Showing 135001 words to 138000 words out of 225640 words
fice daga bq din a fusace ta bar Muhseen tsaye dafe da kuncin idonaa sun kade sun yo ja sosai. Sai da ya kalleni sannan ya kada kai ya fice aka bar ni daga ni sai Nana muna ta kuka babu mai rarashin wani.
ZAKI
By Khadeeja Candy
40....
Kuka Nana tai sosai har sai da na soma jin tsoro domin tsarkewa tana tari har na tsoron kar ta janyowa kanta wani ciwon, a take na yanke kukana na share hawayena na rumgumeta ina bata hakuri, daker na rikata na muka koma daki ta kwanta saman katifa na lulluba mata zane na fito na baro mata dakin, a harabar gidan na fito na nufi gurin da ake ajeye moto na zauna a wani gurin da wani be zai iya ganina ba. Abunda Muhseen yai min ya fi abunda Aliyu ya aikata yi min zafi a yanzu, domin Aliyu akan rashin sani ya aikata kuma ya ba ni kulawar da ta dace ciki har da taimaka min na samu ilmi, na san yanayin duka wannan ne saboda ya goge laifinsa a gurina da gurin Nana, sai dai duk da hakan hakam na fi jin sakewa da shakuwa da Muhseen saboda shi be aikata min komai ba, be kuma taba musguna min ba, sai dai Abunda yai min a yau yasa na ji na fi tsanarsa fiye da Aliyun ma. Ban san wani plan na Momy ba, wata kila ta shirya Aliyu ya aure ni ko da baya sonta saboda ya kara goge laifinsa ko kuma saboda tana so a matsayin surukarta, amman be dace ta yanke wannan hukunci ba tare da jin ra'ayina ba, wata kila tana son ta mana milkin masallaka ne saboda muna gidanta, ko kuma saboda wani dalili na ta na dabam domin na tabbatar ba ni da kima da darajar da Aliyu da kansa zai bukaci aurena ko ya furta cewar yana so na, wata kila tana son ta aura masa ni ne saboda ya rage kyamar talaka domin na lura halinta da na shi ba daya ba, idan ma har da gaske ne abunda Muhseen ya fada wata kila kuma wata ake nufi ba ni ba, a a ba ma ni ba ce sam ba zai ce ni ko da ma cilasta a kai na san ba zai amince ba. Haka nai ta sake sake na na na kulla wannan na kwance wacan har aka kira azahar, ni dai sai na ji gaba daya gidan ya fice min rai, domin zama a ciki ne ya kawo yau har Nana ta ji wannan maganar mai daga hankali na tabbatar da ace bama cikin gidan ko da Muhseen zai zo yayi maganar sai dai ya saka a masa sallama da ni idan na fito ya fada min son ransa amman ba a gaban Nana ba.Ko da na koma dakin na samu ta yi alwala tana kokari saka hijabinta tai sallah, bandakin na nufa na shiga na yi alwala na fito na shimfida dankwalina na soma gabatar da tawa sallah, bayan ta sallame ni ma na sallame sai ga Amina ta shigo da sallama dauke da kular abinci da plates da Siyama na bayanta tana sanye da uniform kamar dazun da alama bata dade da dawowa daga makaranta ba, fuskar Nana kawai take kallon wacce ta kumbura sosai.
“Sannu Nana”
Cewar Amina wani abun mamaki da Nana ta dago ta kalleta sai tai mata murmushi ta kada mata kai, Siyama ma ta mata sannu sannan suka fice. Matsawa nai kusa da ita na soma mata magana a hankali.
“Na boye miki ne saboda kar hankalinki ya tashi ki saka kanki a damuwa, ba da sanin Aliyu akai wannan abun ba, likitan da naje neman taimako a gurinsa doc Asim shine yai wannan aikin ba da sani Aliyu ba.....”
A natse na zayyana mata komai tun daga kan asibitin da kullen ni da Doc Asim ya saka aka yi da kuma neman mu da Aliyu yai ta yi har ma da konewar da kodarta tai da kuma irin kalubalen da na fuskanta a zamana Abuja. Hawaye shar a fuskar Nana tana kallona da murmushi a fuskarta.
“Ba kowa ce uwa Allah ya ke azurtawa da ya kamar ki mai damuwa da matsalar uwarta da nema mata mafita ba, kin jefa kanki cikin matsala saboda ni, kina bukatar abubuwa da yawa amman kika watsar da su kika maida hankalinki a gurina, ban yi zaton samun ya mace wacce zata kula ni kamar haka ba”
Ta fada tana kallona, wani dadi da farinciki na ji ya lullube ni ashe haka ko wane da na kwarai yake ji idan mahaifiyarsa ta yabe shi. Sai na kwantar da kaina jikinta ina jin wani irin shauki da rahama na uwa yana ratsani.Hannunta ta dora saman kaina tana shafani. Har na bude ba ki na yi magana sai ga Momy ta shigo cike da tsoro a fuskarka muryarta har gargada take a lokacin da take mana sallama. Ni ma amsa yayinda Nana kuma na kasa daga kai ta kalli Momy, a gaban Nana Momy ta zauna kamin ta fara cewa komai hawaye sukai mata sallama.
