Showing 180001 words to 183000 words out of 225640 words
komai yanzu ai na daina jinsa, daman warin manja ne kuma ya daina”
Na nufi gurin kular abinci na zauna ya saka hannu ina ci ahankali iyakar dauriya nayi domin har ga Allah yau dai bana son warin manjan nan a kusa da ni wata kila saboda zuwan da mu kai a Las Vegas ne dan sabon da nai a can na wata daya yasa na fara mantawa da abincin naija.
“Aliyu ina son tea”
“Okay”
Ya tashi ya fice rike da wayarsa, yana fita nai saurin nufar bandaki na amayarda da dan abunda na ci na tuwon na wanke bakina na dawo, jinginawa nai da gadon, ina ta tunanin Nana da yadda za tai idan tai arba da mahaifinta.
Ba a wani dade ba sai ga Aliyu ya shigi dauke da mug ya zauna kusa da ni ya kai min tea a baki, kadan na kurba shi ma na ji bana sonsa kuma bana son na nuna masa kar yace dole sai munje asibiti, a dole na daure na hanye rabin myg din sannan na kawar da kai sai ya aje kofin ya janyo ni jikinsa ya kwatar ya ciro wayarsa yana lasawa.
“A kira miki Nana ko?”
Na gyada kai. Be ce min komai ba sai da ya kira Momy suka gaisa ya bani muka gaisa sannan ya sake karba ya ce ta bawa wani a kaiwa Nana wayar ina son magana da ita, yana rike da wayar har aka kai mata ina jin lokacin da suke gaisawa Aliyu har wani kasa yake da kai kamar ba shi, lokacin daya miko min wayar sai ya tashi ya fita daga dakin ya bar ni kadai.
“Nana kina nan lafiya?”
“Lafiya kalau kun dawo lafiya?”
Ina jin yanayin muryarta na san ba kafiya ba, muryarta ya nuna tana cikin damuwa da kuma alamar kamar ta yi kuka ma.
“Lafiya Kalau, Nana mun dawo muna Abuja”
Ta yi shiru bata ce komai ba.
“Nana na hadu da Mai Martaba Sarki Agadaz”
Nan ma bata ce min komai ba.
“Nana”
“Naam”
Ta amsa min cikin kuka.
“Nana kike yi?”
“Idan ban yi kuka ba Ataa mi zan yi? Yanzu haka Yayan yayuna suna nan tare da ni gobe tun da safe sun ce za mu wuce Abuja shi ya bukaci a azo da ni”
“Nana har sun iso? Na dauka ma ba ki ji ba”
“Da yamma suka zo, amman har yanzu ina ta ganin kamar ba gaske ba, wata kila sai idan na yi arba da shi zan yarda, wata kila ya yafe min wata kila kuma wani abun ne dabam zai fada min, hakika ina kaunar haduwa da mahaifina ina kaunar saka shi a ido ne ko da kuwa idan na je tsine min zai yi, amman Ataa har yanzu ina jin kunya da nauyin abunda na aikata”
“Wannan na wuce Nana, ba a iya gyara abunda ya riga ya bace sai dai a tari gaba, ni kaina ina fatar kuma ina tunanin yafiyarce domin ya kirani da jikarsa, jininsa diyar diyarsa, Nana na jidadin ganinsa ko da kuwa wulakanta ni yai ya tozarta ni zan yi farincikin ganin Kakana bayan ke da Lukman da Baba yau ba kara ganin wani wanda yake jinina”
“Allahu Akbar”
Shine abunda ta fada sai ta fashe da kuka ni ma kukan na ke, mun dauki tsawon lokaci a haka sannan na sauke wayar jin kamar kukan zai yi ma Nana yawa na aje wayar kasa ba tare da na kashe ba. Bayan sauke sallah isha'i Aliyu ya dawo dakin ganin yadda fuskata da ido na sukai ya san kukan nai daman haka na ke idan nai kuka abun baya boyuwa ga farin daya mutum.
