Showing 15001 words to 18000 words out of 225640 words
fada wani gurin tabbas da masu kudi fa yanzu an canja nata asibiti amman kuma mu ba kamar su ba ne, kuma idan muka ce za mu canja asibiti kudin magani dawainiya wa zai yi da mu? Na san dai ba za mu hadu da dan albarka likita kamar wannan ba. In ta wannan sake saken na nufi cikin ward din tare da tunanin wata kila likitan be kware sosai ba shiyasa ka Nana ta gagara warkewa garau.
#Team Ataa
#Team Rahma
#Team Aliyu
Masu yi ma Rahama addu'ar mutuwa ita ma lafiyarta kawai take nema ita da mijinta 😀 amman kun fara dora mata tsana tun ba a je ko'ina ba 😑
https://my.w.tt/PWohUhlPv9.
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
7️⃣
Tunanin inda zan kai Nana idan na dauketa daga asibitin ya hana ni runtsawa a daren, ba ni da halin da zan iya nema mata magani a wata asibitin domin na lura maganin nata mai tsada ne kamar yadda Doc Asim yake yawan fada min cewar ya siyo maganin, a yadda yake hidima da mu idan na ce zan canja asibitin zai iya zargin wani abu ko ya ji babu dadi taya ma zan iya fada masa cewar asibiti za mu canja ai sai ya zargi ko mun raina Hidimar da yake damu ne? Da wannan tunanin na kwana na tashi na sake kwana na sake tashi a haka har akai kwana uku ban fadawa kowa ba, sai dai ta wani 6angaren Anty Shukura tana da gaskiya ya kamata na gwada aikin wani likitan ko Allah zai sa a dace ta koma kamar da, maganarta ta cewa indai ba son nake Nana ta mutu ba na canja mata asibiti na daga min hankali sosai har na saka samun sukuni, idan na shiga bandakin da zimmar alwala ko fitsari sai na zauna a ciki nai ta kuka, ban san abunda Allah ya tsara ba, ban san abunda zai faru gaba ba, Nana zata tashi ko ciwon zai yi ajalinta duka ban sani ba, zan rayu da ita na wani lokaci ko a'a duka ban sani ba. Iyakar abunda na sani kuma na ke da tabbaci akansa shine mutuwa kuma Allah baya barin wani dan wani, sai dai na san ina son rayuwar Nana fiye da ta kowa duniya, na rasa mahaifiya yan shekaru kadan a baya, sai na ji kamar ba zan iya hakurin na rasa Nana a yanzu ba.
Bayan na yi kukan na wanke fuskata na fito na zauna a kujerar da ke fuskarta Nana, ita kuma tana daga zaune ta rame sosai sai sauke ajiyar zuciya take tana kallon mutane da ke kai kawo a waje ta window dakin, wani irin tausayinta ne ya kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya mace mai kuzari kamar Nana wacce zata fita bara tun safe ba zata dawo ba sai yamma ta koma a zaune tsayin ma wahala yake mata, lallai Allah kadai ya iya haka.
“Nana”
Na kira sunanta a hankali, a lokacin da ta juyo ta kalleni sai na ga hawaye a idonta, ba ta damu da sharewa ba saboda tasan na ga hawayen babu abunda zata boye min.
“Wani gurin ne yake miki ciwo?”
Na tambaya hankalina a tashe ina komawa saman gadon asibitin inda take zaune na zauna kusa da ita.
“Tunani na ke yi, yanzu idan na mutu ke da Lukman ku za ku shiga wani hali, ba ku da gurin kwana ba ku da komai ban bar muku gadon komai ba sai na bara, ba ku da kowa a garin nan, a can nijar kuma babu wanda ya san inda kuke a nan balle su nemi ku, ba ku da gata yanzu sai na Allah Ataa, jo yanzu da wannan bawan Allah be taimaka mana ba da yanzu kila ka mutu”
Iyakar kokarin da nai shine na rike kuka da hana hawaye taruwa a idona saboda ta karta gani jikinta ya kara yin sanyi.
“Za ki ji sauki Nana In-Sha-Allah za mu koma can gida nijar tare da ke da Lukman mu yi komai tare”
Na fada ina nuna mata kamar ban damu da hawayenta ba.
“Wannan Nurse din Shukura ta bani shawarar wai na dauke ni daga wannan asibitin na kai ni wata”
“A nan ma ai ana kula da kai, kuma kana samum kulawa da abincin duk ana baka da yaranka amman can idan ka je wa se baka?”
“Ni ma na yi tunanin haka Kuma ina jim kunyar likitan ma, kar ya ce ba mu gode ba, amman ta bani shawarar na ce masa gida za mu koma”
“Ataa kana karami kana ta wahala haka nan kullum, idan ka kai ka wani asibitin ina kudi?”
