Showing 114001 words to 117000 words out of 225640 words
a tare da shi amman ko da wasa bachi be ziyarci idonsa ba. Bayan sallah asuba ya dawo dakinsa ya zauna, idonsa na masa nauyi na rashin samun bachi da be yi ba jiya, a yadan bangaren kuma tunanin Ataa ya cika masa zuciya, baya jin zai iya janye ya bawa wani damar daukarta a matsayin mata bayan shi ya fi kowa cancantar wanin ma kuma Aliyu. Idonsa sun yi arba da mata masu kyau masu aji masu natsuwa da hankali ya so mata da yawa saboda kyau amman be taba ganin wacce hankalinsa ya kwanta da ita kamar Ataa ba, kyauwonta ya dauki hankalinsa sosai kusan duk mace daya hadu da ita da kuma wandanda yai so a haya har Mama Fulani tana ce masa ya cika ruwan ido, be taba jin son wata kamar Ataa ba, wani bangare na zuciyarsa yake jinta dabam, ta ina ma zai iya yafe ta a zuciyarsa idan har ya yarda yace zai yafeta hakan na nufin ya zama ragon maza kenan. Kurciyarta mu'alamarta kyauta na daga cikin abunda yasa yake son Ataa.
Da gangan yai zamansa ya ki fita ya karya bangaren Mama Fulani kamar yadda ya saba, ya kwanta a cikin dakinsa ba dan kuma yana jin bachi ba sai dai Mama Fulani ta fahimci cewar yana cikin damuwa, domin ya san matsalarsa ba karama bace a gurinra yadda take tsanar talaka ba zata amince ya auri Ataa ba, balle kuma Ataa din da ta tsana tsana ta musamman.
Maryam ce ta shigo part dinsa ta tsaya daga bakin kofar bedroom dinsa tana kiran sunansa.
“Ya Muhseen Mama ta ce ka fito mu yi breakfast”
Na tare daya juyo ya kalleta ba ya ce.
“Bana ci”
Juyawa tai ta koma ba sai ga Mama Fulani ta shigo dakin hankalinta a tashe.Saman gadon ta zauna ta kai hannun tana tashinsa domin ya bata baya ne.
“Muhseen lafiya kake?”
Juyowa yai yana kokarin tashi zaune kallonta yai idonsa sun kade sun yi ja fuskarsa ta dan kumburo saboda ciwon kan da yake ji da kuma bachin da be samu yi ba.
“Mama ina kwana?”
“Lafiya Kalau Muhseen mi yake damunka?”
“Ba komai kaina ne kawai ke ciwo”
“Ba wani ciwon kai daga ni har Abbah ku jiya da tunaninka muka kwana, ka dawo cikin dare a yanayin da kowa ya ganka ya sam akwai abunda yake faruwa, yau kuma baka fito cin abincin safe ba na aiko Maryam ta kira ka ce wai baka cin komai, yanzu kuma ka fada min babu komai?”
Kallonta yai
“Mama ko na fada miki damuwata ba daukarta za ki yi da muhimmanci ba, ba lallai ne ki min maganin matsala ta ba”
“Mi zaka nema a duniyar da ba zan maka ba Muhseen? Kai fa da na ne karka manta wannan, matukar ina da yadda zan yi to zan maka ka samu ko mi kake so a duniyar nan”
Yaja wani dogon numfashi ya sauke.
“Kamin na fada miki damuwata ina son nai miki tambaya”
“Minene?”
“Mama ba dan ina danki ba, ina son ki fada min gaskiya shin ina da wani nakasu ne da zan ce ina son wata a hana ni? Ba ni da abunda ake so a namiji ne ko kuwa tarbiya ce bata wadace ni ba?”