“Idan har Mahafin Nana ne suka hadu da shi kamar yadda kika fada be kamata ace kina ta damun kanki da kuka kamar haka ba, a tunani farinciki ya kamata ki yi”
“Wani farin cikin Aliyu ya yi har sai an koka, taya kake tunanin mace da aka haife ta tun davta tashi bata san kowa na ta ba, rana tsaka ta hadu da kakanta kai tsammanin murna kawai za tai? Mutumen da ganinsa a tare da Nana shine yankewar zubar hawayenta kuma farincikinta, idan har zai yafe mata ya karbe a yadda take yarsa Aliyu ni ma zan koma ya kamar kowa, mai gata ba kuma gata na naira ba gata na yan'uwan uwa da na uba a tare da ni”
Zaunawa yai kusa da ni daman tun da muke maganar a tsaye yake ni kuma ina zaune saman carpet din da nai sallah.
“Kin ce ba ku da kowa a nan, kin ce ba ki san kowa na ki ba tun da aka haife ki, taya kika gane cewar kina da alaka da wannan mutumen? Babyna mi ya raba ku da danginku? Na dade ina son nai miki wannan maganar amman tunanin sakaki a damuwa ko Mama (NaNa) yasa ban cika damunki ba, kuma ina da burin ko da tsawalla miki da sanin hakan sai na aureki saboda kar na ji wani abu da zai iya zama sanadin da wani a familynki ko nawa zai iya hanani aurenki, na aure ki ba tare da sanin kowa na ki ba sai dan nuna miki tsantsar kauna ni da Momy, Wallahi Ayusher ko da daga sama kika fado zan aureki ba tare da damuwa ba, saboda ke na ke kauna ba wani abun daya shafi dangantarki ba ko kuma asalinki”
Kallonsa na ke hawaye taf a idona wata irin kalar kaunarsa da begensa ne ke shiga cikin raina. Hakika Aliyu yayi min abunda ba kowa ne ke yi ba, auren mace da baka san asalinta ba, ko da dan kyauna Aliyu ya aureni yayi min hallacin tun da be taba bayyana hakan ba ya bari a cikin ransa kuma be taba nuna min ba.
“Ko da ka tambaye ni asalina a wacan lokacin ko kuma anan gaba idan har wannan abun be bayyana ba, ba zan iya fada maka ba, saboda bana son bayyana abunda Nana ta fada min a matsayin sirrin wanda na san jinsa a gurin wani zai iya haifa mata da matsala ko kuma damuwa”
Hannunsa ya kai ya riko nawa.
“Kina da karancin shekaru amman kina da wayo da hikima akan dukan abunda ya shafi mahaifiyarki, hakan na da kyau kaunarki na ta karuwa a raina ta ko'ina”
Dan murmushi nai ina hawayen da suka ji su tsaya min. Sai ya jani jikinsa ya rumgume ni kuma na lafe abuna kamar ba a bangaren Ammy muke ba, domin na fara sabawa da yanayinsa a yanzu.
“Ba ni labari ya kai Mama ta rabu da danginta”
Kamar mai karanta labari haka na jera masa yadda komai ya faru kamar yadda Nana ta fada min. Ya tausaya mata matuka kuma ya nuna min jindadinsa da gwarin guiwar cewar Mai Martaba sarkin Agadaz zai yafe mata ta koma cikin danginta ni kaina na tabbatar da hakan domin na lura da yadda ya nuna damuwarsa da ita.
“Za mu je mu yi ma Mama Fulani sallama sannan mu wuce gida”
Kasa nai da kaina alamar bana son zuwan can. Sai ya mikar da ni tsaye.