“Ban san yadda za ki dauki abun ba, ban san da wace fuska zaki kalli abun ba, ba dan ni na haifi Aliyu ba, wallahi idan za ki tambayi kowa a garin nan wanda ya san halin Aliyu ya san rayuwarsa, zai fada miki cewar Aliyu ba zai aikata hakan ba, yes na sani Aliyu yana da wulakanci amman Wallahi ba zai taba yarda ya zalince ka ba, ba da saninsa a kai komai ba.....”
Daki daki Momy ta jerawa Nana komai ciki har da dalilin hana Muhseen aurena da tai wanda shine dalilin janyo duk abunda yake faruwa yanzu da kuma dalilin aurena da take son ya yi , ashe wai gori Rahma tai mata kuma ta kirani da talaka ta ce ba za a hada ta kishi da yar talakawa ba, a zatonta Aliyu so na yake, a take na ji Momy ta kara burgeni, domin a yadda suke da kudi da arziki da suna a garin sokoto, ba ko. Wace uwa ce zata yarda danta ya aureni ba yar bara a titi wacce ba a san kowa na ta ba, na sani ta cilasta Aliyu yin hakan ne saboda kawai karancinta, tausayinta na cika min zuciya wanda na ke zaton shi ne a zuciyar Nana har ta daga kai ta kalli Momy tana hawaye kamar yadda Momy ma take nata hawayen.
“Kina da damar yanke ko wane irin hukunci, ciki har da maka Aliyu kotu idan har zuciyarki ta natsu da cewar shi ne ya aikata miki komai, kuma na miki alkawari nai ko alfarmar kowa ba za mu nema ba dan a bamu gaskiya a baki rashinta, kina da damar hana Ataa auren Aliyu ki aura mata Muhseen ko wani dabam wanda zuciyarta ta natsu da shi, amman ina rokinki dan girman Allah kar ki ce za ki bar garin nan zuwa wani gari ko wani gidan dabam, ki zauna da mu dan girman Allah”
Momy ta fada tana hade hannayenta guri daya tana rokon Nana.Shiru da Nana tai ne yasa Momy ta juyo gurina tana kallona.
“Ban yi niyar aikata komai a gurinki ba sai alheri, dukan kudirina na kiji dadin rayuwar ki a gaba ne, ina da yakinin Aliyu zai rike ki amana, kuma zai zauna da ke ya rike ki da kima saboda yana son ki, kuma ke din kamar kyauta ce daga gurina, Allah shine shaidata”
“Momy kin rike ne kamar yar da kika haifa ko da rana daya ba ki taba nuna min kyama ko banbanci da yayanki ba, lokacin da kanwar Rahma ta dake ni ki yinta ma Aliyu fada kamar ki dake shi kina fadin ba zaki dauka ba, duka wannan abun da kika min kina kara amsa sunanki an uwa ne a gurina, Wallahi na yarda da ke Momy na rike uwa ta gari.... ”
Murmushi na gani a fuskarta sai ta kai hannunta ta dafa ni.
“Na gode da kika fahimta Allah ya miki albarka”
Tana fadar hakan ta tashi ta fice daga dakin. Nana ta bi Momy da kallo tana min magana cikin yaren buzanci.
“Aliyu ya aikata kwatankwacin abunda na aikata kuma nake ganin kamar ban yi aikata laifi ba, sai ga shi alhaki yana ta bibiyana na bijerawa iyeye, cikin har da samun rayuwara a bara, da rasa kudin magani, babban a ciki shine na cire min koda ba tare da sani na ba, ko wane shafi na rayuwa darasi ne, ko wani littafin kaddara ilmi ne, da ban gudu na bar gatana ba, na bijerawa iyayena ba, da wani be isa ya nuna min yatsa ba, balle har ya taba jikina abunda na aikata ne shekara ashirin baya yake ta bibiyata har yau”
“Nana me kika aikata?”
Sai tai saurin share hawayenta ta girgiza min kai.
“Ban aikata komai ba”
Amsar da ta ba ni kenan ni kuma gudun an dame ta yasa ban sake cewa komai ba.Tashi nai na fito daga dakin na koma can gefen bq din na zauna ina ta tunanin maganar Nana lalai akwai abunda take boyewa kuma abunda ta aikata mai girma ne shiyasa bata son fada bata ma tana min zancen family ta ba, kuma bata taba cewa zata tafi ganin su ba ko kuma ma ta koma gida gaba daya duk kuwa da irin halin rayuwar da muke ciki.
