Showing 36001 words to 39000 words out of 225640 words

Chapter 13 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

ana neman mai aikin a wani babban gidan masu kudi da ke Abuja, sai dai tace ba zata yi komai ba har sai ta zo gurin Nana ta ji ta bakinta dan tabbatarwa, ni kuma na ce mata na yarda ta zo su yi magana, sallama muka mata muka kamo hanyar gida wani dadi ya lullube ni na soma yarda da cewar kukana ya kusa karewa...



ALIYU POV.

Zai iya rantsewa a rayuwarsa be taba haduwa da wata mace yar talakawa mai karfin zuciyar da ta iya tsaya gabansa ta fadawa Rahma magana son ransa ba sai yau, for the first time yau wata ta ciwa Rahma mutunci ya kasa yin komai, har yanzu fuskarta yake gani irin kyau da haiya ta yai arba da shi a fuskarta a yau ko a mafarki be ci karo da macen da kallonta ya saka shi faduwar gaba ba sai yau. Kalamanta da ďai-ďaiya suke masa yawo a kunne, kalma zalinci ita kalma ta biyu daya tsana bayan talauci, yes he's rich and he know be zama dole ya taimaki kowa da dukiyarsa ba, amman yai wa kansa alkwarin ba zai taba yarda dukiyarsa ta saka ya zalinci wani ba, ko da kuwa talakan daya kyama ne. Yasan yadda lafiyata take da muhimmanci tun daga lokacin daya fara neman ta matarsa yana jin tsoron rasa ta a ko wace dakika ita kadai da take a natsayin matarsa hakan yasa shi fahimtar Ataa wacce ita kuma take zancen mahaifiyarta.
Haka sukai tsaye a falon bayan fitar Ataa har na tsawon mintuna talatin ba tare da kowa ya ce uffan ba, daga Aliyu har Rahma da Doc Asim dake ra sake saken yadda zai kare kansa. Rahma jiran take mai kare yace wani abu tun daga lokacin da Ataa ta fada mata ba daidai ba, amman bata ji yace komai ba, sai ma rike mata hannu da yai a lokacin da zata mareta. Aliyu kuma yana ta jiran abunda zai fito daga bakin Doc Asim amman ya kasa magana kamar an daure shi.

“Kodar mahaifiyata ka cire aka sakawa Rahma ba tare da sanin ba?”

Doc Asim yai saurin kallon Aliyu.

“No karya ta ke yi? Ita ta siyar da kodar da kanta, zan iya nuna maka shaida ma, ita ta siyar da kanta”

“Mi zai saka tai maka karya? You know what na yarda da komai amman ban yarda da zalinci ba, ban yarda na zalinci wani na kuma na kwanta nai bachi mai dadi ba, dan ina neman lafiyar Rahma ban ce ka zalinci wata ba, na fada maka ka nemo wacce zata saida zan biya ko dala dubu nawa ne, amman ban ce ka cire ba tare da sanin mai ita ba”

“Amman Dear ai yace siyarwa tai...”

“Silent”

Ya fada sai dai ba cikin daga murya ba, tare da dagawa Rahma hannun wacce ke kokarin kare Doc Asim da nuna abunda yai ba dai-dai ba ne.

“Ka bani amsa da saninta ka cire ko ba da saninta ba”

“Ni ban san wannan yarinyar ba”

Shine kawai abunda Doc Asim ya fada ya dauki akwatinsa ya fice a fusace har gumi na karyo masa idonsa su yi ja alamar ransa ya bace sosai. Yana fita Rahma ta kalli Aliyu sannan ta nufi upstairs cikin bacin rai da zazza6in da da ke kokarin rufeta. Zaunawa Aliyu yai saman cushion yana ta auna irin zalincin da akwai wa Ataa idan har ta tabbata Doc Asim ya cirewa mahaifiyarta koda ba tare da sani ba, mikewa yai tsaye ya bi bayan Rahma a bedroom dinta ya same ta zaune bakin gado tana waya be san me ta fada masa ba, kuma be san da wa take wayar ba, sai dai yana alamar kuka da hawaye a idonta, saurin fisge wayar yai ya kashe kiran sai ya kashe wayar gaba daya, ya zauna kusa da ita.

