Showing 42001 words to 45000 words out of 225640 words

Chapter 15 - Zaki Book 1 Hausa Novel Complete

na koma ya bude mana gate din. Da muka shiga gate din farko sai na hango wani gate din a tsakanin tafiyar wacan gate din da na farko yai taku sittin bayan shi kuma akwai wani dan karami da aka kawata da furanni, banbancin gate na biyu da na uku na ukun irin wannan ne da aka saka kawai dan kwalliya wanda zaka iya hango na ciki na ciki kuma ya hango mai shirin tahowa, na biyu kuma be kai na farkon girma ba, na farko shine kato gashi dogo kamar yadda ginar gidan take.
  A wani kato fili direban ya aje motarsa, yamma da filin an kafa wata katuwar rumfa mai kala wance ta lullube wasu manyan motoci da ban taba ganin irinsu a sokoto ba, da alama gidan kashi uku ne, bayan bangaren da ke fuskarta mai shigowa ga wani can yamma da motoci, kuma akwai wani arewa da motocin, gaba daya gidan da duk wani abu na kwalliyar gidan na glass ne, ya wasu furanni kananan da suka kara haska gidan, bayan wadancan na nesa da mu da na ke hangowa masu tsayi da hudu an musu yar karamar kofa, da alama Garden ne kamar yadda na ji ana fadar cewar gidajen masu kudi suna yin Garden, muna rufe motar sai ga barewa ta fito da gudu daga Garden din da kahoninta tana kallonmu kamin ta juya da gudu ta koma ciki.
Tsuntsun maka ne Peacock har guda hudu ke ta yawo a harabar gidan yana bude fukafukansa abun sha'awa, wani irin shauki ne ya kamani da kuma tsoro a lokaci daya, domin irin manyan masu kudin nan ba su cika ganin kimar talaka ba, balle kuma ace za ka yi aiki a karkashinsu ne.
  Daya daga cikin part uku da suke gidan muka nufa, Maman Salma na gaba muna biye har muka isa, gaban kofar ma duk furanni ne irin na kaskon nan an kawata katuwar kofar da su. Wani dan maballi ta danna taja baya ta tsaya jiran bude mata amman ba a bude ba, sai ta sake danna bayan wasu mintuna, nan ma sai da aka kara bata lokaci sannan aka bude kofar falon. Ba mu ga wanda ya bude mana kofar ba, da alama wanda ya bude komawa yai ya zauna a daya daga cikin manyan sofa din da suke katon falon mai kama da falo uku.
Wani kamshin masu arziki da turaren mai tsada ne ya fara yi mana marhabun kamin ac da ke falon ya karaso garemu. Wasu manyan yan matane su hudu hakince saman kujera suna kallon wani kato tv wanda ban taba ganin irinsa ba tun da Nana na haifo ni duniya. Babu wacce ta juyo ta kallemu daga cikin yan matan balle ta amsa mana sallamar da muke, duk kuwa da irin daga mana hannu da Maman Salma take na alamar mu sassauta muryarmu.
 
“Hajiya Rukaiya da Hajiya Maryam ina kwananku?”

Maman salma ta fada da dukan far'arta sai a lokacin ne yan mata suka dago suka kallemu, wacce na ke zaton ita ce Maryam din ta amsa a kaikaice tana mana kallo ba uku saura kwata, yayinda Rukaiya ta sakarwa Maman Salma Murmushi kadan, sannan wacce ta fi su kurciya ta dago ta kallemu sai ta maida kanta gurin zeeworld din da suke kallo.

“Na ce ko Hajiya tana nan?”

Maman Salma ta tambaya kamar da tsoro, sai wacce aka kira da Rukaiya dazu ta kalli karamar ta ce.

