Showing 81001 words to 84000 words out of 225640 words

Chapter 28 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

numfashin nawa ya daidaita, sai sannan na soma ganin likitoci su uku ashe mutane ne ba aljannuna ba kayan likitocin na su ne nake gani farinsu kamin idon nawa ya waye.

“La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam”

Shine abunda ya fito daga bakina sai na lumshe ido ina fitar da numfashi a hankali. Dayan daga cikin su ne naji yai hamdala ga Ubangiji da alama shi din musulmi ne. Sai na ji dayan ya kira sunana da hausar da da bata fito sosai.

“Aasha”

“Na'am”

Na amsa ina kallonsa sai dai muryar tasa har yanzu kasa kasa nake jinta. Dauke ni sukai daga saman wannan gadon suka dora ni akan wani suka turani zuwa wani dakin na musamman a akan gadon dakin suka dorani sannan sannan suka saka min drip dayan kuma ya saka min bandeji a bayan kaina, sannan suka juya suka fita. Lumshe ido nai ina kokarin tuna abunda ya faru sai na ji an turo kofar an shigo hakan yasa na bude idona sai na ga Kamal cikin shiga ta manyan kaya ya doso inda nake cikin yanayin damuwa.

“Ataa”

Na kalleshi ina kokarin amsawa sai ya kai hannunsa ya taba jiki.

“Kina jin wani abu yanzu?”

“Bana jin komai”

Murmushi yai ya gyara min kaina da gashina.

“Sannu”

Na gyada masa kai.

“Likito ci sun ce abarki ki yi bachi, zan je gida na dawo ke kuma ki samu bachi kinji”

Nan ma kan na gyada sannan na ce

“Na gode”

“Ba komai Allah baki lafiya”

“Amin”

Na amsa cike da nauyin baki sannan ya juya ya fita, ni kuma na lumshe idona bachi wahala yai gaba da ni. Wata kila na kai wa biyu ina bachi kamin na farka, idona na fara budewa ina ta kallon farin silin dakin warin asibiti na soma ji kamin na kamshin turaren Aliyu ya biyo baya, dagowa nai kadan sai na ganshi zaune saman kujera yana ta kallona da cat eyes dinsa ko kyaftawa ba yayi. Nima idon ma sakar masa ina ta kallon fuskarta, sai a yau ake kara tantance kyauwunsa hanci ya sauko sosai ga manyan ido masu daukar hankali.

“Ba na ce ki daina kallona ba?”

Yayi maganar kamar shi ba kallona yake ba, yana takura idan ana kallonsa sai dai shi ya iya kallon wasu har sai ka soma tsarguwa. Rumtse ido nai ina turo baki, sai na ji an buge min bakin da sauri na bude idon na kalleshi yanayim yadda yake sai yai min kamar ba shi ya bugar min bakin ba sai dai hakan be hana na zaburo masa.

“Mi na maka zaka dake ni?”

Kallona kawai yai be ce komai ba ya mike tsaye yana saka hannunsa na dama aljihu sai kuma ya kai dayan hannun sai taba kaina.

“Me zaka mata? Bayan marin da Mama Fulani tai mata wani zaka mata kuma?”

Kamal ne ya shigo hannunsa rike da leda yana fadin yana tare da doso inda nake kwance, Maganarsa bata hana Aliyu tana kan nawa ba, kamar ma be san da shigowar Kamal a dakin ba haka yai domin ko inda yake be kalla ba ni kawai yake kallo yana taba jikina da alama so yake yaji idan jikin nawa da zafi ko sanyi.

“Ashe dai ba Kamal kadai yake iya kula yar aiki ba, idai ko haka ne ya kama ka sauke girman kan nan naka Aliyu”

Dagowa Aliyu yai ya kalli Kamal.