A cikin wannan tunanin ne motar Aliyu ta kunna kai cikin gidan, kawar da fuskata nai dan kar ya ga hawayena na noce kana kasa sai dai hakan be hana daya fito daga motar ya doso inda na ke ba.
ALIYU POV.
“Mi akai miki?”
Ya tambaya fuskarsa ba yabo ba fallasa, sai ta kara yin kasa da kanta kamar tana kokarin boye kukanta. Rainawa yai daidai ita yana leken fuskarta.
“Waya taba ki?”
Banza ta masa ta kawar da fuskarta sai ya mike tsaye ya nufi cikin gidan ya barta da kanshin turarensa. Tun daga shigowarsa falon ya ga tv a kashe babu kowa a ciki ya san ba lafiya ba, domin sun saba kunna tv ko ba sa kallo su barshi a haka, kitchen ya fara lekawa domin ya fi tararda Momy a can ganin bata nan yasa ya wuce dakinta sai ya same ta zaune saman gadonta da magani a hannunta tana sha, yana ganin yanayinta gabansa ya fadi, da sauri ya karasa kusa da ita ya zauna bakin gadon.
“Momy lafiya?”
Momy bata iya ce masa komai ba sai Husna da ke tsaye ce ta labarta masa abunda ya faru. Cikin wani irin bacin rai Aliyu ya mike tsaye da zimmar fita sai Momy ta kirashi.
“Ina za ka je?”
“Momy ba a haifi dan da zai fada miki magana na kyale shi ba, idan ba shi da hankali to yau zan amsa shi”
“Ban yarda ka ce masa komai ba, ban yarda wata magana marar dadi ta fitowa daga bakinka zuwa kunnen Muhseen, ban yarda ba”
Dawowa yai ta zauna babu wani abu a duniyar da ya wuce bin umarni uwa ko da ko ba shi da dadi.Zaman sa da minti biyu zuwa uku Daddy ya shigo shi ma hankalinsa a tashe, domin ko kadan baya son tashin hankalin matarsa kamar yadda ita ma take gudun na shi.
“Kin yi kuskuren aikata abunda kika aikata Hajiya, ba lallai ne Muhseen ya fahimce ki ba, kuma tabbas zai dauka kin yi hakan ne saboda ki hana shi ita ki aurawa Aliyu ita”
Dagowa Momy tai ta kalli Daddy.
“Ban san na yi kuskure ba sai a yanzu, kuma ta hanya daya ce na ke ganin zam iya gyarawa”
Aliyu ya yi saurin kallonta.
“Wace hanya?.... Momy karki ce dai za ki aurawa Muhseen ita? ”
“Ta hanyar bata dama ta zabi wanda ta ke so tsakanin kai da Muhseen ko kuma wani ma dabam, idan kuma bata son auren zai tai ta karatu har lokacim da zata ji karatun ya gundireta”
“Momy karki bata damar za bi Wallahi Ataa bata san wanda take so ba”
“Aliyu.... ”
Daddy ya kira sunansa yana kallona ya kada masa kai.
“Tashi ka fita”
Mikewa Aliyu yai ya fice yana jin cewar abunda Momy take son ta aikata be masa dadi ba.
“Ta wannan hanyar ce kawai na ke jin cewar zan yi ma Ataa da mahaifiyarta adalci kuma na wanke kaina a gurin Muhseen, so babu abunda ba ya sakawa, idonsa ne ya rufe har ya iya fada min ba dadi kuma ya aikata abunda ya aikata, amman ba halinsa ba ne”
“Amman ko ma minene ai be dace yai miki abunda yai ba, tun da ba karamin yaro ba ne shi”
Husna ta fada, sai Momy ta kalli Daddy da idonta dake cike da kwallah ta ce.
“Ina son ka min izini, na tafi Abuja gobe kamar yadda muka tsara, idan ma babu jirgi zan iya zaman mota”
“Zuwan ki Abuja yanzu ba shi da fa'ida, zai kara lalata abun ne kawai”
“Murna kawai zan tafi saboda na fadawa Fulani zan zo gobe nai mata murna”
Daddy be ce komai ba ya juya ya fice daga dakin.Daddy na fita Aliyu ya dawo dakin ya xauna a inda ya zauna dazun.
“Momy kar ki yi haka dan Allah, Wallahi Ataa ba zata taba ce miki tana so na ba”
“Ba kai na ke son ta ce tana so ba, wanda duk zuciyarta ta natsu da shi na ke son tace tana so, idan kana da dama gobe zamu je Abuja tare da kai, Husna ki kaiwa Daddynku abinci”
Tana fadar hakan ta kwantan saman gadon saboda zazzabin da take jin yana taso mata.
ATAA POV.