“Baby je ki kira mata Mama”

Da kamar ba zata je ba, sai kuma ta mike tsaye tana sanye da wasu guntayen kaya irin na turawa wato dogon wando da be kai kasa ba, da kuma t-shirt ta mata mai guntun hannu kanta ba dankwali an yi mata kitson attach tsorayen sun sauko har bayanta. Wata katuwar mattakala ta nufa irinta ta indiyawa mai fadin ta fara takawa a hankali har ta haye sama gaba daya, daya daga cikin dakunan da muke hange ta tura ta shiga. Shiru shiru bata fito ba har kusan awa daya sannan muka hango an bude kofar wata kasaitacciyar mace mai isa da ji da kai ta fito daga dakin tana sanye da wata dakankiyar shadda mai kamar kamfala sai shining take kamar an shafa mata mai. Da ďai-ďaya matar take takawa tana saukowa stairs din wani saurayi mai kama da ita na gafenta fuskarsa dauke da murmushi ya zuba duka hannayensa aljihu.

“Mama ba ki yarda da ni ba”

Saurayi ya fada bayan sun sauko tare yana kallonta. Uffan ba ta ce masa ba bayan hararar da ta watsa masa ta nufi wata one seater da ke fuskantar mu ta zauna, shi kuma saurayin ya zauna hannun sofar yana cigaba da gitse dariyarsa. Maman Salma ce ta fara mika mata gaisuwa ciki da girmamawa daga kasan tile din da muke zaune mu da ita. Sai Hajiyar ta amsa da far'arta kadan tana shigar da idonta can ciki a yayinda take kallonmu irin kallon nan na rashin ganin kimae talaka.

“Lafiya Kalau Ramatu an shigo”

“Eh Wallahi, dama na fada miki zan shigo ai”

“Haka ne, suna wadannan yaran?”

“Eh sune sai ki zabi wacce kike so, idan ma duka za ki dauka ga su nan dai”

Maman Salma ta fada tana dariya.

“Aa daya ta isashe mu,wanke wanke ne kawai sai shara da mopping da dan aikin da zai taso, kin san ni bana yarda yar aiki tai min girki, haka ma Ammy bata son girki”

Ta fada tana daga hannu kamar bata son motsa jikinta. Ina dauke idona daga gareta na kalli d'anta sai na ga ni yake kallo kamar mai mamaki, maida kaina nai kasa na sake dagowa muka hada still ni yake kallo.

“Mama kin ga kyau? Subhanallahi ahsanar halikin amman wannan yarinyar Allah ya miki kyau, you're so pretty”

Ya fada yana kallona daga can inda yake zaune.

“Mama wannan yar Fulanin za mu dauka tashin hankali”

Ya sake fada yana kara kallo da kyau, wanda hakan yasa sauran yan uwanshi mata suka dago suka kalleni, a cikinsu babu wance ta ce ina da kyau suka maida dubansu gurin tv da suke kallo.

“40k za mu biya idan ya miki”

“Eh yayi Hajiya Allah amfana mana su, ke kuma kina da 30k a wata ni ina da 10k ya miki?”

Maman Salma ta fada tana kallona da sauri na gyada mata kai da sauri zuciyarta cike da jindadi har dubu 30k. 

“Bude baki ki yi mana na ji muryarki mana kyakkyawa”

Saurayin ya fada yana kallona, sai Hajiya ta daka matsa tsawa tana kallonsa.

“Muhseen what this?”

Mikewa yai tsaye yana dariya ya nufi gurin da sisters dinsa suke zaune ya zauna. Sannan Hajiyar ta kalli Maman Salma ta ce

“Ki fada mata yadda komai ya ke, sannan ki kai ta bangaren Ammy ta ganta kuma ta nuna mata aikin da zatai”

Maman Salma ta juyo kaina ta nuna min Hajiya.

