ataa dabam, yar aikin gidansu? Yar talakawa yar bara a titi? Dan kari, ita ce kike cewa za ki bata dama ta zaba? Har kike tunanin bata Aliyu? Ko dai kin manta wacece ita?”“Miye abun mantuwa a ciki? Yarinyar da a hannuna ta ke yanzu, talauci ba illa ba ne”

“Aa Wallahi illa ne idan kina da talaucin anya kina ganin za ki iya shiga jirgi ki zo Abuja yau? Na dauka yar wata manyan mutane ce a cikin sokoto ko nigeria ma”

“A haka dai yayanki suke sonta”

“Lalala ban yarda ba, ina dalilin jayaya akan wannan banzar yarinyar? To ko dai ta shanye ku ne gaba daya? Daman ance buzayen nan mayu ne, ke kira min Aliyu yanzu nan”

Mama Fulani ta karasa tana kallon Rukaiya a take Rukaiya ta kira a waya ta sanar masa Mama Fulani na son ganinsa, daman yana garden yana ta kallon gurin da Ataa ta saba tsayawa ta wanke plate dinta gani yake kamar tana a gurin. Be bata lokaci ba ya shigo falon.

“Aliyu Ataa kake so? Ko kuwa Momy ce take son taka maka ita ta cilasta maka?”

Tun kan ya karaso kusa da ita ta aika masa da wannan tambayar. Sai dai be amsa mata ba sai da ya karaso kusa da ita ya zauna.

“Mama na yi wani abun ne?”

“Wa kake so? Wa kake son ka kara aura a matsayin mata ta biyu?”

“Ataa Mama and i need your support”

“My support? Aliyu are you out of your Sense? Yar talakawan yar aikin gidanku”

Yayi shiru be ce komai ba.

“Lalala ban aminta ba ka cireta a ranka tun wuri, eyy yarinya ta samu matsayi har da wani bata zabi ake tsakanin Aliyu da Muhseen ko? Eh lallai”

Daga Aliyu har Momy shiru sukai, Momy bata son saka bakinta saboda Aliyu ne, shi kuma ya rasa kalmomin da zai hada ya fahimtar da Mama Fulani ta ya ma za'ayi ta fahimta, yasan duk wanda zai fadawa yana son Ataa a yanzu zai yi mamaki. Fada sosai Mama Fulani ta fara masa ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, tun yana iya saurare har ya ji kunnuwansa ba za su iya daukar yadda take aibanta Ataa ba a gabansa. Harabar gidan ya fito yana sacikawa bakinsa iska ya busar.Part din Ammy ya nufa daman bata san da zuwansu ba, domin Momy ba ta kira ta fada mata tana nan zuwa kamar yadda ta saba ba. Ta yi farinciki sosai da ganinsa daman ita kadai ce a falon. Ba laifin ya dan sake yayi fira da ita duk kuwa da be saba hakan ba domin zancensa be eh a a ba, sai kuma tambayar wani abu idan ta kama.
   Fried rice da miya ta kawo masa ya karba ba dan yana jin yana son ci ba, domin ko da safe da Lipton kawai ya karya be sake cin komai ba. Wayarsa ce tai ringing yana dubawa ya ga Number Abbah, yayi mamakin ganin kiransa domin ba kasafai yake kiransa ba sai idan wani abun ya taso.

“Assalamu Alaikum Abbah”

“Wa'alaikassalam, Aliyu kun shigo abujar ne?”

“Eh Abbah”

“Ka same ni office yanzu”

“Okay Abbah”

Yana sauke wayar ya aje plate din abincin ya mike tsaye.

“Ammy Abbah yana nema na bari na je na dawo”

“To a dawo lafiya abincin sai ka dawo ko”

“Eh”

Ya fice da sauri cike da son sanin dalilin kiran da Abbah yake masa. Sai da ya shiga part dinsa ya dauki keys din motarsa da ke gidan,sannan ya fito ya bude motar ya shiga. Cikin ka kannen lokaci ya isa kamfanin kamin ya isa office dinsa ya kira a waya ya sanar masa ga shi nan zuwa, sai Abbah ya ce ya jira shi office din yana wani gurin meeting a kamfani, haka Aliyu ya shiga ya zauna har aka kira sallah Azahar ya fita yaje yai sallah ya dawo ya zauna a ciki yana jiran Abbah. Sai kusam uku da yan mintuna Abbah ya shigo office din rike da takardu a hannunsa. Cikinnl girmamawa Aliyu ya gaishe shi ya sama masa yana murmushi sannan ya zauna a kujerarsa mai lilo yana kallon Aliyu ya ce.