“Kin sani idan kina ciwo bana son kina wani dogon motsin, za ki yi street kanki ne kawai”

Kallonsa tai da duba mai mai ma'anoni da yawa idonta har ya fara ja.

“Miyasa zaka yarda da yarinyar nan ka karyata likitan da ya shekara biyar yana maka hidima?”

Be ce mata komai ba, ya kai hannunsa ya share mata hawayenta sannan ya rika fuskarta da hannayensa biyu yana mata magana a hankali yadda hankalinta zai kwanta.

“Za mu magana daga baya, for now ina son ki kwanta ki huta, and promise me za ki yi bachi?”

Ta dauke kai tana hadeye yawu. Sai ya jata zuwa kirjinsa ya rumgume, ya dan kishingida da gadon yana ta kallon sillin kamar mai tunani. Ya dauki awa daya a haka sannan ya soma jin sauka numfashinta mai zafi alamar bachi ya dauke, sai ya kwantar da kanta saman fillo ya lullube ta da blanket ya mike a hankali ya fita daga dakin dare da jan kofar dakin a hankali.

Fitowa yai daga cikin gidan gaba daya, tun kan ya karasa gurin motarsa ya danna key motar ta bude, yana shiga yai nata key tun kan ya kai gate mai gadin ya bude masa gate din yana daga masa hannu, ko kula shi be yi ba ya dauki hanyar gidansu wato gurin Momy, as usual idan babu Nasir ko Mama Fulani a kusa da shi Momy ce abokiyar shawararsa, ko da ma suna nan wani lokacin ya kan kirata a waya ya shaida mata, yau ma yana da bukatar fada mata abunda ya faru yaji nata tunani. He arrived in time a daidai lokacin da Momy ta kara Daddy ya shiga mota tana tsaye tana kallon yadda mai gadin gidan yake rufe gate, sai ta ya sake budewa da sauri jikin har bari yake, ashe Aliyu ya hango tafe. Murmushi tai domin ta san a duk duniya Aliyu kadai ya isa ayi masa haka a gidanta, baya danna horn sau biyu kuma bayana son jira saidai a jira shi, idan kana son kaganin bacin ransa ka kwada bata masa lokaci ko kuma saka shi jira na rashin dalili.
Tana ta kallon dan na ta har ya faka motarsa a inda ya fi masa soyuwa a harabar gidan sannan ya fito fuskarsa ba yabo ba fallasa kamar kullum ya doshi inda mahaifiyarsa take, yadda yake takawa sai ka rantse da Allah takun kasaita ne da nuna isa, alhalin haka tafiyarsa take, kamshin turarensa na ta sanarda zuwansa tun kan ya karaso kusa da ita. Zai da ya rage sauran taku shida zuwa bakwai tsakaninsa da ita sannan ya dabbaka sunnar nan ta murmushi wacce ta kara mishi kyau da haifa.

“Na ga Daddy ya fita yanzu har mun gaisa da shi ma”

“Eh yana ta sauri za su je meeting”

Haka suka jero ita da danta suka shigo cikin falon suna wannan hirar. Saman cushion ta zauna tana nuna masa dinning.

“Ga ragowar breakfast can idan zaka ci kanenka suka raga”

Ya dan yamutsa fuska yana murmushi dan yasan zolayarsa kawai Momy take.

“Momy kin san ai bana cin ragowar kowa ni, ina Sisters”

“Duka suna school”

Ajiyar zuciya ya sauke wanda yasa Momy sake dubansa.

“Wani abun ne?”

Ya jimm na wani lokacin sannan sannan ya kalleta a natse ya ce.

“Momy kin san kwana ki ina ta neman mai aiki ko? Sai ga wata yarinya ta zo gidan neman aiki.... ”

Tun daga lokacin da Ataa ta zo gidan ya jera mata labarin har ya isa zangon da ya fi rikitar da shi. Da mugun mamaki Momy ta kalli.

