Showing 120001 words to 123000 words out of 225640 words
ku maza yake”
Ya nufi hanyar dakinta a fusace tana wugar da zoben.Aliyu ya juyo gurin Muneera ya kwada mata mari mai kyau sai da ta jishi har cikin kanta.
“Karki sake zuwa ki ce za ki taba yarinyar mutane, duk wani abu a tsakanina da Rahma ne babu ruwanku a ciki”
Ta dafe kuncin hawaye na sauko mata tace.
“Saboda wata banza yar talakawa za ka mare ni Aliyu?”
Kara mata marin yai a dayar fuskarta sai ta hada hannu biyu da dafe fuskarta tana fashewa da kuka.
“Talaka ai ta muku rana, ko ba kodar talaka ce a jikin yayarki ba? Ku ba ku san darajar talaka ba amman kun iya wulakanta shi? Bana son wuce gona da iri, ki tsaya a matsayinki na kanwar matata babu ruwanki da rayuwarmu, kuma ki fice min daga gida yanzu nan”
Kamar kyaftawar ido haka ta fice daga falon har lokacin da ta kai gurin motarta bata dauke hannunta daga kan fuskarta ba dan har lokacin bata daina jin zafin marin da yai mata ba.
Rahma na shiga dakinta ta dauko makullin motarta da mayafinta ta fito cikin fushi ta fice daga gidan.
A gidan Aliyu ya kwana cikin bacin rai, be taba jin zamansa da Rahma ya zame masa matsala ba irin yau, iyakar hakuri zama da ita yana yi iyakar kauna da kulawa yana nuna mata amman bata gani, abu kadan ta shafa mayafi zuwa gidansu bayan ta sani kuma ya sha fada mata ba komai ake fadawa iyaye ba, ba kuma komai ne zaka dauka kace ka tafi gida kai ka yi fushi ba, yawan fushi da kai karar miji yana raba kan in-laws da rashin ganin kimar juna da ganin kamar wani na dannen hakkin wani.
Tashi yai zaune yana murmushi ya shafa kansa.Gorin haihuwar da tai masa ne ke bashi dariya daman mace haka take idan ma ita ke daukar dawainiyarka wata rana sai ta goranta maka balle kuma ace lamari ne irin wannan babba. All these years da Aliyu ya dauka na zama tare da Rahma bayan san matsalar daga ita ne ya juyar izuwa ga kansa dan ta samu salama yau shi take gorantawa, sai dai yasan saboda kishi ne komai tai saboda shi ne that's why yake daga mata kafa. Tunawa da zancen roben dazun yasa ya tashi ya sauka kasa ya je gurin data jefarta zoben yana duba har ya hango shi yaje ya dauka yana kallonsa.
“Waya bata zobe?”
Shine abunda ya fara zuwa masa a rai, Doc Bukar ya fara tunanin sai kuma yake ganin kamar Doc Bukar ba zai yi wannan shirmen ba, ba kawo Muhseen a ransa domin ya san Muhseen ya bar garin nan, bayan su baya tunanin wani kuma sai dai idan a boye yake shi be san da shi ba.
Da tunanin wanda ya bata zoben ya kwana a ransa, da kuma tunanin zuwan Rahma gida, shi dai ya daukarwa kansa alkawarin ba zai je bikonta ba domin ba wani abun ya aikata mata da zai sa ta dauki kafa ta tafi gida ba, duk abunda ya fada ya fada nata ne dan ta gyara, beside shi ba son Ataa yake ba to miye abun kishi a ciki after ta san halinsa ba kula mata yake ba ita ma wannan saboda daliline dalilin ma nata.
Misalin takwas da rabi na safe ya shirya cikin kananna kaya ya sauko downstairs ya nufo dinning area, rasa yai mi zai a gurin sai kawai ya koma sama ya dauko keys din motarsa ya shiga ya dauki hanyar arkilla. Ataa ce kawai a falon tana gyara Momy kuma tana kitchen, ba karamin dadi ya ji na samun Ataa ita kadai a falon ba, daman yana son ya tambaye wanda ya bata zoben.