“Hajiya Fulani fada abunda ya faru”

Aliyu ya yi kamar be san komai ba.

“Na me Abbah?”

“Ance Momy ta zaba muku mata kai da Muhseen ko? Shi Muhseen ya ki yarda ya ce ta ka yake so?”

Aliyu ya yi kasa da kansa.

“Na kira Daddynku na yi magana da shi, indai yarinya tana son ka kana son ta za a aura maka ita”

Da sauri Aliyu ya kalli Abbah, sai ya rasa abunda zai ce, sam be tsammaci haka daga gurin Abbah ba.

“Amman Abbah Mama bata so, saboda yarinyar ba yar masu kudi ba ce, tana ganin kamar kaskanci ne a gurina da gurinta?”

“Yarinyar bata da tarbiya ne?”

“Tana da Abbah talauci ne kawai matsalarta”

“Kar wannan ya dame ka idan ka ce zaka biye fulani da tsare tsarenta zaka sha wahala kamin ka samu wacce zata dace da ra'ayinta”“Abbah idan bata so zai zama da matsala a ciki, yanzu haka fadan da ta gama min kenan?”

“Kai iyayen yarinyar sun tashi aurar da ita? Kuma ka tabbatar tana son ka?”

“Momy ce zata mata komai, kuma ba dole ne idan a daura ta tare a lokacin ba, amman daurawar zai kwantar min da hankali Abbah”

“To ka shirya assabar mai zuwa za a daura muku aure”

“Abbah da gaske?”

“Na taba maka wasa? Ka shirya kuma ka sanar da iyeyenta ka sadani da su ni nan zan daura maka aure”

“Abbah....”

Sai kuma yai shiru Abbah ya kalleshi da kyau.

“Wani abun ne?”

“Gaskiyar yarinyar bata kowa a yanzu, daman yan nijar ne kuma mahaifinta ya rasu ba su koma ba, mahaifiyarta ce kawai a raye yanzu haka a gidan Momy take zaune saboda yana ba su da inda za su raba”

“To yanzu ya kake son yi? Ba wata matsala Abbah wannan ce kawai”

“Za a san yadda za ayi, Daddyn ma ya ce zai tambayi yarinyar idan tana son ka In-Sha-Allah za a aura maka ita kar maganar Haj Fulani ya tashi hankalinka”

Gaban Aliyu ya fadi jin cewar za a tambayi Ataa idan tana sonshi sai dai hakan be hana shi murna ba har da zagayawa ta inda Abbah yake yai masa godiya sannan ya taso ya fito office din ransa fari tas. Be taba jindadin zuwansa abuja kamar na yau ba, ganin yake wannan zuwan ya fi ko wane saka shi farinciki da jindadi fiye da ko wane. Haka ya isa gida da farinciki kamar wanda aka yi ma kyauta karin rayuwa. Sam ba zaka ganshi yanzu ka ce shine ya fita dazun a haka ba, yanzu kan kana ganinsa ka san yana cikin farinciki. A daki ya samu Momy da Mama Fulani sai kuma Muhseen da ke zaune gefen Mama Fulani kansa a kasa da alama hakuri yake bawa Momy.

“In banda abinku yanzu wannan yarinyar ce har zata shiga tsakaninku? Wallahi Ni abun har mamaki yake ba ni, abu kamar a shirin film wai kuna son yarinyar nan har da kai Aliyu, duk matan duniyar nan? ”

Aliyu ya nemi guri saman kujera ya zauna yana shiga da fitarda numfashinsa a hankali.

“Na sani Momy ta isa ta zaba min mata, a lokacin da Momy tai min maganar nan raina ne ya bace sosai har na kasa controlling kaina, amman Mama ta nuna min illar abunda nai Abbah ma haka, Momy ina neman yafiyar dan Allah ki yi hakuri”

“Ba komai Wallahi ya wuce a gurina, taya ma zan ga laifinka? Abunda nai kana fa gaskiya yayi kama da son kai, kuma be da ce na yi haka ba”

“Haka shine daidai Momy, ban cancanci zama..... ”

Na dauki lokaci kamin ya karasa ragowar kalamar.“Zama... Mijin... Ataa... Ba... Sai dai har gobe ban yarda akwai wani hali nawa da zai iya hana ni auren Ataa ba... Kuma zan hakura da ita saboda kawai na zama mai biyayya a gareku kuma ba zan sake yin maganar ta ba, amman tana nan a zuciyata”

Jikin Momy ne kawai yai sanyi yayinda Aliyu kuma ya shiga wani tunanin yana ganin kamar Muhseen ba zai hakura haka nan kawai ba, wata kila ya canja shawara ne ko kuma yana shirin bullo da wani abun, amman wannan duk mai sauki ne idan har ya samu ya auri Ataa duk wani abun da zai biyo baya mai sauki ne a gareshi, and it would be better if be fadawa kowa zancen da su ka yi da Abbah ba, har sai idan a tsakaninsu maganar ta fito.