Bayan ya wuce na tashi na shiga ciki na cire kayan jikina na saka uniform din islamiyar da hijab din na fadawa Nana cewar zan tafi makaranta sannan na fito sanye da takalmina na nufi gate na fice abuna, domin an san hanyar da ya bi da ni lokacin da zai kai ni dan haka zan iya kai kaina a kafa ma domin na saba tafiyar kafa.
Ban ankara ba na ga an faka mota gabana tare da bude min ganbun motar.
“Shigo”
Yau ya furta ba kamar ranar da ya kasa ce min na shiga ba, ba musu na shiga na rufe motar sai na dan kalleshi kadan na dauke kai, yanayinsa na canja fuskarsa da bawa mutane tsoro da yi musu barazana ta koma kalar tausayi da damuwa. Sai da ya fara tuka motar sannan kalleni a raunane ya ce.
“Momy zata ba ki zabin wanda kike so”
A tsakanin tambaya da labari sai na rasa wanne yake ba ni daga ciki, tambaya yake za ta ba ni zabin? Ko kuwa fada min yake.
“Ban sani ba wata kila yau ko gobe ko jibi ko anjima”
Sai kuma yai shiru ya cigaba da tukinsa, ni kuwa ina ta karantar abunda yake kokarin sanar min.
“Ba za ki za be ni ba saboda ba ki so na, ba za ki za bi Muhseen saboda ya bata miki rai, Kamal za ki zaba saboda kina jin cewar shine kawai mutumen da be taba yi miki komai ba”
Shiru ya kara yi kamar dai dazun ba sake cewa komai ba har muka isa islamiyar, waya yai ya sanarwa da malamin zuwana sannan ya fita daga motar ya zagayo gefena ya bude min na fito, sai ya tsaya yana kallona har na shige cikin makarantar.Kamin na karasa cikin makarantar malamin jiya nan ya fito ya tarbe ni, wani ajin ya kai wanda ni kadai ce a ciki sai kuma shi da ya dawo dauke da tarin littafai ya miko min. Tambaya ya soma min inda na tsaya a karatuna abunda na ke iyawa da wanda bana iyawa, sai ya fada min cewar zai mayarda ni alifun ba'un ta yadda zai zama ina iya hada harafi da kai na karanta abu, har yana fada min wai sai na yi hakuri domin zan ga a cikin sa'anina ni kadai ce na ke wannan karatun, sam hakan be dame ni ba, domin neman ilmi ne, ilmin ma wanda zai amfane ni duniya da lahira, ban taba jin cewar na girmi karatu ko kuma karatu ya girme ni ba, a kullum fata na bayan samun lafiyar Nana na samu na yai ilmi ko da kadan ne. Bayan ya gama mim gwaje gwajen da zai min ya mayarda da ni wani dakin mai cike da dalibai wasu sa'ana wasu na girme su wansu kuma sun girme me sai dai dukansu suna da karatu gwanin sha'awa abun ke nuna cewar makaranta ba a wasa da karatu.
Karfe shi da daidai aka tashe bayan an saka wata Rukaiyah ta yi mana addu'ar rufewa, haka muka jero muka fitowa daga makarantar wasu na tafe suna fira da abokan tafiyarsu wasu kuma sun koma can wani bangare suna siyen wasu abubuwan na kwalan da makulashe, sosai da sosai na jidadin zuwana makarantar sai ya tuna min da lokacin da na ke karama ina zuwa wacan ilamiyar ta Clapperto ta Khalifa. A inda na bar motar Aliyu fake da zan shiga a gurin na same ta sai dai yana cikin motar zaune kuma da alama ni yake jira. Karasa nai ina kallonsa ta cikin gilashin motar wanda ya kasance fari ba kamar na dayar motarsa ba wanda ya kasance baki, ya kwantar da kujerar motar ya kwanta jikinta ya rumgume hannayensa a kirji ya lumshe ido.Ina kwankwasa kofar motar sai yai saurin bude idonsa ya kalleni tare da miko hannunsa ya bude min motar na shigo, hannuna na kai na rufo motar sannan na maida hankalina gurin littafan da ke hannuna. Shi kuma yai ma motar key mu ka kama hanyar gida.
“Ataa.. Idan Momy ta ce ki fadi wanda kike so ki ce ni kinji....?”
Yayi maganar ba tare da ya kalleni ba maganar ma sai rabewa take kamar an tausar numfashinsa, ban yi mamaki abunda ya fito daga bakinsa ba domin na san Aliyu yana son Momy zai iya komai dan ya faranta mata ya saka ta farinki, Saboda ya cikawa Momy burinta, Saboda ya faranta mata rai ko da baya so na zai iya rokon nai haka domin ya san a yanzu ba zai iya cilasta ni na yi dole ba. Kamar ya san abunda na ke sakawa a rai