“Ina kwana”
Ta dan risina tana gaishenshi be amsa ba har ya karaso kusa da ita.
“Ataa akwai wanda kike so a ranki?”
Wani kallo tai masa kamar bata fahimci abunda yake tambayarta ba.
“Kina da wani a ranki wanda kike so? Fada min karki baye komai”
Kasa tai da kanta tana watsa da kyallen hannunta kamar mai tunani.
“Kamal....”
Aliyu ya dade yana kallonta kamin ya bude bakinsa ya ce.
“Kamal kike so?”
Ta yi shiru bata sake cewa komai ba. Sai ya saka hannunsa aljihu ya ciro zoben ya nuna mata.
“Shi ya baki wannan zoben?”
Sai tai shuru bata ce komai ba.
“Ataa ke nan har kin san soyayya?”
“Ba son sa na ke soyayya ba, kawai dai ina jindadi idan na tuna dan zaman da muka yi lokacin da muke abuja, ba ya kyamata kuma yana kokarin sakani nishadi”
“Lokacin da yai miki wacan siyayyar ne ya siyo miki wannan zoben?”
“Ba shi ya ba ni ba”
“To waya baki Doc Bukar Ko Muhseen ko wani dabam?”
Shiru Ataa tai tana kallonsa kamar wata kurma.“Minene?”
Momy ta tambaya tana fitowa daga kitchen ta nufo inda suke.
“Je ki kawo min ruwa na sha”
Ataa ta nufi kitchen din shi kuma ya matso baya ya zauna saman kujera yana gaishe da Momy.
“Lafiya kalau, mi kake tambayarta?”
“Jikina na ga tana aiki da safen nan”
“Eh nayi na yi ta aje tace tana son ta yu shiyasa na kyaleta”
“Okay”
Ya fada numfashi na tsinkewa shi dai be jidadin jin wani Kamal a baki Ataa ba domin yana ganin kamar ba soyayya ce abunda ya dace da ita a wannan lokacin ba, bata san ma miye duniya ba amman suna kokarin chusa mata wani abun da be dace da ita ba. Kallonta yake har ta kawo masa ruwan a kofi ta mika masa.
“Shaye su ni ba a zuba min ruwa a kofi, je ki dauko min na gora”
Momy tace
“A a bari ni na dauko maka, ai bata san kan gidan ba”
“No Momy ba ri na dauko”
Ya tashi ya nufi kitchen din yana jin wani sabon haushin Ataa na lullube shi domin ya fahimci sam bata san kanta ba.
ATAA POV.
A haka muka tafi be sake tambayata cewar waya ba ni zoben ba, ni kuma ban damu sai na sanar da shi ba, wata kila ma idan ya san gaskiyar Muhseen me ya bani zai rika ganin laifina ne ko kuma wani fadan ya shiga tsakaninsu, domin na lura ko kadan Aliyu baya son ina kula kowa ciki kuwa har da Doc Bukar da nake ganinsa da kima da mutunci, idan ya tarar ina fira da shi ko wata gaisuwar ta hada mu sai ya hade rai ya bata fuska, ko kuma yai ta fushi da ni, ko da yake yanzu fushin nasa ya zame min jiki, ban zan iya fadar laifin da nai masa ba, amman tun daga lokacin da Momy tai masa fadan nan akan matarsa washen garin daya dawo ya tambaye waye ya bani zobe sai na lura da daina sake min kamar da, ni kuma ban damu ba daman ai matar da ta zo min fada ta fada min cewar na shiga hankalina domin be son talaka, daman kuma ni mi zai kai ni sakewa da mutum kamar Aliyu mai ji da kai da ganin kowa na kasa da shi.Satin Nana biyu a asibitim suka sallame ta a tsawon satin biyu da muka yi a asibiti babu ranar da ba ma gaisawa da Muhseen a laptop tun ina tsarguwa har na soma sabawa, a kullum kuma matar sai ta ba ni cake tace daga shi ne. Sau daya ya kawo mana ziyara a asibiti ba tare da sanin kowa ba, domin sai da ya gargade ni akan kar an fadawa Momy cewar ya zo garin nan wai aiki ya zo yi ba zai samu bi ta gidanta ba, ni kuwa a nawa tunanin ya ki sauka a gidanta ne ko yaje saboda Aliyu. Idan na kebe ni kadai bana tunanin komai sai Kamal dan nishadin da muka yi tare da labarin rayuwarsa da ya soma ba ni, tun bayan dana baro gidansu ban sake saka shi a idona ba, hakan kuma ba karamin haddasa min damuwa yai ba, ko yana ina yanzu? A wane hali yake oho? Wata kila ma ya manta da wata yarinya mai irin sunana. Daddy Siyama sau uku ya zo ganin Nana yana da son mutane sosai ya nuna mana kulawa har ya dauki kudi ya bawa Nana bayan irin dimar da Momy take da mu.
