Showing 105001 words to 108000 words out of 225640 words
karshe sun fi shan wahalar rayuwa, amman daga ta zowa a lokacin kurciyarsu sun fi kowa jindadin rayuwa a gaba, ina jin tausayinki sosai ba ba dan saboda jinina ne silar hakan ba, sai dan halin da kika tsinci kanki tun kamin rayuwar ta kawo ki nan, labarinki abun a tausaya miki ne a tallafa miki, tun daga lokacin da ya fada min abunda ya faru ban taba ganinki ba amman sai na samu kaina da tausayinki, daga lokacin da na saka ki a idona kuma sai na fara miki kallon yata, ba fata na ke ba amman ko mahaifiyarki bata raye ni nan mai rikonki ce kuma na kula da ke, ki kwantar da hankalinki Ataa In-Sha-Allah za ki samu duk wani jindadi da wata rayuwar da kika rasa a baya”
Fashewa nai da kuka kalaman da take min sai nake jin kamar Nana mutuwa zatai ta barni, idan ko ta mutu na shiga uku bana da kowa sai Allah. Sai shida har da yan mintuna sannan Momy ta tashi zata wuce gidan.
“Wannan matar sunanta Laraba zata rika kula da Mahaifiyarki ke kuma kina dan samu kina hutawa, kamar yanzu za mu iya barinta sai ki bini muje gida idan kina so, kin ga sai ki samu ki yi wanka ki huta kamin ta farka”
“Aa ni dai ki barni a nan, na fi son ko zata farka ta farka a gabana, ji nake kamar idan nai nisa za ta mutu ta barni”
“Ba zan takura ki ba, amman ita ma zata zauna a nan tana da waya a hannunta kinji kina bukatar wani abu ki yi mata magana zata kira ta fada min”
“Tau”
Na fada ina kallonta da idona da suka gama kumbura. Kudi ta ciro mai dan dama ta mikawa matar wacce ta kira da laraba.
“Ki rike wannan idan tana bukatar wani abun sai a siya, kuma kin san halin yarinya sai dan lallaba duk da nasan ba halinki bane fada amman dai a kara, bama son abunda ya taba yarinyar nan yanzu”
“To Hajiya In-Sha-Allah za a kiyaye”
Daga haka tai min Allah ya kawo sauki ta fice ta bar ni da matar mai sa'ar Nana.Bayan na gama sallah magariba na dawo saman kujerar na zauna ina ta kallon Nana zuciyata na min wani irin zafi, babu abunda ya dame ni a yanzu kamar sanin dangina, lallau rashin yan'uwa a kusa da mu ya saka mu cikin rayuwa mai wahala da tsanani. A yanzu kuma da nake da bukatar sani sai a ace min zata manta da komai? Kife kaina nai a gurin nai ta kukana har aka kira sallah isha'i, sannan na shiga bandakin nai alwala na fito na shimfida carpet na gabatar da sallah isha'i ita kuma tana zaune a saman tabarma tana waya. Bayan na gama sallah na kwanta a gurin ina da hawayen da a yanzu suka zame min kamar farilla. Har ta gama wayar ta tashi tai nata Sallah ta bude abincin dazun ta zuba min a plate ta aje a gabana.
“Ki ci abinci”
Sai da tai maganar na tuna cewar ban ci wani abinci na bayan na safe.
“Bana jin yunwa”
Na fada ina kawar da kai daga barin kallon abincin da warinsa ma baya min dadi. Jan plate din tai a gabanta ta soma ci, ni dai ina a gurin har dare ya soma yi. Jin nai zaman dakin ya ishe ni ina marmarin wani gurin dabam ba nan ba, fita nai daga dakin ba tare da na fada mata ga inda za ni ba ita ma bata tambaye ni ina zanje ba. Fitowa nai harabar asibitin ina ta kallon yadda fitilun asibiti da sukai haske har suna kashe min ido domin idon nawa sun yi laushi sun kuma rage haske saboda kuka da nake. Mikewa nai ya fito daga cikin asibitin ba dan nasan inda zanje ba. Wani bangare nake tunawa na rayuwarmu daga zaman da muka saba yi a bukka da kuma baran da muke har zuwa rasuwar Lukman.
