Showing 147001 words to 150000 words out of 225640 words
da za su bude ba ki na furta kalmar so a gareni tabbas ko zai furta ko ya nuna zai zama babu kamun kai a ciki.
“To kije ku gaisa inyaso sai ki fada mishi an tsayar miki da miji ko kuma kina da wanda kike so”
Da wannan shawarar da ta ba ni na tashi na fita zuwa gurin mutunen, mun gaisa da shi cikin mutunci ya gabatar min da sunansa aikinsa da kuma inda ya ganni wai lokacin da na taso islamiyar nan har ya tambaye ni gidanmu. Kai tsaye na bashi hakuri kuma na fada masa cewar akwai wanda za a tsiyar min a gida, ya nuna min rashin jindadinsa da kuma yi min fatan alheri sannan muka yi sallama. komawa nai bq na dauki littafaina na wuce islamiya zuciyata cike da tunanin ko zuwa yaushe Aliyu zai dawo? Mi ya tsayar da shi a abujar? Ni dai sam ban jindadin rashin dawowarsa ba, ba zan kuma kira abun da so ba, domin ba ni tabbacin ina son Aliyu ko akasin hakan, sai dai na san akwai sabo wanda ko fada kake da mutum dole ne wani lokacin sai ka yi marmarinsa balle kuma yanzu da na fara gane amfanin abubuwan da yai min.
MOMY POV.
Bayan tafiyar Ataa islamiya Momy ta tashi ta debi yan gurin da Mama Fulani ta sako mata a kwali wato snacks da cake ta nufi bq da su, da far'arta ta shiga bq din yana wayance wa kamar komai bw faru ba, ta karanci damuwa a fuskar Nana sai dai bata maida hankaki akan tatauna da Nana akan matsalar ba, a zatonta abunda Muhseen yai ne har yanzu yake damunta.
“Mun yi tafiya shekaranjiya ban fada miki ba, tafiyar ta safe ce shiya saka”
“Babbu komi Hajjiya ya hanya?”
“Al-hamdulillah, ga wannan”
Momy ta mika mata plates din hannunta, sannan ta dora da dalilin zuwanta bq din.
“Daman Daddyn su ne yace a fada miki kuma a nemi shawararki aji ta bakinki, wai yana son indai za ki amince sati na mai zuwa a daurawa Ataa aure da wanda take so ko waye ne, mun hanke wannan shawarar ne saboda hankalin kowa ya kwanta ita kanta hankalinta ya kwanta kin ga ko zuwa sallamar nan ba dadi ne ba, amman idan har aka mata auren dole kowa ya kama gabansa, kuma yi mata auren ba shi yake nufin hana ta karatunta ba no zata cigaba da karatunta a gidan mijin ko kuma a nan idan zai yarda”
“Sati daya?”
Nana ta nanata.
“Nima kaina naga kamar abun yayi wuri, sai dai saboda kwanciyar hankali kowa ake son ayi haka, ina son ki manta da duk abunda ya faru ki tambayi Ataa wanda take so idan a kusa ne sai neme shi idan kuma nesa ne sai a san ta yi tun wuri, idan kuma kina ganin watan yayi tsawo za ki iya fadar lokacin da kike son a saka, nan da wata daya biyu uku ko shekara ma ko fiye da haka”
“A a hukuncin da kuka yanke ya yi, waya sani ko zan kai gobe ma balle nan da wata daya ko shekara, fatar ko wace uwa ai yarta ta samu gurin zaman da ya dace da ita, Na gode sosai Hajiya”
“Karki jin kunya ko nauyin komai Wallahi duk wani abunda nai saboda Allah nai, dan haka karki taba kawo wani abu a ranki, ni da ke an zama yan'uwa kuma zan mata komai kamar yadda nai alkwari In-Sha-Allah, idan tarewar a nan kusa ne ko nesa duk daya ne a gurina”
“Allah ya saka da alheri”
Sosai Nana ta so tayi ma Momy maganar tashinta, sai kuma ta ji nauyi saboda girman Abunda Momy ta zo mata da shi, idan kuma tai mata maganar a yanzu wata kila ba zata fahimta ba, sai kawai ta zabi aje maganar a cikin har na wani lokaci.