“Babyna no matter what Mama Fulani zata miki dole ne ke yi respecting dinta matukar kina respecting din Momy da kuma ni”
Ban ce masa komai ba, domin ba zan iya fadar wata mummunar kalma akan babban mutum kamar mama fulani ba, ba kuma zan iya aibanta dan'uwan Aliyu a gabansa ba, saboda mijina ne kuma ya nuna min kauna be kama na ci zarafin wani dan'uwansa a gabansa ba ko kuma na fadi wata maganar wacce zata sosa masa rai, duk kuwa da kasancewar ban san alakar da ke tsakaninsa da Mama Fulani ba, ba zan taba son Mama Fulani ba har abada saboda irin kiyayyar da ta nuna min da kyama ita da yayanta sai dai hakan ba shi yake nufin na nuna a gaban Aliyu ba, taya zan kauna ci macw da ya kirani da mahaukaciya, mayya, yar talakawa, yar matsiyata, tai min korar kare a gidan nan, ta hanani taba abun gidanta abinci ma sai da na tara dankwalina ta zuba min, daga baya ta ware min komai nawa dabam kamar wata karya, matar da ta mareni na suma saboda kawai ina rokon ta bar ni na yi mata aiki ta biyani na nemawa mahaifiyata magani? Har abada kuma har duniya ta hade ba zan taba manta wannan ba.
Ba ni da zabi daya wuce na bin umarninsa, a dole na bi yo bayansa muka fito tare daga dakin Zee muka sauko kasa inda Ammy take zaune, gaba dayansu kallona suke har Ammy irin kallon na kamar mamaki.
“Wani sakamako sai Allah Aliyu, ka auri yarinyar ba dan ka san kowa nata ba, ba dan komai na ta ba, sai ga shi Allah ya maka sakamako da inda baka yi tsammani ba, hakurin da kai da zama da Rahama Allah ya baka wacce ta fita komai”
Kamar yadda suke mana kallon mamaki haka ni da Aliyu muke musu shi jin irin maganar da ke fitowa daga bakin Ammy. Zaunawa Aliyu yai a kujera ni kuma na zauna kasa inda Humaira take zaune kasa.
“Shiyasa ba a son ka wulakanta mutum ba ka san abunda zai zama ba nan gaba, kuma ba kasan da inda zai iya taimakonka ba, ba dole sai babban taimako ma wani ko alfarma yai maka ya baka ruwa ka sha ai ya jidadin a lokacin da kake jin kishi, waya zai tsammanci ke din jikar babban mutum ce, har ki yi aiki a gidan nan? Ni abunda ban gane ba wai kin san cewa Sarki Agadez Kakani kuwa ko kuma sai yau? Abbah ku ma daya fada min wannan maganar shi kanshi mamaki yake domin abun ya dore masa kai sosai”
Ammy ce dai take wannan maganar tana ta kallona. Aliyu ya kalleni sannan ya sake kallonta ya ce.
“Ta sani, amman ta yi shiru saboda mahaifiyarta bata son maganar”
“Mahaifiyarki ta yi dacen ya Ataa, da baki gudu kin koma cikin dadi kin bar a nan ba, da kuma ba ki saka mata ido har ta wulakanta ba Allah yai miki albarka”
Gaba daya suka amsa da amin, ni kuwa tawa amin din a zuciya take, ina jindadin Ammy tun a wacan zaman da nai tana nuna min kauna bata taba nuna min kyama ko kyara ba kamar Mama Fulani, haka ma Muhseen be taba kyamata ba shiyasa na kasa mantawa da shi a zuciyata halinsa kamar na Ammy ne idan ma ba dan fuskarsa da sanin cewar Mama Fulani ce ta haife shi ba idan ka ganshi zaka tsammaci dan Ammy saboda yanayin halinsu na far'a da son mutane ga kuma marhabun da kowa.