A da mu biyu ne yanzu kuma na zama ni kadai, ina tuna lokacin da Baba yake da fada cewar wata rana zan maza a yarta wata kila yana da rai ko kuma bayan ransa, har ya kama hannun Lukman yana wasa ya ce.
“Ban so rayuwar mu a haka ba, ban so komai ya zama yadda yake yanzu ba, amman wata rana komai zai zama tahiri, Lukman sai zama babban mutum Ataa kuma ki zamu gata mai kyau, sai dai ban sani ba ko kusa ne ko kuma nesa, idan ina da rai zan jidadi idan kuma bana da rai sai ku min addu'a kun ji”
A lokacin da yai wanann maganar yana rike da hannuna da na Lukman.
Yawun bakina na hade ina magana da kaina.
“Baba ka rasu, Lukman ma ya tafi, tsakanin ni da Nana ban san wanda zai riga wani ba, amman ina fatar na rigata, sai dai wannan jindadi da ka ce mana ba zai zo ba har a bada”Hawaye ne ya sauko min a haka na kamo hanyar Clapperto ina hawayen har na iso, cikin dakin kwanon na shiga na kwanta daga bakin kofa ina kallon taurarin dake sama hawaye na ta min zuba na kasa tsayar da su.
ALIYU POV.
Be iya labartawa Momy abunda ya faru ba, domin yasan ita ma ba fahimta za tai ba, wata kila ma shi zata dorawa laifi sabanin Muhseen. Yanayinsa kawai ta gani tasan yana cikin bacinrai, Momy tana ganewa idan Aliyu yana cikin damuwa da bacinrai. Karya yai mata dan kar ta tambaye shi ya ce mata kansa ke ciwo. A gidan ya wuni har yamma sallama masallacin unguwar yai.
Bayan la'asar Momy ta shirya ita da Laraba wacce ta iso suka kama hanyar Asibitin, Momy na fita Husna da Siyama suka tashi suke shige daki gudun kar su yi wani abun yace am masa ba daidai ba, daman Amina tun da ya shigo gidan ta tare a daki tana kallonta. Bayan fitar Momy da mintuna kadan motar Muhseen ta shigo cikin gidan, a kusa da motar Aliyu ya fakata ya fito ya nufo kofar falon. Knocked ya fara yi kamin ya tura kofar falon ya shiga. Aliyu na zauna saman cushion yana kallon Muhseen har ya karaso cikin falon, be ce da Aliyu komai ba ya nufi kitchen a zatonsa Momy na can.
“Kana aiki kamar baka san aikin ka ba Muhseen, taya zaka fadawa karamar yarinya kai tsaye cewar mahaifiyarta za manta da komai?”
Muhseen ya juyo ya kalleshi.
“Wani likitan ne zai fada min idan na yi kuskure amman ba mai kula da Sky Global Resources ba, aikin kamfani kake Aliyu baka san komai akan aikina ba”
“Yes aikin kamfani nake, shiyasa na iya sarrafa halshe na san irin maganar da zan fadawa kowa, ba kamar kai ba da zaka tashi hankali yarinya karama kana fada mata maganar da bata kamata ba”
“Miyasa tashin hankalinka zai tashi hankakinka Aliyu? Saboda kar cutar da kai mata ta fito fili ko kuma saboda akwai abunda kake boye?”
Aliyu ya masa banza yana ciro wayarsa ya danna.
“Son ta kake yi ko Aliyu?”
“Son ta nake yi ko akwai abunda zaka yi? Yanzu ma kaje ka fada mata cewar ina son ta shikenan”
“Very funny”
Muhseen ya fada yana dariya sannan ya nufi kitchen din. Aliyu ya bishi da wani kallon banza.
