Showing 159001 words to 162000 words out of 225640 words

Chapter 54 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

sai da ta gwada min yadda zan yi da kuma yadda zan aje komai a muhallinsa.
Sannan ta zuba mana na mu ni da Nana ta ba ni, sai da zan wuce sannan na lura da Aliyu da ke zaune saman cushion yana danna wayarsa kamar ba shi ne yai min abunda yai min dazun ba.

“Aisha kun gaisa?”

Momy ta kirani sannan ta fada kamin na amsa ya dago kansa ya kalleni fuska.

“Aa”

“To idan kika ganshi ki rika gaishe shi hakan na da kyau kinji, kuma kamin ki karya ki wanke bakinki da brush”

“To ina kwana”

“Lafiya kalau”

Ya amsa min fuskarsa babu murmushi ko wasa kamar ba shi ba. Ni kuma na fice ina ta masa kallon abunda yai min dazun.
Ko da na isa part din wato bq na samu Nana na share saman balcony din saurin aje abincin hannuna nai na karbi sharar nakarasa, sai ta koma cikin daki ta zauna. Bayan na gama na je ma sameta na dauko abun karyawa na aje mata na shiga na wanke bakina kamar yadda Momy ta fada sannan na zo muka karya.

“Ina jin kamar be dace ace har an miki aure Hajiya na zancen tarewarki a sati mai zuwa kuma ace yan'uwana da yan'uwan mahaifinki, ina jin kamar hakan be dace ba, kuma ina jin babu dadi idan na tuna da haka sai dai babu yadda zan yi”

Bayan mun gama cin abincin take min wannan maganar, gabana ne ya fadi.

“Tarewa ta sati mai zuwa Nana?”

“Haka ta roka ita da matar da suka zo jiya, kuma ta ce idan na amince zata fadawa Mahaifin Aliyu sun fada min sun dauke nauyin komai, za su yi duk abunda ya dace, kuma za a hada miki kayan sakawarki wasu tun a nan wasu kuma sai kinje can Saboda kurewar lokaci, tace ba za ayi wani hidima ba amman tana son ta shirya yar walima saboda addu'a”

Kuka na fara yi a take.

“Karatuna fa? Yanzu kenan? Barin zuwa makarantar zan yi? Kuma bokan ma ba za a a saka ni ba?”

“aa zancen karatunki tace yana nan za ki cigaba da karatunki ko bayan aure”

“Aa nana ni ban yarda ba Wallahi bana so, ma fasa auren gaba daya Wallahi ba zan yarda ba, ni ba zan iya zaman da shi ba, wayyo Nana dan Allah karki bari na tare yanzu....”

Shine abunda na ke fada ina rikon hannunta domin har ga Allah na tsorota da wani zaman aure a yanzu, yo ya ma zan yi zaman? Me ake cewa ya tsare tsaren suke ni na zan iya ba, ga wannan kazantar da yake min na san idan ina can sai ya sake min ita, karatuna ma lalacewa zai yi. Babu abunda Nana take sai kallo da fuskar tausayi domin kukan ba na wasa na ke ba.

“Na riga na karba mata ba zan iya canjawa a yanzu ba, Allah yasa hakan shi ya fi alheri”