“Babu, babu wance zaka furtawa so ta ki karba maka Muhseen babu ta babu abunda ka rasa a cikin abunda ake so a gurin ďa namiji, fada wace yarinya ce ta tashi hankalinka haka? Wa kake so Muhseen? Zan nema maka ita ko yar idan shugaban kasa ce”
“Mama Momy ta Aliyu sun bata ni a gurin yarinyar da na ke, saboda suna min kallon mazinaci alhalin ban taba aikata alfasha ba a rayuwa Allah shine shaida ta”
Kallonsa Mama Fulani take tana son tantance abunda ke fitowa daga bakin ďanta.
“Wa kake so Muhseen?”
“Ataa Mama Ataa”
Ya bata amsa kai tsaye yana wani marairaicewa.
“Momy da Aliyu sun yi min daidai, suna nuna maka, hanya kana cewa ba haka ba, sai yaushe zaka level dinka dana yarinyar nan ba daya ne ba? Sai yaushe zaka daina yaudarar kanka? Ka rasa wacce zaka so sai yar talakawa yarinyar zuri'ar kaskantattu, Aliyu ba kamako ba ne irin ka shiyasa ya ke nuna maka ka daina son ta kana ganin kamar takura maka yake amman matsayinka da na yarinyar nan ba daya ba ne Muhseen”
“Miye banbanci na da ita Mama? Talauci? Saboda ita yar talakawa ce ko? Idan har wannan ne kawai miyasa shi Aliyu yake son ta kuma Momy ta goya masa baya?”
“Aliyu ba zai taba son wannan yarinyar ba har a bada, Aliyu ya san abunda yake ba shashasha ne kamar kai ba, ba dan wannan abun daya faru ba ina da tabbacin Aliyu ko a hanya ya hadu da ita ba zai taba bata sadaka ba ma balle har ya taimake ta, kuma ka jira ka gani yana gama taimakonta zai watsar da ita”
A fusace Mama Fulani take wannan maganar ta juya zata fice Muhseen.“A niyarsa ta watsar da ita yasa ya dauketa ya kai ta gurin Momy ko? Aka sama mata daki a cikin gidan, suka sauke ta a ciki aka bata gurin waka da tufafi, ana kula da mahaifiyarta, idan ba sonta yake ba mi zai saka yayi mata duk wannan Mama? And if ba kaunarta yake na mi zai saka Momy bata ba ni goyon baya ba?”
“Ba zata taba baka goyon baya ka auri yar matsiyata ba, yarinyar da ba a san asalinta ba, wata kila ma dangin mayu ce ta tafi da kurwarka tana can tana azzabtar da kai shiyasa kake ta haukan son ta, daman buzayen nan ba su aje komai ba sai bakar maita, Aliyu yana nuna maka abunda kake ba daidai ba ne kai kuma ka saka fahimta, kuma bakinka ya daina furta son wata yar talakawa ga Aliyu har abada Aliyu ba zai taba son Ataa ba ba kuma zai taba son wata banza kamar ta ba, ni na raini Aliyu tun yana karami har ya girma na san waye ďana tir Aliyu ya so Ataa balle har ya aureta”
Ta fada tana tofar da yawun bakinta sannan ta fice daga dakin tana kara fadin.
“Ka mutu indai akan Ataa ne”
Wani irin Muhseen ya ji kamar an saka takobi an fasa kirjinsa an fiddo zuciyarsa an raba ta gida biyu. A take kan ya kara safa masa, daman ya san Mama Fulani ba fahimtarsa zatai ba, ba kuma shige masa gaba zatai kamar yadda ya so ba, ba dan komai ba sai dan ta tsani talaka, kwantawa yai saman gadon ya rumshe ido kamar mai bachi yana jin yadda zuciyarsa ke masa mugun zafi.
A fusace Mama Fulani ta dawo part dinta har wani huci take saboda bacin rai.
“Mama Lafiya?”
Rukaiya dake falon ta tambaya.
“Wai ni Muhseen zai kalla ya fadawa yarinyar can Ataa yake so bayan na gargade shi akan kar ya sake kula ta?”
“Ataa kuma? Yana nufin saboda ita ya shiga damuwa?”