“Zan yi kokarin hana duk wani kusanci na ku ko kebawa ka fada mata magana son ranka, ba zan kyaleka ka rika shigar mata jiki ba kana son cutar da zuciyarta da ita sakare kawai”
Shine abunda Aliyu ya fada a ransa sannan ya tashi ya fice daga gidan gaba daya zuwa gidansa.Be samu Rahma a idan ba, hakan kuma be bashi mamaki ba domin ya saba mata da fita ba tare da ta nemi izininsa ba. Sai dai a tsakanin yau da ta fita da kuma wacan zuwan daga Abuja zuwa nan ya bata masa rai matuka. Yana zaune a gidan har magariba babu abunda yake tunani sai Ataa, ta masa maganganu masu zafi amman yai mata uzuri saboda tana cikin damuwa da bacin rai, zancen zata manta kowa ya fi komai tsaya masa a rai shi yana mamakin yadda ciwon kodarta zai taba kanta har ta manta da kowa.
“All this saboda ni oh Ya rabbi ashe haka jarrabawar nan take? Ni kuma tawa kenan?”
Ya furta yana tsaye jikin karfen stairs yana sauraren kiran sallah isha'i da ake. Komawa yai ciki yai alwala ya fito ya shiga masallacin unguwar yai sallah daya dawo be ma shiga falon ba ya shiga motarsa zuwa gidan Momy. Ko da ya shiga Momy ta shirya abincin dare na su Ataa tuwo da miya.
“Ga abincin ta nan ka je ka kai mata”
Ko zama be yi ma Momy tai masa wannan maganar. Kai tsaye ya nufi dinning ya dauki miyar Siyama ta saka masa tuwo da plates Momy tana ce masa idan ya kai ya dauko na can a wanke. Tare da Siyama ya tafi asibitin saboda ta rika masa kulolin, bayan yayi fakin ya fito tana gaba yana baya har suka shiga ciki. Wannan karon ma be shi sallama ba sai dai Siyama ta fanshe shi tun da ita ta yi sallamar. Bayan sun gaisa da Laraba yai ta rabon ido ko zai ga Ataa be ganta ba.
“Ina Ataa?”
Ya tambaya yana kallon Nana.
“Ta fita tun dazun”
“Ina taje?”
“Bata fada min inda zata je ba”
Fitowa yai sai Siyama tai saurin daukar kayan ta biyo bayansa ta saka su a mota ya kama hanyar gida.A bakin gate ya gaje ta ragowar kulolin ma sai da mai gadin ya rika mata ta shiga da su, sai ya koma cikin asibitin. Harabar ya tsaya yana ta kallon mutane kamin ya sake komawa ciki a zaton mai gadin ward din Aliyu likita me dan haka ya bude masa kofa da kansa ya shiga duk kuwa da kasancewar dazun ya ganshi da wata yarinya tana dauke da kuloli.
“Bata dawo ba?”
Ya tambaya daga shigarsa dakin.
“Eh har yanzu”
Juyowa yai ya fito ya dawo cikin motar ya zauna yana ta tunanin inda zata je cikin daren nan, wata kila Doc Bukar ya fita da ita ko kuma Muhseen daman be ganshi cikin gidan ba lokacin daya shiga, fargabarsa daya baya son ta kebe da wani gudun faruwar wani domin shi yana ganin ba ko wane namiji ne zai iya kallonta ya kawarda ido ya hade yawunsa ba, musamman ganin bata da kowa. Key yai ma motarsa yana rage ac cikin ya fito daga cikin asibitin ya nufi Clapperto road domin ya duba can, idan kuma har bada can gida zai koma ya saka Momy ta kira Muhseen shi kuma ya kira Doc Bukar. Slowly ya shiga cikin unguwar ya kashe hasken motarsa yana tukawa a hankali har ya isa gidansu Farida.