Kara fadawa nai jikinta na fashe da kuka ina ta goga mata jikina kamar wata yarinya karama, bata ce min komai ba bayan hawayen da take har nai kuka na gama na tashi dan kaina na shiga bandakin na wanke fuskarta na saka uniform dina na tafi makarantar islamiya kasancewar ranar Lahadi ce ana zuwa da safe. Sai dai ban sake da kowa ba duk wanda ya kalleni ya san ina cikin damuwa domin har ga Allah bana son tarewar gaba daya ma sai na ji auren ya fita a raina.
Da shabiyun rana aka tashe mu na dawo gida kamar wata marar lafiya, abincin rana kawai na ci Momy ta aiko wai nai wanka za mu fita, sai na shiga nai wanka na shirya a cikin daya daga rigunan da Aliyu ya siyo min a ranar da yaje da ni shopping.
Amina aka kawo ta zo ta kirani muka shiga nota tare muka dauki hanyar gidan Zara mai lalle kalar fatata ta duba ta bani wasu abubuwan ta ce wannan na rika shafawa a jikina idan zan kwanta wannan kuma idan zan shiga da kamar minti goma haka, ni dai ji kawai na ke ba dan ina da niyar yi ba, daga ranar ban sake zuwa makarantar islamiya ba ban kuma sake saka Aliyu a idona ba, idan dare yayi sai Momy ta aiko min da fruits na sha, bayan kwana uku a gidan ta mayar da ni gurin wata kanwarta dake Abuja road, a can akai ta cusa min wasu abubuwa da na ke hadewa daker idan na gama na shiga bandaki nai kukana son raina na fito, duk na kasa sakewa a gidan lokaci zuwa lokaci Amina da Siyama da Husna suke zuwa su dubani, da dare fruit ake ba ni kamar yadda Momy take min a can sa safe kuma ba a bari na karya daabu mai nauyi da na ci kadan sai ace na barta haka a bani kaza mai magani da daci na ci, gashi tsoron matar na ke domin na lura ita ba kamar Momy ba ce sam bata wasa da yara balle ta sake da su, ba kuma wulakanci ba irin halin nan na dattijai.
Kullum sai an kaini gurin Zara ta gyada min jiki, ta shafa min turare na jiki da na kai da kuma na tsiguno, sannan ta ba ni ruwan magani ta ce nai wanka idan ta gama min dilka ni kaina a yanzu ina jin dadin jikina domin fatar jikin har wani sheki take tayi laushi sosai fiye da da, gashin kaina kuwa kamar ba nawa ba, domin kullum cikin shafa masa mai take tana gyara shi, ita kanta yabon kyauna take gaba daya na koma kamar ba ni ba, domin kuwa na fi da kyau da haske duk wani datti na fuskata da jikina sai da aka kawarda shi. Wata kabila ce ta zo ta auna ni ko'ina na jiki sai da ta auna ta sannan ta tafi, haka na rika kwana a gidan kullum idan na yi marmarin ganin Nana sai da a kira min ita a waya shi ma kuma idan Siyama ta zo ko Amina ko kuma Momy ta kira, a gidan matar idan zata hada abunda be kai kmya kawo ba ko wani abu mai nauyi ba sai ta kirani ta nuna min ta tambaye ni na gane, ko ban gane ba cewa na ke na ge saboda kawai a wuce gurin, sai dai kullum sai na sha kukan dare ni kadai ba tare da kowa ya sani ba.



ALIYU POV.

Sai da ta wuce sannan ya mike ya nufi dinning yana fadin.

“Tare kuka shirya abun karyawar ne?”

“Eh wai ina dan koya mata ne kamin taje can ta koya gaba daya”

Yayi shiru be ce komai ba har ya zauna ya bude abinci ya zubawa kansa ya soma ci yana ta tunanin abunda yai ma Ataa a dazu sai murmushi yake a zuciyarsa.

“Aliyu yarinyarnan tana son karatu sosai fa”

Da dago ya kalli Momy.

“Na sani shiyasa na shigar da ita islamiya ai, kuma bokon ma zan saka nan gaba In-Sha-Allah”

“Ina jin tsoro kar aurenku ya saka karatunta tarwatsewa”

“Saboda me? As long as zatai zaman aure ai zan barta tai karatunta, ba ni da matsala da wannan amman Momy..... ”

Sai kuma yai shiru ya kasa karasawa. Momy ta shiga zubawa Daddyn abincinsa tana tambayarsa.

“Amman me?”

“Tsawon wane lokaci zata dauka a gida tana karatun?”

“Karatu yana da lokaci ne?”

“Na yi magana da Daddynka jiya saboda Hajiya Ramatu ta kawo wata shawara har ta saka ni dole sai da naje bq nai magana da Nana ita kuma ta amince ta ce mana ba matsala, da na fadawa Daddynka sai yace shi babu ruwanshi shawara ta mu ce, kuma na kira babbar Yayarku after sallah asuba na fada mata komai ita ta bani shawara makamanciyar wacce Hajiya Ramatu ta ba ni”

Da dago tana ta kallonta, gabansa na dan faduwa irin na tsoron nan idan ba wani abun za a bullo da shi ba, wata kila ace ya kai Ataa wata makarantar boko a Abuja ko kasar waje ko kuma ya barta gida har nan da wani lokaci mai tsawo wanda yake jin cewar ba zai iya haka ba.

“Wani abun ne?”

Sai da Momy ta gama warewa Daddyn nasa abun karyarwa sannan ta ce.

“Wai Mun yanke shawarar Ataa ta tare dakinta next week Saturday”

Wani irin dadi da mamaki da annashuwa da farinciki Aliyu ya ji lokaci daya, amman yai kokarin dannewa saboda kar Momy ta ga haukarsa ko rashin kunyarsa, yayi murmushin dake nuna jindadinsa amman ya boye duk wani jindadin na ainahi a cikin ruhinsa.

“Amman Momy ita ta yarda?”

“Aisha ai bata da matsala duk inda aka bi da ita bi za tai, Nana kuma t amince har ma godiya tai mana jin cewar an dauke mata komai”

“Masha-Allah Allah ya tabbatar da alheri”

“Amin sai ka fara shirye shirye tun a yanzu”

Momy ta fada sannan ta dauki kayan abincin ta fice, wani irin murmushi Aliyu yai ya girgiza hannunsa ya shafa kansa abincin ma sai ya kasa ci.