“Kuma ba ka ji komai a ranka ba Dan wajen Fulani? Ba zuciya da jini ne a kirjinka ba? A zalinci wata ta dalilinku har ka tsaya neman hujja?”

“Amman ni ban ce a zalince ta ba?”

“Miyasa da aka kawo maka kodar baka bincika daga inda ta fito ba? Akan me zaka zuba kudi mai yawa ka ce a samo maka kodar? Ba kayi tunanin ganin kudin zai iya saka Doc Asim aikata komai dan ya samu kudin ba? Ai da tun farko ka samu mai kodar ka yi magana da ita da bakinka, yanzu ga shi ka raya matarta kana cikin farinciki, ita kuma ka jefata a damuwa da bakinciki? Ka ji tsoron addu'ar wanda aka zakinta, kuma ka ji tsoron Allah ya isa, domin idan bata bi jikinka ba, tana bin dukiya da kaddara”

Lumashe ido yai ya bude yana fusar iskar bakina a hankali.

“Ka tuna lokacin da aka ce maka Rahma zata iya rasa ranta idan ba mata wano dashen kodar ba? Ka tuna? Ka auna ka ji ya yarinyar nan ta ke ji? Ita da mahaifiyarta ce, kamar ni ce ko Fulani aka cirewa koda ba tare da saninka ba? Idan ka gano me zaka yi?”

“Zan yi duk abunda zan yi na kwato muku hakkinku”

“To sai aka samu akasi ita yar talakawa ce, bata da wannan ikon bata da wannan gatan, mahaifiyar tana raye ko ta mutu babu wanda ya sani, wane hali suka shiga bayan wannan babu wanda ya sani, ina jiye maku tsoron abunda ta zai biyo baya, amman gaskiya an zalinci yarinyar nan”

“Momy kin san inna sani ba zan zalince ta ba, na yarda bana kula kowa amman bana zalintar kowa?”

“Ka bude zuciyarka kai tunani... Na san kana son matar ka kuma zaka iya komai akan samun lafiyarta, amman ina son na fada maka wani abu, ka ji tsoron addu'ar wanda aka zalinta, kuma ka ji tsoro mutumen da zai ce ya barwa Allah Allah shine zai isar masa, hakan yana nufin babu komai tsakanin shi da kai Allah ne zai wakilce shi ya fidda masa hakkinsa akanka.....”

Kallon Momy yai zuciyarsa cike da tsoro da be taba jin irinsa ba, jikinsa yai mugun sanyi, tsoron abunda zai biyo baya kamar yadda Momy ta ce yasa zuciyarsa rauni...


_____________________

Page daya ya rage mana mu gama free pages In-Sha-Allah. if you want to subscribe pay 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank. sai ku turo shaidar biyan wato screenshot ta wannan number 08036126660, ko kuma katin mtn na 300 ga marasa account ta wannan number 08036126660. yan nijar za ku tura 500fc na line Orange ko Airtel ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta wannan number 08036126660 Za'a saka ku Group.


Thanks 🙏🏻
Ku ziyarci YouTube channel dina, ku danna min subscribe kuma kui sharing. 👉https://www.youtube.com/channel/UCpAkml0pIh6MUnzt9nLh_qQ


*Z A K I*

By Khadeeja Candy


1️⃣5️⃣

Ya dade a gidan Momy zaune gaba daya jikinsa ya gama yin sanyi, yana ta jin kamar akwai laifinsa a cire mata kodar da akai, and if da laifinsa ya akai laifinsa ya shiga ciki bayan shi idan ma ba yanzu ba be tana ganin yarinyar ba, idan yai duba ta wani bangaren yana ganin cewar ba shi da laifin komai, shi dai kawai matarsa yake nemawa lafiya and shi be ce a cire da karfi ba. A masallaci yai sallah magariba sannan na ya dawo cikin gidan, jikin ba kwari kusan sai ya rantse shi be taba jin jikinsa a wannan yanayin, wata kila saboda ba a taba cutar wani a gabansa ba, ko kuma shi din be taba cutar wani da dukiyarsa ko da ikonsa ko karfinsa ba, sai wannan karon, duk kuwa da kasancewar wani bangare na zuciyarsa na fada masa cewar ba shi da laifi.
Yana shigowa falon Sisters dinsa sika make kyam kamar babu wani abu mai numfashi a falon, ko wacce ta shiga natsuwarta, tsayawa yai kallonsu kamar yadda ya saba idan ya shigo cikin gidan domin lura da yanayinsa da kuma halin da ko wace daga cikin kannen nasa guda hudu suke cikin.