Ranar da aka sallamo Nana asibiti da kafafunwanta take tafiya, Momy na tare da ita yayinda ni da Siyama muka yi gaba muna tafiya, motar Amina muka shiga ni da yan uwanta Momy da Nana kuma suka shiga motar Aliyu. Na yi zaton Clapperto road zasu nufa da mu domin sauke mu acan sai na ga an nufo gidan Momy da mu. Aliyu ne ya budewa Nana mota da kansa ta fito tana takawa a hankali tana bin bayan Momy wacce ta wuce gaba zuwa cikin falon. Ina lura da yadda Nana take karewa ko'ina gidan kallon, wata kila ita ma ya burge ta kamar yadda ni ma burge ni a farkon zuwana.
A falon muka zauna Momy na ta murmushi ta ce
“To Nana kin ga gidanmu idan kin dan huta za ku koma bq na saka an gyara muku can za ku zauna ke da Ataa, kuma dan wajen Fulani yace zai nema mata makaranta nan kusa sai ta fara zuwa islamiya, ta bokon ma za a samu wanda zai fara koya mata a gida kamin a saka ta makaranta”
Ban san lokacin da idona ya cika da kwalla ba, na dade ina jiran zuwan wannan ranar da zan koma makaranta na samu ilimi, amman ban samu ba. Kallon Aliyu nai sai naga yanayi ma Nana murmushinsa kadan muna hada ido ya murtuke fuska kamar be taba dariya ba wai kar na ga damarsa.“Na gode”
Na fada murya kasa kasa. Be amsa ni ba sai ma dauke kansa da yai daga barin kallona ya kalli wani gurin dabam.
“Kana ta hidima da mu, bayan nema mana magani yanzu kuma kun kawo mu a muhallinku, kuma za ku nema wa Ataa karatu? Abunda na dade ina mata burin samu amman na kasa bata, ban tana haduwa da mutane masu karamanci da sanin darajar dan 'adam ba irinku, taimakon da kuke mana ya yi yawa da me za mu saka muku?”
Cewar Nana tana hawaye kamar yadda nima na ke yi. Momy ta yi murmushi
“Ba komai ai yi ma kaine, lokacin sakarwa zai zo lokacin da zan nemi wani abun daga gareki ina fatar ki amsa min da hannu biyu”
“Zan karba miki ko mienene a duniyar nan, matukar ina da iko da karfi akansa, ku ne mutanen da kuka mai mu mutum, ban tana mafarki haduwa da ku ba, kuma ba ku taimake ni dan ku samu wani abun daga gareni ba”
Har yanzu Nana hawaye take hawayen jindadi da farinciki. A nan muka ci abinci suka koshi sannan Amina ta raka mu zuwa bq din, wani bangare ne na gidan da aka kawata fulawoyi sam ba zaka dauka cewar bq bane sai idan an fada maka, dan madaidacin daki ne mai bandaki a ciki, haka aka jera dakunan har biyar kowa ne da bandaki a ciki, sai dai na mu shi aka sakawa katifa ta labule da zanen gado aka gyara ko'ina tas kamar ba bq ba.