“Ba a fada min abunda zan yi sai dai ni na fadawa wasu abunda za su yi, a kasa da ni kake Kamal kasan ma kasan takarmin kafata, ya zama dole ka min biyayya kuma ka kalleni da daraja ba zan sake musayar yawu da irinka ba”

“Daman ai ba ku saba ganin kowa da daraja ba, sai mai arziki ko wanda arzikin ya nemo saninsa, ban yi mamaki ba kai ma ai dan wajen Fulani ne”

“Yes dan ta ne, mai sanin darajarta ,kar bakinka ya sake ambatar sunanta idan ba haka ba sai ka yi nadamar saninta a rayuwarka, and i warned you karka sake shiga rayuwar yarinyar nan? Ashe kare ne kai marar zuciya, yanzu kuma umarni na ke baka ka dauke ta ka maida ta gida kamar yadda ka dauko ta kamin nan da one hour”

Aliyu ya fada yana hada babban yatsansa da na uku sai suka bada wata kara kamar an yi tafi, sannan ya nufi kofa ya fice ransa a bace. Da wani kallon wulakanci Kamal ya bishi yana tsaki kamin ya juyo kaina ya kalli ya sakar min murmushi.

*.ZAKI

By Khadeeja Candy

27...


Kallo yake da mamaki yana kara gyara zamansa.

“Waya yaudare ki Ataa wane hali ne ya jefa ki ke da mahaifiyarki?”

Hade kukana nai sannan na sauka daga kan gadon nai tsaye ina kallonsa.

“Na ji sauki za mu iya zuwa gida?”

“Gida gurin Mama Fulani ko gida gidanmu?”

“Ka dauke ni daga asibitin nan ya kai ni wani guri inda ba zan ji kamshi magani ba”

Ido ya sakar min yana ta kallon fuskarsa na bayyana irin tarin tambayoyin da ke zuciyarsa. Sai kuma ya mike tsaye ya aje kazar a kan wani karamin dorowa ya fice daga dakin, ya bar ni ina ta zullumi da tunani wata kila idan an koma Mama Fulani korata za tai da gaske ko kuma ta sake min wani dukan, ni da sam ban jidadin da Kamal ya kawo ni asibitin nan ba domin na san ba da amincewar ta ya kawo ni ba, kuma yadda Aliyu ya fusata ita zata iya fusata ko dan shi. Tare da wata likita mace ya dawo ita tai min umarni da na zauna na zauna kamar yadda ta ce ta duba ni sannan tai rubuta a wata takarar guda biyu ta mika masa ta fice.

“To muje”

Ya fada yana kallona sai na wuce gaba ina ta jin kunya domin kaina babu dankwali gyale ma balle Hijab, ya dauko ledar kazar ya biyo bayana, ni dai tafiya kawai nake ba dan inda zan biba domin ban san kan asibitin ba ina ta bin inda nake sa rai da zaton hanya ce har na fito daga ward din ina jin kunya sai dai na lura kowa be kula da ni ba.

“Nan za mu bi”

Ya fada yana daukar wata hanyar dabam ba tare daya jira ni ba. Haka na bi bayansa har muka isa wani gurin da ake aje motoci ya nufi motarsa ya bude ya shiga ni kuma na bude front seat na shiga na zauna, be kalli inda na ke ba har muka isa gidan, a tsakanin asibiti da unguwar tafiya ce mai nisa ban san ko'ina ba a garin Abuja balle na ce ga unguwar da muka fito ko muka wuce amman duk da tsaye tafiyar Kamal be ce min komai ba kuma be kalle ni ba har ya faka motarsa a harabar gidansu. Ban tana shiga gidan ba sai yau, shi ma gida ne babban mai bangarori da dama domin shi ya fi part hudu duk ban tsaya na tantance ba sai dai shi gidan kasa ne ba kamar na su Mama Fulani da yake gidan sama ba. Shi ya fara fitowa ya rufe motar sannan na sauko daga motar na rufe na fi bayansa cikin rashin sakewa da bakunta a wani gidan da ban ta6a shiga ba.
Yana gaba ina baya har muka isa cikin gidan, da kunya sosai na shiga cikin gidan, su kan na su gidan tsakar gidane farko kamin ka kai ga kofar shiga falon, wasu yan mata biyu na gaban murhu suna suya naman rago sai kuma wata dattijiwa mai kamar yar aiki tana yanka nama ita da wata mata da na ji Kamal din ya kira da Mama.