“Ina Umar?”

Ya tambaya da irin fuskarka nan ta ba wasa.

“Be dawo ba”

Duka su hudu suka hada baki gurin bashi amsa dan sun sani sarai baya son kyaluwa, Momy zata iya tambayarsu abu su tsaya tunani ko wani sha'anin kamin su ba da amsa amman ban da Aliyu baya daukar wannan shashancin a time din da ya tambaye ka time din zaka ba shi amsa, idan kuma kai kuskure wani abun ya fito daga bakinka kuma kai ne a matsala. Juyawa yai ya shiga dakin Momy sai ya same ta zaune saman carpet tana jan carbi. Guri ya samu kusa da ita a kasan ya zauna yana fiddo wayarsa.

“Dan waje bata Fulani ina ta tunani anya likitan nan Asim zai kyale ta kuwa?”

Dagowa idonsa daga jikinkin screen din wayar yai ya kalleta.

“Ban gane ba?”

“Ina tunanin kamar ta jefa kanta a matsala ne, baka tunanin zai iya yi mata wani abun da nan gaba ba zata sake shaidarsa ba? Babban likita mai asibitin kansa kamar Asim ba zai dauki wannan matsalar ba, ba zai yarda ta karya masa aiki ba”

Aliyu yai shiru yana nazari.

“Wannan abu be min dadi ba sam Wallahi, saboda ban jidadi abunda ya faru da yarinyar nan ba, duk kuwa da ban santa ba, amman na san irin zafin da ake akwai ace an cuce ba gashi baka da hali jan hakkinka”

Mikewa yai tsaye yana fitarsa numfashi a hankali ya ce.

“Momy zan tafi gida, na san yanzu Rahma ta farka”

“To ka gaisheta”

“Za ta ji”

Ya juyo yana tafiyarsa kamar yadda ya saba har ya sauko kasa, ya nufi gurin motarsa yana shiga yai mata key ya dauki hanyar gidansa. Yana tafe yana tunanin abunda ya faru da kuma maganar Momy, he find himself in middle of tausayin Ataa da yarda cewa an zalince, every words of her yake tunawa da yadda take furta su, idan har ba zalince ta ba, ba zata iya daga hannunta ta mari babban mutun kamar Doc Asim ba, yadda ya lura da rashin tsoron da ke cikin idonta a lokacin da idanuwansa suke yawo a fuskarsa, ya tabbatar ko kashe Doc Asim zata iya yi a gaban kowa, and Momy was right ba lallai ne Doc Asim iya kyaleta ba.

‘Allah ya isa’

Haka maganarta ke ta dawo masa sabowa a kunne, ga wa zai isar mata, ga Doc Asim ko ga shi ko kuwa ga su dukansu? Haka yai ta saka tunani kala kala har ya isa gida, yai mamakin ganin Motar surikinsa a wannan lokacin, the first thing that come his mind is ko ciwon Rahma ya tashi ne, amman kuma idan ciwon ta ne ya tashi ai shi zata kira ba Daddynta ba. A bude ya samu kofar falon tun ka ya shiga yake jiyo muryar Alhaji Nasiru Gobir. Da sallama Aliyu ya shiga, surukinsa da wani yayan Rahma suka amsa masa, Rahma kan ko inda yake bata kalla ba.
Gurin ya samu kusa da ita ya zauna yana kallon Alhaji Nasiru Gobir wanda fuskarsa ke dauke da damuwa.

“Rahma ta fada min abunda ya faru, daman ta fadawa mahaifiyarta tun a waya, wannan wace irin yar iskar yarinya ce marar tarbiya haka?”