“Wannan sunanta Mama Fulani haka ake kiranta, wacan dan ta ne Muhseen amman Ya Muhseen ake kiransa, wacan ma Anty Maryam za ki kirata, wacan Anty Rukaiya, wacce ta shiga daki dazun kuma Anty Baby, akwai wani na nan shi ma zaki ganshi Shi ma Ya Ahmad za ki kirashi, aikinki idan kin tashi da safe kamin kowaya farka saki zo nan falon ki share ki yi mopping ki goge ko'ina ki shiga kitchen ki wanke kayan wanke wanke ki goge, sai ki jira idan sun farka sun fito daga dakinsu suna karyawa sai ki shiga dakunansu da na Hajiyar ki wanke bathrooms ki share dakin ki goge ki kunna turaren kamshi, a can ma idan zan kai ki haka za ki yi, kuma idan akwai wani dan aiki za a kira ki ki rika”

“Okay In-Sha-Allah zan yi duk yadda kika ce”

“To taso muje can bangaren Ammy”

Tashi nai kamar yadda ta bukata muka fita daga falon muka nufi dayan bangaren, komai irin na bangaren da muka baro ne ban ta kujera domin a can sofa ne a nan kuma cushion ne, banbancin wannan matar da wacan wannan tana da far'a da son mutane ita da yayanta sabanin wacan da ke da izza da nuna isa ita da yayanta.
A lokacin da muka shiga falon duka yayanta su suka gaishe da Maman Salma sannan Hajiyar ta hana Maman Salma zama kasa. Bayan mun gasa ta gabatar da da aikin da aikin da zan yi kamar dai yadda tai min a wacan bangaren, sannan ta gabatar min da matar.

“Wannan sunan ta Hajiya Husaina amman Ammy ake kiranta, wannan yarta ce za ki kirata Anty Zee, wannan kuma Anty Samira, wannan kuma Anty Batulu, wannan kuma Anty Inteesar”

Ammy ta yi dariya tana shafa kan karamar yarta.

“Ai ba sai ta cewa Inteesar Anty ba, Aai yarinyar ma ba zata wuce sa'ar Inteesar din ba, ya sunanki?”

“Aisha amman Ataa ake kirana”

Na bawa Ammy amsar da sauri, sai duk muka maida duban mu gurin kofar shigowa falon da muka ji an bude. Sauran nan ne na dazun da Maman Salma tace na kira da Ya Muhseen ya shigo fuskarsa da far'a kamar dazun, kusa da Ammy ya zauna yana nuna mata ni.

“Ammy ya kika ga yarinyar nan kalleta da kyau dan Allah”

Ta kallini kamar yadda ya bukata sai tai dariya.

“Tana da kyau gaskiya”

“Wallahi mugun kyau ma Ammy”

Sai duk suka saka dariya ni kuma nai kasa da kaina, Maman Salma ta ce.

“Iyeyenta jajayen buzayen nijar ne, bari ma ta cire Hijab gashi har gadon baya”

“Kai iyakar kyau kenan amman Ammy ki ce tai magana mu ji muryarta, na rantse da Allah yarinyar nan ta ruda ni, kin san ni da son mace mai kyau kuma fara”

Ya Muhseen din ya fada yana ta kallona, ni dai ban dago ba, har aka ci aka shude muka yi ma Ammy sallama muka baro shi can shi da ita muka dawo dayan part din na Mama Fulani kamar yadda Maman Salma ta fada min sunanta. A nan tai min jan kunne sannan ta yi mata sallama, sai Mama Fulanin ta dauko tufafi da turare ta mika mata da yan kudi da ba zasu kai 10k ba, Maman Salma na shirin fita Inteesar ta shigo dakin tana sanye da kananan kaya ta mikawa Maman Salma katuwar bakar leda wai in ji Ammy, Maman Salma ta karba tana godiya sannan ta fice, ni ko na bita da kallo ina ta jin kewar gida tare jin kamar na bita mu koma tare.


ALIYU POV.

Yadda yaga hankalin Rahma ya tashi ya sashi kai hannu ya rika fuskarta.

“Ba abunda kike tunani ba ne, Momy ta yi min wadansu maganganu da na ke ganin dacewar abunda ta fada, kuma har ga Allah Rahma kin sa idan har Daddynki Ko Doc Asim suka cutar da yarinyar nan mu ne sila”

“Taya za mu zama sila?”