“Mama ga bakuwa na kawo muku”

Matar ta kalleni tana murmushi sannan ta kalleshi ta ce.

“Maraba da ita ina ka samo mana wannan bakuwar?”

“A fara bata guri da abinci ta ci ta koshi zata ba ku labari da kanta”

“Ina wuninku”

Na gaisheta cikin ladabi sai ta amsa min tana ta kallona sai kuma ta kalli Kamal tai murmushi.

“Sai Soja”

Daya daga cikin yan matan ta fada tana dariya sannan ta doso inda nake ta rika hannuna nufi cikin falon gidan. Ba laifi an gyara ko'ina an kuma turare falon da turaren Awwaba ko ina sai kamshi yake irin na yan sudan. Da kanta ta zaunar da ni saman cushion tana ta kallon gashin kaina daya bazu a jikina.“Karki ji tsoro babu abunda zai iya yi”

Kamal ya fada min yana murmushi ganin kamar hankalina ya tashi da jin kalaman Aliyu.

“Ya ce ka maida ni gida”

Kallona yai sai kuma ya kai hannu ya bude ledar hannunsa kaza ce mai zafi da yoghurt ta sha mai har takardar da aka saka ta ciki ta narke da mai.

“Ban san me zan siyo miki ba shiyasa na siyo miki kaza yar marmari, wata kila kuma ba ki ci abu mai nauyi domin na ga jikin na ki kamar na baby doll”

Ya fada fuskarsa da murmushi yana daukar cinyar kazar ya miko min, sai na kasa karba, na kuma kasa sakewa ba duk irin son nama da nake sai na ji ya fita rai, gaba daya hankalina yana can gurin Mama Fulani da Aliyu, tsorona daya kar korar da Mama Fulani ta ce zata min ta tabbata ga shi Aliyun ma ya fusata wata kila shi ma korata zai yi. Idan ko har suka kore ya zama anyi ba ayi ba kenan, abunda na zo nema be samu ba.

“Karbi ki ci, na fada miki karki ji tsoro, babu abunda zai same ki”

Hawaye ne suka sauko min na kasa ce masa komai kuma na kasa karbar naman.

“Kin fi son ki koma gidan nan?”

Na gyada masa kai sai yai murmushi

“Zan maida ke amman ba yanzu ba, Aliyu be isa ya bani umarni na bi ba, wani fadin rai nashi da hargaginsa na banza ba zai saka nai abunda zai dauka cewar tsoronsa na ke ba, ban san abunda kika yi daya saka Mama Fulani ta mareki ba, sai dai ina ganin kamar be dace tai miki hakan ba dan kawai kina aiki karkashinta”

Kasa nai da kaina na saka hannu na share hawayena, murya can kasa kasa na fara magana.

“Zan jure komai za a min a ko'ina matukar hakan na nufin silar farincikina, samun lafiyar mahaifiyata shine farinciki a yanzu shine abunda na ke bukata kuma shine dalilin zuwana aiki a nan, ka kyale na wulakanta ta dake ni idan tana ra'ayi ta yi min abunda duk ta ga dama, zan jure har na cimma cikar burina”

“Zan taimake ki Ataa zan taimake ki mahaifiyarki ta samu lafiya”

Kallonta nai idonta na zubar da ruwan hawaye na ce.

“Bana bukatar taimakon kowa a yanzu, bana son kowa ya taimake ni na fi yarda da nai komai da kaina, da sunan taimako wani ya yaudare yaudarar da ta jefa mahaifiyata da ni a cikin wannan halin, ba zan sake yarda da taimakon kowa ba, matukar ba talaka ne dan'uwan ba”“Sannu bakuwa ya sunanki hala?”