“So yake yai hakan saboda na tausaya masa ni ko mutuwa zai yi ba zan taba bari ya auri wannan yar iskar yarinyar ba, wai har wani cewa yake Aliyu ma son ta yake Momy ta goya masa baya”
“Taf Ai Wallahi Ya Aliyu ba zai taba son ta ba son ta ba, idan ma ya ji Ya Muhseen ya wannan maganar sai sun samu matsala da shi”
Cewar Rukaiya tana kai bread a bakinta.
“Shine dai dan ya ganta yana son ta sai ya dauka kowa ma son ta yake, maganar Maryam ce kyau nn ne yake dibarsa”“Ni wannan yarinyar zuwanta gidan nan ya zame mana fitina, daga ganinta shi da Kamal har da Ya Aliyu ma suka haukace”
“Kaddara ce ta saka aka kawo min ita daman, ba zan sake daukar ko wace yar aiki ba, dan nan gana sai a a kawo wacce Abbah ku zai gani yace ita yake so ma, shi kuma Aliyu bar ni da shi har wani sauke ta gidansa yake”
“Wata Momy ce ma ba shi ba, kin san halin Momy Allah yayi ta da son jan mutane a jiki ko tsoro bata ji”
“Ai zan kira shi sai na saka ya dauke ta daga cikin gidan nan, idan mai kyau Muhseen yake so ya koma tsason mu mana, akwai kyaun da ya wuce yayan fulanin asali ma, wannan da ba a san inda ta fito ba ni abun nan har mamaki yake ba ni wallahi, mtssss”
Mama Fulani ta fada hakan tana nufi dakinta har yanzu bata daina jin haushin maganar da tai da Muhseen da ta sam tun farko abunda zai fada mata kenan da bata dame kanta da son sani ba, ita dai bata da wani abun a gurin Ataa ba, ta san tana da kyau amman a gurin ko kafi kowa kyau a duniyar matukar baka da nera ko kuma kai ba dan kowa bane, biri ya fika a gurinta indai har birin nan yana da masu gida rana.
Bayan fitar Mama Fulani dakin ya sauka daga kan gadon ya nufi gaban madubinsa ya tsaya yana ta kallon kansa, a zahiri kansa yake kallo amman a badini tunanin mafita yake, har ga Allah yana son Ataa shi a yanzu ma yaji yana bukatar aure daman rashin samun wacce tai masa ne yasa shi be maida hankali gurin auren ba, amman yanzu ya yana jin son aure sosai a ransa, kuma yana matukar jin kaunar Ataa a ransa.
“This is the right time daya kamata nai fighting akan abunda na ke so, this is the right time da zan tsayawa kaina da kaina, ba zan iya barin wannan ta wuce ni ba, idan har ba zata so ni to be kamata ta so Aliyu ba, idan har zan iya hakura na kyaleta to ko ba sonta na ke ba”
Magana yake da kansa yana kallon madubin dakinsa, yana jin wayarsa na ringing amman ya ki ya duba mai kiran ma balle ya daga. Bathroom ya shiga yai wanka yana fitowa ya shirya cikin kananan kaya sannan ya dauki wayar yana duba miss calls din da Momy ta jera masa, kiranta yai da dayan layinsa da be cika kiran mutane da shi ba.
“Momy ina kwana?”
“Lafiya Kalau Muhseen, miya nai ta kiranka ka ki ka daga? Kuma ya wuce na tare da ka min sallama ba?”