“Babu rashin cancanta a aurenka da Ataa, saboda son aure kake mata kuma zaka auri Ataa matukar ta bude baki ta furta cewar kai take so”

Mama Fulani ta tari numfashin Momy tana daga mata hannun.

“Saboda girman Allah ki daina wannan maganar ma, wani irin ta zaba sai ka ce wasu awaki ko gwanjo? Muhseen dai ya gane kuskurensa kuma ya dawo a hanya, Allah ya raba su da wahala amman yarinya ta zame mana bala'i”

Har cikin ransa Aliyu ya ji kalmar bala'i da ta kira Ataa da ita har sai da yaja numfashi ta sauke.

“Na hakuri da Ataa Momy ina mata fatan miji na gari, and zancen Amina ina son a bani kwana biyu zan yi shawara”

Momy ta gyada masa kai idonta na cika da kwalla zuciyarsa na raya mata bata tai daidai ba, kuma bata kyautawa Muhseen ba. Mikewa yai tsaye jiki a sanyaye ua fito daga dakin da ya sauko kasa sai da ya saka hannunsa ya dafa zuciyarsa ya daga kansa sama ya hade yawu sannan ya cigaba da sauka stairs din.Aliyu ma tashi yai ya fice daga dakin zuwa cikin motarsa, wayarsa ya ciro ya kira Husna ringing biyu ta daga tana kiran sunansa.

“Husna ki je bq idan Ataa na nan ki kira ta gefe ki bata waya”

“Tau”

Bata kashe wayarba domin ta san halin yayanta baya son a kashe masa waya, yana jin lokacin da tai sallama ta shiga ta gaishe da Nana ta tambayi Ataa Nana ta ce masa ta tafi makaranta, sai dai bata amsa masa ba sai da ta fito daga bq sannan ta kara wayar a kunnenta.

“Yaya bata nan wai ta tafi islamiya”

Be ce komai ba ya kashe wayar zuciyarsa na raya masa wani zai tare ta a hanya yai mata magana ko ya yaba kyauta.gaba daya yanzu hankalinsa ya koma gurin Ataa ya manata da kowa da komai da ke gabansa.


ATAA POV.

karfe shida muka taso daga ilslamiyar kamar dai jiya, maganganun Nana na ta min yawo a kwakwalwa ga kuma tunanin abunda ya baro ta da familynta ya tsaya min a rai, guduwa dai ta alama amman miye silar gudurwar da har take ganin abunda aka aikata mata sakamako ne a gurinta? Ga kuma maganar Aliyu ma ta tsaya min a rai ashe zai iya zubar da kansa kamar haka ya furta min kalamai irin wadannan? Haka nan kawai na ji ina da bukatar ganin fuskarsa wata kila dan na kara tabbatarwa ne ko kuwa dan jiya ne abun ya faru na ke son sake faruwarsa a yau duka ba zan iya yanke hukunci ba a yanzu.

“Assalamu Alaikum”

Wata kyakkawar muryar mai dadi sauraro ta yi min sallama ta bayana, sai na juyo na ina amsawa tare da kallon mai sallamar. Bakin mutum ne cikin shadda ruwan kasa da hularsa mai haske taba ni ka ji hadisi sajensa ya kwanta gwanin sha'awa kama ganinsa ka san irin ustazan nan ne da ko kallon mata basa son yi.

“Dan Allah ina ne gidanku?”

“Lafiya?”

“Lafiya Kalau nuna min kawai na ke son ki yi”

“Can mai jan gate”

Da hannu na nuna masa kasancewar ina daf da gidan ne.

“Na gode”

Sai kawai yai gaba ya bar ni a gurin tsaye da mamaki, da kallo na bishi har sai da na daina hango shi sannan na karasa gate din na buga aka bude min na shiga ciki, harabar gidan na ke hangowa ina son tantance abunda na ke hangowa Doc Bukar ne tsaye da Daddy suna gaisawa, har na yi kamar ban gansu ba zan wuce sai Doc Bukar ya kira ni.

“Aisha....”

“Na'am”

Na amsa sannan na juyo na doso inda yake tsaye, har kasa na risina na gaishe da Daddy ya amsa min da far'a yana nufi kofar falon ya bar ni da Doc Bukar tsaye muna gaisawa.