Tun daga lokacin ya fara shirye shirye kamar yadda Momy ta fada masa, kudi ya cire mai yawa ya bawa wata yayar Momy yar kasuwa ta siyoma Ataa expensive clothes da tsarkoki masu kyau da tsada shoe dinta ma abun kallo ne, kusan kala talatin aka mata nata na sakawa wai na yanzu da kuma na kwaliyar amarci kamin a dinka mata na lefe idan komai ya laba hankali ya kwanta zai mata cikakken lefe domin yana son ya mayarda ita mutum ita ta zama tana fita da shiga irin ta yayan manya.
Bayan gidan da suka zauna d Rahma yana da wani gidan dabam mai kyau da tsare, wanda ya so ya aje Ataa a ciki ita kuma Rahma ya barta a wacan ma'ana ya raba musu gida saboda gudun fitina sai Momy ta hana ta saka Daddyn ya ba shi dayan gidansa mai part uku da ke unguwar koko road.
Sabon fenti aka yi ma gidan duk kuwa da kasancewar ba a taba shigarsa ba, saka kara kawata shi aka gyara wasu abubuwan, sannan Momy tai order wasu furnitures daga Kaduna masu tsada da kyau aka kawo aka zuba a dayan bangaren na Ataa gaba daya furnitures din bangrenta fafare ne tun daga dago har kujeru da duk wani abu na kwaliyar daki, gurin curtains din ne kawai akai musu surki da ja da sai kuma carpet din shi ma ja, after two days da kawo furnitures aka saka Electronics da wasu abubuwan na kawata gida.
Kayan kitchen kuma wata mai siyarda da kayan kitchen aka bawa kwangila da shirya komai on Friday aka saka. Ba Aliyu kadai ba, Momy m da yan'uwanta da Daddy da Abbah sun yi ma Ataa hidima sosai gurin gyara komai na gida. Sai dai duk wannan farinciki da jindadadi Ataa zata tare da Aliyu yake idan ya tuna cewar Babu Mama Fulani za ayi sai ya ji babu dadi, gashi tun lokacin da abun ya faru ta daina daukar wayarsa balle kuma ita ta kirashi da kanta Momy ma idan ta kira bata dagawa, sai dai ya kira Maryam ko. Rukaiyah ya tambayi lafiyarta.

Kamar yadda Momy ta tsara ranar Saturday akai walima, ba a yi wani taro ba domin ba kowa da kowa Momy ta gayyato ba, saboda kurewar lokaci wasu ma jin abun na Momy ne yasa suka zo ba tare da an gayyoto su din ba, wani abun mamaki har da Maryam da Rukaiya da kuma yayan Ammy, wanda Momy take sa ka ran Abbah ne ya turo su da kansa, domin Mama Fulani dai fushi take ba zata taba cewa su zo ba, ko da yake wani lokacin Mama Fulani ta kan yi wani abun dan hada kan zuri'ar ta da kuma yayanta.
Sosai Momy tai farinciki da ganinsu kuma ta jidadin zuwan na su.


ATAA. POV.

Ban kara tabbatar da cewar da gaske ne ba, sai da maga ana ta hidimar bikin, tun ranar laraba aka saka nai wa ka da ruwan lalle mai ja sosai, ranar da ta kama jumma aka zo aka kara gyara min gashina har gida, ba kitso aka min ba sai dai an gyara min shi yadda na ke jindadin zamansa a kaina. Lallen ma dan ubansu aka min mai kyau gaske, tun da nake a rayuwata ban taba yin lallae ba sai yau ashe haka yake kyau a fatata farin kafata dana hannuna ya fito fes lallen mai ja ya fito fes, domin ja ne kawai aka min da shi babu digon baki ko daya.
Ranar assabar na tashi da wani azababben ciwon kai saboda na wuni na kuma kwana ina kuka da tunanin. Da yamma aka sake saka ni nai wani wankan wata mai kwaliyar ta zo ta shirya ni tai min fentin nan na kanti sai na fito kamar ba ni ba, dogon hancin nan nawa sai ya kara fitowa kowa cewar yake na yi kyau ni dai nawa idone kawai zuciyata kuma cike da kuka. A mota mai kyau aka saka ni aka tafi da ni gidan Momy a can na tararda taro har an fara walimar ma, a cikin mutanen da suka halarta da su Yayan Mama Fulani da Ammy Maryam da Rukaiya har bana son hada ido da su saboda harata da suke. Duk wani wa'axi na Malamar ban ji ko daya ba, I hawaye kawai nake har kwaliyar tawa ta hoda ta soma gogewa, na sha hotuna sosai. Kamin Momy ta saka a sake maida ni gudin Kanwar tata Hajiya Mairo sai dai wannan karon tare da duka yayanta muka tafi da kuma wasu bakin fuska da ban sani ba. Ta ba ni abinci amman na kasa ci ruwa ma kasa sha nai sai gani nake kamar mafarki na ke. Bayan na gama sallah isha'i wata mai kwaliyar ba wacan ba ta sake zuwa ta gyara ni na saka wasu tufafin lace ne ash color mai kyau da ja mayafi sai kuma ta kalmin suma kala daya da gyalena sarkar kuma irin wannan ce mai ruwan gol wata kila ma gol din ne ban gane ba. A gidan Momy aka sake dawowa da ni tare da yan matan dake tare da ni aka kai ni gurin Nana wai ta min huduba sai aka fita aka bar ni daga ni sai ita, riketa nai na fashe da kuka ji nake kamar idan na tafi na tafi kenan ba dawowa. Ita bata iya ce min komai sai kuka take har wata yar'uwar Daddy ta shigo zata fita da ni sai na rike Nana gam ina kuka kamar yadda ita ma take yi tana rike da hannuna.