“Akwai kudin da ya ba ni ya ce na siya abincin ranar ba na fada miki ba? Kuma akwai wada muka dan samu da aka zo ganin ki zai kai dari takwas idan mum hada dubu goma kenan har da yan canji ma, sai mu je wani asibitin mu gani ko za mu dace”
“To ai sai ka fada mata ko?”
Ta fada a nufinta na fadawa likitan.
“Eh zan fada mishi amman ba za mu ce masa wata asibitin za mu ce masa gida za mu koma kin ji?”
Ta gyada kai, kamar likitan ya san abunda muke tsarawa sai ga shi ya shigo dakin rike da wasu takardun fuskarsa a sake kamar kullum.
“Ya jikin?”
“Ka ji sauki”
Nana ta amsa masa, sai ya ciro daya daga cikin takardun ya miko min.
“An sallame ku, ya kamata ku koma gida hakan nan, ki cigaba da bata magani da zan ba ki kinji?”
Na saka hannu biyu na kar6a cike ladabi da kuma murna.
“Ai za ki iya ganewa idan an rubuta mikia jikin maganin ko? Kin yi boko?”
“Eh amman bakin primary kawai ina karanta abu idan ba mai wahala ba ne, ko kuma idan hausa ce”
Sai yai murmushi.
“Ai na san ba kya ganewa kan”
Yana rufe bakinsa wasu nurses biyu suka shigo dakin dayar tana rike da ledar magani dayar kuma tana turo wheelchair. A nan ya karbi maganin ya rika nuna min yadda za rika bata su kuma Nurses din suka dauki Nana suka saka ta a wheelchair din, sannan ya saka suka kwashe mana duka kayanmu suka fitar waje, ban ma san an samu napep ba sai da na nade tabarmu da ke waje na yi ma mutanen sallama na janyo hannun Lukman muka biyo bayan nurses din.
“Allah ya saka da alheri ya biyaka”
Ita ce addu'ar da muke ta masa ni da Nana, har aka saka ta Napep din ni ma na shiga Lukman na shiga gaba tare da mai Napep din. Sosai na so muje wata asibitin amman Nana ta ki ganin kamar za mu kashe kudi ne kawai, wai a ga magani nan ya ba mu kudin sai mu siya abinci da su a cewar ta, daman can Nana ba son kashe kudi take ba sai dole, balle wannan da take ganinsa da yawa har dubu goma.
Har kofar kangon gidan mai Napep din ya kawo mu, sai na umarce shi daya shiga ciki ba musu ya shiga ciki, ni na fara fitowa na rika Nana ta fito tana tafiya ďuke dan bata iya mikewa tsaye dai-dai, Mai Napep din ya cire mana duka kayanmu da suke bayan Napep din ya aje mana zan ba shi kudi ya ce Doc Asim ya bashi sai kawai nai masa godiya na shiga da Nana cikin kangon gidan na samu wani guri da anke zaton sitting room za ayi da shi na shimfida mata bargon na kwantar da ita. Lukman ya shigo da sauran kayan, ni kuma na dauki tsitsiya na hau sharar gurin dan yai datti sosai, sai da gama share duk fadin gurin sannan na dawo kusa da ita na zauna.
Wani dadi na ji a lokacin da na kalleta lallai uwa mai dadi idan bata a cikin gidan sai yai babu dadi, idan kuma tana nan sai naji dadi duk kuwa da kasancewar ba a lafiye take ba amman ina son ganin abata.
Ba mu dade da zaman ba akai kiran sallah la'asar sai na tashi nai alwala nai sallah sannan ita kuma na debo mata kasa tai taimama tai sallah, ba a maganar Lukman daman shi tun da ya gama saka mana kayan ciki ya fita yawonsa.
Sama sama muke ta firar mu da ita, yawancin firar da muke ta kwantar da tai asibiti ne mutanen da suka zo ganinta da kuma alherin da likitan yai mana, bayan sallah magariba na dauko maganin na sake bata kamar yadda ya fada min, da isha'i muka kwanta a gurin zuciyata cike da tsoro ina ta ganin kamar macijin nan zuwa zai yi ya sake tsaran Nana ko ni ko Lukman, amman Allah ya tsare mu har gari ya waye babu abunda ya same mu, yau ma ban yi sallah da wuri ba sai da rana ta fito, bayan na gama sallah na je na samu gawayi na wanke bakina sannan na ba Lukman kudi na ce ya siyo mana koko a inda ake saidawa da kosai da suga, ba laifi ta ci sosai ni ma na ci duk da kasancewar ina sha'awar waina amman bana son na siya bayan shan kokon gudun kar kudin mu su yi saurin karewa, kara kawai na hakura har zuwa gobe sai na siya da safe mu karya da ita gaba daya.