“Aisha”

“Kai kai sunan Mamanmu ne”

Ta nufi wata hanya da ke kamar corridor sai ta ga ta fito da gorar ruwa da kofi a hannu ta kawo gabana ta aje min.

“Ki fara shan ruwa kamin abinci ya zo”

“Na gode”

Na fada ba tare da na kalli ruwan ba, sai ta tashi ta fice daga falon ta bar ni nan zaune ina ta kallon yadda aka kawata ko'ina na falon. Wata budurwar ce ta shigo dauke da farantin nama da yaji a gafe ta aje mika min.

“Ga shi ki saka a baki bakuwar yaya”

Ta fada da kamar zolaya.

“Ina Kamal din yake?”

“Ya fita yanzu amman ya ce mu kula masa da ke”

A yanzu ma murmushi take tana maganar ni kuma na mike tsaye ina kallon kofa na ce.

“Bari na leka gidan Mama Fulani kamin ya dawo”

“Okay kin santa ne?”

“Eh na santa”

Shine kawai abunda na fada mata na nufi kofar ina ta sauri na fito daga falon.

“Aa har kin fito?”

“Eh nan zan je gidan Mama Fulani na dawo”

Na bawa matar dazun amsa sai ta amsa da.

“Okay sai kin dawo”

Kamin na isa gate din gabana nata faduwa ina ganin kamar haduwa zan yi da Kamal ya dawo ya hana ni fitar, ina samun nasarar ficewa daga gate din na tsallaka titi da sauri na buga gate din gidan Mama Fulani mai gadin ya bude min na shiga da sauri kamar wacce tai sata. Gadan gadan na doshi cikin gidan duk irin faduwar gaban da nake ji da tsoro arba da Mama Fulani sai na danne shi na tura kofar falon na shiga da sallama. Tana tsaye tana magana da suka yan matan nan na dazun da suka zo baki da kuma yayanta ta juyo ta kalleni.

“Me kika dawo ki yi?”

Durkusawa nai daga inda nake tsaye bakin kofar na hade hannayena ina rikonta.

“Dan Allah dan girman Allah ki yi wallahi ban san ya kai ni asibiti ba, kuma ban ce ya kai ni ba, dan Allah karki kore ni”

“Da ya kai ki asibiti da kar ya kai ni uwarsu daya ubansu daya a gurina, amman tabbas yau ba za ki kwana a gidan nan ba”

“Ki tausaya min dan Allah saboda Mama nake wannan aikin, bata da lafiya kudin maganinta nake nema”

“Ni nan da kika ganni ba ni da uwa da uba duka sun mutu marainiya ce ni, kara ke ma har da iyayenki a raye, wuce kije ki hada kayanki yanzu nan bana son ko minti talatin ki kara a gidan nan”

Ta fada cikin daga murya tana nuna min kofar fita. Siyama ta kalleta ta da tausayawa ta ce

“Mama ki yi mata hakuri idan ta sake sai ki koreta”

Sai Rukaiya tai karaf ta ce.

“Wallahi ni bana ma son minti biyar ta kara a gidan nan wacan yarinyar da kike gani tun da ta zo kullum sai wani mummunan abu ya faru”

“Za ki wuce ko ba zaki wuce ba”

Mama Fulani ta daka min tsawar da ta sakani mikewa tsaye a razane na fice da sauri. Garejin na dawo na zauna ina ta kuka mai karfi wai ko wani zai ji ya zo ya tambaya dalilin kukana yajd ya bata hakuri amman babu wanda ya zo har na ji muryarta tana kiran Zaharadden direba.

“Ki fito yanzu nan ko na shigo cikin na ci miki mutumci”

Da sauri na tashi na dauki jakar tawa na nufi garden na dauko ragowar tufafin dana shanya tun rana na saka a ciki na dawo garejin na saka sauran da musasshiyar farfesun kazar dana shanya na saka cikin jakar da siyayar da Kamal yai min, sannan na saka Hijab dina na fito ina hawaye na tsaya jikin garejin ina kallon kudin da take ba wa direban.

