Showing 189001 words to 192000 words out of 225640 words
idan kika aje kiyayyarta a zuciyarki ba tare da kin nuna mata a gabana ba, Mama Fulanu tana da muhimmanci da daraja da kima a gareni wanda Momy ma ba zata so ki wulakantata ba, Mama tana son cikin nan ko da ko bata so ki ba saboda cikin jikinki nawa ne, tana jin kunyarki da mahaifiyarki da tasan da zuwan wannan abun tace da bata aikata miki komai ba”
“Miyasa sai ni Aliyu? Wata kila da asalina be bayyana ba, da har yanzu Mama Fulani ba zata ce tana jin kunyata ba, ko ba ni ba ko wane dan'adam mai daraja ne Aliyu, idan babu talaka wallahi masu kudin ba za su iya rayuwa ba, da babu talaka fada min wa zai zo gurinta nema har ta gane cewar tana da arzikin? Wa zai gina mata gidan da zata zauna? Wa zai tuka mata motar da zata hau? Wa zai mata wanki da guga da gyaran gida ko na sani abun idan ya kama? Wanda ba shi da jinkai yake so da kauna da tausayi ba kyara da tsangwama ba, abun Alfarinka ne ace yau kana da abunda zaka iya dafawa ka bawa wani ko kuma ya taimaki wani a cikin taimakon da Allah yai maka, tarin dukiya ba abun alfahari ba ne tarin imani da yawan taimako da kyakkyawan aiki shine abun tinkaho da bugun gaba, ranar lahira a wareka a bainar jama'a a karramaka akan aikin alherinka shine abun jindadi, ba a tsare ka ana tuhumwar ka da daga inda ka samo dukiyarka ba kuma taya ka kashe ta? Wa ka zalinta da ita waya amfana da ita? Wani aiki kai ita saboda Allah? Aliyu ya zaja ji idan Allah ya tsayarda Mama Fulani a gabansa ya tuhumeta akan zalincin da tai na wani ko musgunawa saboda ita tana da dukiya shi ba shi da ita ba? Wanda ya baka dukiyar da kansa ya tambayi ka dalilin wulakanta wani saboda abunda ya baka shi ya hana shi? Miyasa ba zaka fada mata gaskiya ka nuna nata abunda take ba daidai ba ne? Talaka kan kaurai zai dade da shiga mai kudi yana can yana amsa tamaboyoyin dukiyarsa, ashe ko dukiya da zata saka ka fadin rai da wulakanta wasu ba abun tinkaho ba ce matukar ba ta taimakon bayin Allah ce da addininsa ba”
ATAA POV.
hawaye na ke yayinda na ke maganar ba da Mama Fulani kadai na ke ba, har da Aliyu na ke domin shi ma rayuwarsa kenan kamin yanzu, da kuma duk wani mai halin irin nasa. Yadda na ga jikinsa yai sanyi sosai ya karantar da ji cewar sakona ya isa a inda nake son isar da shi domin hawaye na gani a idonta yana ta kallona.
“Na gode Allah daya bani mata kamar ke, yarinya ce ke amman mai hankali da natsuwa da hangen nesa, ina son ki ina son abunda cikin cikinki”
Ya fada yana murmushi. Hannu na saka da kaina na share masa hawayen na rumgume shi da kaina ina jin wani irin dadi marar misaltuwa.
RAHMA POV.
Kamar yadda ta yanke shawara samun Daddy ta ta fada masa cewar zata koma dakin mijinta sai ta fara samun Mommy da zancen a lokacin Mommynta na jimmamin al'amarin da Daddyn Rahma ya fada mata a waya wanda ya hana shi dawowa. A jiya kamar yadda yai alkwari.
“Mommy ba ki ce komai ba”
“Mi zan ce Rahma? Anya ma Aliyu zai kalleki ma yanzu kuwa?”
“Me kike nufi?”
“To ya samu wacce ta fiki komai”
Raham ta saki baki jin irin maganar da mahaifiyarta take da kanta.
“Mommy ke da kanki kike fadin wannan maganar? Ko kin manta wacce Aliyu ya aura ne?”
Mommyn da juyar da fuska cikin damuwa.
“Bana son fada miki abunda zai zame miki tashin hankali ne”
“Minene dan Allah fada min”
“Kin san sarkin Agadaz wanda ya zo?”
Rahma ta gyada kai cike da son sani.
“To kakanta ne, duk uwar dukiyar da muke tinkaho da ita ta gidansu ce, ke kiji wani al'amari”
Rahma ta girgiza kai.
“Mommyn kin gane me kike fada min kuwa?”