Muna ciki zaune sai ga Farida ta zo, ashe jiya bayan dawowarmu daga asibitin ta je aka ce mata an sallame mu. Mun sha fira sosai ba tabar gidan ba sai da ta soma jin iskan hadari na tasowa alamar hadarin daya hade sama yana daf da tasowa. Sannan tai mana sallama ta tafi, tafiyarta da mintuna kamar hudu zuwa biyar na hango wasu mutane sun doso inda muke dukansu maza. Gabana ya dan fadi kamar yadda na Nana ma nasan sai ya fadi, suna isowa suka fara fisge dan zanen a muka saka muka tare kofar da shi saboda sanyi suka jefar.
“Wai ku wasu irin mutanen? Ko wacan lokacin ba an muku magana ba, wato shine kuka dawo ko? Mai gidan yace mu koreku dan an fada masa kun dawo ashe ma cikin gidan kuka shige kuka zauna dan rainin hankali”
“Dan Allah ku yi hakuri Wallahi mamana bata da lafiya kuma babu inda zata laba sai nan”
Na fada ina kallon fuskokinsu na marasa imani da ganinsu irin yan sara sukan nan ne ya turo mana marasa tarbiya. (Area boys)
Aiko kamar jiran suke nai magana sai biyu daga cikinsu suka dauki Nana suka kai ta can kusa da gate suka aje dayan kuma ya turani waje da karfi, Lukman da tsoro tuni na nufi inda Nana take da sauri idonta cike da tsoro, sai kuma suka shiga ciki suka fara shuri da kayan mu da ke ciki sai da suka fitar da komai da kafa sannan suka fito suka nufo inda na ke tsaye ni da Nana muna muka suka ce mana idan muka sake shiga ciki duk suka dawo sai sun sassara mu, kuma mu nemi wani wajen tun kan dare yai mana mu bar gurin kwanon da aka saka dan fara zagayewa kamar za ayi gate.
A gurin muka tsaya ni da Nana da Lukman har aka fara ruwa, daga ni har Nana babu abunda muke sai hawaye Lukman na tsaye yana ta kallon ta bata fuska sosai kamar ya fasa kuka. Sai da naji an fara yayyafi sannan na rika Nana da zimmar mu koma ciki sai ta rike hannuna ta girgiza min ka alamar ba zata koma ba.
“Idan an gama ruwa sai mu fito”
Na fada da muryata ta kuka, sai ta girgiza min kai alamar ba zata ba, hakan yasa na nufi kayanmu na dauko bargon da likitan ya siya dan mu rika kwantawa ni da Lukman akai na lulluba mata na shiga ciki Lukman ma shigo muka fake a ciki ruwa na dukan kanmu. Wani abun Allah kuma sai akai ruwan da kama da bakin kwaya ga sanyi sosai domin har da kankanra suke. A take Nana ta fara tari jikinta na ta karkarwa jin hakan yasa nai saurin bude bargon sai na ga jini duk ya bata mata baki har ya sauko saman rigarta ashe tarin da take jini take fitarwa, rumgume ta nai na fashe da kuka ina daga kaina ina kallon ruwan saman da ke saukowa kamar a cikinsu wani zai kawo mana dauki....
Wayyo Nana 😪
https://my.w.tt/PWohUhlPv9.
*Z A K I*
By Khadeeja Candy
8️⃣
Sai da ruwan suka dan tsagaita sannan na samu damar mikewa tsaye ina daga Nana daga jikina. Ta galabaita sosai har wani lumshe ido take tana budewa amman wani abun mamaki idan ta kalleni sai tai min murmushi, wata kila so take ta kwantar min da hankali ganin irin yadda na ke ta kuka kamar ba gobe, a saman bargon na kwantar da ita duk kuwa da irin sanyin ruwa sama da ke jikinshi na nufi inda kayanmu suke na dauki Hijab dina da shima ya gama jikewa na saka a haka na fita daga kangon gidan da gudu zuwa nemam nepep, bakin titin gawon nama na fito duk wacce na tara bata tsayawa wata kila saboda ruwan be gama daukewa ba gashi dare ne, daker na samu wata wacce babu kowa a ciki ta tsaya da sauri na shiga ciki ina fadin.