“Ka tabbatar ta shiga mota sannan na mika mata sauran kudi, idan an isa kaduna ta hau motar sokoto ai tasan gidan ubanta idan aka sauke ta a can”

“To Hajiya”

Ya fada yana karbar kudin tare da zagaya wa wajen motar ya bude ya shiga.

“Zo ki wuce mun rabu da kaya”

“Kudin aikina fa?”

“Aikin da ko wata ba ki yi ba? Je ki turo ubanki ya zo ya dibar miki”

“Ubana baya duniya Hajiya, ya tafi idan zan ki je zan je kowa zai je, amman Allah zai dibar min hakkina”

Shine kawai abunda na iya fada cikin kuka na nufi motar na bude na shiga, ina jinta tana ta zagina. Hawaye ne suke ta min zuba har muka isa tashar, a lokacin da direban yai farkin na bude zan fita sai na ji ya ce.

“Ki yi hakuri da rayuwa, haka take zuwa juyi juyi Allah ya sauwake mana talauci ni da ke mu daina zama karkashin kowa”

Da na kalleshi sai na ga hawaye a idonsa.

“Amin”

Na amsa sannan na sauka daga motar shi ma ya fito, sai da yaje gurin yan Union ya hannata musu ni ya basu kudin motar zuwa kaduna da kuma kudin motar Kaduna to sokoto sannan ya ciro dubu biyu ya mika min.

“Gashi ki rike wannan Allah ya kai ki lafiya sai wata rana”

“Na gode”

Na karba da hannu biyu ina ta hawaye kamar wacce akai wa ido dan hawayen kawai.

“Lafiya Mutuwa akai miki?”

Daya daga cikin mutanen ya tambaya. Sai na girgiza masa kai ina jan magina.

“Aa ba mutuwa akai min ba”

“To Allah ya sauwake”

“Amin”

Shi ya nuna min motar da zan shiga sannan ya bawa direban kudina da kuma kudin motar da zai saka ni ta Kaduna sannan na shiga na zauna muna jiran karin wasu mutum biyu. Ban dade da zaman ba aka kira sallah la'asar sai da aka kira sallar na tuna da cewar ban yi sallah azahar ba, sauri na fita daga motar na nufi gefen masallacin nai alwala da butar su sannan na nufi wani dan daki dana hango mata na shiga na shiga ciki nai sallah, na fadawa Allah bukakata kuma na kai masa kukana na kuma roki mafita akan dukan lamura na. Ba bar tashar ba sai biyar da kwata sannan direbamu ya kama hanya.ALIYU POV.

Da mugun bachin rai ya fita daga asibitin yana cikin motarsa Momy ta kira shi ta fada masa cewar an sallami Rahma kuma ya zo ya tafi da ita, jin wannan labarin yasa ki sakewa daga bachin ran da yake ciki sai ya dauki hanyar asibitin. Ko da y shiga ciki ya samu Momy da Mommy Rahma suna fita Rahma na zauna tare da kanenta guri daya fuskarta babu walwala, ganin Aliyu ya saka kanen nata suka tashi daga saman gadon suka dauki wasu kayan da za a tafi da su suka fice. Da murmushi Aliyu yake kallonta amman ita ka kasa sakewa kamar ba ita aka sallama ba.

“Amman na ce idan mun wuta yau zuwa gobe za mu tafi da ita can sokoto ta samu kula kuma idan tana kusa da mu ita kanta zata fi walwala”

Mommy Rahma ta fada har Aliyu ya bude ba ki zai yi magana sai Momy ta shiga kuma ta shanye duk wani abu da yake da niyar fada.

“Eh nima na yi wannan tunanin hakan zai fi, shi kanshi Dan wajen Fulani ai ba zai ki ba, Allah dai ya bata lafiya muma ai goben za mu koma”

Shiru yai be ce komai ba, saboda Momy ta saye bakinsa. Mommyn Rahma da Momy tare suka jera a gaba suna tafiya shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login