“Aifa sai ki yi, yanzu haka Daddynku na can gurin sarki ya fada min ya sha kuka jiya har idonsa ya kumbura saboda Ataa ta fadawa Mai Martaba abunda mu kai musu”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u Innalillahi La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam, jama'a Mommyn da gaske ko karya? Taya to taya how how how Mommy”
Ta fashe da kuka ta mikewa tsaye sai Mommyn tai saurin riketa.
“Ke ke saurara kwantar da hankali”
“Taya zan kwantar da hankalina Mommy fada min taya ya zama kakanta taya? Wallahi hakan ba zai yiyu ba, sai dai idan wata Wallahi ba ita ba”
Zaunar da ita Mommyn tai ta jera mata komai dalla dalla kamar yadda Daddynsu ya fada mata a waya domin ya fada mata cewar ba zai dawo da wuri ba sai Mai Martaba ya koma da ko rakiyarsa kawai zai yi Abuja ya dawo.
“Wayyo Allah na na shiga uku Mommy mutuwa zan yi yau, wayyo zuciyata wayyo kirjina wayyo raina”
Faduwa tai kasa tana da kuka da ihu kamar an mata mutuwa. Gaba daya yan'uwanta sai da suka taru a dakin suna ta jimamin al'amarin gaba daya abunda suke tunani Mai Martaba zai iya kwace duniyarsa daga hannun Daddyn gaba daya cikinsu ya duri ruwa. Haka Rahma ta kwana ta wuni tana da aikin kuka da tunani kala kala ada ya tsara yadda za tai zaman kishi da Ataa saboda tana yar talakawa to yanzu kuma ba ta san irin zaman da zatai ba.
Washe garin ranar da Daddyn ya dawo duka suna zaune falonsa dukansu suna cikin damuwa har shi domin Mai Martaba ya kama hanyar zuwa jigawa tun jiya ba tare da shi ba, kuma be ce komai akan abunda Ataa ta fada am mata ba, shine abunda yakr ta ba Daddyn Rahma tsoro.
“Ni wannan abun har mamaki yake ba ni, abu kamar a mafarki”
“Ai ba ki san a mafarki ba sai da yarinyar nan ta fara fadin abubuwa a gaban mai martaba kaina kamar ya tsare, kunya ta rufe ni ai ban san lokacin da fashe da kuka ba”
Cewar Daddyn Rahma bayan Mommyn ta fadi nata.
“Baku tunanin abun nan zai min yawa da kuke ta maganganun nan a gabana? Tun da na tashi lafiya bata isashe ni ba, ga auren da Aliyu yai yanzu kuma yarinyar nan azo ace wai cikin dukiyar gidansu muke rawa da tumami, haba Daddyn haba ba a kyauta min ba”
Ta fashe da kuka, Ikram ta ce.
“Haba Rahma ya za ki yi da ikon Allah? Kullum idan ina fadar cewar abunda ake a gidan nan ba a kyautawa tun daga kan mijinta da kuke biyeta tana juya shi yadda ya zo da kuma yadda kuke yi ma mutane sai kuna ganin laifina kuna ganin ban kyauta ba ko kuma ni ban gane kan dawon garin ba, yanzu ai wa gari ya waye? Tsakani da Allah Rahma ciwon nan na ki tsoron Allah ya kamata ya Kara miki, ciwon kadai ya isa ya saka ki fahimcin cewar dukiyar ba komai ba ce tunda ta kasa baki dauwamammiyar lafiya ko ta hana ki ciwo ko mutuwa, wani yana can da talaucin amman lafiyarsa kalau hankalinsa kwance yana cikin farinciki”
Mommyn ta daka mata tsawa.
“Haba Ikram yar'uwarki kike fadawa wannan maganar? Ba zaki barta ta ji da abunda yake damunta ba?”
Rahma ta mike tsaye tana hawaye ta nufi dakinta, saman gadon ta fada ta kwanta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita, tana jin wayarta na ringing ta ki ta daga sai da ta sha kukanta ta koshi sannan ta shiga bathroom ta wanke fuskarka ta fito idonta sun yi ja sosai kanta har wani haukan ciwon yake. Wayar ta duba ganin number Aslamiya matar Nasir yasa ta kira ta tasan ba zai wuce ta labarta mata cewar ubangidan Daddyn kakan Ataa ne ba.
Sai dai a lokacin da ta dauki wayar bayan sun gaisa sai labarin ya sha banban ta labarta nata cewar Ataa na da ciki. Wani irin abu Rahma ta ji kamar tana zaune a saman kaya, ta mike tsaye sai ji tai dakin na juyawa mata bata san lokacin da wayar ta subuce daga hannunta ta fadi kasa ba, cikin jirin ta fara takawa ta nufi kofa tana fadin Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, so take ta fita taje gurin da sauran yan'uwanta suke kar ta rasa ranta a dakin ita kadai. Kamin ta kai kofar ta fadi kasa ta kwala wani irin ihu sai numfashinta sama-sama. Jin ihunta yasa kowa ya taso da gudu suka nufo dakinta.