“Kawai raina ne ya bace, amman ki yi hakuri dan Allah”“Ranka ya bace saboda na fada maka gaskiya Muhseen? Har ga Allah yarinyar nan yanzu ba soyayya ce a gabanta ba, bana jin ta san wani ma wai so, ta mahaifiyarta take shiyasa ban goya maka baya ba, komai ai dan a hankali ne”
“Ba abunda kike ce min ne kawai ba Momy, har da yanayin da na ga Ataa din wata kila wani abun Aliyu yace mata a kaina domin na ga tana daridari da ni ba kamar da ba”
“Idan ma wani abun ya fada mata ba damuwana ba ne, kai na ke son ka kwantar da hankalinka idan komai ya daidai kai kanka ka sani ni mai nema maka auren yarinyar nan ce tun da har ka furta kana son ta”
“Na gode Momy, amman Mama ma bata so ta min fada sosai yau saboda Ataa tana ganin kamar be dace na aureta ba, jarabawa ce kawai Momy kuma na hakura da ita”
“Haba dai, wane irin ka hakura da ita kuma? Fulani uwa ce kawai ba uba ba, ba ita zata maka aure ba, kuma zan tattauna da ita amman sai hankali ya kwanta komai ya daidai ta na maka alkawari”
“Na gode sosai Momy”
Daga haka ya sauke wayar a kunnensa ya saka aljihunsa ya dauki abubuwan bukatarsa ya fice daga dakin.
ALIYU POV.
Da yamman ya koma gida ba dade wurno road din ba saboda ya san ran matarsa yana can a bace. Kamar wanda aka koro haka yai fakin a cikin gidan ya fito da sauri ya shiga cikin falon. Kai tsaye dakin Rahma ya wuce ganin bata falo sai ya samu a dakin ma bata nan, be kawo cewa tana dakinsa ba domin ba ta cika shiga dakinsa idan baya ciki ba, sai ya sauko ya leka kitchen be same ta a nan ba, tunani daya ne ya zo masa arai wata kila ga hi fushi ta tafi gidansu.Remote ya dauka ya kashe tv falon sannan ya nufi dakinsa yana bude batulan rigarsa. To his surprise yana shiga dakin ya same ta zaune kasa kusa da bed dinsa tana hawaye. Cikin sanyin jiki ya karasa kusa da ita ya zauna yana kallon fuskarta.
“Minene Rahma?”
Dagowa tai ta kalleshi tana hadi yawun bakinta idonta yayi ja sosai alamar ta dade tana kukan kenan.
“A daina kula da ni a yanzu, da a da nd da kanka zaka dawo ka ba ni magani ko ka kira waya ka tambaya idan na sha amman yanzu baka damu ba, ka canja Aliyu ka tashi daga sanin da nai maka zuwa wani dabam, babu ruwanka da matsala a yanzu, da a da ne ba zaka iya zuwa ka kwana wani gurin da ba kusa da ni ba, idan ko har ba kusa da ni ba to a gida zaka kwana ba wani gurin ba, ka kwana a gida ka bar matarka ta sunna saboda wata matar da baka san inda ta fito ba, kana tunanin ka min adalci kenan?”
Hannunta ya kama ya rike yana matse shi cikin hannunta.
“Na sani wata zan zama babu ni, ina kawo abubuwa da yawa a rai, kamar samun lafiyata a can baya, yanzu kuma mutuwa ta, samun haihuwa wata rana da kuma dawwama a haka, amman ban taba kawowa cewa zaka so wata macen bayan Rahma ba, amman na ga ni ba ma ji nai ba, ba zan iya dawainiyar kishi a yanzu ba Aliyu idan har ka fara son wata ka sallame ni ka ji da ita ni kuma na ji da ciwo na, na sani ka yi kokarin zama da ni, amman idan ka yi hakuri wata kila ba zan dade ba zan tafi na barka sai ka auri wacce kake so, na kasa fadawa iyayena matsalar nan tun bayan wacan matsalar da muka samu na san idan har na fada musu za su nemi raba aurena da kai, saboda gudun bacin raina, amman bana son aikata hakan ya zama kamar butulci a gareka na san zaka kalli cewa iyayena ba su kyauta maka ba...”
Matsawa yai kusa da ita ya jata jikinsa ya rumgume.“Babu kowa a cikin zuciyar Aliyu sai Rahma, ke kadai na ke so Rahma ban daina son ki ba kuma ba zan daina ba har abada, ba wai na gaji da dawaniya da ke ba ne, wannan dawainiyar da ke da yarinyar nan ma saboda ke ne, duk wani hali da yarinyar nan ta shiga saboda ke ne, bayan tausayinta da tsoron ta shiga wani hali babu komai a zuciyata, ba son ta na ke ba Rahma”
Dago kanta tai ta kalleshi.