Karasowa yai da motar har dakin kwanon ya matsa ta can inda kofar dakin take ya sauke gilashin motarsa yana hango dakin mai duhu da farin wata ke haskawa, fitowa yai cikin motar a hankali ya nufo dakin ya haska screen din wayarsa daga nisa ya hango Ataa a kwance ta takure guri daya tana bachi kanta na gurin kofa. Wani dogon numfashi yaja ya sauke sannan ya koma cikin motar ya zauna ya bar kofar motar a bude. Idan ya tafi ya barta be san abunda zai iya samunta ba, idan kuma ya tashe ta wata kila wata bakar maganar zata fada masa ko kuma tai masa ihu. Sosai ya so ya tafi sai kuma ya ji ba zai iya kyaleta wani ya zo ya yaga mutuncin ta ba, idan ta kara shiga wani halin a yanzu yana jin kamar shine sanadi, kwantar da kujerar motar yai ya jingina yana ta kallonta tana bachi sai sauke ajiyar zuciya take har shi ma bachin yai gaba da shi.
*Khadeeja Candy ce*
ZAKI
By Khadeeja Candy
33...
Ban kwanta da niyar bachi ba na kwanta ne kawai na wani lokaci da zimmar idan na dan hutu tunanin ya fita a raina na koma asibitin, daga nan bachi yai gaba da ni ban sake sanin inda nake ba sai da sanyin azuba ya soma saukowa kiran sallah ya karade ko'ina sannan na bude idona mika nai ina jin yadda jikina yake ciwo saboda kwantarwa da nai a takure ga kuma dadewar da nai a kwancen. Hango mota na facing din inda na ke yasa ni saurin tashi zaune kamin na mike tsaye ina kallon kotar duk da kasancewar akwai hudun asuba sai dai a akwai wutar nepar gidansu Farida da ta hasko inda muke ba kamar Jiya dana kwanta babu nepar ba.
Gabana ne ya soma faduwa ina ta tunanin inda babbar mota zata fito irin wannan, sai kuma nake ganin kamar na taba ganin kalarta sai dai ba zan iya shaidar ta waye ba, wani karin abun tsoro kofar motar a bude take kuma babu kowa a ciki. Na hade yawu ya fi sau a kirga saboda tsoro gabana sai faduwa yake. Koma nai can kuryar dakin ina ta kallon ko zan samu wani abu na boya, tsoro duk ya kamani sai a yanzu nake ganin wautata na kwantawa ni kadai a gurin yanzu idan sace ni aka zo yi fa ya zanyi? Idan kuma wani abun za a mim babu mai cetona. Hawaye na fara yi a take na dan tako zuwa gurin kofar ya leko kaina, ina lekowa Aliyu na dago kansa ya kalleni yana zaune a gurin ya jingina da kwanon dakinmu wani abun mamaki a kasa ba tare da ya shimfida komai ba. Saurin komawa nai cikin zuciyata na raya min cewar ba shi ne ba, domin shi mai girman kan tsiya da kankantar da mutane ba zai zauna a nan ba, idan ma ya zauna mi zaiyi? Amman idan ba shi ba ne waye? Aljani? Domin kamaninsa da na wacan Aliyu bil'adam daya ne. Sake kai kaina nai zan leka sai shi ma ya leko cikin dakin.
“Ataa kin tashi?”
Jin muryarsa yasa na tabbatar da cewar shi din ne, amman kuma me yake yi a nan?
“Aliyu ne?”
Banza yai min kamar ba zai amsa min ba.
“Fito muje gida gurin Momy kamin mutane su taru”
Ya fada yana kabe kasar dake wandonsa.
“Kai din ne?”