ALIYU POV.
After Nana ta huta, Amina ta nuna musu bq ita da Ataa. Sai ya rage falon daga shi sai Momy.
“Momy Rahma bata gida har yanzu”
Kallon mamaki Momy tai masa.
“Ban gane ba?”
“Tun wacan lokacin da muka samu misunderstanding akan matsalar Ataa shikenan tai fushi ta tafi gida”
“Kana nufi duk tsawon lokacin nan bata gidanka?”
“Tana gidansu”
“Kuma iyayenta ba su kira sun bincike matsalar ta ba?”
“Da za su kira ai da sun kira ko kuma Abbah ta ya kira Daddy ya ji ko mienene matsalar”
“Hmmm Allah ya kyauta, abunda suke yi ma yarinyar suna ganin kamar so ne ko gata Wallahi suna lalata mata rayuwa ne kawai, abun kadan yarinya tace ta tafi gidansu sai kace wata mai shan nono”
“Ni dai Momy so na ke a shirya mu da ita na yi alkawarin ba zan je bikonta da kaina ba domin ni ne mai gaskiya”
“Ai da ka bi ta tawa ka barta can gidansu ta dandana zaman gidan ta ji idan da dadi kamar na gidan miji, kishi hauka ne ko cewa kai tana son Ataa laifi ne balle baka furta ba, haka ake rayuwa”
“Momy ni dai ayi hakuri a dawo min da matata dan Allah”
“Na ji sai Daddyn ka ya dawo ai ko?”
“Tau na gode”
Ya fada, ba dan komai yake son a dawo masa da Rahma ba, sai dan yasan ita kanta tana cikin damuwarsa a yanzu duk kuma abunda ta aikata saboda shi ne, domin tana son sa tana kishinsa ne, after that yana son matarsa a kusa da shi shi kanshi ya san yayi hakuri iya hakuri har na sati biyu ba tare da Rahma a kusa da shi ba, hakan na matukar damunsa domin ya san ita kadai ce a duniyar ke iya yaye masa wannan kishin da yake ji matukar ba alfasha zai aikata ba.
Husna ce ta fito manne da waya a kunne tana tambayar Momy ina Ataa.
“Wake nemanta?”
“Ya Muhseen ne ya ce a akai mata waya”
“Tana bq”
Momy ta bata amsa sai ta nufi hanyar fita daga falon, Aliyu ya bita da wani kallo kamar ita ce Ataa.
ZAKI
By Khadeeja Candy
37...
“Momy idan ba ki takawa Muhseen burki tun yanzu ba, zai iya wuce guri fa”
Momy ta masa kallon rashin fashimta.
“Wuce guri kamar ya?”
“For god sake Momy taya zai rika nunawa yarinyar wata soyayya a yanzu? Allah kadai yasan irin kalaman da ya ke furta mata”
“Shi kiranta a waya har wani nuna soyayyah ne? Idan ma haka din ne ai sonta yake sai ya fara nuna mata yana sonta? Dan wajen Fulani ka rika kyautatawa Muhseen zato, ka fi kowa sanin cewar ba mugun mutum ba ne kuma ba dan iska ba ne”
“Na sani, amman ke kanki Momy kin san Mama Fulani ba zata bari Muhseen ya auri Ataa ba saboda tana ganin darajar Ataa da ita ba daya ba, shi kansa ya sani kawai yana son ya batawa yar mutane lokaci da rayuwa ne kawai, daga lokacin da ya samu damar kaiwa ga jikinta Wallahi ba zai sake cewa yana sonta ba, domin kyauta yake gani, kyaun da idan ya samu dama zai iya zaga mata rigar mutunci shikenan kuma ta daina burge shi, idan ba a taka masa burgi yanzu ba nan gaba karatun da ake son ta yi ma kasawa za ta yi domin soyayya kawai zata sakawa gaba”
Murmushi Momy tai tana ma danta wani kallon na fahimtar wani abun da shi Aliyu be san da shi ba.