ALIYU POV.
be Momy sun koma tare ba saboda yana jin zaman sokoto yana gundirarsa, abunda Rahma tai masa kadai ya isa ya saka shi jin baya son zama gidan da suka kasance suna rayuwa a ciki su biyu, ga kuma tunanin cewar Ataa ba zata zabe shi ba, so yana ganin kamar komawarsa sokoto karin bakinciki ne kawai a gurinsa bayan wanda na Mama Fulani take masa a nan. Domin Abbah ya fada mata matukar aka tambayi yarinya ta amsa musu da cewar tana sonsa za a daura masa aure da ita sati mai zuwa.
“Wallahi Aliyu ka ma ce ka fasa idan ba haka na zan yi wa yarinyar nan raashin mutunci, sai na sa ta raina kanta sai ta gwammace a haifo ta duniya ba, ba zan taba karbarta a matsayin suruka ba, na kuma zan taba son ta ba, kar kuma ta ce zata kira da wani sunan ko ta tako inda na ke, kuma idan aka daura auren nan sai na taka har sokoto na ciwa uwarta mutunci na ga wanda ya tsaya musu a garin sokoto, wai har da hada baki da Abbah kun ce sati daya ko? Saboda ayi saurin yin abun ai kana jin kasan yarinyar ba yar kowa bace kuma ba neman auren suke sun ga dan arziki, wai Aliyu baka ma kunyar ace yarinyar nan ce matar ka?”
Daga ita sai shi ne a dakinta take mishi wannan fada, sai ya shafa kansa ya ce.
“Ni kaina ban tsammaci haka ba Mama, amman ya za'ayi”
“Baka ma san abunda za'ayi ba kenan? Abunda za ayi kawai ka fasa auren yarinyar nan domin ko na aureta ba zan bari ku samu kwanciyar hankali ba, ga yan mata nan ai babban abunda za akayi ka bawa Rahma haushi a yanzu ka auro wanda ubanta ya fi uban Rahma arziki, amman ba yar bara a titi ba, bara fa Aliyu bara”
“To zan yi tunani Momy”
Shine kawai abunda ya fada mata ya tashi ya bar mata dakin saboda Maganganunta basa masa dadi, sam be son ya ji mai zagin Ataa a yanzu.
MUHSEEN POV.
tun bayan da yai maganar da Nana a waya ya zuba ido yana sauraren abunda zai faru, yasan indai tana da hankali da tunani ba zata bari yarta ta zaba tsakanin shi da Aliyu ba, da ace Aliyu ya samu shi ya rasa kara dai su rasa gaba daya, domin shi be ga ta inda zai rika kallon Ataa a matsayin matar Aliyu ba, a cikin Familyn a yanzu haka yana ganin kamar abu ne mai wahala ya ce zai samu wacce ta yi mishi ta kwanta masa a rai kamar Ataa, shi da ya dade yana burin auren mace da abokansa zasu susuce idan sun ganta kuma mai jini a jika kamar Ataa yanzu kuma ace Aliyu ne madadinsa, har ga Allah ya hakura da aurenta amman baya son Aliyu ya aureta kara dai ace bata cikin familynsu gaba daya. Tun daga ranar da ya bawa Momy hakuri be sake yarda sun yi ido biyu da Aliyu ba, kwata kwata baya shigowa gidan a lokacin da ya san Aliyu na cikin gidan, idan ya shigo yana part dinsa sai Aliyu ya fita sannan zai fito, dukan abunda kunnuwanta suke son ji wanda Ataa zata zaba, idan shi ne zai yi farinciki sai dai ya cire rai saboda ya san ba zata zabe shi ba kamar yadda yake ganin cewar ba zata taba zabar Aliyu ba.