“Amman Aliyu saboda ita ka zo nan ai, kuma tana gidan Momy kana kula da ita”
“Momy ta sauke ta gidanta ne saboda ba su da wani gurin zama a yanzu, idan aka barta ita kadai zata iya shiga wata rayuwar dabam, ba saboda ita kawai na zo nan ba har saboda ke kin sani Rahma ina kauna sosai mi zai saka ki tashi hankalinki?”
“Aliyu kana da kyau da siffa mai kyau ba ko wace mace ce zata daga maka kafa ba, balle kuma ace kai na nuna mata so da kanka, ina kishin ka so wata Aliyu ina jin zuciyata kamar zata fashe ina jin duk ranar da ka auri wata mutuwa zan yi”
Ta fada tana kamkameshi kamar zata shige cikin jikinsa. Wani kalar tausayin matarsa ne ya lullube shi shi kansa ya san be kyauta mata ba, ya kwana wani gurin bayan ita tana gida tana sammanin dawowarsa. Saman kanta yai kissing yana shafa bayanta.
“I'm sorry”
“Yanzu yarinyar tana ina? Gidan Momy ita da mahaifiyarta ko? Ta tare a can so that ka rika ganinta tana jindadi ko? Na sani ai tana son ka, dole ai zata so ka”
“Yarinyar nan ba son kowa ne a gabanta ba, mahaifiyarta na asibiti tana jinya? Hankalinta yana gurin mahaifiyarta ne”
“Wace asibiti?”
Be amsa ta ba, ya cigaba da shafa bayanta, ita kuma bata sake tambayar ba, bata bar jikinsa ba sai da aka kira sallah magariba. Sannan ya daga ta daga jikinsa ya shiga bathroom yai alwala, tana ganin ya shige ta yi saurin mikewa tsaye ta nufi dakinta wardrobe ta bude tana duba kayan cikin ba dan zata saka ba sai dan ko shigowa yai ya tararda ita tana wani abun. Be shigo dakinta ba sai dai ta ji lokacin daya sauka kasa ya bude kofar falon ya fita. Gurin windows ta koma tana lekensa, hangoshi ya fita ba tare da mota ta san ba zai je nesa ba wata kila da yayi sallah zai dawo gida.
Dawowa tai ta dauki wayarta ta turawa Muneera sako sannan ta goge ta shiga bathroom din dan yin alwala.ATAA POV.
Mun wuni da Nana tana ka ce bakinta, muna ta fira kamar ba rashin lafiya take ba, a yadda na ke ganin ta samu sauki a yau kawai na gode Allah ba adadi, domin idan abun ya daure a haka Nana ta dauko hanyar samun sauki fiye da wacan aikin da aka mata a asibitin Asim. Sai dai hakan be hana na wuni da rashin jindadi kalaman Muhseen na bankwana a gareni ba. Da dare Husna da Siyama suka kawo min mana abincin dare sosai suka so na bi su zuwa gida amman na ki, ko ba komai na san Nana zata fi sakewa idan ta gan ni zata fi sakewa ni ma kuma hankalina zai fi kwanciya idan ina ganinta duk kuwa da na san ba wani maganin zan iya mata ba.
Ni da Laraba muka ci abinci dare a ranar, sannan muka kwanta a Bedsheet daya Nana kuma tana saman gado, bachinta take da ninshari har garin Allah ya waye. Asubar fari aka tashe mu ni da Labara masu wankin daki muka fito waje sai da aka gyara duka ward din sannan muka dawo. Na yi zaton Aliyu ne zai kawo mana abun kari sai naga Husna da Siyama kamar dai jiya, bayan sun yi ma Nana ya jiki suka dauki