“Daman na zo gurin Aliyu ne kuma ba ya ne sai ga Daddy ya shigo muka gaisa”

Na yi shiru ban ce komai ba sai gyra littafaina na ke hannuna.

“Daman kullum ina son na zo mu gaisa sai Aliyu ya ce ba ki gidan, ya mai jiki?”

“Al-hamdulillah”

Ganin ina masa ciki ciki kuma babu sakewa a tare da ni ya saka ya bude motarsa ya dauko kudi ya miko min.

“Gashi ki gaida Mama”

Kasa Karba nai, daman ko lokacin da nake bara ina neman kudi dalili ne wanda a yanzu babu shi.

“Aa na gode”

Na juya na nufi bq din na bar shi a gurin tsaye, sai da na shiga na cire uniform dina na saka wata doguwar riga sannan na ji tashin motarsa a lokacin Nana ta fito daga bandaki.

“Kin dawo”

“Eh Nana ya jikin na ki?”

“Al-hamdulillah, Hajiya ta dawo?”

“A a wani abun ne?”

“Idan ta dawo ki sanar da ni, ya kamata mu tafi wani gurin kuma tun kamin mu saba da nan”

“Wani gurin zamu je kuma Nana?”

“Eh In-Sha-Allah”

“Amman miyasa?”

Bata ba ni amsa ba Siyama tai sallama ta shigo wai na zo Daddy yana nemana, Hijab dina na dauka na saka na bi bayanta jin kiran Daddy da kansa na sam abu ne mai muhimmanci, har part dinsa ta shiga da ni yana zaune kasan carpet da kofin ruwa a gabansa da waya har biyu yana dannawa. Ko a. Lokacim da ya amsa min sallamata bw kalle ni ba ya amsa min ne kawai sai Siyama ta mike ta fita ta barni. Kaina a kasa lokacin daya aje wayar ya soma min magana.

“Abunda ya faru ya riga ya faru ki manta da komai kuma ki dauka komai be faru ba, mu tamkar ya muka dauke ki dan haka za mu iya yi miki komai kamar yar da muka haifa, ki janye maganar Momy ko ta Muhseen ko ta Aliyu, na ba ki kwana biyu ki je ki yi tunani ki fada mana wanda kike so, sati mai zuwa auren kuma ba zai hana ki karatu ba za a miki auren ne saboda ki samu natsuwa kowa ma ya samu, Momy za tai maganar da Mahaifiyarki idan ta dawo gobe wannan tsakanina da ke ne”

Sati daya? Kamar wata yar tsana? Kamar ua sati daya? Sum gaji da mu ne ko kuwa dai suna son tsawwalawa mana ne ko kuma wani abun ne da dabam.da wannan tunanin na taso na dawo bq kaina a kulle.
ZAKI

By Khadeeja Candy

42...


A daki na samu Nana zaune ta rafka tagumi tana kallon kofa kamar mai jiran shigowata. Nima damuwar ce a fuskata na maganar da Dddy ya fada min yanzu, sai dai na yi kokarin moye tawa damuwar tare da tambayar abunda yake damunta da kuma dalilin barin gidan da take son mu yi bayan na fara karatu a yanzu abunda na rasa shekaru da dama.

“Nana miyasa kike son mu tafi? Momy ta roke ki da mu zauna kuma karatun da na fara dainawa zan yi Nana idan muka tafi”

Hawaye na gani a fuskarta.

“Ina ganin kamar zaman gidan nan matsala a gurin na ina ganin kamar son ki ya haddasa wata kiyayya ko kuma fada a tsakanin yan'uwa biyu, Hajiyar gidan nan ta mana karamci iya karanci ba kowa zai yarda ya zauna da irin mu ba, amman ta zauna da mu ta nuna mana kauna, ban san miye alakar Muhseen da Aliyu ba, na san dai yan'uwane amman yan'uwanta kan da ina ne ban sani ba, bana son na zama silar rushewar wasu iyalin bayan barin nawa da nai”

“Nana miyasa kika yi wannan maganar?”

“Na baki shawara auren Aliyu ne a mahangar da na ke ganin ta dace da ke kuma na ke ganin kamar ba zata cutar da ke ba, na san ba ki san so na kuma ba lallai ne ki iya fahimtar komai a yanzu ba wata kila sai gaba, kina da damar zaben wanda kike ganin ya dace da ke Ataa kuma wanda kike jin ya kwanta miki a rai”

“Miyasa kika ce haka?”

“Sayan tafiyarki islamiya, Husna ta shigo da waya tana neman na fada mata ta kin tafi makaranta, an jima kadan kuma sai Amina ta zo wayar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login