“Idan ma haka ne, ai sai ta aureshi ta cigaba da karatunta a gidansa ja ga babu wani zancen daukar hankali, kai ka kanka mai nemawa Muhseen aurene fa, balle kuma ni da na ke uwarsa, hankali dai ya kwanta kawai”Mikewa Aliyu yai tsaye domin maganar Momy sam bata masa dadi ba, dinning ya nufa ya zauna ya zubawa kansa abincin rana da be samu ci ba ya maida hankalinsa yana ci ba dan abincin yana masa dadi ha duk kuwa da kasancewar abunda yake so ne aka girka, ba kuma zai iya fadar dalilin rashin jindadin abincin ba, ci yake hankalinsa na can gurin Ataa wacce Husna ta kai mata waya, kamin ta dawo duk ya takura, ji yai ba zai iya hakura ba ya tashi ya fice daga falon gaba daya zuwa bq, a gurin aje motoci ya samu Husna tsaye tana jiran Ataa dake can gefen fulawoyi ta gama wayar ta bata wayarta.
“Ke kar Muhseen ya sake kiran wayarki ya ce ki bawa Ataa ki kai mata, na hana daga yau”
“To ba zan sake ba”
Ta amsa da sauri tana gyada masa kai. Ya nufi inda Ataa take zaune wayar a kunnenta tana murmushi hannu kawai ya mika mata alamar ta bashi wayar, sai ta tsaya kallonsa ba dan ba ta fahimce shi ba sai dan jira take sai ya furta.
“Wani wayar”
Ya furta da karfi sai ta mika masa tana kallonsa da fararen idanuwanta masu kamar madara ta turo masa baki alamar ta ji haushi, katse kiran yai sannan ya nuna ta da wayar.
“Karki sake waya da Muhseen a cikin gidan nan”
Bata ce masa komai ba bayan idon da ta sakar masa shi kuma ya juya ya koma gurin Husna ya mika mata wayarta sannan ya bude motarsa ya shiga ya bar gidan.
Duk abunda suke Momy na hangensu ta windows din kitchen murmushi tai tana ta kallon yadda Ataa ta turo baki, ta sani da ace wata ce a cikin kanensa wata ta turo masa baki yau sai ya fasa bakin nan amman da yake Ataa ce gashi ya tafi ya kyaleta, yadda Aliyu yake nuna kishinsa akan Ataa ta sani sarai son Ataa yake ba wai yana gudun shigarta wani halin ne kawai ba, sai dai shi din be san yana yi ba. Shigowar Husna a kitchen din yasa Momy barin jikin windows ta kalleta still tana murmushi.
“Momy kin ga Ya Aliyu da fusata wai kar na sake bawa Muhseen wayata su yi waya da Ataa, gashi Yanzu Ya Muhseen din kiran ma yake na ki dagawa ban san mi zan ce masa ba”
“Ina hangenku ai, idan ya sake kira kice ni ya kira a wayata zan bata su yi wayar”
“Okay tau”
Husna ta juya ta fice daga kitchen din, Momy ta dafa kitchen cabinets tana fadin.
“Lokaci da yana zuwa, zancena zai tabbata wata rana, zaka duka har kasa kana rokon yar talakawa ta so ka lokacin da ba zan iya maka komai ba, domin ba zan zabe ka na bar Muhseen ba ko kuwa ina son hakan, amman ko ba komai son yarinyar nan zai maida kai namiji na jidadin da kake kishi a yanzu, at least zata koya maka kishin matarka, zaka fahimce wayewar zamani da boko ba komai ba ce idan aka hada ta da addini”Ita kadai take magana da kanta cikin yanayin na rashin jindadi. Ba ta bar kitchen din ba sa da ta dora girki dare. Yau Daddy