Aliyu ya juyo gefensa ya kalli Rahma sai kuma ya sake kallon mahaifinta ya ce.

“Ba ta fada maka abunda akai wa yarinyar ba?”

“Ko ma mi akai mata ai ba mu muka ce ta siyar da kodarta ba, irin talakawan nan da kake gani Aliyu ba su da komai a ransu sai hassadar nai arziki, idan suka ganka da arziki ji suke kamar su kashe ka su kwashe dukiyar, shiyasa tsakaninmu da talaka aiki kawai mu biyashi, wata banza a banza bata isa ta shigo har cikin gidanki ta fada miki maganar banza ba, watan ma kuma talaka!”

“Daddy har da kai ta ciwa mutunci, wai a gidanka ta raba ka koreta ni da kai duk ba musan darajar talaka ba”

“Zan sa a binciko yarinyar da iyayenta sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando ba ne”

Duk abunda ake Aliyu ba ce uffan ba, har Daddy yai musu sallama ya fita, a lokacin ne Rahma ta tashi ta nufi dakinta, shi kan sai da yaji tashin motar surukinsa sannan shima ya mike tsaye ya bi bayan Rahma. Gaban madubi ya same ta zaune tana cire dankunnen da ke kunnenta, kusa da ita yaje yai mata kissing sannan ya zauna gefen gadon yana kallonta.

“Miyasa za ki kira Daddy ki fada masa maganar da bata kai ta kawo ba?”

Da mamaki ta kalleshi

“Wannan abun ne be kai ya kawo ba? Yarinya karamar yar talakawa kamar wannan ta fada min magana son ranta ka ce be kai ya kawo ba? Aliyu ka san me kake fadi kuwa?”

“Amman ai zalintar ta akai? Yanzu kuma sai ki fadawa Daddy bayan kin san zai iya daukar wani mataki?”

“Amman mu muka zalince ta? Daman can matakin na ke son ya dauka shiyasa na kira shi na fada masa, tun da kai ka kasa komai sai ma rike min hannu da kai dan kar na dake ta”

“Sanadinmu aka zalince ta, kodar mahaifiyarta aka cire Rahma aka dasa miki? Kuma kike tunanin ba zatai wani hargagi na huce haushinta ba?”

Juyo tai gaba daya ta kalleshi da kyau.

“Kana magana Aliyu kamar ba kai ba? Lafazin da ke fitowa daga bakinta yana karantar da ni cewar ba kai ne ba?”

Hannu ya kai ya kama hanyayenta ya cigaba da mata magana a hankali kamar yadda yake mata dazun.

“Dear, zan iya juye yi wa mutum komai amman ban da zalinci, an riga an cuci yarinyar nan, kuma kodar nan an dasa miki ita wannan kadai ya isa yasa jin tausayinta waya sani ma ko mahaifiyar ta mutu”

“Tausayi Aliyu? Tausayi? Tausayi fa ka ce? Mi mukai mata da har za mu ji tausayinta? Mu muka zalince ta ne? Akan mi zaka yarda da yarinyar daka soma gani cikin kwana biyu, saman da likitan daya saba yi maka aiki shekara da shekaru? Ban taba ganinka cikin wannan yanayin ba Aliyu, ba ka taba ce min na ji tausayin wani ba, baka taba ce min kana tausayin wani ba, wanin ma talaka irin wannan yar shekara a gidanka”

“Ba tausayinta nake ji ba, ina kallon abunda akai mata ne a matsayin zalinci, and be dace ki saka Daddy a wannan maganar ba, zai iya unkura yi mata wani abu sanadinki, ni fa na yarda da wulakanta kowa na ci mutunci kowa kuma na kyama ci kowa amman ban yarda karfin iko ko dukiya su saka na zalinci wani ba, ba zan iya da hakkin wani a kaina ba”

Kai ta girgiza masa tana murmushi irin mai ciwon nan idonta na cika da hawaye.

“Ban taba yin wani abu ka ce ban yi daidai ba sai yau,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login