*Allah ka ba mu ikon yin domin ka. Bari domin ka, k'i domin ka, so domin ka. Wanda duk be ji tsoron hakkin wani ba kuma be ji tsoron Allah ba Wallahi ya yi aikin banza. Allah ka raba mu da aikin dana sani, ka doramu a daidai alfarmar Annabi Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam*
6k Words 😲
Kun sha karatu har kun gaji.
*Littafina na kudi ne, biya duniya ko kuma inda mutum be da su indai rubutun nan hakkina ne. *Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
*Ina mata son rage kiba? Ina mazan da kiba ta hana su sukuni? Ina masu jikin yai kyau kamar na yarinya? Ina masu fama da kujera ko wani ta bo a fuska? Ina masu fama da hawan jini? Masu diabetic? Ag cera an gwada yayi an tantance ingancin babu shakku ko kadan. AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*
*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
A lokacin da ya shiga wanka ni kuma sai na dauko tsintsiya na share dakin lokacin da na fito da sharar a falo sai gashi ya fito daure da tawul a jikina ya tsaya bakin kofar dakin yana kallona. Nima kallonsa nai ganin be ce komai ba yasa na ce.
“Har ka gama wanka ne?”
Be ce min komai ba sai ma kara hade fuska da yai, tunani na tsaya na san dai kamin ya shiga wanka ban masa wani abun ba, kusan ma tun da aka daura mana aure Aliyu be taba yin fushi da ni ba sai amman yadda na ga ya hade rai na san ba lafiya ba. Kallon jikina nai duk da nasan ba a jikina ba ne matsalar domin ni kadai ce a falon ba tare da kowa ba balle har ya ce wani ya ganni babu Hijab.
“Wani abun nai ba daidai ba?”
Na tambaya ina turo baki kamar nima din wani abun akai min.
“Yanzu ba dan neman magana ba, miye na wani daukar tsintsiya ki yi shara daga nan sai kice mopping za ki yi ki yi wankewanke da wasu abubuwa ko? Na san halinki ai, kuma can da da kike ke kadai ba ki yi ba sai yanzu da kuka zama ku biyu?”
“Ina yi ai ko lokacin?”
“A gidan Momy ko? Tun da aka miki aure kin taba shara? Sai yanzu za ki tsiro saboda neman magana kuma idan na ce ki daina ki fara min gardama?”
Na jefar da tsintsiyar.
“Na daina, naga gidan yayi datti ne kuma babu mai sharewa”
“Da muka dawo haka kika ganshi? Kin san lokacin da ake shigowa a share ko a goge ne?”
Na rausayarda kai.
“Wuce ki yi wanka za mu je mu yi ma Mama barka da tashi, kuma za mu koma asibitin gurin likitan”
“Mi zai min?”
“Zan siyo magani a can kuma ina bukatar ganinsa dan ya fada miki irin abubuwan da zaki rika ci da yi da kunnenki kiji domin ni kin raina ni idan na ce ki daina sai kokarin yi za ki yi”
“Aa ban fa raina ka ba”
“Zamu gani”
Ya fada yana jam kumatuna ba tare da ya mim murmushi ba, a dole na koma ciki nai wanka na shirya kamar yadda ya bukata, a tare muka fito da shi yana kallon yadda yake kallon tafiyata wata kila so yake yai sauri ko na taka ba daidai ba yace da gangan na ke yi saboda ina da ciki. Shi ya bude min motar na shiga sannan shi ma ya shiga ya zauna, sai ya kai hannunsa a bakinsa yana karanta abunda ban san ko minene ba sannan ya saka dayan hannunsa ya daga Hijab dina ya bude rigar zanen da ke jikina ya shafa min addu'ar a ciki. Sannan yai ma motar key daman tuni mai gadin ya bude mana gate, a hankali ya fara tukin har muka fito daga cikin gidan.
Na yi zaton gidan za mu fara zuwa sannan mu wuce asibitin sai ya fara zuwa asibitin sai dai ba wacan ba ce domin wannan katuwa ce sosai ga ma'aikata ta ko'ina gwanin ban sha'awa. File aka fara bude min sannan ya sake tambaya ko ina jin sani abun bayan abunda na fada mishi jiya.
“Bana jin komai”
A nan ya sake rubuta wani abun a farar takadar ya mikawa Aliyu.
“Ka kara mata da wannan, wannan kuma results dinku ne na jiya congratulations”
Aliyu yayi murmushi yana kallona, kunya ce ta rufe ni nai kasa da kaina ina watsa da yan yatsuna cikin Hijab.