“Aure ai ya gaji haka, dan Allah ku yi hakuri sai kace wandanda akai wa mutuwa? Haba dai”

Shine abunda mutane suke ta fada ganin irin yadda ni da Nana muke ta kuka sosai, babu wanda ya san abunda na ke ji sai ni yau zan rabu da Nana wai wani aure zan yi auren da sai a yanzu na ke jin nadamar amincewa da Aliyu da nai da na sani na ce ban shirya auren kowa ba sai na zauna ni na Nana mu yi ta rayuwarmu. Batan fitowa da ni bangaren Nana aka kai ni Gurin Momy dakin na cike da mutane a haka tai min nasiha sai na rike hannunta ina ta girgiza mata kai ina kuka ita ma kanta sai dai ta yi hawayen.

Daker aka fito da ni aka saka ni a motar ina da kallon bq din Nana na tsaye jikin windows tana kallona ita da wasu yan'uwana Momy wata kila hakuri suke ba ta, a gidan baya aka sani ni tare da wasu mayan mata sauran yan matan kuma suka shiga sauran motocin, aka dauki hanya da ki hanyar da ban san wace unguwa ce ba domin kaina a kasa yake ina kuka har mutanen da ke cikin moyar suka soma tsarguwa da ni. Mun dade muna tafiyar sannan muna iso wani gida da ban san ina ne ba jin ana guda yasa gabana faduwa kuma na kara rushewa da kuka.
Wata matar ce da ba zan iya shaidar fuskarta ba ke rike da hannuna tana nutsawa da ni a cikin gidan har muka isa falon da ke ta kamshin turare sannan muka wuce uwar daga ma'ana bedroom nan dai kamshi ke tashi da kuma mutane a ciki da ba xa su fi mutum biyar ba bayan falon da ma da akwai wasu a nan. A tsakiyar gadon aka zauna da ni sannan aka fesa min wani turaren aka kara gyara min mayafina yadda zai sauko min da kyau. Sai da dattijawan cikin suka min addu'a kuma suka min huduba akan zaman aure hakuri yi na yi ba ri na ba ri da kuma toshe kunnu akan dukan abunda zan ji ko na gani.
  Sannan suka tafi aka barni da yan mata masu kokarin bude mayafina su ga fuskata ni ko har lokacin hawaye na ke, ina jin wani yanayi da ban taba jin kaina a ciki ba, hakika ban san aure ba, ban san miye aure ba balle abubuwan da suke cikinsa, amman iina jin darajata ta karu na bar kulawar Nana da tarbiyarta na koma gurin ta Aliyu kamar yadda Momy tai min huduba. Wata sabuwar rayuwarce zan fara fuskanta wata kila mai dadi ce ko akasin haka, wata kila mai sauki ce ko kishiyarta, wata kila kuma na samu duka biyun wato dadi da daci sauki da kuma wahala.
   Bana iya gane lokacin da aka shigo da Aliyu hayaniyar maza kawai na ji a dakin wasu na zolarsa, ban daga kaina a cikin mayafin na kalle ko su waye da waye a abokansa ba, amman nasan sun hausa mutum biyar kuma ba za su sama da mutu goma ba, baki gado ya zauna yana ga kamshin turarensa mai dadin shaka. Nasir ne ya fara yi mana nasiha sannan wani abokinsa ya dora sai kuma suka rufe da addu'a tare dayi mana fatar samun zaman lafiya kwanciyar hankali da kuma zuri'a ta gari. Da dai daya suka fara fita sannan sauran suka fice har da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login