Na tambaya dan tabbatar, nan ma be amsa ni ba ya nufi motarsa ya shiga, wannan miskilancin nasa kadai ya isa ya tabbatar min da cewar shi din ne dai ba wani ba.Fitowa nai ba dan na daina jin tsoron ba sai dai wannan karon ba zan iya musa masa ba. Takawa na fara yi ina kallon fuskarsa da wayar hannunsa ke haskawa sakamakon danna ta da yake. Zagayawa nai dayan side din idonsa n kan wayarsa amman hakan be hana shi sanin na karaso kusa da motar ba sai hannunsa ya mika ya bude min motar ni kuma na shiga ina kallonsa har ya janyo murfin motar ya rufe be dauke idonsa daga kan wayar ba. Nima na rufe gefena sai yai motar key ya kunna fitilar motar a sannan ya daga kansa ya kalli gabansa yana ribas kamin ya dawo kan hanya mu fito daga cikin kwanar mu hau titin Clapperto road. Kallonsa nake ina ta mamakin yadda mutum kamar Aliyu mai taka ma da kudi da ji da kai ga isa zai zauna a gurin kamar wannan.
“Miyasa ka zauna a nan gurin?”
Ya kai minti biyar zuwa bakwai kamin ya amsa ni har na dauka ba zai amsa ni ba.
“Idan na barki kika kwana a nan wani abun ya same ni kuma ni za ki dorawa laifin ai, kin fita ba ki fadawa kowa inda za ki ba”
Ya fada still be kalleni ba.
“Sa gaske kwana kai kana gadina? Da gaske gadina kai?”
Sai a lokacin ya kalleni be ce min komai ba ya faka motarsa gaban wani masallaci sai da ba kusa da shi sosai ba ya fita daga cikin motar ya bar wayarsa a nan. Ajiyar zuciya na sauke har yanzu na kasa daina mamaki ina ganin kamar ba gaske ba, maganganun Doc Bukar nata dawo min akai. Ni dai ina zaune a gurin har yai sallah ya fito ya dawo cikin motar, ashe ma daga masallacin zuwa gidan Momy babu nisa sosai domin tafiya kadan yai muka iso bakin gate din gidan.Sau daya ya danna horn sai kuma ya kalli inda na ke har lokacin kallonsa nake kallon mamaki da tunani.
“Bana son kallo na sha fada miki”
Dauke kaina nai daga barin kallonsa na maida idona gurin yatsun hannuna da nake juyawa cikim dayan hannun, har aka bude gate din jikina be daina ba ni cewar idonsa na kaina ba, mistakenly na dago kaina sai muka ido kallona yake sosai kamar mai son ganin wani abu a fuskata saurin maida kaina nai kasa sai aka bude mana gate din sai a lokacin ya dauke kansa daga gareni ya tuka motar ya shiga ciki, daf da kofar falon ya faka motarsa ban jira ya bani umarni ba na bude na fito kamar yadda na ga ya fito, yana gaba ina binsa a baya a hankali har muka isa gurin kofarz jikina nata kamshin turarensa daya cika motar. Knocked yai sau daya be sake yi ba har na wani lokaci sannan na ga ya dora wayarsa a kunne.
“Zo ki bude mana kofar falo”
Ko minti biyu be yi da sauke wayar ba Amina ta bude mana kofar falon, a maimaikon ya fara shiga sai ya tsaya kallona da ido ba zai iya cewa na wuce ba sai dai so yake na fara shiga kamin shi. Ina ganin hakan na wuce ciki sannan shi ma ya shigo daya saka wayarsa aljihu.
“Shiga da ita ciki tai sallah”
Wani kallo Amina tai min kamin ta sake kallon Aliyu tai saurin dauke kai.
“Zo muje”
Ta fada tana nufar upstairs. Kallonsa nai na ga ni yake kallo sannan na dauke kaina na bi bayan Amina. Dakinta ta kai ni ta nuna min bandaki na shiga na yi alwala ko da na fito har ta shimfida da min carpet da Hijab dina nai sallah sannan na mike tsaye da zimmar fita daga dakin zuwa kasa sai na ji ta ce.
“Ya ce wai ki kwanta ki huta”Saman gadon ta na hau kamar