ATAA POV.
wasa wasa akwa kwashe kwana biyu har uku Aliyu be dawo ba, ban kuma ji Momy na zancen dawowarsa ba, sai dai bana wasa da zuwa makaranta na da lokaci yayi rashin fara bokon kuma sai ya fara damuna wanda na san da Aliyu na nan da yanzu ya saka ni ko ya samu wanda zai saka ni, domin ina ganin sha'awar yadda Siyama ta ke shiryawa ta tafi makaranta da safe har jin na ke kamar na bita.
Ranar Alhamis ranar da Momy ta cika kwana hudu da dawowa daga Abuja, Daddyn ya dawo da rana ya aiko Momy da kanta ta kira ni ni da Nana, tun daga lokacin da na ji kiran sai gana ya soma faduwa domin ina jin cewar zai tambayi idan na yanke shawara ne. A part dinsa muka taru gaba dayanmu har Momy da ni da Nana da kuma Daddyn kansa. Ni da Nana muka zauna kasa Momy kuma tana zaune a kujera daya da Daddy, babu yadda ba tai ba Nana ta tashi ta zauna saman kujera amman Nana ta ki. Bayan Daddy yayi gyaran murya ya soma magana da Nana kamin ni.
“Hajiya tace ta tatauna da ke akan maganar auren Aisha, kuma kim fahimta ina fatar ba mu danne miki hakki ko tauye ki a wani abun ba”
“Babu ko kadan”
“Mashallah, Aisha kwana ki na kiraki tun Hajiya bata nan na fada miki kije ki yi shawara ki fadi min kuma ki fadi a gaban kowa cewa ga wanda kike so, saboda kar ya zamana mun tauye miki hakki ko saka ki abunda be kamata ba ko kuma ba ki tashi ba a yanzu, dan haka muna saurarenki karki ji nauyin baki ko kunyar fadar komai ni na baki dama, idan ma ba ki da wanda kike so a yanzu ko kuma kina ganin kamar abun ya yi kusa za a iya daga miki kafa har zuwa lokacin da kike so”
Kasa cewa komai nai kaina yai mugun nauyi har ya sauko min ciki ido, gaba daya falon ji nai yana juyawa gabana ya shiga faduwa.
“Aisha... Ke mike saurare”
Ya maimaita jin na yi shiru har na wani lokaci, yawun bakina na hade ina da motsa yatsuna a cikin hijab.
“Yana da wahala ta iya furtawa, ba al'adar mu bace furtawa ka tsaye ka ce ga wanda kake so”
Momy ta fada, sai Daddy ya ce.
“Muhseen kike so?”
Na girgiza masa kai alamar a'a.
“Akwai wani wanda kike so ne?”
“Kamal kike so?”
Momy ta tambaya sai na girgiza mata kai a nan din ma ina hade yawu.
“Kina da wani wanda kike so ne?”
Na kasa cewa komai ko matsin sai na kasa yi.
“Aliyu kike so?”
Daddy ya tambaya. A take wata irin kunya da ban taba sanin ina da ita ba, ta rufe kai kasa da kaina gabana sai faduwa yake idonuwana suka cika da kwalla. Tasowa nai na baro musu falon da sauri kafafuwa har hadewa suke kamar za su tarde ni na fadi. Da gudu na nufi Bq na fada saman katifa na fashe da kuka na rashin dalili.
ALIYU POV.
Yana zaune falon Momy Husna ta kira, sai ya ki ya daga kasacewar yana cin abinci ne, after few minutes Amina da kira shi nan ma be daga ba sai da ya gama cin abincin, yana kokarin bulbula zuwa ya sha Maryam ta zo da waya ta miko masa wai Amina tana son magana da shi. Ya dade yana kallon wayar sannan ya karba ya kara a kunnesa yana kai ruwan a bakinsa.
“Ya Albishirinka....”