Ta tambaya hawaye na sauko mata, wani irin mugu zafi take jin zuciyarta na mata saboda zafin kishi, ita kanta bata taba sanin cewar tana da kishi kamar haka a zuciyarta ba sai yau, jin Aliyu yana zancen wata yasa har kanta sarawa yake, nan da nan jikinta yai zafi zzazzabi ya rufe ta, ta soma jin sanyi na sauko mata.
Haka yasa hankalin Aliyu tashi sosai, da sauri ya daga ta zaune yana dubata.

“Maganar da na yi ce ta saka ki haka? Ko ciwon ne ya taso? Tashi muje asibiti”

Kai ta girgiza masa alamar ba zata je ba, mikewa yai tsaye ya ciro wayarsa kamar zai kira Doc Asim likitan daya saba dubata sai kuma ya fasa ya kira wani likitan dabam. Abun ka da kiran mai arziki nan da nan likitan ya iso, ya duba ya bata magani yai mata allura sannan ya tafi. A bayanta Aliyu ya kwanta ya rumgumeta ya Lumshe ido kamar mai bachi kuma ba bachi yake ji ba, har yanzu maganar Momy yake tunani, a idonsa kuma Ataa ke masa gizo lokacin da ta wanke fuskarta ta fito gashinta har a baya tana nunawa Doc Asim fuskarta dan ya gane ta. Sai a yanzu ya fahimce dalilin daya saka take shafa bakin abu a fuskarta da kuma nikab din data taba sakawa lokacin da ta so gidan, yana tuna duk wata haduwa ta su, tge first fasa mishi mota da tai wanda har yanzu be san dalilinta na yin hakan ba, ko dai ita ma ta tsani masu kudi ne kamar yadda shi ma ya tsani talaka? Ya tuna lokacin da take masa bara a jikin mota har rigarsa ta taba ta, ya cire rigar ya saka boot, irin kallon tsoron da ta rika masa ne ya dawo masa sabo, wanda har ta kasa janyewa daga jikin motar shi kuma ya kasa cewa ta kauce ya shiga motarsa sai da Nana ta janyeta, da tears din da suka cika idonta har suka zubo a wacan lokacin, yasan ta ji tsoronsa ne kamar yadda kowa yake jin tsoronsa amman duk da haka tana da karfin zuciyar tsaya ta fada masa magana mai zafi ba tare da tsoro abunda zai biyo baya ba, kamar yadda ta fasa masa mota ma, da kuma fadan da tai masa jiya, yace ba a nuna shi da yatsa har ta saka yatsa biyu ta nuna shi da su wai ita ga masifaffiya marar tsoro.
Dan murmushi ne kadan ya bayyan a gefen fuskarsa, shi kansa bw ankaro da murmushin yake ba har sai da ya ji yana kokarin fadada, da sauri gusar da murmushin ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya kai dubansa ga Rahma wacce ke ta bachi ya sumbanci saman kanta ya sauka daga kan gadon ya nufi downstairs, wayarsa ya ciro haka nan kawai yake son labartawa abokinsa Nasir abunda ya faru, he don't know why maganar take son damunsa.

Misalin biyu da rabi Rahma ta farka, ta tunanin maganar dazun ta shiga bathroom tai wanka, har ga Allah ta ga mijinta a cikin yanayin da bata saba ganinsa ba, yai mata wasu kalamai da bata san shi da kula da su ba, idan ta tuna irin kyau Ataa kuma sai tsoro ya kamata, gaban madubi ta zauna tana kallon kanta, iya aunawa ta auna tabbas ita ma din mai kyau amman ko kadan bata kamo Ataa ba, wata kila Kyau Ataa ne ya rude shi har ya soma tausayinta yana ganin abunda akai mata ba a kyauta ba, ita a duk zaman shekara shekara shida da tai da shi bata taba jin yayi maganar wata mace ba, sai wannan yarinyar.