“Doc ka fada mata abunda ya kamata tai da wanda be kamata ba da abubuwan da zata ci”
Aliyu ne ya bukata da kansa, a take likita ya fara lissafa min irin abubuwan da zan rika ci da kuma aikin da zan yi wanda ba mai wahalarwa ba.
“Aa no doctor ni fa ko bokitin ruwa ba zata dauka ba, balle wani shara da wanke wanke”
“No ai aikin yana da kyau amman kar ayi na kashe kai”
“Ko na raya kai ba za ayi ba, balle na kashe kai, ina ciki fa aka ce Alhaji”
Aliyu ya fada yana nanatawa, shi kuwa likitan sai dariya yake, ni dai gaba daya kunya ta gama kamani har bana iya daga kaina.
“Ta so muje”
Tashi nai ina tafiyar cike da kunya shi kan tuni ya kai kofa har ya bude min kofa yana jira na fito, sai na fita sannan ya fito, ba ko kunya ya kama hannuna zuwa gurin motarsa da kansa ya bude min sai da na shiga na zauna sannan ya rufe ya zagoyo gefensa ya zauna, tukin mota yake amman gaba daya hankalinsa da tunaninsa na kaina, minti biyu uku sai ya kalli inda na ke.
“Kina son wani abu? Kina jin wani abu?”
Yayi min irin wannan tambayar ta kai sau takwas kamin mu isa family house na su, a harabar gidan ya faka motarsa har na kai hannu zan bude sai ya danna dan wani abu dake gefen motarsa motar ta rufe, kallonsa nai sai ya fara min magana a natse.
“Kin dai ga cikin mutane ne, bana son ki je ki ci wani abun da zai lalata miki ciki ko ki ci da yawa, kuma ki ci yaji ko ki zauna da yunwa, da ama ace Mama ce kadai ko Ammy zan iya yi miki magana a ganbansu amman Mama (Nana) ba zan iya miki magana a gabanta ba, pls ki kula da kanki”
“Tau”
“I love you”
Ya fada sannan ya cire abun ni kuma na bude motar na fita ta nufi bangaren Ammy, sai na ji ya kira ni.
“Babyna, za mu fara zuwa mu gaishe da Mama”
Juyowa nai na karaso inda yake tsaye ba tare da na ce masa komai ba, a tare muka jera muna tafiya zuwa part din Mama Fulani, yana ta kallon yanayin tafiya kamar mai kirga yadda na ke takawan. A falo muka samu Mama Fulani zaune kanta sanye da hular wanka hannunta kuma rike da brush an zuba masa mai daurin kirji ne a jikinta sai kuma wani karamin tawul da ta rufa a saman jikinta, Rukaiyah ya mata kafafuwanta. Zaunawa yai kusa da ita, ni kuma na zauna a dayar kujerar sai kallona take kamar bata taba ganina ba, gaba daya ta wani yi sakuku kamar ba ita ba, ni ban taba ganinta a cikin yanayin tausayi ba sai a yau.
“Mama yanzu kika tashi?”
“Eh Aliyu”
Ta amsa tana aje numfashi.
“Na'am, amman Mama ba ki jindadi ko?”
Ya tambaya cikin yanayin da ke nuna tsantsar kulawarsa a gareta.
“Muhseen ya duba ni ai, kuma yanzu idan nai wanka na karya zan sha maganai”
“Mama ina kwana”
Na fada ina dan risino kaina alamar girmamawa, sai ta kalleni kawai ta kasa amsawa kamar mai jin nauyi ko kunya, mikewa tai tsaye ba tare da ta amsa min ba ta nufi hanyar dakinta sai da tai rabin stairs sannan ta juyo ta kalleni sai kuma ta dauke kai ta shige dakin.
“Ku baku iya gaisuwa ba ne?”
Maganar Aliyu ta saka na maida duba a gurin Maryam da ke gyaran cucumber da kuma Rukaiyah wacce ta gama matsawa Mama Fulani kafafuwanta.
“Ina kwana ya Aliyu?”
Har sauri suke gurin gaishe shi suna hada baki.
“Ba ni ba ita, matata ce yadda kuka respecting dina haka ita ma za ku mata”
Ya fada babu alamar wasa a tare da shi, a tsakanin Rukaya da Maryam ban san wa yafi wani nauyin baki gurin gaishe ni ba, ni kan wani irin kunya da girma ne ya rufe ni a lokacin ba dan na san sai ya cilasta ni amsawa ba da ba zan amsa ba, sosai na ji daraja ta ta dagu, ba kuma dan sun san wacece ni a yanzu ba, sai dan auren dan'uwansu da ke