Misalin tara da yan mintuna muka fito daga bangaren Ammy muka nufi bangaren Mama Fulani, kamar yadda nai wacan karon wannan karo ma baya baya na tsaya Saboda tunanin irin kallon da zata min ko ta fada min wata maganar marar dadi. Shi ya tura kofar falon ya shiga sannan ni ma na shigo babu kowa falon sai tv da ac da ke ta aikinsa. Kai tsaye ya nufi upstairs hanyar dakinta ni dai ina biye da shi har muka isa cikin dakin da na ke sharewa na yi mopping amman a da. Ba Mama Fulani kadai muka tarar ba har da Rukaiya da Maryam da Baby suna zaune dakin, suna ganinmu sukai tsit da alama wata maganar suke tsaka da tattaunawa, ina daga bayan Aliyu ban karasa shigo sosai cikin dakin ba, sai ya matsa gefe ya matso da ni kusa da shi yadda zan bayyana tsundun a cikin dakin. Aiko a take Mama Fulani ta sako min ido tana min wani irin kallo ba na lafiya ba, ba kuma zan bayyana dalilin kallon ko manufarsa ba.
“Mama za mu wuce gida”
“To Aliyu sai da safe”
Ta fada amman idonta na kai har lokacin, sai Aliyu ya kalleni yai min magana kadankadan kamar mai bawa yaro umarni ko kuma mai koya masa abunda zai ce.
“Ki ce mata sai da safe Mama”
“Mama Fulani sai da safe”
Na fada kamar yadda ya ba ni umarni sai tai saurin kawarda fuskarta daga barin kallon nawa da take na tsawon lokaci, ba kuma kawarwa irin ta tsana ko kyama da tsangwama ba, irin kawar nan ta kamar mai tunani ko kuma wanda ya rude ko yake jin kunyarka. Ni na riga juyawa na fito daga dakin sannan Aliyu ya fito ya tararda ni har kusa sauka downstairs din.
Ya riga ni isa harabar gidan tun kan na karaso ya janyo motarsa ya bude min front na shiga na zauna na ki rufe ganbun motar da gangan na tsaya ina kallonsa murmushi yai ya bude gefensa ya fita ya zagayo inda na ke ya sumbaci goshina.
“Dama ai kin saba bar min mota a bude tun kina budurwa kuma na zo na rufe balle yanzu da kika zama gimbiyata”
Ya fada sannan ya rufe motar ya zagaya gefenta ya shiga motar yai mata keys muka dauki hanyar gida. Sai da ya biya ta wani shago ya siya mana kayan zafi da kaza sannan muka isa gida. Da kansa ya fita ta zagoyo inda na ke ya bude min mota ina saukowa ya saka hannunsa ya ruumgumo ni kamar wata yar baby ko kunyar mai gadinsa da ke hangen baya ji, ni kuwa duk kunyarsa ta rufe ni.
“Wacan Dattijon Baba fa yana hangenmu”
“Sai me dan ya tsinkaye mu? Be san na aure ki ba ni ko kuma be san namiji na taba matarsa ba? Is normal ma ai ba waji abun nai miki ba dafaki kawai nai, kuma shi ai ya saba ganin hakan idan muna tare da Rahma”
Ya fada yana bude gidan vaya ya dauko siyayyar da yai mana da dayan hannunsa yayinda dayan hannun yake makalle da ni kamar zan tsire masa. Da hannu daya ya rufe motar muka nufi cikin gidan ni da shi.
Ice cream kawai na sha daga cikin abubuwan da siyo mana, domin jin nai bana bukatar komai kuma bana jin yunwa, sai da mu kai wanka ni da shi a tare kamar yadda ya saba min sannan muka saka tufafin bachi muka kwanta. Misalin biyu da wani abu na dare yunwa ta tasheni a dole na bar jikinsa na sauka daga kan gadon na nufi wutar dakin na kunna ko da na juyo sai na ga mutun yana kallona.
“Yunwa na ke ji kazar da ka siyo zan ci”
Na fada ina dan wara kamar mai jin kunya.