“Ba rin garin nan za mu yi, kara mu koma Abuja inda ba ta ma can balle hankalina ya tashi, idan muka koma can ni kadai zai kula da ni sai aikinsa, amman nan wannan bakar Momy zata iya damunsa da maganar yarinyar nan, kuma zai iya son ta tunda tana da kyau, amman a can ai be ganta ba, kuma mun yi nisa da Momy ba wannan zancen, daman can na san ba so na take ba”

Ta fada tana murzawa jikin expensive cream, sannan ta shafa turare da powder ta mike tsaye ta nufi wardrobe. Tana cikin daukar kayan ta juyowa ta kalli Aliyu da ya shigo dakin cikin kananan kaya.

“Aliyu Abuja na ke son mu koma cikin satin nan, na gaji da garin nan”

Magana take masa amman kwatakwata ba ita yake kallo ba kirjinta yake kallo yana hade yawu, kamin ya kai hannu ya shafata zuwa bayanta yana kokarin kwance tawul din.

“Magana na ke maka fa”

Be kula ta har ya kwance tawul din ya soma shafa jikinta.

“Alwala nai sallah zan yi”

Sai da ta fadi hakan sannan ya saketa ya matsa baya yana tsosar lips dinsa kamar mai shan sweet, har cat eyes dinsa sun soma canja kala kamar ba shi ba.

“Ka ji ni Abuja na ke son mu koma, na gaji da garin nan”

“Ki yi sallah sai mu yi maganar”

Ya fada yana fadawa saman gadon kwance ya runtse idonsa yana shafa kyakkyawar fuskarka da dayan hannunsa, dayan kuma ya saka shi cikin kafafuwansa ya matse sosai, yana jin lokacin da Rahma ta kabbatar ta sallah ya bude idonsa ya tashi zaune, sai wayarsa tai ringing alamar kira, ganin Nasir yasa shi tashi ya fita daga dakin dan baya son yin maganar a gaban Rahma tun da ya kula da bata son hakan. Saman cushion ya zauna yana picking call din,

“Ya?”

“Daidai, amman Aliyu ya kamata ka dawo Abuja akwai aiki da yawa a nan, kuma kasan akwai abunda be yiyu sai an saka a kamfanin nan”

“zan zo amman ba yanzu ba, akwai abunda na ke son yin?”

“Akan yarinyar nan ne?”

Aliyu yai shiru be ce komai ba, wanda hakan ya Bawa Nasir damar cigaba.

“Yana da kyau ka tabbatar yarinyar nan ba ta cutu dalilinka ba, saboda kar abun ya zo yai ta damunka ko ya shafe ka”

“Kawai dai bana son kallon da take min na azzalumi”

“Ka bata hakuri to kuma ka fada mata gaskiya cewar ba da saninka akai komai ba, ko da nasan ba zaka iya ba”

“Hakuri....”

Ya maimaita, bayanin ma yana jin ba zai iya mata ba, sai dai ya saka wani yai nata ko ya rubuta mata a rubuce, balle kuma har kalmar bada Hakuri ta shigo tsakaninsu, abunda yake jin ya zama wajibi akansa kawa ya wanke kansa daga kallon azzalumin da take masa ne.

“Amman kasan inda take?”

“No”

Ya bawa Nasir amsar a takaice sannan ya kashe wayar ya mike tsaye ya nufi upstairs...





*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Ko da ya shigo dakin ya samu Rahma ta gama sallah tana kokarin tashi tsaye, haka ta dauki carpet din ta jefar gurin akwatinta dan bata iya ninkewa sannan ta aje.

“Dear ina da ina Daddy ya ke gina gidajen da be karasa ba?”

“Gurare da yawa wani abun ne?”

Ta tambaya tana kallonsa sai ya zaunar da ita ya zauna a kusa da ita yana sakar mata murmushinsa kadan.

“Da ina da ina?”

“Akwai wani Clapperto road, akwai a ali akilu akwai a guiwa da sauran gurare, mi za kai?”

“Ina son na duba mai girma ne sai na yi ma Daddy magana mu bude karamin kamfani da shi”

“No Aliyu ni fa bana son zamanmu a garin nan, gaskiya ni Abuja na ke son mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login