Shiru yai ya kasa cewa goro jinin zuciyarsa na gudu da sauri ya rika shan ruwa har kana jin wucewarsu a makoshinsa.
“Ataa ta ce kai take so kai kai kai”
Mikewa yai tsaye da sauri sai sa ruwan da ke bakinsa suka tsarke shi a take ya fara tari a gurin. Ya sauke wayar ya kalla ya sake maida a kunnensa.
“Say it again....”
“Ataa tace kai ta ke so, kuma mamanta ta yarda a daura auren wannan week din”
Bude baki yai kamar zai yi magana sai kuma ya kasa, ya mikawa Maryam wayar ya shafa kansa ha zauna da sauri yana da mamaki, before yai sujada a gurin yana ma Allah godiya, then ya mike tsaye ya dauki wayarsa ya nufi motarsa Nasir ya kira ya fara labarta masa abunda ya faru. Sai shafa kansa yake yana ganin kamar ba gaske ba, ko da ma tirsasata akai a gurinsa ba komai ba ne zai iya kula da ita. Ba shi da wanda zai taya shi murna a nan daga Mama Fulani har Muhseen and he don't want to celebrate it with Ammy saboda kar Mama Fulani ta ji haushi.
“Nasir za a samu jirgi yanzu?”
Ya tambaya with full farincikin a ransa da jikinsa da ruhinsa.
“I don't think so amman bari na kira na ji”
“Now pls”
Kamin Nasir ya kira ya fada masa cewar babu jirgin yau sai dai gobe har ya matsu. Haka nan kawai farinciki ya saka shi shiga mota ya zaga garin Abuja da kewaye sai murmushi yake kana ganinsa kasan yana cikin farinciki da jindadi. A gangan ya ki dawowa gida gurin Mama Fulani ranar dan baya son ta bata masa farinciki a yau. Da dare ya kira Momy baki har kunne ta kara tabbarta masa da hakan. Kasa kwana yai a daren saboda farinciki yana ta ganin Ataa a fuskarsa, kamin gari ya waye duk ya matsu. Tun 7 ya isa airport bayan jirginsu sai 10 zai tashi, a gurin Nasir ya same shi ya taya shi murna haka yai ta kira har ten sannan jirginsu ya tashi.
Na dade ina kukan har na shigo ta same ni a dakin, hankalinta ya tashi sosai ganin kukan nawa ba na wasa ba ne.
“Lafiya Ataa?”
Tashi nai zaune Ni kaina ba zan iya fadar dalililin kukanawa ba, sai dai na kasa daina hawaye ina jin wani bakon yanayi na rabata har yanzu na kasa daina jin nauyin a kaina da kuma zuciyata ban taba sanin cewar haka ake ji ba ko kuwa dai ni na ji haka Saboda ban saba ba abun ya zamo min bakon al'amari?
“Ba kya son shi?”
Na kasa cewa komai.
“Karki cuci kanki Ataa idan ba ki son shi ki fada na san yadda ake idan aka gabatar maka da wanda baka so, karki cutar da kan ki”
“Ni ma ban san dalilin kukan ba, amman har ga bana jin wani kwankwanton ko tatamar zabar Aliyu da yai”
Har lokacin da na ke maganar hawaye be daina sauko min ba. Murmushi Nana tai ta kai hannunta ta share min hawayen fuskata.
“Ina fatar mijinki ne na har abada, kuma ina fatar zabin Aliyu ya zame miki alheri a rayuwarki, rayuwar da na ke miki fatan samu ina fatar ita ce a yanzu take rabarki, kuma fatar wannan zabin da kika yi ba zai raba kan iyalan gidan nan ba”
A cikin raina na amsa da amin sannan na kwantar da kaina jikinta. Na kara fashewa da kukan, sai da nai mai isata na samu natsuwar ruhi da zuciya sannan na tashi na shirya na wuce makarantar islamiya, yau a inda na zauna jiya na zauna kusa da wata budurwa mai far'a wacce na zauna da ita jiya, sosai na maida hankalina gurin karatu amman na kasa karanta komai sai tunanin abunda ya faru nake har aka kusa ta shi.