“Zauna ba ri na dauko miki”
Ya fada yana saukowa daga kan gadon ya fita daga dakin, ni kuma na zauna saman kujerar sai gashi ya dawo da kazar a plate da lemu. Dan karamin tebur ya janyo ya dora plate din sannan ya miko min hannu na taso sai ya nufi bandaki da ni, wani lokacin yadda Aliyu yake min abu kamar wata yar baby abun har mamaki yake ba ni, wata kila saboda baya son yawan magana ne shiyasa ya son ya yi maka abu kawai ba sai ya furta ya ce kai ba wata kila kuma kuanar ce kaiwai yake nuna min. Sai na wanke bakina sannan muka fito na dawo inda na zauna dazun na zauna yawuna har tsinkewa suke kamin na ci kazar. Kusa da ni ya zauna ya saka hannunsa yana bare min yana ba ni a baki ina ci sai da koshi sannan na cige masa hannu da gangan, sai yai saurin cire hannunaa daga baki na dauki nawa yatsan ya kada a bakinsa ya cigeni kamar wani yaro karami, aiko ba shi ri nai ihu saboda zafin da na ji, sai yai saurin rufe min baki.
“Shiiiiiiii dare ne”
Ya fada kadan-kadan, dariya nai kamar yadda yake dariyar, sannan ya dauko lemun ya ba ni na sha sai ya aje ya matsar da teburin can gefe, ya kwanta saman kujera ya janyo ni na kwanta a kirjinsa, a nan muka kwana har safe yana rumgume da ni sosai a kirjinsa. Bayan mun yi sallah Aliyu ya kwantar da kaina jikinsa yana karatun kur'anin daya saba, ba dade yana karatun ba na tashi daga kwancen da na ke a cinyarsa na sauko falo na nufi kitchen domin samun abunda zan sakawa cikina saboda wata azzababbar yunwa da na ke ji. Freezer na fara budewa sai na ga dukan abunda yake ciki yayi kankara sai na bude dayar da bata aiki na ga Apple da sauran fruits a ciki, apple din na dauko na wanke shi a fanfan kitchen din na soma ci kamar wata mayunwaciya. Ina cikin cikin apple na hudu na ga mutum ya shigo kitchen din da tsage tsage a fuskarsa yana sanye da kananan kayan. Ba shiri na fasa ihu ina ra kiran sunana Aliyu shi ko mutunen sai daga min hannu yake alamar ya kwantar da hankali, tun yana magana da turanci har ya dawo yi da hausa sam ban dauka ma ya isa hausa ba. Da gudu Aliyu ya shigo kitchen din hankalinsa a tashe.
“Minenen?”
“Wacan mutumen.”
Na nuna shi.
“Mai mana girki ne”
Mai girki sai na ji abu wani iri, namiji da girki to miyasa wacan zuwan ban ganshi ba? Ko da yake kwana kawai mu kai mu ka wuce Lagos.
“To ta ina ya shigo?”
“Yana da makullin falon ne ko bana nan zai iya zuwa yai girki ya tafi”
Ya fada min sannan ya juya gurinsa..
“Abdulgany daga yau za ka daina shigowa cikin gidana nan, Nasir zai tura maka kudinka na wata ba zaka mana girki ba”
Risinawa nai ya fara bashi hakuri yana ta rokonsa ya yafe masa idan akan ya ba ni tsoro ne, sai ya fada masa ba dan tsoro ba ne wai yana kishin matarsa ne ba shi da bukatar ganinsa a gidan yanzu. Babu irin magiyar da be yi ba amman Aliyu ya ki saurarensa har sai da ya hada masa da fada sannan ya fice daga gidan.
Misalin tara da rabi Aliyu yai mana oder abincin, muna cikin kiran Abbah ya shigo wayrsa sai da suka fara gaisawa sannan ya sanar masa inda yake ya same sa a can.
“Yi sauri ki ci Abbah na nemanmu”
“Har dani?”
Na gyada min kai, da sauri na tashi na bar cin