“Mu bi ta nan marar lafiya za mu dauko”
Kamar yasan halin da nake ciki sai ya shiga kwanar Clapperto road da gudu muna kawowa kangon gidan na ce ya shigo ciki, da taimakon mai napep din muka saka ta ciki sannan na nufi jakar da kudin suke ciki na bude na daukosu gaba daya sun jike har sun hade guri daya, ni da Lukman muka shiga da sauri mai Napep din ya ja zuwa Uduth wato Usmanu dan fodio teaching Hospital, kamar yasan daman can nake son kaita. Ta sabon gate din emergency ya shiga da mu, ba laifi nurse din sun karbo mu hannu biyu sannan suka ce na je na karbo kati, da gudu na bazama cikin asibitin neman inda ake siyar da katin domin ban sani ba, hasali ma ban taba zuwa asibitin sai dai na bi na wuce, wata mace ce ta nuna min gurin da na isa ban samu layi sosai sai yan kwarorin mutane wata kila saboda yana dare ne. Amman a haka sai na kasa bin dan karamin layin na shiga rokonsu ina ta kuka.
“Dan Allah ku taimaka min na karbi kati mamana zata mutu dan Allah”
“Zo nan a baki”
Wanda ke layin gaba ya fada sauran kuwa kallona kawai suke jikina shakaf da ruwa har diga suke a kasa. Gabansa na shiga na mika dari biyar a bani katin sai ya ce min basa son kudinbda suke jike, mutumen nan ya ciro dubu daya sabuwa hul ya miki na karba hannu biyu na ba mai bayar da katin sannan na rubuta sunanta ya miko min katin da chanjina kusan dari hudu ya cire har da yan kai, a wautata sai na mikawa mutumen canjin.
“No rike, Allah bata lafiya”
“Amin na gode”
Na juyo da sauri zuwa inda mahaifiyata take, ina isowa likitan ya hau min tambayar ciwonta nai mishi bayani.
“Maciji ne ya tsare ta wata biyu da yan kwanuka da suka wuce, shi ne na kaita asibiti likitan yai mata tiyata ya cire dafin macijin, amman yace ta daina taba ruwa bata son sanyi shine yau ruwan sama ya doketa ta fara tarin jini”
“Dafin maciji ake yiwa tiyata? Allura dai ko?”
“Aa tiyata yana nan a cikinta ma”
Na fada ina girgiza masa kai. A take ya rubuta mana wasu abubuwan ya dauko wata takarda ya miko min.
“Ku dauke ta yanzu kuje a mata hoto”
Sai nurses din suka dora min ita akan wheelchair na soma turara muka fito daga dakin ina rike da takardar, daman Lukman na tsaye bakin kofar be shiga ciki ba. Da tambaya na isa gurin da aks hoto sai suka ce sai naje can wani guri na biya kudin sannan na kawo musu shaidar biyan, haka na barta a gurin na isa inda suka kwantanta min na bashi takardar da wacan mai hoton ya bani sai ya fada min kudin da zan biya.
“Dubu biyu da dari bakwai”
Na ciro kudin na bashi shi ma sai ya ki karba wadanda suka jiken wai basa son irinsu.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”
Shine abunda na fada na ji kamar na dora hannuna a kai na kurma ihu iya karfina.
“Kawo kudin haka”
Ya fada yana mikon min hannunsa wata kila yaji tausayi na ne, a haka na mika masa dubu uku ya bani canji tare da shaidar biyan kudin sannan na juyo da guduna na dawo na kawo ma mai dauka hoton, sai da akai ma mutun hudu sannan aka shiga da ita aka dorata akan wani gado suka shafa mata wani mai a jiki suka dora mata wani abu mai kamar dutsin guga suna ta yawo da shi a cikinta. Bayan sun gama suka dora a kan kujerar wheelchair suka ce na fara zuwa na kaita can gurin likitan sai na dawo na karbi hoton.
Haka na turata na koma da ita a dakin da ke cike da majiyanta na tsaya a inda likitan ya saka aka sauketa dazun na kira wasu nurses suka zo suka taimaka na dorata saman gadon, sannan na kama hanyar komawa, abun ka da mai hankali tashe sai hanyar ta bace min ita kaure mutane ba tare da na kula ba. Har na kai ga yin kaura da wani likita zan wuce na ji an fisgoni an dawo da ni.
“Ke ba ki ga ni ne hala?”
Sai na kalleshi amman bana iya ganin fuskarsa saboda hawaye na cika min ido.
“Hoto zan karbo kuma gurin ya bace min”
Na fada cikin kuka mai karfi.
“Wow cute girl”
Ya fada kadan-kadan sannan ya nuna min gurin.
“Doc Muhseen yi sauri pls”
Wani mutumen mai sanye da uniform din nurse ya fada sai mutumen ya sake ni da sauri yai gaba ni kuma na nufi inda ya nuna min. Ko da na koma har an fitar da hoton sai