“Yau ba za ki biya ba?”
Na dago daga tunanin da nake na kalleta.
“Zan biya”
“Na ga an kusa tashi ne, ban ma san sunanki ba”
“Sunana Aisha”
“Okay ni kuma sunana Asma'u”
“Kai ashe ke mamana ce”
“Ina da sunan Mama kenan?”
“Eh sunan Mamana ne”
“Eyee daga yau Mama zaki rika ce min”
Na yi murmushi tare da tashi na nufi gurin da malamin yake zaune ana biyawa, na biya harufan da na iya ya kara min wani na taso na dawo inda na ke ma zauna sai yarinyar ta ba ni yasin kanzo wai ko ina so, rai na biya dan haka na karba ina lasawa na ji yaji kamar zan hauka ce da sauri na mika mata ragowar ina fiddo halshena waje ,sai ta saka min dariya ita da wata yarinya da ke gefenta.
“Aisha Aliyu ta so ana kiranki”
Malamin nan da Aliyu ya danka ni hannunsa ranar ne ya shigo yana fadin hakan, ni kuma ban kula ba domin ban dauka da ni yake ba duk kuwa da kasancewar ni yake kallo kuma na san gurin saka sunan form din daya tambayi ni Aisha Umar na fada masa.
“Aisha Aliyu”
Ya maimaita yana kallona sai na nuna kaina.
“Ni...?”
“Eh ta so ana kiranki”
Na tashi ina ta tandar baki saboda yajin na fito na biyo bayan malamin sai ya juyo ya ce min.
“Dauko littafanki?”
Ba musu na juya na je na dauko na biho bayansa, ina ta mamakin dalilin kirana Aisha Aliyu da yai.
“Kije waje ana jiranki”
Na nufi gate din cike da tunanin mai kiran nawa a wannan lokacin da ba a tashi a makaranta ba. Ina fitowa ya hango Aliyu jikin motarsa sanye da kakanan kaya yana kallon inda na ke tsaye da alama daman ni yake jiran na karaso, wani irin tattausan murmushi da ban taba sanin yana tare da shi ba ya rika aiko min yana min wani irin kallo mai wuyar fassara, yayi masifar kyau saboda Murmushin ya kawata fuskarsa har sai da ya saka gaba faduwa, kasa karasawa nai a na tsaya a gurin gate din ina kallonsa sai ya gyara tsayuwarsa ya rumgume hannayensa a kirji yana ta kallona kamar zai cinye ni, daga bisani ya dago daga jikin motar ya daso inda na ke, kamin ya karaso nai kasa da kaina kunyarsa ta rufe kamshin turarensa kuma ya zagaye ni siffar zatinsa ta hana ni sukuni. Hannu ya miko min na san be saba taba ni ba dan haka na mika masa littafan hannuna sai yai gaba ya bar a gurin, sai da ya isa gurun motar ya bude front ya juyo ya kalleni sannan na fara takawa da sauri gudun kar wani ya fito ya hango mu daga dalibai ko malaman makarantar. Ina isa na shiga na zauna sai ya rufe motar ya bude gidan baya ya saka littafan nawa ya zagayo mazaunin direba ya shiga yai mata keys muka hau babban titin unguwar, na yi zaton ko gida zai maida sai na ga mun wuce hanyar gida sai tafiya yake da ni, ni ko sai tandar baki na ke saboda yajin da na ke ji tun ina yi a hankali har sautin ya fara fitowa, da sauri ya maido da hankalinsa gurina kamar ba tukin mota yake ba ko kuma na ce ba a kan titi mike ba.
“Kin ji ciwo ne?”
Na kasa magana.
“Ko yaji kika ci?”
Na gyada masa kai alamar eh, sai ya faka motarsa gefen titi ya fita daga motar ya tsallaka titi ya shiga wani shagon be dade ba ya